shi wanan din da ban ko san sunan sa ba ya kafe ni da surutun tsiya a gida.
Daga cikin aljihun shi ya ciro kwalin sigari yana kokarin kunnawa a lokacin.
Wani kallo da ban san na watsa mashi ba na harara na watso mai a lokaci daya sai naga yai murmushi yana cewa sorry fa na manta ne ku matan hausawa bakwason cigiratte a kusa daku.
Nace ba matan hausawa ba kawai ai duk wanda yasan ciwon kan shi da daranjan kan shi bai wanan dabian mara kyau ko a gaban waye.
Murmushi mai kama da yake yayi tare da kakaro murmushi a fuskan shi a lokaci guda.
Ya kalli a gogon dake daure a hannun shi yace ok beauty ni zan tafi koda baki fada min sunan ki ba amma ni zanci gaba da kiranki da beauty kamar yadda ya dace dake din.
Yace zan tafi gida kada hajiyata taga na dade tai min fada ina na tsaya haka ni kuma ban iya fada mata nayi gamone da wata zukekiyar budurwa a gida brother na.
Sai lokacin na danyi dariya har fararen hakora na suka baiyana a fili nace fada kuma kamar wani dan karamin yaro can ?
Au baki san ana ma babba ma fada bane idan yana fita yawo akai akai ko yayi wani abinda ba daidai ba a rayuwan shi ?
Nace Allah sarki hakane fa amma kuma gashi naga ba aima fadan shan taba ba kuma ?
Yace cikin murmushi tare da hade yawun bakin shi tare da dan rankwafowa gare ni kamar mai rada yana cewa.
Kin san yaro ya iya yiwa manya wayo yanzu kaf gidan mu ba wanda yasan da ina shan cigari yanzun ma daurowa tayi hakan.
Nace cikin mayde bakina kadai bari zaifi ma alheri a rayuwan ka don badadewa ba za, a gane hakan tunda kadawo gaban iyayye.
Yace hakane fa kin kawo shawara mai kyau kuma anan zan kula da hakan insha Allahu.
Har ya juya ya fara tako yake cewa sai dai kuma beauty bata ban wayan taba mu dan dinga gaisawa ko jefi jefi.
Nace ban da waya ai don ni karamace anty da daddy suna hanani rike waya a gidan nan.
Kallona yayi cikin mamaki kamar zaiyi magana sai kuma ya ci gaba da tafiya har ya kai kofa sai kuma ya tsaya yana saka hannun shi ga aljiihun shi ya ciro waya guda biyu yana cewa dani.
Ungo wanan kafin su dawo sai muna gaisawa dake ta nan ko yaya kika gani beauty ?
Nayi murmushi nace kabar wayan ka don ni bani ketare maganan magabata na gaskiya.
Yace ba kidai son gaisawa danine kawai amma ai bazakice min baki da saurayin dakike gaisawa dashi ba ta waya yadda kike babba yarinya dake haka ?
Nace saurayi ni na kada kaina cikin dakewan fuska nace kun kun kun badai Rahama ba kan sai dai idan wata can.
Yace nice name kamarki kamar sunan ki suna mai dadi haka ai yanzu ma koba komai kinga aina karu da sanin sunan ki ai.
Yatako zuwa inda nake cikin wani murya mai kama da umurni yace karbi wayan nan Rahama please.
Kabar wayan ka ni ina da waya sai dai na baka nombata kawai ka saka a naka ka kirani dashi.
Ya sauke wani asirttacen ajiyan zuciya yace dama nasan cewa yarinya haka kamarki bazata rasa waya ba ai.
Na fara karanto mai yana sakawa a wayan shi yace ya gode sai kin jini ke nan.
Ban amsa mai ba yasa kai yafice daga part din na sauke ajiyan zuciya tare da bin shi da kallon takaici.
Nai nadama da bashi nomban wayan da nayi ranan don yana fita ya fara kiran layina wai yana sheda min ya isa gida lafiya.
Nace a gaida mutanen gida yace zasuji insha Allahu ya gode.

********* ********* *********
Tun muna damuwa da kadaicin dake damun mu a gida har muka sake jikin mu muka koma normal life din mu yaran sun fimu sake jikin su sosai don ba wani damuwan komai a tare dasu tunda suna samun kulawa tankar uwar su na gida.
Idan ka gansu neat dasu ba kazanta ba yunwa ba damuwa akan komai koda yaushe suna lake a jikina yadda suke so.
Abinda kuma sule so ban kiuyan yi masu shi ko yaushe haka yasa suka kara sake jikin su sosai damu.
Ga gajiye tana nata kokarin sosai don ina bata girma yadda ya dace a matsayin ta na wacce ke gaba dani a gidan.
Matsala ta daya yanzu shine bakon da yakira kan shi da suna Ibrahim yada yake kokarin kutso kan shi a cikin rayuwana.
Don yawan wayan shi na matukar damuna a yanzu zai kirani a yini kusan sau goma albarka.
Sai dai ban yarda na sake jikina dashi ba na fahinci yana son kulla alakar soyayya ne dani wanda ban tashi yin soyayya da ko wani da namiji ba alokacin nan da nake tsakiya ga karatuna.
Dama ya damay ranan wani yamma ya matsa yana son yazo gida ya ganni nake cewa dashi yanzu ko lokacin kaina banda shi..
Don karatun jerabawan da nakeyi wanda ya matso min a lokacin don haka yayi hakkuri kada yazo.
Yake cewa ba matsala Allah ya bada saan jerabawa zai jira har nagama exam sai ya fara zuwa nace dadai yafi kan.
Yace amma zaici gaba da kirana muna gaisawa a waya kamar yadda mukeyi.
Nace hakan ma gaskiya ba karamin takura bane a gareni gaskiya don hakan yana yawan dauke min hankali ga karatuna.
Ikon Allah Rahama yaya kike son nayi to?
Nace ban gane yaya nike son kayi ba da da babu ni yaya kakeyi a baya ?
Yace hakkuri nace to ko yanzu shi zakayi din idan kaga kana iyawa.
Naji yayi murmushi yace amma idan nazo gaida yaran brother dina zakiyi min alfarma ina ganin ki ko bamu gaisa ba ko ?
Nagane wani salon wayau yake son yi min kuma anan.
Nace ai gidan ku ne nan kana da ikon zuwa duk lokacin da kaga dama amma ba wurin Rahama dai kan don ban da time ni yanzu.
Mukai sallama bayan yai min godiya yakashe wayan nima na kashe tare da bin wayan da harara kamar shine a tsaye gabana.
Dama muna waya ina jin call na shigo min na duba naga anty ce a layin da sauri nai salati nace kaji sheri ko har anty ta kirani sau biyu wanan dan surutun ya hanani ji.
Da sauri na kirata bata daga ba har kiran ya tsunke dama nasan idan ta gani zata kirani again.
Sai ko ba akai ko second ba kiranta ya shigo min a wayana da rawan jiki na dauka ina sallama.
Muryan ta radau ta karba min sallama na na fara gaida ita bayan mun gaisa ne take cewa dani.
Dawa kike waya haka mai tsawo Rama nai maki kira har biyu baki daga waya ba ina jin ana samin line busy.
Nace lah Anty ba wani bane fa wani can yake damun rayuwa na kwanan wai shi dan uwan daddy ne yace wai ko sunan shi Ibrahim ?
Tace da karfi Ibrahim Ibrahim kamar tana mamaren sunan can tace badai Ibrahim din gwago Safiya ba nace haka yace.
Tace yaushe Ibrahim ya dawo kasan kuma har ya gan ki nace ranan ne yazo neman ku shine ya ganni ya tsireni da surutu har ya matsa min sai da ya karbi lanbar wayana.
To ki dai yi a hankali don in dai Ibrahim ne nasan yana da matar dake jiran shi tun bayan tafiyan shi acikin family din su.
Nace anty ni ina ruwana dashi shine kawai ke haukan shi shi kadai amma ni inani ina tsayawa wani shirmay yanzu.
Tace dadai yafi maki alheri wallahi ki natsu ki kama kanki irin su ba abin yarda bane don sun san yadda zasu sace zuciyar mace.
Ta tambayi yaran nace da ita gasu nan sunyi barci yau sunce sunyi game ne a school shine suka gaji sukai barci da wuri.
Ta tambayi gajiye nace tana kitchen tana wanke wanke tace na gaida ita nace zataji take cewa dama na kira nane naji lafiyan ku don tun safe yau bamu gaisa ba daku.
Nace lafiya kalau muke anty yaushe zaku dawo ne anty duk gidan ba dadi wallahi baki.
Tace cikin dariya Rama dawowan mu ba yanzu ba gaskiya don akwai maganin da nake sha ga kuma daddy ku akwai ayukan da yakeyi a nan.
Mukai sallama tana cewa na shafa mata kan yaran idan sun tashi ince mummy tana gaishesu nace zasuji anty.
Daddy dake tsaye fitowan shi ke nan daga wanka ya kashe ta da ido yana cewa dawa kike waya naji kina kiran Ibrahim.
Tace Rama ce mana nakirata har sau biyu bata daga kira ba tana waya shine yanzu ta kira nake tambayan ta dawa take waya take ce min wai Ibrahim din gidan gwago safiya ne.
Yace da wani irin murya mai kaushi Ibrahim Ibrahim kuma ?
Yaushe ya dawo garin har ya gan ta kuma ?
Tace wai ya kwana da dawowa bayan tafiyan mu ya dawo garin yazo gida shine ya ganta ya takura mata kuma sai da ta bashi layinta.
Tabashi layinta kuma ita Rahama bata da hankaline da zata dauki layinta taba mutum irin ibrahim mayaudari dashi.
Wanan dan iskan yaro tayi haukane halan da zata ba Ibrahim layin wayan ta kuma ?
Tana jin hakan yadda yake magana a hasale dariya ya kamata take cewa to may ye kuma don taba dan uwan ka layin wayan ta shiba na miji bane ?
Yai mata wani irin kallo yace eh lalai kuwa namiji ne kuwa tace to kagani yashigo layin da maza ke nuna bajintan su ne shima ayi dashi.
Yace ai sai suyi din amma dai kin san ko waye Ibrahim tun farko da kike wanan magana balle yanzu da yazo turai idon shi ya kara budewa haka .
Tace ni yanzu may kake son nace a nan tunda yana son ya gwada saan shi ne a kan ta kuma.
Yace baki da hankali Saade har ke da kanki ke wanan magana haka akan yar uwarki kuma kan Ibrahim.
Tace Ibrahim fa dan uwanka ne besty yaya kake son na hana shi hurda da yarinyar dake gidan ka ai Rama na da hankali bazata yarda tai wani abinda bai dace ba ai.
Yace ok yayi kyau matsalan ki ne ai hakan banawa ba don haka dabara yarage akan ki yanzu ni ba ruwana.
Tunda kin san yaron nan uwar shi ta fada muna an mashi mata a dangin su tun bayan tafiyan shi.
Tace aiba aure aka daura mashi da waccan dib ba don haka yana da right din canzawa yanzu.
Ya shiga sake sutura a jikin shi ba tare da ya kara mata wani magana ba ita ko sai dariyan mumuke take mashi a ran ta.
Washe gari da yamma after five sai ga Ibrahim yazo gidan Allah ya taimakeni ina ban daki ina wanke unders di yaran da nawa nan ya samay su a falo suka shi hira da yaran.
Gajiye ce tazo ta kyankyasa min zuwan Ibrahim din a lokacin don haka ma sai na turo kofan bayin na rufe kaina aciki ban fito ba.
Sai da yagaji da zamane yake tambayan yaran ina anty sukecewa tana ciki tana aiki ne yace suce Uncle Ibrahim yazo yana gaishe ta .
Nasir yazo yana kwankwasa ban dakin daga ciki nake tambayan waye yake cewa shine wai uncle yazo yana gaisheki a falo nace je kace ina amsawa ina abune .
Nan ya karaci zaman shi da shirmay da yaran da zai tafi ya basu wani farin leda da yazo dashi a hannun shi.
Ya tafi baiji dadin rashin fitowan da banyi ya ganni ba a lokacin ina fitowa kiran wayan shi ya shigo min na dauka naji yana sakin ajiyan zuciya yana fadin nagode.
Nazo don na ganki amma kika boye kikaki fitowa nagan ki ko zanji sauki a zuciya na.
Amma kika ki fitowa nagan ki Rahama why da kike min rowan ganin ki ne hakawai ?
Ya kamata ki tausayawa wanan dan bawan Allah naki da ya susuce da son ganin ki kamat zan yi hauka.
Dariya ya bani yadda ya ma rairaice murya kamar da gaske bayan nasan da yaudara yazo min already yana da wace zai aura ko a gida cikin dangin shi.
Nace gashi ko fuskan nawa koda ka gani a lokaci ba zakaji dadin ganin shi ba don a hautsane yake yanzun haka saboda aiki kan fuskan dan kauye yadda yake ai dai.
Yace babu ruwan ki ni dai ai ko yaya yake ni nace naji nagani zan gani a hakan .
Nace next time if you are among the lucky one's.
Yace insha Allahuma ina ciki don ba a taba Ibrahim raggo ba a duniya ai.
Yace ki karbi sako a gurin dana nabashi sako ya baki da fatan zakiyi farin ciki da wanan sakon da zaki gani.
Nace na gode koda banga sakon ba nasan sakone daidai da na yan kauye ai .
Murmushi yayi yace ina jinn dadin sunan yar kauyen nan da kike kiran kanki dashi don alamane na sauki kai gareki.
Nace to nagode da harka fara fahintar halayena don haka ka kula da sauran nan gaba.
Yace indan dai har za, a bani dama na fabinta a hankali ai nafi kowa farin ciki nace yayi nagode sai anjima.
A daidai wanan lokacin daddy ya shigo tsararen gidan su da suke can zaune shida iyalinshi idan sunje kasan.
Ya samu anty a kwance da danta suna barci a hankali ya dauki wayan tare da kwashe lanban wayan da yake ta muradin samu daga gareta kuma girman kai ya hana ya tambayi matar tashi.
Bayan ya yi nasaran kwashewa batare da matar shi ta sani ba ya sauke shu, umin murmushi a fili cikin sanda yafice daga dakin.
Can ya koma waje kasa ya sauko gurin motar shi tare da samun kan shi da kiran layin wayan.
Ina zaune ina sawa Nasir kayan barci muna shirin kwanciya a lokacin naga kira da lambar kasar waje sai dai ba anty bace to waye nace a fili.
Na dauki wayan daidai lokacin da yake shirin tsinkewa tare da sallama cikin murya mai taushi.
Daga inda yake a tsaye ya runtse idanuwan shi a hankali don jin wanan muryan da yayi.
Ya daure ya amsa min da muryan nan nashi mai gadara sai lokacin nagane dawa nake magana.
Yace yakuke nan na amsa cikin ladabi da lafiya kalau muke daddy yaya anty da jinior yace gasu suna barci ne.
Sai nai shiru ina sauraren shi yace Rahama kina jini ko nace eh daddy.
Yace dama akan wanan yaron ne da naji kuna waya dashi watau Ibrahim nake nufi nace eh daddy .
Yace to ina son kiyi hankali dashi kada ki yarda ki fada tarkon yaudaran shi ki mayar da hankalinki ga karatun ki shi yafi maki alheri kinji ko ?
Na amsa a sanyaye da eh daddy yace nagode Allah yai maki albarka nace amin daddy kukala da kanku don Allah kafin mu dawo nace insha Allahu daddy.
Har zai kashe wayan sai naji yace dani anty ki batasan na kiraki ba don haka ba lalai bane tasan da hakan ?
Nace insha Allahu daddy nakuma gode nai massalama na kashe wayan ina mai bin wayan da kallon mamaki.
Mamaki nakeyi may zai sa daddy yace don yai min fada da kada na bari kuma anty taji hakan.
Ban fahinci komai ba a ciki na dai aje wayan tare da karasa yaron da yai barci ko a lokacin.
Sai lokacin ne naga ledan da Ibrahim ya bayar a bani na jawo ina budewa naga turare ne na mata masu tsada guds uku sai set din agogon hannun irin na mata shima ma igiyan daurawa a ciki kala kala duk kayan da ka saka akwai kalarshi da zaka iya sawa dashi a ciki.
Abinda daddy bai sani ba idon anty biyu koda ya shigo tunane ya hana ta barci ta tashi tana nazari a ranta har yagama abinda yake yafita idon ta biyu tana kallon shi sai dai batan lanban waya dauka ba a wayan ta.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYABA HAKKIN AMANA YANA KANKI YAR UWA DON ALLAH NAGANIN KI, , , ,

31

Zaune yake a falo hankalinshi na saman system din shi da yake bincike a ciki.
Sai jinior dakebarci da ga gefen shi saman dogon kujera hankali kwance yaron daya gama rikici ya samu ya lalashe shi har yai barci a lokacin.
Ya mayar da hankalin shi sosai ga abinda yake yi a hankali take sauko zuwa inda yake zaune.
Sai da ta karaso gap dashi ne ta yaji motsinta amma hakan baisa shi ya daina abin da yakeyi ba.
Yau kwana biyu ke nan da ya dauki wayan ya ya dauki lanban da batasan ko na waye ba don haka take son ta tabbatar da zarginta a kan shi.
Sanin halin mijin nata da
Showing 120001 words to 123000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41 Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153