kike sakawa ba da yawa.
Tace wallahi Jinior zan gwagware ka yanzun nan da kai nake magana ko may idan can bana sha ai anan yanzu inda ake saya sai nasha yadda raina ke so tunda nasan karowa za ai muna.
Sai bayan na dawo ne ina dakina zaune a saman abin sallah Aisha ta shigo dakin tana gaidani da dawowa na tambaye ta babu dai matsalan komai akan bakin mu ko ?
Tace ba komai wallahi nan muka wuni dasu muna hira a falo sai dai Amirace ma nake ganin za, a samu matsala nan take fada min abinda ya faru da bana gidan.
Murmushi nayi bayan nagama sauraren ta nace kyale ta Aisha kada ki taba mata magana akan komai da zatayi ko ta fada a gidan nan ai gidan ubanta ne itama dashi take takama da hakan.
Tunda naji take taken Amira da zuwan ta sai na san yadda zan zauna da ita don mu rabu lafiya ba matsalan komai ga zuwan su.
Sosai nake basu kulawan da ya dace ba abinda yafi burge su a gidan kamar irin kayan motsa jikin da ke a wani daki inda daddy kanyi asubancin shiga yana motsa jikin shi a ciki.
Ko yaushe suna ciki wai suna motsa jikin su don suna daukan abin kamat kayan wasa a garesu ni kuma bana hana su yin komai.
Ranan da wuri na dawo gida don ina son da yamma inda zaga gari dasu don yanzu ina fita da kaina da mota cikin gari.
Bayan kowa ya shirya ne muka fito don zuwa wurare suga garin da idon su tun wurin shiga mota taso ta samuna rikici wai ita sai gaba zata zauna tare dani.
Dana fahinci may take nufi sai nace a,a ai ku duk mata ne don haka Nasir da Jinior zasu zauna a gaba Nasir da bai magana yaji dadi yace ilove you mum.
Tunda muka fita ana hira a mota tai shiru tana kallon ko ina ba wanda yabi ta kanta muna tafe muna hira ina nuna masu wurare a garin.
Daga nan mukaje wani park dasu nan na koma gefe sukai yadda suke so a gurin da zamu dawo muka biya Sahad store dasu ssayayya ssosai mukayi muka dawo gida duk jikina ba dadii karfin hali ne kawai nake don yaran.
Amma hakan bai boyu ba a gareni don sai da nakai kwance na danyi zazzabin kwana biyu na mike.
Kwana biyu dda jin sauki na kuma na kwashi yaran har asibitin mu muka shiga nakai Nasir yaga barack din sojoji yakara jin dadi sosai a ranshi.
Bayan mun dawo gida ne na huta sai na tuna da wani kayan unders dana sayowa Amira a hand bag dina na mike na nufi dakin da take don nakai mata kayan.
Waya take babu tantama nasan da mahaifiyar ta take wayan tana cewa mummy bakiga yadda ta koma bane sai sayayya take muna kamar bada kudi ba wallahi.
A daidai lokacin nai sallama a dakin kuma naji abinda ta fada nace ai waya kikeyi ashe ga wanan kayan naki a handbag dina na gani ashe ban saka leda ba damuka fito.
A yatsine tace dani kawai ok ta karba na fito daga dakin batare da saka komai a raina ba, abinda ban sani ba kullun cikin waya take da uwar tana fada mata abinda akayi da wanda tagani anan din.
Ashe da daddy zai wuto da Nasir sun yi gardama da ita tace bata yarda ba shikuma yace sai ya gani shine tai dabaran turo Amira tace sai dai idan dukka yaran zasu tafi yace aishi yafi buukatan hakan don tasan idan da Nasir kawai akazo bazataji komai ba gare shi.
Satin su uku tare damu uban ya shirya su suka koma gida ba don yaran sun so ba don ko ita Amira din taji dadin wanan zuwan da sukai min din.
Ranan da suka koma gida tun ranan ta fara tsiyayawa uwarta labarin irin abinda suka gano a can din.
Nasir dake zaune ranshi ba dadi yace kai munafunci baiyi ba wallahi yanzu ke duk irin abinda akai muna na gata har kinga wurin gulma anan ?
Ranta uwar ya baci tace dashi rufe min baki mara tunane kawai da baian ciwon kan shi ba an barmu anan cikin wahala ana can anajin dadi.
Yace yaushe ma daddy din ya zauna a gida wanda idan ya fita sai yamma yake dawowa gidan kuma in badon inta little mum takai mu yawo ba yaushe daddy ke da lokacin mu ma.
Bayan kwana biyu da karban girkin ta sai da sukayi ba dadi da Saaden kkan abinda yara sukace mata a kaina.
Nan ya rufe idon shi yai mata tas yace wallahi sai dai tayi hakkuri in bata gode ma abinda yake mata ba tana ina yi gaba shi yagaji da fitinan ta kullun.
Yace ashe dama kin tura yar kice don taje tai CID a can to kinji abinda ranki ya baci duk irin kokarin da akaiwa yaran ki amma baki gode ba yace ni na riga na aje zancen ki ko wallahi ba yau ba tunda baki da tunane.
Ya kuma samu Amira da Ihisan yai masu tas yace masu munafukai ai sunyiwa kan su don ba zasu kara zuwa ko ina ba.
Yaran sunyi kuka sosai sun kuma yi da sun sani da basu fadawa iyayyen nasu komai ba da suka gani acan Amira harda karya ta hada wuriin fadin zancen ta.

********* ********* *********
An bugo min cewa mahaifina baida lafiya hakan ne yasa na shirya zuwa gida don a yadda aka bugo min ma sai nake ganin kamar baida raine.
Tare da daddy muka tafi lokacin cikina yana da wata hudu a jikina amma ba a ganewa don in ba kayan aiki ke a jikina ba to kuwa baka rabani da hijjabi ajiki na.
Da dare muka sauka ban shiga wurin kowa ba tunda ni da nai tafiya ba wance tazo taro na sai duk suka share ni kamar ba zuwa nayi ba.
Sai washe gari da safe har mun shirya zuwa kauyen mu naga ba zan iiya share anty ba hakana ko banza nice kasa gareta ai.
Na shiga wurin ta mu gaisa tunda nai sallama tana karyawa ta dago kai muka hada ido gabanta yai wanii irin mugun faduwa don gaba daya na sake mata na canza kamar ba Raman da taa saani ba nata a baya.
Komai nawa ya koma na wayyayin mata ba sakin fuska nima a idona na gaida ita ta amsa min a gadarance.
Nai mata yaya gida cikin rashin damu yarona yana tafiya yana saye da dogon wando da riga mai dogon hannu da takalman shi masu tsada sai kamshi yakeyi gashi fari kwal dashi sai gashin kanshi mai zubin na fulani.
Ina rike da hannun shi ban sake shi ba don kada yai mata wani abin kuma nace zan shiga gida don baba ne baida lafiya mukazo.
Allah ya sauwa tace dani muka fice tabini da kallon harara takke ta dauko wayan ta ta buga wa yar uwar cin mushen ta tace wai Rahana kin koga abinda nagani kuwa ?
Nan dai take bata labari tace wallahi ki matse mata kada ki bata kafa kikuma fada mata ta tuna da asalin ta kada ta manta daa bazanki take rawa har yanzu.
Falon daddy na shiga iinda tun kan na karasa kamshina ya sanar dana ciki ina tafe falon suna ciki da matan shi duk su biyun a lokacin sai dai kamar magana sukeyi dashi.
Baba na ganin mahaifin shi ya fisge a hannuna ya nufi wurin shi ya dane jikin uban yana fadin daddy cikin gwalancin yara take uban ya gane mai yake nufi.
Nai masu sallama tare da gaishe suy ban damu da ko su karba min ba sai dai alama ya nuna sunyi mutuwar zaune a wurin.
Na juya nace cikin dan hausan na daya koma na yan Abuja yanzu daddy mun shirya muna son mu tafi ke nan.
Yace a, a Rahama ina tare zamu tafi ki dan bani minti biyar na fito please don ina son in shiga na dduba shi kinn san damun koma ni tafiya zanyi nace ok sai ka fito ina waje.
Har na juya naji hindatu tace da daya layan wuya inda an haihu da yawa aiko mijin bamu gani ma saui dai labari a haka dai za, a dawama da da daya kamar laya.
Kamar na wuce sai na juyo nace nagode maa Allah Allah yasa mashi albarka amma kila gado nayi na haihuwan da dasyan yadda naga wasu sunyi.
Ke wallahi kama kan ki kada kiga an rike maki maciji kina wasa da bindin shi bakifi kowa ba don kkowa ma yasan hanyan bin miji idann ya tashi ba sai an hada da yaudara ba da cin amana.
Bin miji ai isane duuk waccee ta shirya tazo mu tafi don ni nayi gaba , a, a Rahama kudai tsaya kuyi abinku amma kada ki sani a ciki.
Nace Anty Zulfa da wanda yai magana ai nakeyi ba dake ba daga haka nafice abina na barta nan tana kumfar baki a falon.
Bai dade ba sai gashi ya fito muka dauki hanya shi ke jan mu nii dashi ne a gaba yaran suna baya.
Sai da muka kusa fita garin kano naji yace watau ku mata halinku daya wurin hauka keda kikazo duba mara lafiya ina ke ina tsayawa hauka haka.
Nace cikin bacin rai daddy abin matan nan ya isheni ne wallahi mace haka da bakin son fita ko yaushe daga zuwa na jiya jiya zata hauni da balai wallahi a shirye nake da kowan su don nagaji da hakkuri hakana.
Bai kara magana ba muka dauki hanyar kaauyen mu a can ya barmu zamuyi kwana biyu mu dawo mu wuce mun samu jikin baba din yayi sauki sosai.
Yai masu goma na arziki yai muna sallama ya dawo ya barmu a can zamu ga yan uwa kowa sai fadin canzawan mu yakeyi.
Nai mamaki kwarai yadda innata ta fahinci ina da ciki ajikina haka da sauri abinda kowa bai gane ba sai ita don sai najii tace dani.
Amma tun kan ki yaye yaton nan kika samu ciki ko gabana ya fadi nadago klai nace hakanane inna tace Allah ya inganta ya rabaku lafiya nace amin.
Wanan katon na kwana a giidan mun mun sha hira da mahaifina kamar bashi ba munci mun sha daga nauin abincin kauye da muka dade bamu samu ba.
Amarya baba ta haihu sai haba haba take dani ta rasa inda zata sani ranan don daukaka da na samu ta haihu tana goyon diya mace itama.
A yadda na fahinta ciwon sugar ne ya kama mahaifina sai dai ban tabbatar ba na dai ce idan na koma sai su shigo asibitin mu a auna ashi a gani.
Bai so zuwaa amma da kyat na samu ya amince da zaizo naa saya mai kayan abinci na masu sugar nace ya fara ci mu ganii.
Kwanaan mu biyu hamza yazo ya dauke mu mun sha gata sosai a gida muka dawo kano da yamma na samu gida ya rikice don matan daddy sunce sai suma yaje dasu Abuja din don basu yarda ba case din daa na samu anayi ke nan don tun a mota Hamza ya fara kyankyasa min labarin halin da ake ciki.
Yace daddy ya haukace masu donn yace idan sukai tsiya ko kin gama ma bazaki dawo ba a raina nace dama hakan ne ai don nasan da wuya asibintin da nake su sake ni.
Ban bi ta kan kowa ba na shige part dina da mutane na gajiye tanata faman dawainiya damu cikin rashin gajiya don harda helen mukazo garin.
Sai washe gari da rana na shirya tsab zan tafi na gaida iyayyen mijina da yan uwan shi, kafinn in fita na leka anty a part din ta mun gaisa ta tambayi mai jiki nace ya samu sauki.
Nace zan tafi na leko su Hajiya har furin Abba zan shiga don kada taji naje yazama min matsala kuma a tsakanin mu duk da yanzu ban gudun shi idona ya bude ko.
Na juya nakai kofa tace dani Rahama sai na dakata don jin yadda ta kirani sunan da ya dade banji shi a bakin ta ba haka yasa na fahinci tana da magana mai girma ke nan.
Najuyo ina fuskantar ta batare dana koma na zauna ba tace ke yanzu kina ganin wanan cin amanan da kuka dauko yi muna keda maigidan shinee daidai komay ?
Bafa ke kadai bace matar shi yaran nan da suka dawo sun fada min duk abinda kike a can ban yarda ba sosai sai yanzu da idona ya gane min nagani.
Nace ashe dama ba hutun arziki su kaje min ba leken asiri ne yakaisu ke nan ?
Tace aiko sunyi bai baci ba don dukiyan uban su ne suke ci bana wani ba kuma don ke baki da hasara da daya ke gareki a gidaan shi yasa kiika sa uban su gaba da wawaso ko ?
Murmushi nayi nace dayan ma na gode da Allah yabani nima na kada nawa a cikin naku kinga suyi zumunci da yan uwan shi don nabar tarihi nima.
Au lallai naga kuwa kije abuja kada ki manta cewa duk abinda kike takama yanzu dashi nice dai din nan silar shi.
Nace ban taba manta halarci ba komai kankantar shi damani shiya nake shanye duk wani dacin da kike zuba min don ni ba butulu bace.
Yaushe kuma?
Butulci yafi wanan da kike min kuma ai ya baci nai maki rana kin min dare kina son rabani da miji ki kuma rabashi da diyan shi.
Nace cikin girgiza kai Anty tare na ganku har diyan ku don haka ni Rahama ban taba tunanen wanan kalman ba a raina don ni ba azzaluma bace kuma nasan ya kamata ako ina.
Wuyan ki ya isa yanka komai yanzu zaki iya fada min ai don kina ganin kin kai, ddon kina takama miji yana a hannun ki.
Nace cikin dan murmushi kamar maganan bai zafe ni ba babu inda nake don har gobe a karkashin ki nake.
Don nabu abinda nake maki a baya wanda na fasa yin shi ayanzu, na fannin biyayya sai wanda naga baki ra, ayin shi nake dainawa don haka girman ki da kimarki yana zaune daram a zuciya na ko yaushe.
Miji kuma ni a suwa da ya zama nawa in samu mutm da iyalin shi ince zan shige gaban su ni har yaushe na shigo cikin ku ne ma ?
Tace Zamu zuba tunda abinda kika zaba ke nan nace mu zuba alherin nan da kika saba yi min ina maki Allah ya kare mu daga sherin shedan.
Ban tsaya sauraren ta ba na juya na fara tafiya sai naji tace takamar ki dai da dayan da kika jefa a cikin mu shine kadaran ki waike kin haifi namiji ko ?
Akara haihuwan mu gani iin haihuwan ya zama banza ke nan a gidan kowa ta kwaso sharan ta tace sai anan zata juye shi a cika muna gida da diya barkatai.
Maganan yaci min rai sai kuma na tuna da abindake ciki na a yanzu wanda kowa bai san dashi ba sai ni da Zarah da ubangijin mu kawai.
Nai murmushi nakai hannuna ga cikina take ko naji cikin ya wani dan harbawa don tun ranan da mukai tafiyan nan mai nisa naji ya fara dan min motsi kadan kadan.
Ina fita mukai kicibis da Zulfa tace ashe kun dawo nace eh anty ya baby traana lafiya tace dani sai dai Rahama gaskiya ki mayar da hankalin ki akan abinda ke shirin faruwa a gidan nan bawai nai magana bane don wani abu a, a ni kawai dai nasan kowa kan shi ya sani.
Nace naa gode sai na dawo tace a dawo lafiya na samu yara na jirana a waje nan muka samu Jinior da Nasir sukace zasu bimu nace dasu mu tafi.
Duk da nasan fita dasu zai kawoo matsala gidan su daddy muka fara kai gaisuwa naji dadin yadda Hajiyan dadi ta karbe ni tana kuma yi min nasiha akan hakkuri da jama,a tace duk abindda zanji nayi hakkuri naci gaba da biyayyana don mai hakkuri yana dafa dutse yaci.
Shima Alhajin shi yai min nasiha akan rayuwa mai kama da wa,azi kan zaman takewa naji dadin fadan su a gare ni sai gidan mama laraba don ba nisa da gidan su daddy din.
Abban anty nakai mai shadda da turare da zuma ya nuna jin dadin shi da ganin mu sosaii yai min fatan alheri da saka min albarka tare da kara rokona nai hakuri da yar shi.
Har gidan Aisha da Fatima muka shiga daga can muka wuce zuwa gidan Zarah can muka bata lokacin mu gurin hira tare muka fito zuwa gidan Anty Amina da hajiyan harka na sada zumunta.
Mun shigo gida tun a get maigadi kewa Nasir kabi hajiya uwarka bata sani ba har anyi tashin hankali tsakanin ta da Alhaji a gidan nan.
Nace ai a gaban Amira muka tafi don haka ansan fitan mu dasu muna shiga gidan ba a dade ba sai na ji ihun yaran yana tashi sai dai ina ganin jinior ne ta samu gamin shi.
Ban shiga bada hakkuri ba sai fatan
Showing 291001 words to 294000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98 Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153