da tsohon nan Rahama don bana wasa da lamarin shi.
Nai murmushi nace anty nima ai Abba nane bana wasa da zancen shi sai dai bavan nan namu ya faye cine anty.
Tace kajiki da wani zancen banza akwai wanda bai ci ne a duniya Rahama kina sin muyi fada dake ne ko kibar min tsoho yaci son ranshi kamar kowa.
Nace ban ma samu zuwa gaida Abba din ba da nazo tai murmushi tace a to kila shi ma aban yabi sahun mu ne yanzu ana ja da baya dashi.
Naji kunyar maganan ta nace kai haba anty dawa kuma nake ja da baya ni babu komai wallahi don dai ban kusa ne kawai.
Tace a dai bar zancen Allah ya dai ya sauwaka kawai tace kwana ki da yaran ki suka zo sallah suke fada min irin rigimar da kuke kwasa da dayan uwar tasu.
Murmushi nayi nace kai maman Ihisan ai halinta sai ita bayan haka ban kara komai ba ga zancen duk yadda taso taji wani abu ga zaman namu ban yarda taji komai a wurina ba.
Mun dan taba hira na mike nace zanje naba yaran magani kafin suyi barci tace ta Allah tashe mu lafiya nace Amin anty na fita zuwa part dina.
Nai mamaki kwarai a yadda naga wanan sauyin gun Anty haka kamar ba ita bace zanzo gayarwa tana daure min fuska kamar bata son amsawa a baya.
Washe gari ban samu fita ba don nagaji da yawon da muka sha a gida da mukaje sai washe gari muka tafi gaida mutane har gidan su daddy da Abban anty saida na zagaya don washe gari zamu koma Abuja da safe.
Na shiga tun dare naiwa Anty sallama take bani hakkuri na hakkura da yara da sauran jama a nace nagode anty tace a kuma yafe mu don Allah dai Rahama.
Nai murmushi nace kai haba dai anty may kuma ya kawo wanan magana hakan ni baki min komai ba wallahi.
Tace umm, umm Rahama ki dai yi hakkuri ga abubuwan da suka faru don Allah abar komai ya wuce haka na nace anty wallahi baki min komai ba Allah dai ya yafe muna baki daya tace amin ta kawo tsaraban data hada min sai da nai mamaki sosai wallahi.
Mun isa Abuja da rana sosai koda muka shiga gidan yai tsit kamar ba kowa cikin sa ga ko ina kamar ba a shara nai mamaki ko ina helen data bar wuri haka ba gyara.
Mun shiga min huta a dakina Aisha ta mike ta fita zuwa dakin su lokacin na samu na mike nafara gyaran wuri nima sai dai ina mamaki ina helen taje hakane wai ?
Ga matar gidan ban ganta ba koma na ganta ba halin na tambaye ta nasha bakar magana gun ta don ba karamin aikin ta bane yin hakan.
Can sai ga Aisha ta shigo take cewa dani anty kamar fa helen bata gidan nan don banga kayan ta ba gaskiya.
Nace kamar ya bakiga kayan ta ba tace wallahi ba komai nata a dakin nan sai wanan shegen bujen da kika hanata sakawa tun zuwan ta.
Kafin naii magana sai ga daddy ya shigo yana gyara hannun rigat shi doguwa dake jikin shi, yana fadin shi zai fita sai Aisha ta mike tabar dakin.
Nace daddy na dawo banga helen ba kuma Aisha tace dani babu kayan ta ma a gidan gaba daya ta kwashe kayan ta.
Yace yaya akai haka kin bata kudin watan tane da zata tafi ?
Nace nima shine yaban mamaki ai wallahi yace ki tambaya mana kiji ko ina ta tafi aji kada yarinyar mutane ta bata ko wani abu ya samay ta ai zargin ki kuma.
Yai min sallama ya tafi sai dai duk abinda nakeyi zuciya na fan yake da tunanen yarinyar a raina sai da yamma yaran suka dawo suka samu mun dawo.
Da murnan su suka zo taron mu har dakina Nasir sai daukan kannen shi yake yana murna da fanin su sai washe mai baki suke suma suna farin ciki da ganin shi don sun saba dashi sosai dama.
Jinior yace wallahi mummy naji dadin dawowan ku na matsu ki dawo dafa taliya ba dadi kullun muke zuwa school watarana ma ba komai muke zuwa hakana.
Nace helen batai maku ne ni ban ganta ba ma dana dawo ko ina ta shiga ban sani ba tun dazun nake neman ta.
Wai mummy baki sani ba shi da Atika suna hada baki wurin cewa ai maman Ihisan ta koreta sai data mamareta ta kore ta kuma a cikin dare ta watsa mata kayan ta waje tace ta wuce tana ta rokon ta amma bataji ba a gidan neabours din mu ta kwana.
Nace what duka da kora akan may zata kora min ita tunda ba zaman ta takeyi ba agidan nan ?
Atika ta marairaice tace Anty don ma baki gani ba wallahi ranan helen ta bani tausayi sosai wallahi danace tai hakkuri tace wai saura ni sai na bar gidan nan tunda ba gidan ubana bane .
Raina yai matukar baci sosai nace innalillahi wa inna alaihin rajiun yanzu wani irin rashin imani ne haka ka kori yarinya diya mace a cikin dare.
Jinior yace wallahi mum harda Ihisan tana ta zagin helen tana ce mata wai barauniya munafuka muguwa.
Basu dade da dawowa ba baban su ma ya dawo ashe dama yaje ya dan sayo kayan bukata ne irin dagin abin breakfast.
Ban mai magana ba sai da ya dawo da dare yana zaune ya fara cin abinci nazo falon na gaida shi yake cewa dani ya gajiyan tafiya nace Alhamdullahi.
Sai na samu wuri na zauna yana cin abinci kamar da kyat ita ko hamshakiyar tana zaune ta hakince ko kallon inda nake batayi ba balle na samu sannu da zuwa.
Da zamu tafi har kofan dakinta nake ina sallaman ta tai min Allah ya kai lafiya amma yanzu na dawo ta kasa yi min sannu da zuwa.
Can ya dago kai ya dan dube ni don yasan ba dabia na bane zama a wurin su idan suna tare irin hakan ko can a kano din har nan Abuja din kuma banai masu hakan.
Yace yaya dai kakata don wata raba haka yakance dani idan yaso zolayana wai na haifi baban shi da surukin shi sai na dan gyara zama nace dama magana nazo muyi dakai da ita.
Yace wa hindatu nace ita nazo ne ka tambayan min ita dalilin ta na korar min yarinyar dana dauko amana san nan kuma korar yarinya diya mace a cikin dare koma may tayi ai a sahirta mata harda safe ko a bari na dawo.
Yace subbahanallahi a cikin dare fa hindatu kika kori yarinyar mutane may tai maki dakika kore masu diya hindatu ?
Shiru tayi kamar ba da ita yake magana ba sai da ya kara maimaitawa da karfi tace na kore ta don ba zan iya zama da barauniya ba.
Yace may ta satar maki haka da har kika yankewa yarinyar mutane wanan danyen hukuncin babu tausayawa ko kadan a zuciyar ki hindatu ?
Sai tai shiru yace bayani nake so daga gare ki kafin naje neman diyan mutane inda ta shiga kuma ki sani wallahi idan yarinyar nan ta fada wani hali wallahi ki kuka da kanki don Abuja kin sani ba karamin gari bane.
Tace to don may bayan na kirga nama kowa ga yadda zan saka guda guda shine ita zata zo ta tsamay biyu ta cinye.
Yace wa,iyazu billahi Hindatu agidan nawa aka koma kidayan nama kuma yaushe aka fara hakan ban sani ba a gidan nan ?
Tai shiru ya koma kaina yace Rahama yaushe kuka fara kidaya nama kuna sakawa yara guda guda ga abincin su ?
Nace ni ban san lokacin da aka fara masu haka ba ni dai nasan zubawa muke masu yadda ya dace ?
Kai ya fara kadawa yana kiran kalman innalillahi cikin takaici yace hindatu ina zaki da alhakin yaran nan da kika dauka haka har ki kori diyar mutane akan nama nama fa a gida na ?
Sai ya kira jinior da karfi saiga yaron yazo da gudun shi bayan ya amsa yace daddy gani yace zauna yaron ya samu wuri ya zauna daddy yace jinior fada min ya akayi helen ta bar gidan nan.
Sai yaron ya dago kai ya kalli hindatu sai yai shiru uban yace tambayan ka nakeyi kayi shiru sai ya sake kallom ta yace a, a a dama maman ihisan bata sani bane ashe ihinsan ce ta kara nama.
Sai sai tace kai muna fukin Allah wace ihisan ta kara nama din yace banaji da kike koran helen tace maki itace ta kara ba biyu ba bata iya cin tsoka daya a abinci sai kikace tai maki shiru dama kingaji da zaman ta a gidan da ita ake maki munafunci sai kikai ta marinta kika watsa mata kaya waje tana baki hakkuri ihisan ta shure ta tace ta fice a gidan nan bakwa son ganin ta.
Daddy ya dafe kai yace kai kai hindatu wallahi baki da imani ko kadan a ran ki har dukan diyar mutane kikayi bayan kora kuma ?
Tace nagane kana son kaga laifina don wanan yar kafiran da aka aje muna gida saboda wace ta ajeta tafi kowa ko may ?
Yace rufe min bakinki idiot stupid mara hankali da tunane kawai baki da imani don bake kika haifi yar ba zaki mata haka ina ruwan ki da addinin ta tunda ba gidan ki take zaune ba.
Nan yai mata kaca kaca itama din bata kyale ba ranshi yai matukar tashi yace wallahi shi halinta ya kai mai ko ina yace yakike so nayi dake hindatu ?
A can idan na barki dasu ba zaman lafiya a nan din ma ba kwanciyan hankali wai ke wata kalar macece da bata tsoron Allah shin don ke kadai ne akayini don may in har ni kike so to ki zauna lafiya da duk wanda nake tare dashi mana.
Tace kana da gaskiyan ka ba laifin ka bane anje gida an kaika gurin malaima sun maka asiri idon ka ya rufe baka ganin kowa da kima sai ita.
Yace kamar yadda ke kika saba kaini idan kin je gidan ko haka kike ganin kowa ma sanan shi ke nan shiga boka da malam mutun ya daiji tsoron Allah tunda rayuwan mu ba a hannun mu yake ba mutuwa na iya riskan ka ko yaushe.
Ya mike a fusace ya fita bayan fitan shi sai kuma ya sake dawowa ya dauki keys din motar shi ban dai san ina zai tafi ba a lokacin.
Muna nan zaune sai zagi da cin mutunci takeyi nace ni banda lokacin ki don yanzu ba shi ke gabana ba yar mutane da kika salwantar ne a gabana.
Tace na salwantar sai kisa nima ya salwantar dani tunda sai abinda kikace.
Nace kika ce dai ke da kika san yadda ake sa mutum ya yayi abinda bai ashi yi ba ki daiyi ki gama gani nan bari nan takalmin kaza.
Tace komai shuumanci ki Rahama wallahi ni Hindatu nafiki sheri nace niko na sani nakuma fi kowa sanin hakan tunda ba imani gareki ba kan komai.
Ranan gamuwa da ubangiji yana tafe ranan da babu yafiya ga bawa sai aikin da ya shukawa a zaman shi na duniya.
Sai ki tayi tunda baki da aikin yi ni kinga inda na nufa don ina da abin yi a gabana yar mutane da kika salwantar don bakin kishin ki shike gabana ba hauka ba.
Sannu mai abinyi ai ban san kina danayi ba sai da kika fada karatun ma da kike wa mutane sallo dashi mun san komai kudi ya bayar kikaci.
Nace to ke abada kudi mana kici ashe na isa tunda har za a iya kashe kudi a kaina a samo min abin yi ba in zauna zama sa ido da hassada da bakin ciki ba.
Aiko kamar na yaba mata bargon balai nan ta kara harzuka tayo kaina da masifa da jidali inda take shiga banan take fita ba.
Ina shiga daki na kara lalabar wayan matar da nake ba kudin watan helen don tun da yamma nake kiranta waya na ringing ba a dauka sai nai saa ta dauka wanan karon.
Maganan data fara min bayan ta dauka shine haba doctor Rahama yanzu abinda kukaiwa yar mutane kun kyauta ke nan ku kori yarinya a cikin dare haka ?
Badon tai dabaran shiga gurin makwabtan ku ta kwana ba yaya kuke son yarinyar nan tayi a cikin daren nan.
Nan na shiga bata hakkuri tace gaskiya abinda yasa bazan boye maki ba shine don tun zuwan ta wurinki bamu taba samun matsala dake ba.
Yanzu kuma da wanan abin ya faru ta fada muna cewa baki gari kishiyarki ce tai mata haka gaskiya da munyi karan ku an dauki mataki kan dukan da akai mata tunda ba duka acikin dokar mu.
Hakkuri na shiga bata tace dani na bari suyi shawara suji yadda za, a yi zan iya kiranta washe gari naji yadda suka yanke akan maganan.
Tai min sallama na kashe wayan ina jin kunar rai ga yadda hindatu tasa na ke rokon su da suyi hakkuri akan laifin da bani nayi ba.
Daddy sai goma da wani abu ya dawo gidan har lokacin ranshi yana a bace yazo dakina yana ce wa dani naje nayi reporting ne a nan area din ko za a ganta nace ta ta koma can inda ake dauko su ashe.
Yace an ganta ke nan nace dashi eh tana can har munyi magana dasu sun nuna min bacin ran su sosai sunce badon ba a taba samun matsala ba damu da sunyi kara kan dukan da akai mata.
Yace yes suna da right din da zasuyi kara mana tunda ita waya taba dukan mata ya amma tana iya dukan diyan wasu kan laifin da ba nasu ba.
Dukkan ku bazan lamunci duka ba a gidan nan akan ko wani yaro wallahi sannan ku sani gaba daya yaran nan amana suke a gare ku duk wanda yaci aman dan wani sai Allah yaci nashi.
Ya sa kai ya fita daga dakin ranshi a bace na sauke ajiyan zuciya bayan fitan shi don na gane nufin shi ajan yaran shi ne da yaji ana saka masu naman miya sai an kidaya yake wanan fadan ko gani yake duk haka mukeyi dani da ita cin aman yaran nashi mukeyi ke nan a bayan shi.
Tana shiga daki ta kira wayan uwar ta tana cewa da ita wallahi mama wanan shegiyar Rahamar shuumace ki duba fa yanzu gaba daya ma na rasa gane kan dear yau ma fa a gaban ta yai min cin mutunci akan yarinyar nan dana kora.
Mama sai kudi muke kashewa amma kamar bama yi ni wallahi ina bakin ciki na bude ido naga wanan yar iskan a gidan nan yarinya kamar manya nayi kamar ba ayi.
Kiduba fa shi wanan mutumin fa cewa yayi bata dawowa gidan nan in ma har ta dawo ba ita ba kwanciyan hankali da maigidan amma ji yadda ta dawo ko gezau babu a gare ta.
Uwar tace waini kan dai ko baki abinda akace kiyi ne dakyau Hindatu abin akwai ban mamaki a cikin sa fa.
Na ga dai in ba wanan bakan da akace ba banga abinda kikace ya kamasu ko shi ai ba haka yadda muka so ba yayi tunda ni a zatona suna tare har yanzu suna hurda kece dai baki ganewa.
Tace shi ne ai mama amma gaskiya zan maida hankali sosai ga duk abinda akace nayi na dinga yin shi daidai da dadi da rage a ciki.
Washe gari na karbi girki sai dai duk abinda nake yi hankalina yana kan wanan danyen hukunci da aka yankewa yar mutane ta sanadi ya zama dole yanzu na maida hankali akan duk yaran don Allah kadai yasan abinda ake masu a bayana kuma a hana su fadi.
Don yadda jinior yayi a gaban uban shi ya nuna anyi warning din su sosai akan maganan shiyasa yaji tsoron yin magana a gabanta don a daki sun mayar min da komai yadda akayi din.
Bayan na gama na kwashe nai yadda muke da abincin na shiga don nai wanka na gyara jikina don aikin da nasha.
A yanzu ban da wani buri a raina idan ba na samun sauki ga lalurar dake tsakanina da daddy ba don bani ba koshi dake da wasu matan yana samun sasauci a ranshi ya dan damu da matsalan sosai.
Don da zamu dawo ina zaune a gaban mota yake cewa dani Rahama may yasa da kika je gida kika kasa fadawa su baba halin da muke ciki ni dake.
Na juyo da sauri na dan kalleshi sai tunkin shi yake hankali a kwance nai shiru ban ba shi amsan tambayan shi ba.
Yace na dauka zaki fada ai koshiyasa kika matsa min kina son zuwa gida ki duba su ashe ni zato ne kawai nake sai nai mamaki da naji baba maigari yace baki fada masu komai ba.
Na juyo da sauri nace kafada mashi fa kace ya gyada kai yace kwarai kuwa banda kunya dana fada masu ko ?
Nace a, a ni bance ba amma naga maganar tana da nauyi fada ne a gaban manya shiyasa kawai nai mamaki.
Dama ban tsanmani din zaki iya fada ba kawai dai zatone nakeyi shiyasa ma na yanke shawaran zuwa
Showing 333001 words to 336000 words out of 456145 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112 Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153