dakin ta tana waige waigen bayan ta.
A hankali naci gaba da aiki ba tare da na damu da abinda nagani a gare ta ba don zargi ta nakeyi kawai nagama na kwashe a kula ina fito daidai ta sake fito sai naga ta dan kadu tace ashe kin tashi nace da ita eh har ta fara tafiya take cewa tun dazun kike nan ne ?
Nace yanzu na fito in samawa yaran nan abinda zasu dan ci tace oho yayi sai ta juya ta koma dakin ta nikan na wuce zuwa dakina .
Ance zance baizo maka sai kana tsaka da sallah shedan ya dinga rudin ka da zantutuka barkatai a zuciyar ka.
Irin hakane yazo min kan na duba backyard dinan naga may matar nan take boye min Aisha nasawa kira tashigo nace ta matso kusa da inda nake zaune saman sallayana.
Cikin rada nai mata bayanin abinda nake son tai min tace ba matsala ta fice daga dakin.
Takai min ti ashirin sai gata ta dawo dakin take cewa dani naga ni anty a razane nace wai da gaske tace Allah ko.
Nan muka bar zancen har zuwa dare nasan Aisha zata iya aiwatar da komai yadda ya dace.
Mun fito muka dora girkin abinda za ai buda baki a ranan tunda mu zamuyi duty .
Yi wana dora wancan sauke wanan har muka kamala komai da za aci na jera shi inda muke zama ai buda baki.
Tunda nake aikin nake ganin tafita takoma haka taitayi nace da Aisha ta saka ido idan naje sallah akan matar nan .
Bayan kiran sallah saiga yaran sun fito sun taru a falo nan mukai buda baki na tura yarta tace tazo tasha ruwa.
Sai gata tafito dakin tana ganin yadda muka taru ana raha kowa na farin ciki yana shan fruit da drinks din dana hada a wurin.
Sai ta bata rai ta juya zata wuce bata zauna ba nace bissimillah mana ga abin buda baki nan an aje tace barshi kawai har anjima ta juya ta koma dakin ta.
Mun gama muka shiga sallah amma Atika na gurun ta kasa ta tsare sai gata tafito tana tambayan Atika ke baki zuwa sallah ne kowa ya tafi tace sai anty Aisha tafito zan shiga taso yiwa yarinyar jan ido sai taga bazata gusa ba nan da can dole ta barta an bata mata plain din ta.
Sai bayan sallah ya shigo gidan ina daki Atika tazo ta kirani wai nazo daddy ya dawo ban dade ba na fito nai mashi sannu da zuwa ya karba ya shige dakin shi don ya sauya kayan jikin shi zuwa masu sauki.
Ruwa na hada mai yai wanka ya fito falo ina daki tare da yaran ban fito wurin su ba don naji muryan su a falon tare.
Ihisan ce ta shigo take fada min daddy yana kirana falo na karaso ina kara gaidashi da shan ruwa tana zaune gaf dashi tana tsiya ruwan juice din abarba a cup.
Ya dago ya kalle ni lokacin da nake zama saman kujera yace kin shige daki kin zauna da yara bayan kin san cewa nafito kuma .
Nace na dauka ba wani abinda kake bukata don na aje ma komai da zaka bukata wurin.
Yace baki zoba waye zai zuba min abincin nacu sai na dan kalli inda take zaune ina nufin bagata ba a wurin ta zuba mai.
Nadai sauko na zuba mai komai yadda ya dace na fara kwashe sauran zan shige dasu kitchen tace ina kuma zaki dasu ni ban ci ba ?
Nace ba tare na zuba maku dashi ba na mu yana can sama table ajiye nai saurin kwashewa na bar wurin da kayan zuwa kitchen tabishi da kallo ko zaiyi magana.
Na riga da na shirya amsan bata a lokacin koda zaiyi magana kan hakan sai baiyi ba din har nakai na aje.
Na fito naso nq shige sai naji a jikina ni daddy yake kallo sai dai naki yarda na dago na kalle su.
Yace Rahama daidai na dan juya na amsa naam daddy yace yaran ki sun ci abinci ko ?
Sunci tun dazun daddy yanzu fruits salad suke sha kafin su kwanta yace yayi kyau.
Na fahinci daddy yana da wata manufa akaina ranan don haka naki bada fuska yadda zai samay ni da sauki hakana.
Yana gamawa na fara kwashe kayan hindatu dake zaune ta cika fan don ko magana batayi ranta ya baci dani.
Ban koma wurin su ba na shige daki abina na samu yaran sun watse sai Aisha ke gyara wurin da suka bata.
Wanka nayi na shirya na haye gadona na mimike abina ina waya da zarah sai dana gama Aisha ke cewa dani anty na dauko fa nace abune aciki tace wallahi helen nasa ta ciro yana can mun boye shi a wani gyrin mun mai fitsari a razane nace Aisha kina da hankali idan wani ayan Allah ne fa ?
Tace a, a wani abune kamar tsoka da gashi an sosoka mai allura a jikin shi kamar mutum mutumi.
Nace wa iyazu billahi injin kun jefar tace helen ta fita dashi can bayan gida sai da muka wargaza shi gaba daya muka fitar dashi takardan dake ciki muka boye kawai.
Muna nan muna magana akan zancen daddy ya shigo dakin sai Aisha ta gaidashi tafice daga dakin ta bar mu a ciki nida shi.
Kallona yake ni kuma naki dago kai mu hada idanuwan mu ni dashi yace humm kawai tare da karasowa inda nake.
Rahama wai har yanzu fushin ne kike baki daina ba ko may ?
Nace fushi ni bani fushi da kowa ai da ina fushi aida ba haka ba ba yanzu nafito wurinka ba can fallo inda kuke zama daine banayi har a soka min magana tunda ni banje na takurawa mutum ba.
Yace naso ace tun kan hindatu tazo ta fahinci halin da muke ciki kin daina wanan fushin haka na don Allah ki sake jikin ki ki bar wanan fushin hakana.
Nace na huce indai nice yace koke fa in ba haka ba ko yaran ki abin zai iya shafa ai.
Ya juya yana fadin ina jiran ki a dakina ban tanka shi ba ya fice daga dakin nabishi da harara kawai har ya fice.
Har sha daya da wani abu ban je gun shi ba sai ga wayan shi ya shigo min na dauka lokacin har na soma barci.
Yace wai kin manta da nine anan komay may ke damun ki ne haka wai Rahama may kike son bullowa dashi ne a tsakanin mu ?
Ina ce mun riga mun yi magana kin ce komai ya wuce yaya kike son nayi da raina ne please.
Ban yi magana ba sai mikewa da nayi na gyara shiri na fice daga dakin inda na samu yana kwance ban bata lokaci ba na kwanta nima.
Ya sauke ajiyan zuciya tare da birginowa inda nake a kwance yakai hannun shi a jikina.
Abin mamaki ranan duk yadda daddy yaso yakai a gare ni sai ya kasa duk kokarin shi a kaina abin yaki sai ya koma tankar mace a guna.
Ya koma yana sauke nunfashi gefe daya tare da wani irin tartso zufa a jikin shi ni dai ina kwance lamo nima mamakin hakan nakeyi yau a gare mu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , , , ,

79
Wanan matsalan da ya faru tsakani na da daddy sai ban dauke shi komai ba a raina ko banza ma acikin watan mai arbarka muke watan kara kusantar bawa ga ubangijin shi.
Ban sa abin a raina ba don ban dauke shi wani babban matsala bane a wurina sai na samu daman yin ibaduna yadda nake so.
Yau shine karo na uku da abu daya ke ta maimaita kan shi sai ya kusan kaiwa gare ni sai wasa ya canza sallo aiki.
A bu daya dake ci min rai shine rashin walwalan da naga daddy baya ciki a yan kwanakin nan.
Don zai zauna yayi tagumi da gani akwai abinda yake tunane a ranshi tun abin na damuna har na fitar da damun a raina tunda bai fada min komai ba.
Na fito falo daga dakina don in danyi hira da yaran dake gida yau weekend ba su zuwa school a gida zamu wuni tare dasu don haka nakan yi na zauna da su na wani dan lokaci muna hira a tsakanin mu.
Hiran mu muke kwasa ga tv na aikin shi sai faman dariya muke a tsakanin mu banji sallaman shi ba sai ganin shi mukayi a tsakiyan falon ya shigo gidan.
Nan yaran har ni muka shiga yi mashi sannu da zuwa ya samu daya daga cikin kujerun falon ya zauna akai tare da dafe goshin shi da hannuwan shi.
Sai duk muka bishi da kallo Nasir ne ya fara mikewa zai shige sai daddy ya bude idanuwan shi da sukai ja yace No zauna abinka mana kuyi hiran ku.
Yaron ya koma ya zauna inda ya tashi sauran ma sai suka zauna baiyi magana duk zaman da yayi sai lumshe idanuwan shi da yayi.
Nace dashi daddy yau lafiya kake kuwa naga ka dawo wanan lokacin ya dan bude idon shi ya sauke su gare ni yace inaga dai azumi ne yasa min jin ciwon kai yau don ni ban faye saurin yin ciwo ba haka.
Sannu muka fara yi mashi yana amsawa can ya dan dago yace Nasir ina Ihisan take banganta ba nan cikin ku.
Kafin Nasir yai magana sai jinior yace da uban tunda mum din ta tazo ai ta daina zama tare damu ko school muka tafi sai ta dinga muna abinda taga dama yanzu ma saboda ita late mukeyi zuwa schoool da safe.
Daddy yace may yasa baku fada min ba tunda ta fara hakan yace kira min ita dakin nasu sai yaron ya mike tafi gun kiran ta.
Tare da uwarta suka fito falon inda uwar kecewa dashi kadawo ashe yace eh kawai ya juya kan ihisan yana cewa may yasa kowa na falo a na hira kika shige daki ke ?
Yanzu nake jin duk kwanakin nan bakya fitowa da wuri sai kin sa yan uwan ki yin late a school daga yau kada na sake jin haka daga gareki.
Sai uwar take cewa wata sabuwa yau kuma Ihisan ce akaiwa kulli bani ba babu dai yadda zakuyi damu gani nan bari nan wallahi.
Yace ke dakata wani irin magana ne wanan kuma haka sokike abarta tana cutawa yan uwan ta kullun ta sa su makara ko may aida ba haka takeyi a baya tare suke fitowa su wuce.
Inda nake tajuyo tace yanzu Rahama baki ji kunyan fadin wanan maganan ba wa karamar yarinya zakiwa hadi wurin ubanta.
Murmushi nayi nace da ita cikin dariya Allah sarki Rahama mai dadin suna yanzu kuma nice na fada mai don ina bakin ciki da Ihisan ko may ?
In ba bakin cikin ba may zai sa ki mata hadi gun ubanta hira banda kilibibi may kike koyawa yaran suyi in ba gulma ba.
Wai hindatu may yasa baki da tunane ne ina ruwan Rahama a cikin wanan zancen yanzu da ita ake zuwa school din ko may wai ?
Ta juya gun Nasir tace kune kilababbun da kuke cewa haka ko zaku hanata zama da uwarta ne ko may yan bakin ciki da sukai gadon mugun abu a gurin uwar su.
O my god wai may nene haka kike yi hindatu na fa fada maki bana sin irin haka so kike karnaiwa ihisan fada ko may idan tayi ba daidai ba ?
Wanan cin amanan nata da kukaitayi don bana nan yanzu nazo babu wanda zai saka min ya a gaba da mugun manufa in yarda don da baifi da ba
Ihisan dai ba yadda zakuyi da ita don ta zamay maku kashin bakin tunkuya ta Allah bata ku ba ta juya ta wuce fuu zuwa ciki.
Yarinyar ta samu wuri ta zauna a takure yayin da falin yai tsit bayan wucewan ta ciki sai Nasir ne yace dani mum yau ki muna wanan miyar bindin saniyar da kafan shi mana please ?
Nace Nasir an barka a tasha sai dai ka fadawa maman ihisan tai maku don yau itace da girki sai yaran suka bata rai yace ni yau shi nake son ci wallahi.
Nace bari banda gobe sai nai maka duk abinda kake so sai uban yace saboda may baza ki masu ba tunda shi suke so sai nai shiru nasan yin zai iya jawo man matsala gun matar shi.
Yaran suka ce daddy yace ki muna shi inji jinior nace kaida baka azumi ina ruwan ka da abin shan ruwa na masu azumi ne kawai wanan.
Aisha tashi ki ciro min ki dan saka a ruwa ya sake kafin na taso kin san wuyan dahuwa ne dashi.
Ihisan ce ta mike zuwa dakin su nasan ko ta fadawa uwar ne sai gani nayi ta fito ta shiga kitchen din a lokaci sha daya na rana lokacin yin abin buda baki baiyi ba.
Amma haka ra babake kitchen sin wai tana aiki nikan ganin ta shiga banyi yun kurin tashi zuwa abinda zanyi ba din.
Ba ita ta gama ba sai bayan uku da wani abu na rana na shiga na dora masu girkin sai gata tafito daga daki tana shiga naji tace may aka dorawa wuta haka kuma ?
Bayan wanan uban abincin dana dafa sai an kara dora wani kuma again wanan ai ya zama barna ko ?
Nace abinda diyan masu gida ke so shine zan dafa masu tace haka za a kare wurin yiwa diyan kishiya bauta babu gode balle na gode.
Gyara dai maganan ki ko kin manta nima ina da masu ci a ciki ne da zakice hakan.
A dai bari su girma kamar kowa mu gani ba wanan ya ta tsitsai din ba da ba a san da su ba a gidan.
Nace a wwurin ki ne yake amma agun wanda ya yanka masu rago yasan dasu kin san ance mai karami watarana shi keda babba insha Allahu.
Magana take so yai nisa na fahince ta sai na sharer ta naci gaba da aikina sai naga yaa dace na hada tuwon farar shinkafa aci dashi ba bata lokaci na dora na fara aikin shi sai dai ba yawa sosai.
Da muka sha ruwa shi muka ci muka bar faten doyan da tai muna wanda har ya yi karfi ko don yin shi da akai da wuri.
Koda daddy ya shigo ya samu yaran a falo suna cin abincin su a zaton shi shi aka girka a gidan saida ya gama ya fito ya zauna cin abinci ya na budewa faten ya tare shi a fuskan shi take ranshi ya baci.
Da karfi ya kwala mata kira don kwance take tun shan ruwan ta jikin ta yai mata nauyi ta mike ta fito kai babu dan kwali ba wani kwalliyan da tayi.
Tans zuwa yace may ye wanan saboda Allah yanzu hindu abinda zanci ke nan a gida na a matsayina na wanda yai azumi kko may ?
Tace may kuma yayi don Allah kai mutum baima gwanita ka gode mai yace may ye abin gwaninta anan a faten doya ke kullun ba zaki iya yiwa mutane abincin kwarai ba don kiuya kawai kada ki motsa jikin ki komay ya kawo haka.
Ni gaskiya ba zan lamunci hakan ba wanan ai cutawa ne gare mu may aka rasa a gidan nan da baza a girka muna abincin kwarai ba ?
Ni shi na iya kuma shi nayi ba zan wahal da kaina ba don a yabe ni ko wani abu mutum na fama da azumi yai aiki ya gaji a kawo mai wani korafi can kuma ?
Ya ce yayi kyau za a ko jimu a gidan nan dake idan wanan abincin zaki dinga girka muna tace iin hakane sai dai naiwa mama waya akawo min wata yar aikin don ba zan iya wanan wahakan ba gaskiya.
Yace yanzu dabara ya rage gareki ai idan tazo sai ta girka iya bakin ki don ba zan auro mace ba tace bata iya min girkin da zanci.
Ya kwalawa jinior kira yace kira min mummy ku a dakin ta yaron yazo kirana ina ba haidar nono na ce gani tafe yaron bai gama shan nono ba na mikawa Atika shi na fita.
A zaune na samay su yadda na ga zaman su yau yasa nasan akwai matsala ke nan na karso ina mai barka da shan ruwa ya karba min a dakile yace ina abincin da naga kinyi ?
Na kai idona kan faten dake gaban shi fari nace nabawa yaran yace babu ko kadan a bani nai dan shiru can nace akwai shi yace a bani don Allah ?
Na juya na koma daki na dauko mai cikin wanda za suyi sahur dashi na kawo mai har miyan da komai.
Na aje ban tsaya ba zan wuce tace indai kili bibi abin yi ne sai mu zuba mu gani dama sherin da kike son kulla min ke na yasa kikai wani girki.
Ban iya sheri ba ni da bakin maigidan naiwa yaran girki ki
Showing 318001 words to 321000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107 Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153