bakuwa suka shigo naji gabana ya fadi ras nace innalillahi wa inna alaihin rajiun a cikin zuciya na na karasa da Allahuma ajirni fi musibuti wa, akalilli hairan min ha.
Take naji natsuwa yazo min a lokaci daya na daure na fito daga kitchen din daidai lokacin da yai daidai da shigowan maigidan shima.
Fuskan shi asake yake fadin ashe har kun iso ko tace wallahi ko kasan sammako mukayi don mu iso da wuri dama.
Sannu da zuwa nake mata amma sai tai kamar batajini ba tai wani sharewa na juya wurin shi ina mashi sannu da dawowa ya amsa min hankalin shi na kan su.
Na juya zan wuce naji yace ina kuma zaki Rahama ga baki anyi na waiwayo ina kallon su kafin nai magana naji tace bakuwa dai nikan aiba bakuwa bace a gidan nan.
Murmushi nayi kawai na sa kai zan wuce yace ina tambayan ki zaki wuce kuma mana ?
Sallah zan shiga nayi lokaci ya gabato na bashi amsa da hakan na fara tafiya abina batare da na tsaya ba yace idan kin idar da sallah ki samay ni a falo na shige abina ina jin suna dararakun su nace lokacin ki ne mata.
Alwalan na shiga na dauro na fito na shimfida abin sallah nafara gabatar da Nafila sai na kawo azahar nayi ban tashi ba na zauna ina rokon ubangijina da yai min kariya akan hindatu dama ko wani mai kina.
Can bayan wani dan lokaci naji muryan shi yana kiran sunana daga kofa sai dana dan dauki lokaci na fito falon ya zaune itama din tana zaune a gefen shi bakuwar ina tsanmani tana daki ne.
Na iso wurin naji yace kin shiga kin zauna kuma bayan na fada maki idan kin idar ina jiranki a falo nace ai gani yanzu na idar da sallah dama.
Na samu wuri na zauna a daya daga cikin kujeran dake falon ban dago kai na kalli gurin da suke a zaune ba kamar zata shige mai jiki.
Ya dan juyo yana kallona nai kamar banga yanayi ba don ba zan ba da fuskan da zata zo min da zafi ba don nasan a shirye ta tako garin da ganin yadda take wani fisge fisge.
Hindatu tace dear ya sauke ajiyan zuciya ya dan waigo inda nake yace Rahama nace naam daddy yace magana nake son yi daku tun yanzu kafin yaran nan su dawo daga school.
Ai muna jin ka tace dashi yace ba wai na hada ku nan bane don aita min rigima ko tashin hankali ba a gida na kawo kowan ku nan ne don mu zauna tare mu tsira tare bana son jin fitina ko hayani daga kowan ku a gidan nan in ba haka ba ran mai shi zai baci.
Sai kuma zancen yara yarana kun san bana son banbamci kowa ya rike min su kamar duk ku kuka haife su da cikin ku.
Ina ga sauran bayani kan kwana wanan ya rage a tsakanin ku kuka san yadda zaku raba abin ku dai.
Sai tace ai wanan ba matsala inkaji fitina dama an dauko shine kowa ai yasan halin kowa a cikin mu banga abinda za, a tsaya kuma fadi ba yanzu.
Kwana kuma yadda muke a baya can gida haka zamuyi ko yanzu two two days kowa yayi ya fita ba shike nan ba.
Na juya nace shike nan zan iya tafiya kagama ko yace shike nan abinda zan fadi dama bana son jin komai a gidan nan .
Na mike na barsu zaune tun kan na shige naga takai kwance a jikin shi yace a, a baki da hankaline hindatu Azumi fa mukeyi.
A raina nace duk abinda kika zo dashi dai gida kika zo don yanzu ba Rahaman da bace wanan da kike fadawa son ran ki.
Juyowa nayi na kira Aisha tazo daki ta samay ni dama tunda naji cewa zata dawo nan nasa suka dawo dakin dake kusa danawa hannun mu daya dasu.
Ta shigo tana dauke da Haidar daya tashi daga barci nace kai har ka falka ke nan wanan barcin dai baikai ko ina ba.
Ta zauna nace da ita dama ina son kara ja maki kunne ne akan zaman matar nan damu na dai fada maki har helen don babu ruwan ku da harkan ta.
Tace anty na sani kuma Atika ma naja mata kunne tun jiya har helen din yanzu ma na fadawa helen din tazo.
Nace shike nan ba wani abu bane dama tace abinci fa nace yadda
naga wanan matar tazo Aisha bari muga gudin ta tukun don kada muyi tace kuma waya samu.
Bata fita ba nan ta zauna abinta muna hira helen ma ta shigo tace dani anty naga dare ya fara abinci fa sai dai naga wanan matar a kitchen tana bude bude nace yi zaman ki mu gani.
Can muka fara jin kamahin girki na tashi a gidan sai da nai sallah la, asar na fito daga daki na samay ta tafito daga kitchen din nake cewa ashekina ciki bata ko kalli inda nake ba tace eh kawai ta shige.
Na koma daki abina ban jima da shiga ba yaran suka shigo gida sai ga su sun samu bakuwa a gidan Ihisan kan da murnan ta ta fada a jikin uwarta.
Tace wa yaran ku halan kunyi bakin ciki da ganina ne naga kunyi wani cirko cirko kuna kallona kamar kun ga bakuwa.
Jinior baiko bi ta ianta bw sai cewa yake ina little mum din mu take helen da ta kwaso shayi ta daka mata tsawa tace ke yar aiki kizo ki kwashi kayan nan ki wanke.
Sai yarinyar tace anty bata bari na wanke masu kaya ita ke wankewa ko Aisha tace to ni ba antyn bace maza zoki kwashe su.
Kamar nasan sunayi sai gani na fito daga daki naga helen tana wanke kayan abincin namu nace da ita helen yaya haka bana hanaki ba ashe ?
Tace wanan bakuwar anty ce tace na wanke mata na fada mata tace sai na wanke kafin in magana sai najita daga baya na tana fadin eh nice nan nasa ta wanke muna su.
Nace amma ni bani bari ta wanke muna kayan ibadan mu don ba musulma bace ko kin manta watan azumi muke watan ibada ne.
Na manta kin san bani azumi ne sai yanzu danaji daga bakin ki dai na tuna kallon mamaki nai mata kawai nace helen bar kayan na wanke su shige dakin ki.
Sai cewa tayi dama nasan akwai tsiya akan yaran nan dake don dama naji komai gamay dasu to ki sani duk wace tazo cin arzikin mu ba zan barta ba.
Sai lokacin na juyo nace da ita wasu ko wasu kan ai kina ganin su dole ki barsu inda kika gansu din.
Tace haka kika ce ko nace kwarai kuwa ai kema kina da ya da ar aiki sai ki saka su don ban saka naki ba.
Na wuce abina na barta a tsaye ta fara haushin ta data saba don ba yau ne farkon ganin ta ba a gare ni nasan ta nasan halin ta tun a baya.
Ina shiga daki sai ga Nasir da Jinior Nasir ke cewa dani little mum wai may wanan matar tazo yine a gidan nan yaushe ne kuma zata koma ta barmu please da zuwan ta tafara wa mutane fada a gida haka.

********* ********* *********
An sha ruwa kowa yana dakin shi gidan ya koma shiru ranan daga hindatu sai daddy ne a zaune a falon ga abinci dafa duka data dafa ya saka a gaban shi tun cibi daya daya diba ya hade shi da kyat bai sake iya kara na biyu ba.
Don yaji da kaurin kuna dake tashi ga abincin ga ba magi ko mai naiji ba wai shi may azumi zai yi buda baki dashi.
Sai faman surutu take zuba mai yana dai amsawa da kyat da eh a, a don biye mata kada ranta ya baci.
Na fito daga dakina dauke da Haidar na samay su zaune a hakan na gayar dashi da shan ruwa ya amsa da fara,ar shi yanawa haidar wasa.
Ban saukr yaron ba na juya abina na wuce zuwa kitchen don Nasir ne ya fito dani nai mashi abinda zaici ba zai iya cin wanan abincin ba.
Miya na hada dole a cikin daren nan na zuba shinkafa a rice cooker na dafa masu shine yaran gaba daya sukaci suka kwanta niko na sha tea kawai.
Washegari abinci ne tule an barta dashi a kitchen ta fara fada da masifa don taga tunkuyar da naiwa yaran abinci da shi.
Ta kwasa fuu taje ta fadawa maigidan harda zancen helen da yadda mukayi a jiya din sai da ta fada mai komai.
Ina jiran yai min magana sai banji yayi ba haka ta zubar da abinci mai yawa tunda ba almajiri ko wani mabukacin da zata iya ba anan.
Yau da zata dora ina dakina tun safe barci nake kwasa abina can baba ya tayar dani da kuka nasan yunwa yake ji na fito indan dama mai cooker orth yasha ko zai muna shiru.
Na samu ta fito daga kitchen tace yauwa dama naso fitowan ki yanzu.
Don naji naga jiya kun hada kai da yara sunki cin abincin dana dafa yau dafa dukan taliya zan masu sai naga shegen da zaice baici kuma.
Murmushi nayi mata kawai na shige abina tabiyoni kamar tana zargina har na dora abinda zanyi nagama na fita na dawo falo na zauna nakira Aisha ta kawo yaron.
Sai da Aisha ta fito da yaron har sun zauna nace ta fifita mai yai sanyi a bashi sai naji tace amma wanan da kika damawa yaronki kin dai san na baban su ne ko idan ya kare fa ?
Nace sai ya sawo wani dama ai dan shi ne yasha ba dan wani ba kuma tare suke sha da uban dama.
Ai bashi kadai ya haifa ba ba zan yarda da son kai din nan ba kowa ma ai shi ya haife shi ba wanda ya tsinto a bola cikin su .
Kin ga sai ki dama kowa yasha tunda ko banza gaki a kitchen ai ko abu mai sauki kankana.
Rahama wuyan ki fa na lura tun jiya ya fara kauri to bari kiji bakin cikin ki da tashin hankalin ki za a katse maki jin dadin rayuwan ki anzo an gwamatse ku to sai dai ki mutu.
Nace kai ji wani magana kuma nan wanan kuma ai sai Allah dayayini ya isa ya katse min jin dadi ba mutum banza ba irin ki.
Ranta yai mugun baci tace nine banzan zan gwada maki wallahi ni hindatu ba banza bace a gidan nan sai na lahira yafiki jin dadi angaji an koma kauye inda akafi wayo dama kwashe kwashen Saade ne yakaimu ga haka itama din kin mata halin ku na yan adam kin rabata da mijin ta.
Nace koke baki fi karfin hakan ba a gare ni nace dadin abin dai ina da asali ba cirani nazo yi ba garin mutane balle ace ba a san sunan kauyen mu ba.
Aiko sai zagi ta uwa ta uba kamar ba azumi takeyi ba nace ni bani zagin ki don nasan hukuncin zagi ga Allah kuma ina ibadana ke kinyi kadan ki rusa min ibadana.
Haka muka sha ruwa tana rusa muna fitina har magariba kowa ya shige muka barta a wurin.
Tun dawowan shi gidan ya fahinci akwai matsala don maigadi ke cewa dashi tun waje oga bakuwar nan fa tana da masifa tana matsawa uwar dakin mu yau fitina suka wuni yi.
Yace dashi sharf ita ma bakuwar matatace kamar yadda uwar dakin naka take matana don haka mind your self ya wuce shi fuu yana bashi hakkuri.
Ran shi a bace yafito daga dakin shi bayan ya sauya kayan jikin shi zuwa na shan iska yana zama sai ga Jinior ya fito yana cewa daddy I can't eat this food.
Ya dakawa yaron tsawa ya juya rai a bace ya fice daga falon sai gata tafito ta zauna a gefen shi bata dade da zama ba Nasir ya fito zai fita daga gidan uban ya hango shi.
Yace ina zaka yanzu da daren nan soja yaron ya tsaya ya dan juyo yace zan fita na samo wani abu a waje ne don bama iya cin abincin nan gaskiya.
Ya juya gareta yace hindatu wani irin abinci kika dafa ne yaran sun kasa ci tai wani irin shuumin dariya tace sun kasa ci ko makirci dai.
Dafa dukan taliya ne nayi masu shine za, ace sun kasa ci ni duk iskancin yaro dashi da wanda ke turo shi ai ina iya shi wallahi.
Kafin yai magana sai ga Ihisan ta fito tace mama nifa bana iya cin wanan abincin ya yi yaji da yawa ba haka little mum ke muna abinci ba ko Aisha.
Yace you see,
Ita kuma wanan din waya kulla mata makirci da tazo da wanan maganan bafa yau ba ina maki wanan complain din kan abinci akwai komai amma ai abinci ba test ba komai.
Tace a hasale yadda na iya nakeyi bakuma wanda zai sani nayi abinda ban tashi yi ba ehe,
Ina sawa yarona parmpers naji yana kirana na fito da yaton a hannu na a zatona fadan dazun ne zai yi magana a kan shi.
Sai da nai mai barka da shan ruwa na samu wuri na zauna ina sauraren shi inji may zaice dani.
Yace ga danki can daki yanzu ya fito zai fita na tambaye shi ina zai tafi wai zaije ya samo abinda zaici baya iya cin wanda aka dafa masu.
Nace subbahanallahi Nasir a Abuja da daren nan ina zaka haka karami dakai yace gasu nan har jinior shiyazo ya fara samu na sai ihisan kuma sai ki sama masu abinda zasuci yanzu.
Dama haka kike so yar iska shine plan din da kika shiryawa yaran tun ian nazo nai murmushi na sabala dana a kafada nace basu saba cin kazanta ba tun wurin uwar su yanzu ko ba yadda za, ayi su iya cin jagwalgwalen ki sai a koma kitchen a koyi girki don an wuce wurin.
Ke ke ke hindatu may na fada maki tun farko bana son irin wanan jidalin kikace min bazakiyi ba yau kwanan ki nawa da zuwa da har zaki fara muna fitina haka tun jiya kike complain ke anyi maki abukaza.
Yanzu ina dawowa aka tare ni tun waje kun wuni kuna jidali a gidan nan bayana wallahi duk ina kwasan ku ku koma kano gaba dayan ku ko.
Na ce yafi nono fari a wurina ai can ma gida ne ba wani matsala ko can tace karya ne munafuka don ki min bakin ciki ko to ba inda zan tafi nazo ke nan zama daram.
Nace gaki ga gidan ai na shige gurin yara suna kwance kowa a cikin damuwa na zauna bakin gado Nasir ya dago kai yana kallona yace little mum barka da shan ruwa nace kunci abinci sai sukai shiru nace tambayan ku nake kun yi shiru mana.
Wallahi mum abincin ba dadi kuma yana wani wari wari nace yanzun may zakuci, da kuka zauna daki bakuyi magana ba ?
Jinior yace naje gun daddy ya koro ni nace kaima da gangan yanzu dai ba wanan ba ku tashi muje kitchen muga may zamu dafa mai sauki.
Da saurin su suka mike muka fito daga dakin nan muka wuce zuwa kitchen tare da yaran cikin sauki na hada masu abinci mai sauki sai gasu sun fito suna dariya harda ihisan na zubawa na kira Aisha ta dauki namu zuwa part din mu.
Nan suka zauna wurin uban nasu suka zauna suna hira suna cin abinci cikin jin dadi da walwala har suka gama suka dan yi hira suka mike zuwa dakin su.
Ni dai muna dakina da Aisha, da Atika sai helen dake biye damu nadauko ta ba dama na kore ta cikin mu kuma.
Anan da yake barcin azumi ne har barci ya kwashe su ban tada su ba na barsu nan sai asuba muka falka don yin sahur na riga na tanadar masu abin buda baki na dauka nakaiwa yaran nasu sai dana tabbatar da sun tashi sun shiga brush na bar dakin nasu.
Ban kwanta ba na shiga dan zirgazirga kafin ai kiran sallah na gama na zauna saida nai sallah na tayar da yaran suma sukayi suka fara shirin zuwa school.
Barci na nayi sosai koda na tashi na samu Aisha ta gama duk wani abinda ya dace ayi shi.
Wanka na fada ban damu da son zuwa gaida daddy ba don nasan baya gidan a lokacin don goma da wani abu a lokacin.
Gidan tsit sai kace ba kowa a cikin sa kowa na dakin shi yana barcin azumi a lokacin wanka nayi na fito don sama ma yaran da basu azumi abinda zasu ci.
Ina kitchen ina karainiya naji kamar motsi a falon ban tsaya juyowa ba naci gaba da abinda nakeyi a kitchen din.
Can dai na sake jin motsi sai na dan leka hindatu ce naga tafito kamar daga backyard din mu da alaman rashin gaskiya a tare da ita.
Na lafe don karta san ina kitchen din a lokacin da sauri ta shige
Showing 315001 words to 318000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106 Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153