da malam wanan ai sai jahilai keyin shi yanzu wanan wa,azin da akewa mata ko yaushe ai ya ishi mutum tsoron Allah.
Gyara kanki zakiyi sosai wallahi yadda zaki zarce kowa a shimfida indai shimfida na daidai akomai kanzo da sauki ga mace.
In kina gyara wallahi sai ta raina kanta shima bai kara ganin ta da wani kimacan balle makircinta ya hauki garshi.
Nace Zarah duk wani abinda zanyi Attu fa tai min shi da zan zo may kuma ta rage yanzu nayi.
Tace tunda an fada maki guri daya ake tsayi ga harkan ba zauna nan har su kwace maki miji kina kallo wallahi.
Wani abu zatayi bayan wanan duk burgan aikin dai yanzu shine gyara ga mace.
Ko ki jayon mijin ki akanki ko kinaji kina gani ki zama yar rakiyan mata duniya don haka ki tashi tsaye kinji na fada maki.
Nai dai gyara tare da sauke numfashi nace ni ma duk kaina ya rude na rasa may zanyi yanzu wallahi.
Wani abu kuwa zakiyi banda ki tsuma kanki ta hanyar sha da tsuguno, wanka da shafawa da kuma matsawa wanda ya dace ba mai cutarwa ba.
Nace zarah duk ni kadai tace dake dawa dake da wanda kuke shan dadin tare kike son yi ko may ?
Don Allah dai Zarah daina wanan zancen wasan muyi maganar gaskiya please.
Nace ni ki fada min abinda zanyi kin tsaya kina min shakuyanci kuma.
Tace ni dai gaskiya mama na ce ta hadani da matar da nake karba a gurin ta idan zaki iya sai mu samu lokaci daga nan mutafi ai maki kafin wanan bakin baturen mijin naki ya dawo mai kaidan tsiya.
Na sauke ajiyan zuciya nace sai ki fadi ranan da zamu tafi don na fito da shiri na ko tace ki bari banda gobe sai mu tafi ai ba nisa sosai da nan din.
Mun rabu ina ta tunanen zancen zarah da mukayi nace wai yanzu wanan abin ya zama ma mata al,ada ke nan su ma mazan zamanin sai da hakan ?
Ita ko Hindatu takira mai gidan ya kai sau barkatai bai daga waya, sai zuwa dare ya dauki wayan ya fara mata masifa yace haba hindatu kin kira dayakin kira biyu ai sai ki gane ina da uzuri ne hakan.
Ni ina zangane tunda bana tare dakai ni dama ba wani abu bane illa tambaya nake son yi da sanin ka yarinyar nan Rahama take fita ma da mota ?
Yace yanzu saboda wanan kawai kika daga min hankali da kira ina cikin meeting.
Ai ba kawai bane sai gaskiya ita waye da zata dauki motar ka tafita dashi don ace mata wa a gari ?
Yace mama tana mana tunda motanane ba na wani ba tashiga koda wani magana ne akan haka ?
Tace magana kai Allah dawo dakai lafiya don haka ba zai taba yuyuwa ba yace ya riga ya yuyu tunda kinyi magana da dai baki min wanan fitsara ba kin bini da lalama dana fada maki dalilin yin hakan danayi.
Amma yanzu ina jiran inga abinda zaki yi din tunda wani ya saya min motar da zai hana ni yin son raina daga haka ya kashe wayan ya shiga mota sai masaukin su.

********* ********* *********
Kamar yadda muka alkawari muna fitowa bamu tsaya shiga pratical ba ranan da motana muka fita don ita bata shigo ba da mota.
Wani gida mukaje a uguwar sharifai gidan baida girma sosai mukai sallama muka shiga daga ciki.
Matane agidan birjit da masu nikaf da masu gyale da masu hijjabi suma sun zo don gyaran harka kawai kan mazajen su.
Muka samu wuri muka zauna watace ke hira mijin ta da kishiryar ta tana fadin wai saida tai shekara bakwai mijin ta ya kaurace mata tunda yai amarya.
Amma yanzu gashi tunda ta fara amfani da kayan hajiya mai gyaran harka mijinta sai rawan kafa yake akanta.
Jikina yai sanyi nace a raina Allah dai yasa ba shirka a wanan gurin wanan dadin danaji matar nan nayi haka.
Mun kusa awa daya muka samu shiga wurin ta wani falo ne babu komai sai tarin kaya nau,i nau,i irin na amfanin mata.
Wata farar mace ce mara jiki fara tas da ita tana ganin Zarah tace manyan gari ashe ana ganin ku ke nan ?
Zarah kwana biyu suka gaisa nima na gaida matar tace ikon Allah ana kama a duniya wallahi.
Wanan yarinyar kamar su daya sak da autar mu komai nasu iri daya wallahi sai mukai dariya tace ikon Allah har dariyan ma naku daya wallahi ko.
Zarah tace haka ake kama wani lokaci matar tace dani ke yar nan garince halan ?
Nace eh tace niko kinga asalin mu daga damagaram muke aure ya kawo ni sokoto daga can mijina ya dawo nan har Allah yai mashi rasuwa dayake ina waban harkan sai naji dadi ban koma gida ba na zauna nan nida yarana.
Allah ya jikan musulmi yai masu rahama tace amin nagode.
Zarah tace hajiyan harka wanan kawatace ta kut da kut tare muke karatu da ita sai dai tana da kishiyoyi itace ta hudu a gurin mijin su.
To kin san dai komai anan zuwa mukayi don Allah hajiya a haska muna ita don ita haka take zaune cikin su zikau.
Tace asha kaunata wake zama yanzu haka kawai ai mazan yanzu baki samun daukaka a gare su sai da wanan harkan.
Duk wacce tace zata zauna wallahi ba zugi ba zata koga ba daidai ga maigida.
Balle ke dake da kishiyoyi har uku ina zama ya ganki ai ance in kana da kyau kara da wanka.
Nan dai ta shiga yi min wa,azi da nasiha kan zama da miji har ma da kishiya kan kada na yarda nai aikin da baidace ba ga rayuwa na.
Naji dadin nasihanta don na hango akwai addini sosai tare da ita don sai wanda yasan Allah zai maka wanan nasihan haka.
Tace insha Allahu zan taimaka maki da abinda ya dace wanda ba zaki nakasa ba a gurin mijin ki ki daina tsoron cika bakin kishiya tanayi ne kawai don ta razana ki.
Tace dani ke, ke bashi ruwa yasha ko shi ke sha da kan shi ma,ana ya dauko nace ni ke dauko mai tace ya kwana gidan sauki ai.
Ruwan nan sai ki bude ki juye a cup sai ki karanta bissimillahi kafa dari uku da goma sha uku ciki ki dinga bashi ya sha ko kuma dari bakwai da tamanin da daya kina bashi yana sha har tsawon sau bakwai.
Zaki iya kuma tofa Allahu ya wadudu a ruwa kafa arba,in daya har sau uku ki bashi yasha a ruwan da kika tofe din.
Zaki samu kwalli wanan fari mai dutse ki nika shi ya zama gari sai ki tofa mai (wara fa, anahu man kanan aliyan ) kafa arbain da daya, dinga shafawa a ido duk lokacin da namijin ki ya kalle ki zai ga kin kara mai kyau da sha,awa gare ki.
Zaki samu ruwa na kanzon tuwo sai ki barshi ya kwana a wuri mai kyau amma a fili sai da safe ki dauko shi ki zauna zama irin na bauta ki karanta la,illah ha, illah kafa uku sai li, ilafi quraish kafa uku a cikin sai rabbi ziddini ki fadi sunan mijin ki sau uku ki shanye.
Yana kawo daukaka da farin jini a gurin namiji sosai ba kadan ba a gwada yana da alfanu mata.
Tace wanan ke nan sai kuma wanda yanzu zan baki na amfanin ki kuma.
Kin san kina da kama da kaunata sai naji kawai ina son ki har cikin raina ganin ki nake kamar autar mu wallahi.
Ta jawo wani roba tafito da wani sabulu tace kinga wanan sabulun yana da hadi a cikin shi sai ki samu sabulun wankan ki ki hada dashi ki kwaba kina wanka dashi ko yaushe akwai lalle da majigi da habba da hulba duk a cikin hadin sai abin mallaka da akai amfani dashi ciki.
Ta kara miko min wani turare mai kamshi tace karbi wanan turaren na motsa sha, awa ne shi kafin ki je gun maigida ki tabbatar kin motsutsuke jikin shi dashi sai ki kawo wanda kike amfani dashi ki dora sama don ya kawar da kamshin wanan din kada a gane mudai mukatan mu ko kadan ne ya shaka kawai.
Wanan kuma hayaki ne zaki dinga tsugono an hada shi ne ta igiyar akalar rakumi a cikin sa.
Na dago kai na kalle ta tace kaunata ke nan idan ke baki jashi ba kina kallo sai wata ta jaye maki shi ai.
Wanan abin ba tsafi a ciki bokan ki ne a dakin ki don sai dashi aure yanzu muddin kina son tsufa a dakin ki to sai kin hada da hakan ko.
Kinji ance ki nemi lahiran ki tun aduniya da kuma so da kauna a gurin mijin ki to sune nan babu boka babu malam sai ayoyin da akai fani dasu a gurin hadin.
Tabani gumba tsumi da sauran abubuwa har da wanda zanyi kumshi koda a yatsan hannuwa nane .
Tace naje na gwada su kawai sai wani lokaci idan mun hadu zata bani wani tare da jadda mi cewa ayau fa mace bata kamaluwa idan babu kwaskwarima gare ta don mazan sai da haka ake zaman lafiya.
Keda kada kiyi wanda zaki kaucewa imanin ki ki cutar da miji da kishi amma indon wanda zaki gyara kanki ne malaimai sunce kiyi .
A sanye na sauke ajiyan zuciya na dago kai tare da duban ta nace hajiya nawa zan bada ?
Tace cikin murmushi gaskiya kinci albarkacin yar uwata don gashi na baki harda abinda ban taba ba Zarah irin su ba.
Zarah tace ai mamaki kawai nakeyi wallahi ina jira kigama ne naciki tara.
Tace wanan autar muce ai kin san dole kuma na gyara autar mama ko kada kishiya ta koro muna ita.
Gaskiya ne hajiya inji Zarah .
Na sake cewa na gode hajiya nawa zan bada ?
Tace a gaskiya ita zarah ta san kayana takuma san amfanin su da wata ce Allah sai dubu hamsim zuwa sama zaki bada.
Amma yanzu kibani yadda zaki iya ai yanzu muka fara dake sai nan gaba zan baki har wanda zakiyi nafila dashi.
Nace to haji in na bada ashirin ban so kaina ba da yawa tace babu damuwa kawo goma kawai kaunata ko zan samu ladan zumuci a kan ki don autar mu na baki hakan.
Nai mata godiya mukai mata sallah kan duk yadda naji zamu dawo insha Allahu.
Bayan mun bar gidan ne muka dawo gidan zarah ita tabani abubuwan hadi wasu ma ta hada min na wuce dasu gida nai mata godiya.
Ban shiga dakin anty ba sai da nakai kayan part dina na boye nai wanka sannnan na dawo gaida anty.
Tun daren ranan na fara amfani da wasu daga cikin kayan da ta bani don su girdu a jikina kafin mai gidan ya dawo.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA, , , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YABI HAKKIN HA,INCI GAREKI, , ,
48

Sannu a hankali nake aiwatar da komai da hajiya mai gyaran harka ta bani.
Sam ban bari kowa a gidan ya fahinci abinda nake yi ba sai na fakaici idon mutane nake yin yadda ta fada min so nake na fahinci gaskiyan al,amarin.
Haka yasa na dage gurin gwada amfanin su ko hakan zai yi wani fa,ida.
Ita ko Hindatu nacan ba zama ba tsayi ta fada nan ta fada can bata gurin bokaye gurin malamai da masu kayan mata.
Burin ta daya shine ta samu kan maigidan ya kasance bai ganin ko wace mace da kima da daraja sai ita.
Gashi duk inda ta tafi sunan Rahama ne dai a bakinta ita dai ai mata aikin da zai dakushe haske Rahama ga mijin su a baki daya takoma ita da babu ita agidan duk daya.
Kudin ka yasha kashi sosai ita kuma tasha kayan kulli da wanka har da shafawa.
Duk ta yo kayan su ira ta tafi hanne yar aikin ta ta tafi mata uwarta taje mata yan uwanta suje mata haka ma aminan ta suje mata duj kan dai abu daya takeyi.
Sai da ta tabbatar ta hadu akan komai yadda take bukata ta sawa kanta sauki da hakkuri hakana.
Jira kawai take maigida ya dawo ta fara aiwatar da nufinta akan shi kamar yadda nima nake jiran ya dawo na gwada kayan mai kayan harka akan shi.
Bani wasa da tashi cikin dare nayi nafila na roki Allah ya kare ni da duk wani sheri da kulli akan duk wacce ta bini da mugun nufi Allah ya mayar mata da aniyan ta akanta.
Sai na gamsu da addua na nakan dan koma na kwanta kafin ai sallah asuba na tashi kuma na kara tilawa.
A bangaren hindatu nasha binne binne da yayafin rubutu a duk inda zan taka.
Allah ya rufa min asiri bana fita daga part dina ko wajen gida sai nayi addua a bakina na neman tsari daga gurin ubangiji na Allah.
Na kuma gode don Allah yai min dauki akan hindu da sherin ta don kar nake kallon ta.
Inda na san akwai magana kaina cikin dare ina part din anty a zaune hira muke a kan Abban ta muna dariya Gajiye bata riga ta rufe kofan baya ba don tana son fita ta kwaso wasu kaya da ta bari a baya .
Haka yaba hanne yar aikin hindatu dama samun shigowa don ta yayafa abinda wani malami ya basu su zuba min a kofa na.
Gajiye na fita ta hango kamar innuwar mutum a gurin yana zuba wani abu da karfi tace waye waye a gurin nan ne ?
Da sauri Hanne ta juya tabar gurin jikin ta na ciri taa gudu zuwa part din su Gajiye tabi bayan ta amma ta saurin shigewa babu kowa a gurin.
Jin ihun ta yasa muka mike muka nufo gurin tace da karfi kada kuzo nan hajiya akwai matsala wallahi.
Cak mukaja muka tsaya tace bari ta haska wuta a gani ta kunna wutan ta Hanne ta kashe mai haska dogon coridor din.
Wani ruwan rubutu ne ko tsimay oho, da wasu bakaken abu a cikin sa.
Gabana ya fadi ras anty tace na shiga uku gajiye waye ya zuba wanan abin anan ta fada muna abinda ya faru.
Anty tace yanzu wake da aikin nan haka Allah ya mayar wa mai shi da aniyar shi don Allah yafi shi.
Gajiye tace ina zuwa ta wuce zuwa baya sai gata da wani abu a wani tsohon roba ta zuba a gurin.
May ye wanan din kike zubawa Gajiye tace hajiya fitsari ne kin san yana kashe dafi da asiri shi.
Bayan ta zuba tasa abin shara ta share tafita dashi takawo moper ta goge gurin tsab gabana sai faduwa yake min.
Anty tace mu koma daga ciki ranan a dakin anty na kwana duk jikin mu yai sanyi sosai kan wanan abin.
Gajiye ke cewa Hanne nake zargi wallahi don babu tantama itace nagani ba wani ba.
Yanzu ai zato muke idan baka iya kama barawo ba sai shi ya kama ka.
Gajiye tace ranan fa da safe koda na fito naga kofan falon mu kamar an tona muna shi sai aka kawo ruwa aka zuba ko ina mutum bai gane komai.
Anty tace shine baki fadi ba Gajiye tace hajiya may fadin zai yi amfani na dai zuba bowli a gurin ma ranan don ban yarda da hakan ba.
To Allah ya kyauta mukace amin baki dayan mu haka yasa na kara kula da kaina sosai nasan da akwai sherin da ake kokarin kulla min.
Haka yasa na kira inna ta na fada mata halin da nake ciki itama hankalinta ya tashi.
Tace zata fadawa maigari halin da ake ciki takuma je ta fadawa Attu ta koma gurin malam Musa ta fada mai.
Yake cewa ta fada min na kwantar da hankalina ba dai ina yin adduoin da ya bani ba da zanzo kuma abinda yai min insha Allahu wani asiri bazaiyi tasiri ba akaina Allah zai kare ni insha Allahu.
Sai da nai kwana uku ban shiga part dina ba ina tsoro itama anty tsoron hakan take ji.
Sai dai takan min sheri muyi ta dariya ga kwana na hudu nagama addua na na fara shiga naji kuma hankalina yai matukar kwantawa sosai.
Kwana biyae sai ga Fatima yar gurin maigari an turo ta guri na da abubuwa daga shi maigari din ya turo min.
Na dawo school na samay ta tazo da murna na tare ta mun dan zauna part din anty muka kwasa muka koma guri na.
Sai da dare muna shirin kwanciya bayan mun rufe part din ne ta fitar da sakon tai min bayanin su dalla dalla.
Banyi sanyi a kafa ba na fara amfani dasu kamae yarda yace min duk na tsari ne kayan.
Naji dadin zuwa Fatima a gurina muna zama muyi hira bata da son jiki kafin na fito
Showing 207001 words to 210000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70 Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153