ni dai haka tace na fada maki idan kin fito tace ashe akwai tsiya ko a gidan nan.
Wa take nufi zai dinga zama mata gadin gida ita tana zuwa gun aiki kai lallai namiji muna fuki ne wallahi.
Yanzu shi abin da suka kulla ke nan dama ban sani ba sai kawai naji zancen daga sama kawai wai an fita gun aiki.
Ni bazan dauki wanan tsiyan ba wallahi ya dawo naji ai ba ita kadai tai karatu ba da za, ace wai wani aiki za, a fita.
Za, a dai fake ga sabara a halbi barewa kawai da sunan aiki ba wanda za, a daukowa cuta a lakakawa muna zaman zaman mu.
Ita dai Aisha ta wuce tabarta tana faman fada don ba sa,ar ta bace balle ta tsaya bata amsa kan maganan ta.
Ta kasa hakkuri ta dauko waya ta kira daddy inda take shiga ba nan take fita ba yace cikin tsawa kan ki daya kuwa Hindatu ?
May ya kawo wanan magana haka da kikeyi ba dadin jin ni dai ke auren Rahama da yarda na kuma ta fara aiki ba gaban kan ta tayi ba.
Tace ai dole ka yarda tunda angama dakai sai abinda tace dakai takeyi yace ita Rahama din tace ita mana.
Yace ashe takai mace ke nan a wurina tunda sai abinda ta sani nake yi a rayuwana yana fadin haka ya kashe wayan shi don bai iya sauraren haukan da take mai lokacin.
Na samu karbuwa sosai a gun aikin anbamu office din mu kowa yasan inda zai zauna an kaini fannin mata don dama a kan su nai karatuna watau ganycology.
Ranan wa yanda muka saba dasu cikin likitocin suke ta muna murna da samun aikin da mukayi tare da su.
Matar farko dana fara karban matsalarta tana fama da bleeding na tsawon kwanaki ban sha wani wahala ba na gano case din ta bayan na tura ta ai mata wasu awo daya dace ayi kafin na gane case din ta din.
Na bata gado itace pecent dina na farko don haka ta samu kulawa sosai a wurina don nai mata abinda ya dace ta samu har inga yadda case din zai tsaya wanda ba komai ke damun ta ba sai peibros dake damun akasarin mata a yanzu idan jinin bai tsaya ba dole muyi mata aikin shi.
Don matar ta riga da ta manyanta ta haura shekara arbain ko da haihuwa dole ne a cire mata mahaifan ta don kada ya zama mata cancer nan gaba.
A gajiye daddy yazo ya samay ni yana zaune cikin motar shi na karaso wurin da yake ya bude min na shiga na zauna yake cewa dani a gaida doctor Rahama da aiki.
Nai dan murmushi nace dashi ina zare rigar likitan dake saye a jikina daga sama kai daddy abin kuma yar zolaya ce kuma yau ?
Yace to naga baku da hutu ne da zaran kun saka wanan rigar da kike cirewa kamar imanin ku ya gushe kuke zama.
Dariya nayi kawai muka fara hanya sai da muka fita daga haraban asibitin na sauke ajiyan zuciya nace dashi daddy ya amsa da naam nace nagode nagode ubangiji ya bar kauna ya kara rufa asiri yace da akai may kuma wanan irin adduan da godiya haka ?
Nace badon Allah da kai da anty ba da ba zan kai ga wanan matsayin da Allah ya kaini ba a yau nasan Allah ya nufa da zan zamo haka din to amma kuma kunr sanadin hakan gare ni ai.
Yai dan murmushi ya shiga round about din da zai kai mu kwanan unguwar mu yace ki dau godewa Allah din da kika fara fada don shine ya hukunci hakan a gare ki.
Ban taba tsanmanin matana zata taba aiki ba a duniya amma sai gashi ke karatun ki ya zamo dole na barki ki fita ki taimakawa alumma dashi.
Nai dan murmushi nace kamar kasan case din farko dana fara karo dashi abin akwai ban tauayi sosai ga matar wallahi.
Yace ai ku likitoci kuna fama da case iri iri balle ma ku dake fannin mata ai abin naku sai nake ga kamar yanzu yafi matsala sosai.
Mun kusa kai gida yace Rahama na amsa mashi yace ina son ki saurare ni da kysu kiji may zan fada maki.
Sai na mayar da hankalina sosai a gareshi yace ba hundatu ba duk wani wanda zai yi magana akan aikin da kika soma yi bana son ki biyewa mashi har ku bata min rai.
Yana fadin haka nasan akwai magana a kasa ke nan don haka ya zama wajibi a gare ni da nai taka tsantsan dakowa don dama nasan dole sai an samu wanan matsala tunda cikin matan shi babu mai aiki kuma duk sunyi karatu gwargwadon hali.
Aiko ko da muka shigo gidan taji yara na muna sannu da zuwa tana daki sai yar aikin ta kawai na gani a waje don matar babu ruwan ta da saka kanta ga harkan kowa ba kamar hanne da tai zama da ita bace a baya wanan ta girmay wa hanne sosai tasan ciwon kanta.
Ni dai na shiga daki naji fitina ya barke a tsakanin su inda nake jin muryoyin su yana tashi.
Ban fito ba amma ina jin komai tunda gida daya ne tana fada wai banfi kowa ba da zai barni ina fita wurin aiki.
Sai ga Aisha ta shigo dakin nan take labarta min maganganun da tayi da bana nan.
Nace kyaleta sai dai kare ya mutu da haushin kura don nagaba yayi gaba ko na baya sai labari.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , ,
83
Ranan sunyi fada sosai a tsakanin su ina jin yadda take surfa min zagi daga dakina amma ban taka masu ba tunda badani take masifan ba.
Saboda yara na fito falo don na duba su don tunda na dawo ina dakina ina hutawa saida nai sallah na fito inda suke na duba su.
Muna zaune tare dasu suna min hiran baba yadda ya kwashe a makaranta karon shi na farko.
Munyi dariya sosai muna cikin dariya ne sai gata ta fito daga dakin ta a hasale take don har lokacin tana jin masifa a tare da ita.
Wa za,a gwadawa boko ni da naga alhudahuda sarkin karatu ana gwada min yin karatu mace bata fu mu balle a fifitata a gare mu sai a san wanda za za, a bari gadin gida.
Ni dai ban kulata ba taci gaba da cewa in asiri ne ai gida mutum yazo mu zuba kafan wando daya da mutum mu gani a gidan nan.
Kamar nace da ita ai munzuba ba yau ba tunda wani dadi naji a wurin ku tun shigowa na gidan kowa da irin nata surfan a kaina ai.
Amma saboda maganan da mukayi dashi a mota naja bakina nai shiru ban taka mata har tayi ta gaji ta shige ciki.
Case dai har yakai gun iyayye ban san yaya akayi ba kwana biyu naga sun shirya a tsakanin su nace miji da mata ke nan tsakanin su sai Allah.
Naci gaba da zuwa aikina hankali kwance sallah babba na gaba towa don yazo gab a lokaci sai shirye shiryen sallah ake ko ina.
Haka ne muma a gidan mu sai faman shirin sallah mukeyi ba babba ba yaro kowa na zumudin zuwan wanan lokacin kamar yadda ko wani musulmi ke fatan ganin shekara ta zagayo irin hakan.
Ranan ya dawo yake fada muna mu shirya ranan laraba zamu tafi kano sallah gaba dayan mu gidan nai saa ina up a lokacin da tafiyan zai kama ke nan.
Don har mu tafi mu dawo ina da dan lokaci a wanan season din na bukin sallah da za, a yi din.
Nan kowa ya shiga shiri ni dai a raina ban so ba don nasan babu abinda zamu je yi sai fitina a tsakanin mu a can.
Amma da yake babu yadda zan yi dole na hakkura na shirya ba tare da na nuna komai ba a fili.
Ranan da zamu tafi lokaci da da duk wani musulmi idan ka gan shi busy yake ba kama hannun yaro ga kowa.
Tafiyan da zamuyi ranan ya kama nice keda girki don haka nai muna abincin da zamuci a mota don yara.
Mun fito har lokacin hindatu bata fito ba sai na zauna gaban motan don ganin nice mai girki sai bayan wani lokaci tafito tana shan kamshi.
Gaban motar inda nake zaune tazo ta tsaya a kaina ni dai bance da ita komai ba sai shine bayan ya gama rufe ko ina na gidan ya karaso gare mu.
Yace a, a ya baki shiga ba ke yake cewa da ita tai mai wani irin kallo tace a ina kake son na zauna yace ba wuri ne a motan halan ?
Tace a saman kanta kake son na hau na zauna ko may ko baka gani ne kai ?
Yace ya salam hindatu may yasa kike son rigima ne ke ko yaushe ina kin san komai kuma kusan kece kika kawo wanan matsala mai girki ce zata zauna a gaba indan irin tafiyan nan ya kama .
Tace nan ai ba kano bane ko kuma ai acan din ne nai magana ba a abuja don haka sai kasan yadda zakayi.
Ya dan kallo inda nake zaune na rungumay haidar a jikina yana shan nono muka hada ido naga yanayin shi ya shiga rudani sosai.
Tsam na daga yaron daga jikina na fito daga motan na bude gidan baya na shiga tare da rufo kofan da nake daga gefen shi.
Ta sauke ajiyan zuciya cikin fisgan jikin ta takai zaune sai ya zagaya ya zauna mazaunin driver don shi da kan shi zai ja motar da muke ciki inda Hamza yazo zai kwashi yara da yan aikin mu.
Sai daya zauna ya juyo inda take zaune yace koma baya ki zauna ke ma, tace saboda may ?
Yace haka nace ko baki ji bane ba matar da zata juyani yadda ranta ke so wallahi kin ji na fada maki.
Bata fita ba tai zaune ya jiwo idanuwan shi sun canza kala yace ba dake nake magana ba kina bata muna lokaci haka ?
Taja tsuki ta fice daga motan ranta a bace ta dawo inda nake zaune a baya ta zauna tare da jawo ganbun motar da karfin tsiya ta rufe gwaram.
Ya kada kai tare da kutawa ya fara jan motan sannu aa hankaki muke fita garin har lokacin ba wanda yai magana sai dai idan zai tsaya ya sai wani abu ya fita daga motan kuma komai daban daban yake sayowa kowan mu baya hadawa.
Ba mu isa kano ba sai uku na rana don haka kowan mu a gajiye yake duk da haka ban wuce part dina ba sai da na fara zuwa mu gaisa da anty.
Ina ganin ta gabana yai mugun faduwa nace anty lafiya kike kuwa tai dan murmushi tace Rama ina ko naga lafiya yau na kai sati biyu ina fama da jiki sosai amma yanzu Alhamdullahi na samu sauki ai.
Nai mata sannu tare da tambayan mutanen gida tace duk suna lafiya ban jima ba na mike zuwa nawa sasshen don na dan huta.
Na samu gajiye a falo tazo taron mu muka gaisa nai mata yaya gida ta kawo abincin da tai muna don taron mu nan na bar su Aisha suna ci na shige ciki don na rage kayan jikina.
Nai wanka nai sallah na sauya kayan jikina zuwa dogon riga na fito falon don na danci abincin da akkai muna.
Gajiye ta sake dawowa nan muka zauna muna ta zabga hira da ita nacee gaskiya Gajiye banji dadin ganin anty ba ga kwanaki da muka zo tayi kyau sosai amma yanzu duk taa ramay wallahi.
Tace bari hajiya ai yanzu ma taji sauki ke nan idan da ga satin da ya wuce ne ai abin ba kyau taji jiki sosai wallahi.
Nace Allah ubangiji ya bata lafiya tace amin na zauna naci abincin sai dai ba wani mai yawa ba sosai ba don raina ba dadi tun fitinan mu na safe.
A bakin Gajiye nake ji irin yawan fitinan dake faruwa a nan din inda take fada min komai nace kai kishi dai baiyi ba wallahi gashi kuma a jinin mu yake.
Ban fito ba sai bayan ishai don mun dan tsaya yan gyare gyare a shiyan don wuri ba mutum raggage ne sosai ba kamar yadda idan akwai mutum yake tsab ba.
Na samu anty zaune da yaran ta sun kewaye ta sai faman zuba mata hira suke Nasir yana kwance a three seater ya daga kafan shi daya ya tokare bango dashi.
Ina shigowa bayan nai mata sannu tare da mata mun samay su lafiya sai na juya wurin jinior daya manne ma jikin nata.
Nace kai kuma big man may ye haka baka ganin bata jin dadi kawani manne mata haka kamar zaka koma ciki da kai ?
Ta dan shafo kan yaron tai murmushi tace kai haba Rama yaro yaga uwar shi kice kuma kada ya manne min nace yana nan yana aikin shi zuba ko.
Tai dariya tace yana bani labarin fitinar uwar su ne kai wanan bata bari a zauna lafiya ki dai ta hakkuri da kowa Rama nagode kwarai wallahi yaro sai hakkuri kokai uwar shi balle yana ganin baka haife shi ba.
Murmushi nayi na dan dukar da kaina nace anty aiko ba wani matsala a bangaresu wallahi don suna da dadin zama gashi suna maida hankalin su sosai ga karatu.
Tace kai Rama ai in kan yaran nan ne baki taba bari a fadi don Allah Rama yadda kika rike min su amana ko bayan raina ki rike min su haka don yaro sai hakkuri .
Nace haba anty tare da abinki zaku raka har tsufa insha Allahu Allah dai ya baki lafiya tace kai Rahama ho tsufa yanzu ganin tsufa ai sai dace.
Tace da ace ba a gunki suke ba hankali baya taba kwanciya da zaman su can da wata amma kinga yanzu ko da banji komai a wurin su baa hankalina a kwance yake don ko a nan suke ya tsaya haka balle ni yaushe nake ta yaro ma can .
Kin ganshi harda wani sallo yazo min wai shi a can mummy su bata bari su kwanta sai sunyi wanka da dare sai sunyi kaza da kaza don iyayi.
Dariya nayi kawai tace ubangiji ya raya maki naki zurian su taso tare da yan uwan su kunya naji ban iya cewa amin ba a fili a gaban ta.
Sai kuma muka dauko hiran aikina take cewa dani kwanaki waban da ta maida kowa irin ta ai ta bugo tana fada muna wai ga abinda yai maki ya barki kina aiki mu muna gida.
Don haka sai mu hada mai kai tace idan ita ta manta aini bazan taba mantawa ba ina aikina amma saboda su dole na aje nabi ra, ayin su.
Sau nawa yana bamu kudin jari tunda sunce su sana,a zasuyi amma kudin ya kare har dubai ta fara zuwa ban san ya akayi ba kuma ta daina.
Ita kanta yasha bata kudi fiye da kowan mu idan sunyi tafiya amma sai a rasa ina kudin ke shigewa haka ?
Yanzu dai naji akan aikin ki wai suma sai ya nema masu aiki yace ya basu right kowa ya nema kema bashi ya nema maki ba ai.
Nai murmushi nace anty ni bani bakin ciki da aikin kowa wallahi tunda ba a jikina kudin zaifito ba balle.
Ranan munyi hira sosai har dare ya soma nai mata saida safe na koma wuri na inda dama a gajiye nake na samu har yaran sun kwanta muka rufe part din sai safe.
Da safe na fara raba dan tsaraban da nazo dashi na aikawa Zulfa abinda nazo masu dashi ita da yarta nai mamaki da tace a dawo min dashi sun gode don ba halinta bane.
Ashe tasha zugi sun hada kai kan zancen aiki akan lalai suma sai ya nema masu aikin yi kamar yadda nakeyi haushin hakane yasa tace a dawo min da kayana.
Ban damu ba na karbi abina na ci gaba da aikawa masu so suka karba da godiya da murna da fatan alheri.
Kagin a fara kiciniyar aikin sallah na shirya da yamma zuwa gaida iyayyen daddy da sauran mutane kada nazo ban samu zuwa da wuri ba nai laifi gin hajiyan daddy din don tana son a bata girma sosai a rayuwan ta.
Na samay su zaune a falo na gaidasu taja yan jikokinta a jiki tana masu wasa tace dani Rahama ga yaran kamar sun saba dani mana basu da kiuya ko kadan.
Muna gidan sai ga daddy yai mamakin ganin mu yace nan kuka zo ashe nace eh muka gaidashi Alhajin shi yace shi yasa nake son yar tawa ai akwaita da hankali.
Kaga ta kawo muna yara mu gan su gasu har suna batun kwace min mata na don tun shigowan su suke manne da ita sai shigowan ka suka yo gun ka.
Murmushi yayi Alhaji yace yaya jikin ita Saade yayi sauki ko ?
Yace ta samu sauki ina son idan an gama sallah na fita da ita
Showing 339001 words to 342000 words out of 456145 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114 Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153