haka kamar kumshin tsohuwa.
Idon su a kaina har nafito nida Farida daga cikin motan Farida na zagin su sai abin ya bani dariya.
Kam uban nan lalai ma wanan shegiyar yarinyar ta samu guri wallahi yaushe ne ma har ta iya mota a gidan nan ne wai ?
Ji shegiya kamar yar tsana sai karfin tsiya yar iska wanan idan ban kawar da ita gidan nan ba sai tafi uwar dakin ta iya sheri wallahi.
Zulfa tace bari mu zuba da ita a gidan nan mugani sai nayi maganin ta tabar gidan nan adole ta samu arziki tana ci kamar na uban ta.
Shima na zaci zaiyi zuciyar nashi yace tabar maigida ne wallahi amma sai shiru kake ji ba wani motsi bai dauku maganan da zafi ba.
Yaya zakice nai dauka da zafi ba da zai tafi ya sallamay ki ne ke ni fa tun rana yaudauki zafi dani sosai wallahi ko kallon gefen da nake bayayi ma.
Kinga kuwa ya dau maganan ke nan kin san halin shi ai bai magana sai dai ta kuntatawa mutum kawai.
Muna kawowa sai tin da suke muka gaidasu muka shige abin mu ban tsanmani sun karba muna ba ma mu dai mun shige abin mun barsu a gurin suna shewa nasan zagina sukayi.

****** ********* ******
Ranan da aka tashi da azumi weekend ne baka jin motsin komai a gidan uguwan ma da garin tsit yake kowa na gidan shi ana barcin safe.
Nima sanin cewa ba school kuma ba wani aiki tashi nayi na hadawa yara break din su nakoma na kwanta abina don nacewa gajuye tunda asuba tayi kwanciyan ta kawai sai rana muyi aikin mu.
Can cikun barci nake jin muryan anty tana tayar dani na bude udona tana tsaye akaina ta caba kwalliya wanda nasan sai Daddy yana gari take yawan kwalliya haka nasan kuma baya nan.
Na mutsuke idona tare da amsa mata namike tace to tashi kina nan kina ta barci tundazu ga abin arziki ya samay ki.
Nace ni anty tace kefa taso muje muga motar ki da daddy ya zo maki da ita tana waje nima yanzu yazo yake fada min haka.
Nace anty Daddy ya dawo ne kuma yazo min da mota kikace fa ?
Taso don Allah ban son yawa surutu ina azumi na muje mugani kafin wasu su rigamu ganin ta.
Gaba daya part din muka nufi gurin murna da sowan mune ya hankaltan da mutane gidan suka fito sai gani sukayi muna kallo mun shiga muna dubawa a hankali .
Mamaki suke tsakanin ni da anty motar waye yadda muke dauki sun rasa may motar a cikin mu.
Haka yasa sukai shawaran cin ma maigidan suji waya saya wa mota muke murna haka yan part din mu.
Suna zaune da Bashir a falin shi suka shigo falon Zulface take cewa munga ana murna ne wa aka sayawa mota gidan nan.
Yace wani ya turo ku ku tambayeni hakan ko may hindatu tace muna dai son sani ne tunda muna gidan yace ok motar farkatace da kukace na sayo mata shi.
Wanan ma ai rashin adalcine mu matan ka baka saya muna ba muna binka ka canza muna shi zaka sayowa wata banza can da ita.
Rahama din ce banza Zulfa ba banza take ba may take din matakarce ita da zaka saya mata abinda mu baka saya muna ba .
Ba matana bace amma a yanzu tunda ana zargina ina son ta shiya nake son kawar da zargin ya zama gaskiya koda kudin ku na sai mata mota da abin zai damay ku kuma bayan da bakin ku kun fadi ina son ta ne.
Shiru kowan su tayi sai bashir ne kecewa yanzu dai ba wanan ba kubar wanan zancen haka don Allah don gaskiya baku kyauta ba sanin ko waye mijin ku bai kamata wanan zargin da sheri yafito daga bakin ku ba haka.
Nan dai Bashir yai masu fada akan basu kyauta sai cewa sukayi daga karshe sunji sunyi kuskure amma zancen mota fa yaya za, ayi.
Yace ba zan saya ba don banda niyar haka idan kuma wata takara min zancen mota a gidan nan ranta zai baci sosai a gidan nan.
Wanan magana mu muna can muna murna sashen anty su kuma masu gidan na can suna faman fitina a tsakanin su har takai iyayye sun shigo ga maganan.
Mama Zulaine ta biya ta kira mama laraba sukazo gidan tare jin da mama larabane yasa shi dawowa gidan daga inda yake.
Suna nan zaune har yashigo falon shi suka shiga yace akira mai anty tazo bata bata lokaci ba ta tafi.
Nan mama Laraba ke tambayan may ya kawo haka zaka sayawa Rahama motar shiga matan ka baka saya masu ba?
Shiru yayi don ran shi a bace yake sosai a lokacin mama laraba ta sake maimaita tambayan ta yace mama kudina ne kuma ra, ayina ne hakan shike nan.
Mama Zulai tai farat tace shike nan zance ya zama gaskiya dama yariyar nan zaman cin amana kawai aka kawo ta yi a gidan nan don samun wuri harda samun matan gida da duka.
Ke Saade duk kece da wanan makircin kin san komai kan yarinyar nan amma kika dauko ta kika aje ta a gurin ki takoma baya tana ci miki mijin ku ta baya.
Haba mama wallahi haka ba halin Rahama bane ni wanan yarinyar banga abindata tsare masu ba a gidan nan haushinta kawai suke ji don zaman ta a guri ai ba Rahama ce kawai a gidan zaune da mu ba.
Ni may yasa ban taba damuwa da duk wani dake karkashin su ba sai sune zasu damu da yarinyar mutane .
Ai haka ma zakice tunda ta riga ta asirce ku a gidan tana yadda take so yarinya haka fikiu fikiu da ido kamar ita ta tsara kan ta har zaki jawo wa kan ku wahala da ita.
Mama wanan maganan da kuke yi fa yana kara tunzura ni ne wallahi mota dai ni naga dama na saya mata ban damu da duk wanin abinda wani mutun zai fada akan haka.
Zargin kuma da suke min na barsu da Allah shi zai saka min ni da wanan yarinyar.
Salati mama Zulai ta saka tana cewa yanzu akan shedaniyar yarinyar nan kake jawa matan ka Allah ya isa Alhaji ?
Yace ai cewa nayi idan sheri sukai min idan kuma ni neman ta nakeyi ai kinga a kaina abin zai dawo min ko ?
Haka dai suka zauna basu fahinci komai ba don sun rasa gane kan shi ga baki daya nan zulfa ta shiga surfa min zagi ni da anty tana ja muna bakar Allah ya isa karshe ficewa yayi ranshi na mashi kuna ranan dai haka akai buda baki rai ba dadi a gidan.
Yana zaune yayi buda baki a falon shi wanda ba wani abin buda baki aka shirya mai ba saka makon mai girkin na cikin fushi tana son jan ajin ta a matayin ta na mace gareshi.
A kasa yake zaune saman kafet din dake tsakiyan falon nashi goran ruwa da fruis din daya sayo a gefen shi.
Kan shi ya dafe da hannu daya saboda kan nashi ya dau zafi a lokacin ji yake kawai ya saki matan nashi ya huta da wanan tashin hankalin nasu dayaki ci yaki karewa garesu.
Wata zuciya daga ban gare zuciyar shi ke bashi shawara ya sallami Rahama kawai daga gidan ya huta da zargin dake damun matan shi akan ta.
Na yau daban nagobe daban duk akan yarinya daya abin ke faru idan kaji fitina akan wani dake gidan.
Bayan duk halatcin da yarinyan ke masu agidan akan diyan su zuwanta yasa ta yiwa diyan shi tarbiyan da iyayyen su suka kasa basu a baya sai bakin kishi da suka sa agaban su.
Yanzu yaro daya gan shi zai gaidashi suna karatu na addini komai tare da yaran takeyi bata daukan kan ta wai ta girmay wa yaran don kawai ta saka su a hanya madaidaiciya.
Yace a hankali shi kadai zaune a mamakeken falon shi Ya Allah ka agajeni kai min mafita akan wanan matsalan a gidana.
Idan nace kai tsaye Rahama ta barmin gida ban kyautawa Saade data dauko taba a gidan kuma tana taimaka mata nima nasan da hakan.
Matsala dai dayace rikicin su da matana ko yaushe wanda kuma idan an bibiya sune ko yaushe basu da gaskiya akan fitinan.
Fitinan da sukeyi ga Sa,ade yanzu ya koma gun yarinya mutane wanda ba komai ke kawo shi ba sai cin fuskan da suke kokarin yiwa wacce ta kawo ta gidan a gaban ta.
Wanda koma waye ba zai lamunci hakan ba a gaban shi don ba kowane keda hakkuri irin na ita sa,aden ba yanzu.
Kawai barin su zanyi suci haukan su ai dawowa zasuyi a hanya su fahinci gaskiya da kan su.
Haka dai ya kare zancen zuci da mika al, amarin shi ga ubangiji tun da shine ya kaddari zaman su haka a gidan.
Sallaman Saade da iyalin ta sunzo gaida shi da shan ruwa ya katse mai tunanen shi.
Kusan nice tafe a baya dauke da Jinior a hannuna nan muka zube kasan kafet muna mashi barka da shan ruwa daddy.
Ya amsa cikin dan sakin fuska yana cewa kun sha ruwa lafiya kowa yace lafiya lau daddy har dasu Amira da basuyi azumin ba cikin mu.
Ganin babu komai na shan ruwa a gaban shi yasa anty cewa yau baka samu abin buda baki ba ke nan an dau fushi dakai ?
Inajin haka namike inacewa yaran suzo mu tafi sai naji yace miko min jinior nan na dan taba shi na karasa inda yake na mika mai yaron ya karbe shi yana cewa dat is my boy.
Na durkusa nace daddy nagode Allah ya kara rufa asiri yace amin sai a dinga tuki a hankali don kin san garin akwai cunkoson motoci da yawa banda tukin ganganci don Allah.
Kuma ki mayar da hankalinki ga kararun ki don ki cin ma burin ki na zama likita dakike so ki taimakawa wasu kema nan gaba.
Na sake tausa muryana kasa nace nagode daddy yace ba matsala sai ki yi ta hakkuri da kowa agidan don a zauna lafiya insha Allahu nace muka fice daga falin nashi nan muka bar anty tare dashi.
Muna fita tace Allah dai ya kawo saukin wanan fitina haka mutane basu son azauna lafiya agida kullun da sabon fitinan da suke fitowa dashi idan gari yawaye.
Na kuma fahinci duk sheri da makirci yana gurin Zulfa da tana boye halinta amma zuwan yanzu tafitar a fili da halin ta sai wani hafin kan sheri da sukeyi a tsakanin su don ganin sun cutata min a gidan nan.
Yace hadin kan banza tunda ko kan su basu bari ba ina hadin kan yake anan ?
Besty nabaka shawara kaki dauka ne suluntion daya ne shine ka auri Rahama shike nan amma kaki nifa ni na san hikimar dake cikin ha, , ,
Don Allah Saade ki rabani da wanan shirmay naki naji da abindake agabana please ?
Kai ke ganin rashin dacewan haka amma ni nasan da zaka zauna kai naziri dakyau ka hango abindana hanga baza ka ki shawara na ba ai.
Nan dai ta mike tana mashi sai da safe ta fice daga part din yayin da yabi bayan ta da hararan jin haushin ta a lokacin.
Na yakai kan shi saman kujeran da ya jingina bayan shi tare da lumshe idanuwan shi yana tunanen wai ita sa,ade wata irin mace shin a duniya ?

********* ********* *********
Wanan satin haka azumin ya kasance muna agidan farkon shi babu dadin rai ga matan gidan da maigidan duka.
Sai ranan da anty ta karbi girki ne yasan ya samu taron watan azumi da biyan bukata don mun hada mai kayan buda baki kala kala an jera mai.
Ita kuma tayi kwaliya irin daya kamata na taron maigidan a gurin ta yadda ya kamata haka ya man ta da damuwan shi.
Koba komai Saadatun shi, na son farin cikin shi akoda yau she da itace suke da matsala bazata barshi haka kamar mara galihu ba a gidan shi.
Tana zaune a gefen shi inda ya zauna daga gefen ta yana saye da jallabiyan maza daya sauya daya shigo gidan daga gurin sallah asham.
Ya kalli irin kayan buda bakin da aka girka mashi inganttaciyar cima ne na zamani aka hada mai mai warawarw jinin dan adam don wanan watan mai alfarma.
A haka muka shigo gaida shi wanda duk yamma idan yana garin da watan azumi kowani part zasu shigo yi mashi barka da shan ruwa.
Namiji ke nan gashi da karamin shekaru amma Allah ya bashi wanan girman haka mata har uku mai a gida kowace tana ji da kanta kuma duk zaman shi sukeyi.
Zaune yake kamar kullun idan zai sha ruwa a kasa da alama ya gama buda baki koda muka shigo falon don yana dan kishingide ne yakara bayan shi ga kujera.
Ita kuma anty tana zaune daidai saitin kafan shi suna fuskan tar junan su taba kofan shigowa falon baya.
Yaran nasu ne agaba sai gajiye da Farida dake bin su kamar kullun nice a baya koda kuwa da anty zamu shigo gurin.
Daga can dan nesa kadan nida gajiye da Farida muka tsugunna muna gaida shi ina dauke da jiniyo a hannuna .
Idanuwan shi na akan mu lokacin da muka tsugunna muna mashi barka da shan ruwa ya amsa yana kokarin kawar da idanuwan shi garemu.
Anty ce ta juyo garemu tana cewa aa shi wanan ai na dauka ko yayi barci ne fa ?
Gajiye tace idon shi biyu yanzun dai suka gama kwasa da uwar dakin shi wai sai ta bar sallah ta dauke shi.
Miko min shi nan inji anty na nufo ta da yaron ta mika hannu ta dauke shi daga gurina tana fadin kaji ba dan gatan maman shi harta sauya ma kaya kuma kana mata rikici.
Gajiye ke fadin hajiya a rage kayan ne a shiga dasu ta juya tana kallon shi ya lumshe ido yana kada kafa dayan daya daga a hankali.
Tace dashi a kwashe kayan ne yace tare da bude idanuwan shi No abarshi in an jima zan dan kara ci ne.
Sai dai wanan abincin a tafi dashi nagama dashi ke nan yanzu tace wa gajiye a kwashe gajiye ku tafi dashi idan bazakuci ba a mikawa maigadi kada ya lalace a banza.
Rama kin ko ci abincin kuwa don ke idan kina ciwo bakya son cin komai, da sauri ya bude idanuwan shi yana kallon mu tare da tambaya may ya samay ta kuma ?
Tace dashi kanta ke ciwo tunda rana take kwance kasan ta da karfin hali haka ta tashi tai girkin nan da ciwon kan.
Ki dauko mata panadol a daki tasha ko zai bari ya bata amsa tace don Allah dan jirani Rama wanan mai zukan ya kama nono ko.
Shi da kan shi ya mike zuwa dakin shi sai gashi da magani a hannun shi ya miko min tace ga ruwa nan kisha don nasan ba sha zakiyi ba idan kin fita.
Ko haka kikeson zama likita kina gudun magani sai son yiwa wasu allura kikeyi ke.
Na bare maganin a gaban su ina hadewa Zulfa tashigo da yarta wani kallo ta watso min daga inda nake duke ina shan magani Hanifa tayo kaina ta rugumay ni tana cewa anty zan kwana a gurin ki kimin story.
Da wani karfi uwar ta jaye hannun yarinyar a gurina tana fadin mara zuciya kawai zonan na rabaki da irin tsiya bakya ji ke.
Wai ke zulfa may ye matsalarki ne yarinya baki bari tayi yadda take so ne wai may ye a cikin haka kuma tace ansha ruwa lafiya?
Tana rike da hannun yarta gam ajikin ta ta samu daya daga cikin kujerun ta zauna.
A hasale ya karba mata na juya zan fita jinior dake shan nono ya saka kuka anty take cewa dawo dauki abinki kada ya damay ni.
Dole na juya na karbe shi muka fita ashe bayan fitana sunyi kaca kaca kan abinda zulfa din tayi a gidan.
Take cewa babu ruwan shi abarta da yarta ita ta haifi abinta tasan zafin abinta don haka ya kyaleta lumshe idon shi yayi yana mai jin kunan abinda suke mai a ranshi.
Ya kyaleta ne wanan lokacin don idan ya tsanan ta magana za, a ce akan Rahama ne yakawo fadan ga zargin da ke tsakanin shi da yarinyar.
Washe gari tun asuba na taya gajiye gyaran part din mu bamu kwanta ba sai da muka gyara komai muka wanke kayan abinci fariida kan bata saba da irin aiki haka ba ta koma ta kwanta kafin ai sallah.
Bayan mun yi sallah gari ya dan haska muma muka kwanta don mu rage lokaci muyi barci.
Barci sosai nakeyi hankalina a kwance can cikin barci nake jin ihu na tashin hankali a gidan da kyat na bude idanuwana dake da nauyin barci ihun a cikin gidan akeyin shi kuma ba mutun daya ba kamar ma harda namiji nake jin ihun.
Cikin matsanacin tsoro da firguci namike zaune farida ma dake gefe na tamike ai muka kwasa
Showing 105001 words to 108000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36 Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153