din.
Nai masu sallama na karaso dakin sai dana samu wuri na zauna da kyat hajiyan idon ta a kaina take cewa to ashe ku duk gidan a koshe kuke kowa yai nauyi ke nan a gun zulai nake ji wai itama Zulfa dan matashin ciki ne da ita.
Yanzu ke kuma gashi nagan ki haka a niki dake kamar wacce ma ta kusa haihuwa da alama dai.
Loman tuwon da hindatu zata kai a baki bata san lokacin da ya fado mata a zani ba, ta dago kai tana min wani irin kallon kurulla da sauri.
Na sauke wani dan gajeren murmushin ka saita nace da hajiyan sannun ku da zuwa tace mukan ai har mun huta kune da sannu ai yanzu.
Nace yaya kufan jikin naki ta dauki kofin ruwa takai a bakin ta sai da tasha ta koshi tace dani jiki Alhamdullahi naji sauki don na samu manyan likita sun bani magani ai.
Allah ya kara sauki nace da ita na juya gun Farida da ko kallo ban isheta ba sai abincin ta take ci nace da ita hajiya Farida ya kwana biyu tace a tambayeku ku manyan gari.
Nasan gatse taimin don har gobe duk inda ta zauna fadi take wai sabodani daddy yaki auren ta nai wa daddy asiri na aure shi.
Na mike da kyat tsaye nace da ita ni zan koma hajiya a huta gajiya Allah ya bamu alheri.
Bayan fitana Hindatu tace amma hajiya Rahama takai babban munafuka a duniya ida ba yau da kika fadi zancen cikin ta ba, ban taba jin kuma wani yai maganan ba a gidan nan.
Hajiya kikace harda Zulfa nada ciki ko mayne don ni maganan mamakine ma yake bani wallahi kai lalai akwai makiran mata a gidan nan ashe.
Bata zauna ba ta mike tabar falon zuwa bugawa mahaifiyarta waya ta sanar da ita abinda taji a gun hajiya yanzu.
Binta sukayi da kallo hajiyatace ita ke nan sarkin son kai bata taba son kowa da karuwa a duniya sai kan ta.
Ban koma daki ba wurin mama Altine na shiga tana zaune ta mike kafafuwan ta da tasbaha a hannin ta tana ja a hankali.
Na gaida ita tare da tambayanta mama kinci abinci kuwa ?
Nakai idona ga kulan dake aje a gefen da take zaune ta ce na dan tsakura Rahama yanzu na gama tunane duniya ta addabi zuciyana.
Sai yanzu nake ganin hikimar marigayiya na yin abinda ta aiwatar a baya gamay dake.
Yau da ace baki gida nan Rahama ina naga kafan shigowa cikin wanan daulan duniyan haka ?
Ai watakila dako yan jikokin nawa ma bazan gan su ba balle labarin su amma kinga yanzu yau gani zaune a gidan cikin mutunci kamar yar tawa na da rayuwa.
Sai kawai ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi nima dai kukan na saka amma haka nake lalashinta ina share nawa hawayen.
Ina fadin haba mama yanzu ke kina wanan kukan idan yaran suka gani abin zai dawo masu sabo a rai don ko yaushe a cikin wanan radadin suke suna dai shanyewa ne don irin kulawan da suke samu a gun mahaifin su.
Ta share hawaye tace a gunki dai Rahama shi namiji ai bashine mai alhakin kula da yara ba sai mace uwar goyon su dake gida ko yaushe.
Rahama ba don Allah ya hada yaran nan da ke ina zasu iya zama a gidan nan cikin wa yan nan matan uban nasu haka.
Murmushi nayi nace aiko a haka zasu zauna din dasu dole tunda uban baida wasa wurin harkan iyalin shi.
Tace dani Rahama Allah dai ya jikan Saade nace amin mama tace anya yaran nan kuwa zasu iya biyo halin uwarsu a dunitan nan yarinya da abinta bai rufe mata ido ba ga son zumunci da sanin darajan dan adam.
Nace ai anty ta dabance wallahi samun mai hali irin nata sai an tona don ba kowa zai iya abinda takeyi ba sai wanda Allah ya ba irin rayuwan.
Mun dauki lokaci muna hira da ita na marigayiyan har akai kiran sallah magariba sai muka tashi don yin sallah.
Da dare daddy ya shigo gaida zuwa sun dan dade suna hira da ita ya mike ya yai mata sallama ya fito ya dan tsaya wurin yaran suna hira dashi.
Ina daki zaune ya shigo da zaifita yana cewa yaya dai ko duk gajiyan ne haka dama kyale ki nayi ki tafi ki dandana ai.
Yadda kike haka har kice zaki tafi wani buki a hakan dake rukuruku kamar wani abin dole can.
Na dago kaina nai murmushi nace daddy bukin Zarah ce fa ida banje ba tunda ina iya zuwa ai ban kyauta ba kafa san yadda zarah take da kokari itama.
Rashin zuwa na zaisa bataji dadi ba a ranta sai dai baza ta iya fada min bane don haka gara kawai dana daure na tafi ai.
Yace ai yanzu gaki kina mukurkusa ke kadsi a daki, nace ai nz huta har barci saida nayi da muka iso ban wani wahala sosai ba ai.
Nace ga mama nan munzo da ita ta dan huta kwana biyu tare da mu ta dabe muna kewa.
Yace aiko kin kyauta wallahi dama tana cikin raina sosai don bai kamata mu kyale ta ba haka a can sai taga don yarta bata raye ne muka fita batun ta.
Don Allah nasan ba sai na fadi ba ma abata kula yadda ya dace kada taga don yarta bata nan taga banbanci koda yake kema ai uwar ki ce ita din.
Nace daddy indon wanan ne kada kaji komai a ran ka don mama banda abinda zan saka masu dashi a duniya nan don sune sillan zamana haka a rayuwana.
Murmushi yayi ya juya ya fice daga dakin na kwalawa Aisha kira tazo ta bani wani abu don tashi aikine gare ni wasan dadi.
********* ********* *********
Washegari da kaina na shiga kitchen ina shiryawa su hajiya da mama abinci don nasan idan na barwa yaran bai wuce su yi tea da irish da kwai kawai su tashi.
Miya nake hadawa don har na gama dafa abinci hankalina yana gun abinda nakeyi don haka banji shigowan shi ba sai muryan shi da naji daga bayana yana fadin.
Wai may kike yi haka a kitchen da kan ki na dan juyo gare shi cikin dan murmushi ina fadin barka da fitowa ina kwana daddy.
Ya karaso yana fadin yaya gajiyan tafiya koda yake naga alaman baki gaji ai tunda ga ki a kitchen da safen nan.
Nace wai abinci nake kokarin hadawa su hajiya mai dan nauyi don nasan yaran nan idan na barsu shirmay zasu yi min kawai.
Ban san cewa ya karaso har inda nake tsaye ba sai jin shi nayi ya rungumoni ta bayana tare da sauke hannayen shi a saman cikina yana dan tabawa a hankali.
Ajiyan zuciya na sauke a hankali nace daddy baka gudun wani ya shigo ya samay mu a hakan nan yanzu.
Yace and so what, ?
Idan wani ya shigo din wata na rike ba matana ba, ban rike ki ne kike a haka murmushi na karayi na ce kai daddy dai.
Hannun shi ya kara saukewa a saman wuyana ban san lokacin da na sauke wani irin ajiyan zuciya ba a hankali.
Nace daddy kada fa wata daga cikin matan ka su shigo nan kasan bani ce dakai ba yau gaahi kuma kazo kana rike ni haka ?
Yace matsalan ku ke nan wallahi kishi to na sake ki matsoraciya kawai na dan sake murmushi nace yafi min sauki ai.
Ya dan ja baya daga inda nake ina rage gudun gas din da nake amfani dashi din sai jaji yana cewa yaya zamuyi ne da zancen hajiya don bamu samu ganin wani babban likita ba.
Don ganin su yayi muna wuya andai bata magani shi take amfani dashi har ta danji dama sai kuma gashi daren jiya kuma abin ya dawo mata.
Nace yaya take jine wai ?
Yace tace wani abu ke tsaya mata a ciki kamar da yana mata ciwo wani lokaci kuma har yakan ma hana ta tafiya.
Murmushi nayi nace at this age da take take jin wanan gaskiya ina fa sai an mata aikin shi zaifi don ko tasha magani ya bari watarana zai iya dawo mata da karfi yai barazana a gare ta.
Yace wai Rahama may zai hana ki dubata a nan gida ki gani ko zaki fahinci abinda kyau ?
Nace da sauri wa ni daddy?
Kana ganin ma hajiya zata yarda da aikina har ta bari na dubata gara kawai kuje asibitin a dubata a can nima zaifi min sauki wallahi.
May zai hana ta bari a dubata yadda take fama da jiki haka kawai ki gama zanzo mu shiga gunta sai ki dan fara dubata don Allah.
Daddy banki ba amma dubawa a gida kamar sabawa doka ne kaga ba wani abin gwaji da zai nuna ga ainihin abinda ke damun ta din.
Yace nace ki dai duba min ita bashi ke nan ba ban son mu tsaya muna gardama haka don Allah nace shike nan bari na gama zuba abinci nazo.
Daga wurina wurin hajiyan nashi ya koma yake sanar da ita cewa zan shigo na dubats yanzu idan na gama aiki don haka ta shirya.
Da sauri ta dago daga kwance tace wa ni nice Rahama zata zo duba har wacce Rahama din yau she ta zama wata likita can da tai ilimin gane ciwo na.
Raliya dake hada mata tea tace ai shine gara dai aje aga babban likita zai fi yadda take ji din nan.
Fada mashi dai ke yar albarka amma haka kawai ka dauko min wata matar ka can kace wai ta dubani yo Allah na tuba kai da ka dauke ta wata tsiya sai kaje ta dubaka yadda ta saba amma bani hauwa ba kan.
Sai Raliya ta sake fadin ga dai likitoci manya da suka san aiki ko bayani kai masu sai sun fada ma matsalarka.
Ke rufa min bakin ki banson raini noses kawai ke kin san abinda ta sani ne ko aikin ki ne hakan kada na sake jin bakin ki a cikin maganan nan.
Tace Allah ya baka hakkuri daga fadar gaskiya sai a lake min kuma, yace rike gaskiyar taki na fada maki.
Ke yi shiru gaskiya ne bai son a fadi ranan littani ki shirya ki kaini asibitin kin ji tunda shi ya nuna ya gaji da zuwa.
Yace haba hajiya akan may za gaji da alamarin ki tace baga shiba kuwa kazo min da wani zance watau ni gani gidahuma ko na zauna matar ka tai min shirmay ta kashe ni.
Yace haba hajiya aikin nan fa aikin ta ne kin sani sai dai idan wani manufa ne zai hanaki bari ta duba ki din don dai nasan Rahama har case din da yafi naki ta na dubawa don yanzu haka ma har naji ta fadi maysalan ki ko da komai.
Taceina ruwan gobe da nisa ta zama yar magori ke nan ashe tun ba a ga mai ciwo ba har an san matsalan shi.
Bai yi magana ba ya mike ya bar dskin tabishi da harara tace ka zauna yarinya karama tana juya ka yadda taso har ta kawo gare ni don raini.
Sai lokacin Farida tai magana tace wai ma hajiya har wata Rahama ne can zata tsaya dubaki wai yaushe har tai wani karatun kwarai banda galihun da yai mata.
Raliya tace ashe kema kin gane ni fa nasan komai kallon su kar nake kawai ana muna barazana wai ga likita a gida.
Ko aikin ma ai sai anga daman fita ake fita yin shi likitan kwarai ne zai ta zama a gida ba shiga gun aiki to ire iren su sunyi yawa a wirin yan galihu.
Amira ce ta shigo da sallama tana cewa a, a hajiya ashe dai sauki yazo ga shayi naga zaki tausa da bread.
To ga abin karyawa inji mummy mu tace na kawo maki saura ki lashe kwanon tace cikin tabe baki har wani abincin zan lashe kwanon akai abincin naku da maggi da mai ke yawa cikin sa.
Sai su Farida da Raliya suka kwashe da dariya kyeta hajiyan tace may kuka dafa ne wai nasa bai wuce shayi da kwai dai shine cimar naku ai.
Amira tace wa ai mummy mu tafi da nan bude kigani mana nasan sai kin ci ko may ye ma tace ja,ira nice zan bude bude dai naga shirmay naku.
Ta fara bude kulan tueon semo sai kular shinkafa da miya da kaya ganishing a cikin sa sai kular miyan yauki da wani na cow leg sai kulan miyan kaji naman yanka manya manya.
Tace ja,ira ashe kin san may kukayi kike min shakiyanci dama kamar kun san shayin nan ya ishe ni wallahi tace mummy mu cefa tai maki shi da kanta keda hajiyan maman mu.
Tace shine tai barnan nama haka daga inda Raliya take zaune tace ai kin san nama a gidan nan ba matsala bane da yakare kawo masu wani za, ayi .
Sai hajiyan tace dole ma tunda baida aiki sai na zuba masu dadi suna ci Amira tace cikin tsiwa kowa ma ai yana zuba mai tunda ba fridge din gidan nan da babu nama irin namu a cikin sa don tare ake sayowa kowa lokaci daya tana fadin haka ta mike tabar su tace cikin daga hannu bye bye aci lafiya ko.
Ni dai banga yazo ba ni kuma banyi magana ba sai dana gama komai na shirya na shiga gaida ita ban dade ba na fito don na samu tana cin nama Farida kuma yadda naga ta daure fuska ban ko bi ta kan ta ba ma gaisawa mukayi sama sama na fito abina.
********* ********* *********
Ranan monday ban samu fita ba ina gida Raliya ta kwashe ta zuwa asibitin bayan daddy ya basu kudin komai yadda zai ishe su don ya tafi lagos aiki.
Sun tafi sun ga likita bayan tayi bayanin komai ne sai likitan ke cewa zan tura ku wurin doctor Rahama Abdullahi ta duba ku don wanan fannin ta ne kuma itace zata tsaya tai maku yadda ya dace da kyau.
Ya kira massinger shi ya kai min file din su office dina yace ku bishi zuwa office din ta suna zuwa ake cewa dasu yau bata fito ba wai bata jin dadi suka koma gun mutumin da sukafito.
Yace da zakuyi hakkuri har tazo da zaifi akwai masu iya duba ku ba wai babu ba amma ita tana da experices kan wanan matsala na mahaifa so sai don a germany tai karatun shi.
Kallon juna sukayi da yai maganan sai kuma sukaji yana cewa ina ga matsalan cikine don tana da tsohon ciki idan ba zaku gaji ba zaku iya dawowa zuwa gobe nasan zatafito don tana da aiki da zatayi gobe.
Sai dai ku fito da wuri don ku ganta kafin ta shiga aiki gani ta yai maku wuya.
Likita yanzu kana nufin ba wani da zamu gani bayan ita din tunda bata nan ya da bugi table yace akwaisu da yawa ma sosai kuwa.
Bari na tura ku wurin wata ita naga tashigo dazun sai dai zaifi kyau kuga ita wanan likita din dana fada maku ne.
Ya tura su wurin doctor Lami tana tare da wata take cewa at dis age wannan case a gare ta da dai suga doctor Rahama Abdullahi naga zaifi kyau.
Kara kallon juna sukayi sai ita doctor din da sukazo gunta tace mama matsalan ki fa aiki za ai maki don samun lafiyan ki.
Aiko ta mike tashiga fada ta cewa Raliya su tafi don tana ganin kamsr basu san aikin su ba ma a nan.
Tun a hanya daddy ya kira Raliya yana tambayan ta sun tafi asibitin ne take cewa eh gamu hanya ma dawowa gida yake cewa da ita kun ga likitan ko sai tai shiru can kuma tace dashi eh mun gan shi .
To may sukace daku ne akan ciwon nata tace gadai hajiya din sai ta mikawa Hajiyan nashi wayan ta kara a kunnen ta.
Ya gaisa da ita tare da tambayanta yaya jikin jata take cewa dashi da sauki yace may likita yace daku ?
Tace wa yan nan mashiririta may suka sani asibiti kamar wanan wai ace muga Rahama itake da masaniyan irin matsala na fiye da kowa.
Yace ban gane ba hajiya tace ba zaka ko gane ba kaidai don wata yar banzan yarinya ma cewa tayi wai aiki zasuyi min.
Nan yace dama ko Rahama ta fada min haka na tace sai sunyi maki aiki don samun lafiyan ki.
Tace bakaji ba dama ai nasan bakin su daya hadin baki sukayi da ita wai ace dole sai na gan ta don ta nuna min ita din takai ta isa.
Yace hajiya yanzun dai zan dawo yau sai a san abin yi tunda abin na matsa maki haka zan zo muje aji ko may ye hakana.
Allah ya dawo dakai lafiya tace dashi sukai sallama ya kashe wayan shi
Showing 399001 words to 402000 words out of 456145 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134 Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153