tayi koda ta tsaya tambayan shi ba wai zai fada mata bane don ko fuskan haka ma bata gani a gurin shi ai.
Inda watan shi ke aje saman desk din da system din shi yake takai hannu tana daukan wayan tare da fadin ara min wayan ka na danyi amfani dashi don Allah.
Har yace mata uhum yana maici gaba da abinda yakeyi ko may ya tuna sai yakai hannu alaman ta miko mai wayan tare da tambayan ta ina naki ke ?
Tace baida issashen kudine a ciki, yace da ita har yaushe na loda maki kudi a waya may kikayi dashi keda ba wani waye kikeyi ba.
Tace ara min kawai ido ya tsura mata kamar yana son gano wani abu a gareta babu zargi ko wasa a idon nata yasa ya mika mata wayan ta dauki nata tana kokarin saka layin mahaifinta data fi zargi sai ga sunan mahaifinta ya fito ta kawar tana dan tunane can Rahama ta fado mata a rai ta kai gurin nombba na tana kooarin sakawa sai taga an rubuta .
DHT mamakine ya kamata don haka cikin daurewa ta kira layin nawa sai kusan zai katse na daga da sallama batai magana ba don taji may zance , ina dauka nafara gaidashi tare da cewa daddy yaya anty da jinior muna gaida anty da jinior muna matukar kewan anty daddy adawo muna da anty mu please ?
Na karawa Amira dake kusa dani wayan ina fadin Amira ga su anty da daddy sun kira mu.
Tai murmushi dataji muryan Amira tana cewa hello Daddy tace amira mummy ce yarinyar tai ihu tace mummy please yau zaku dawo gidan ba dadi baku sai dai anty Rama kuma munajin dadin anty Rama tana bamu abin dadi da bakinan mummy tana kaimu yawo park mun je munga lion ni da Nasir da anty da Gajiye.
Saida naji yarinyar nakiran mummy yasa na fahinci anty ne a layin to kuma shine batai magana ba tabarni ina zuba hakana may ke faruwa da ita ne wai ko kuma jikin ne ?
Na karbe wayan a hannun yarinya na fara zuba mata shagwaba ina cewa haba anty na dauka daddy ne ai a layin don shekaran jiya yakira mu da wanan layin sai kuma nai shiru na tuna da warning dina da daddy yayi ranan.
Murmushi tayi tace Rama ke nan waike yaushe ne zaki girma kidaina wanan shagwaban haka ?
Jin suna wacce anty takira yasa shi saurin dago kai da sauri yana kallon ta batare da yai magana ba yana kallon fuskan ta sai murmushi takeyi tana sauraren abinda nake fada mata.
Niko cewa nake anty shagwaba kan ai sai ranan da kika yaye ni kila zan bari wallahi anty na matsuki dawo kullun saina bude dakin ki na shiga na dinga shakan kamshin ki watarana har kuka nake don missing din ki da mukayi.
Dariya na bata tace aiko sai dai kiyi ta shiga daki shakan kamshi na don ba ranan dawowa gare mu sainan da tsawon wani lokaci.
Nace cikin kuka shagwaba wayyo antyna don Allah ki dawo kada na mutu jiya fa har zazzabi nayi na rashin ki a gidan nan.
Tace ki mutu kuma Rama rufa min asiri please inkin mutu ai na shiga uku.
Nace to anty yaushe ne zaku dawo wallahi muna son ganin jinior sosai munyi kewan shi munyi missing din ku anty.
Tace ina ganin likitane Rama kuma daddy kin san aikin shi bana hutu bane shima aiki yai mai yawa sosai anan.
Nace to anty injin daddy bai saka ki wanan bacin rai din don fa ni ina tsoro kada yai ta maki fada ban kusa balle nayi kuka ?
Kai kedai Rama mashirirciya ne wallahi yanzu don daddy na sani bacin rai sai kiyi ta kuka nace eh mana anty ji nake kamar na shake shi anty don wallahi idan yana bata maki rai nakan ji kamar na make shi shima ran shi ya baci.
Ban sani ba ashe tunda tace daddy kike jin haushi anty ya wauce wayan a hannun ta yana sauraren abinda nake fadi gamay dashi.
Sai ji nayi yace ai sai ki kasheni ki huta ko stupid idiot na kike jin haushi Rama dip na kashe wayan da sauri tare da dafe kaina a fili ina fadin ma shiga uku.
Gajiye da take zaune sai kalloni tayi tana fadin may ya faru nace cikin kwalalo idona waje ashe daddy yaji abinda nake fadi shine ya zage ni.
Gajiye tace dani ai maganin ki ke nan ba bakiji ba shiga tsakanin miji da mata basai Allah ba.
Nan shiga damuwa ranan ina fadin aiko na gata kaina wallahi yanzu ni daddy yaji irin hsushin shi da nakeji tafaru ta kare min nasan zamana a gidan ya kare ke nan.
Tun mutumin da nake zaune a gurin shi yaji ban kaunan shi ai shike nan nawa ya samay ni sai komawa kauye ke nan.
Nace idan na koma kauye karatuna fa nace na bashi hakkuri ya yafe min to amma kuma ai abinda kunya gaskiya.
Can kuma yana kashe wayan anty ta kalleshi tana murmshi take cewa hmm Rama ta ke nan boyar Allah.
Wani kallo ya watso mata mai kama da harara yace wanan yarinyar ko zanyi maganin ta wallahi ni take fadan magana haka a kaina.
Anty ta murmusa tare da zama dan gefen shi kadan tana cewa akaina Rama na iya komai besty shi yasa nake son ta wallahi.
Yace ai ban taba sanin rashin kunyan ta ya kai haka ba sai yau din nan ni zatace wai zata shake ko ta make ni ?
Ita har yaushe ta sanki ta san dadinki haka anty tai dariya tana cewa bar min yarinya na please kada ka damay ta.
Ya dan dago kai yana hararan ta yace cikin kutawa zata gane bata da wayo wallahi.
May zakai mata besty ?
Anty ta tambaya cikin son sanin abinda zai aiwatar a kaina yace ina ruwan ki amma ai naga ni ba ruwana da shiga harkan ta balle ta min wanan mumunan shedan haka.
Idan baka shiga harkan ta ba ai kashiga na anty ta ko itako nice bata so taga kana batawa din.
Bata makin may nayi ni din, tace bukatana a kan ta mana gareka ?
Shine ta fahinci kana sani bacin rai a dan lokacin nan wanda da tasan dalili nasan da ta fi fushi dani bisa gareka.
Ai idan baki barima sani zatazo tayi tunda harkin jawo karamar yarinya tana fadin bakaken magana na batanci haka akaina.
Maynene maganan bataci data fada a nan kuma daga tana fadin ra, ayin ta kawai kuma.
Oh wanan ba bakar magana bane a gurin ki ko har kina dariya haka don bake ta bata ba ke nan.
Haukan Ramane baka sani ba kuma besty ai Rama tunda ta watse mama lauratu a kaina tun tana yar ficiciyar ta nasan bata wasa bace akaina.
Yayi kyau yace tare da mayar da hankalin shi ga abinda yakeyi bai kara magana ba.
Ashe ma kana da layinta a wayan ka ban sani ba ai na dauka baka dashi.
Kallon ta yayi yace kamar yaya ina da layinta bake kika bani ba a baya.
Tace ni kuwa kadai tuna amma bani ba dai kan Rama dake tsoron ka kamar may zanbaka layin ta kuma?
Yace a, a bata tsoro na da batace zata makeni ba ai wanda kake tsoro ai baka ko gigin furta kalami mai sauki a kan shi balle wanan.
Gaskiya ni dai ban san kana da layin ta ba sai yau din nan danagani a wayan ka yanzu.
Cikin basarwa yace to wai samay idan ina da layinta ba, a gida na take zaune ba don na samu layin ta kuma wani matsalane kece dai baki san ina dashi ba dai.
Wani kallon zargi tai mashi tare da kawar da kanta tana mamakin shi ita zaiwa muna funci don ya saci wayan Rama a wayan ta ko may ?
Bayan gashi Rama ta fada da bakinta da layin ya kirata shekaran jiya kenan lanba ya dauka daya dauki wayan ta ranan.
Shine girman kai ba zai iya bari ya tambayeta ba sai ya dauki wayan ta don muna funcin maza ya kwasa.
Baibada kafan ta sake mai maganan ba ita ma bata sake bi takan maganan ba ido tasa mai taga gudun shi kawai.
Amma abinda mamaki fa ji yadda take binshi akan zancen yarinyar nan yake wani basar yau kuma don yana son nombata shine zai munafunce ta damay yake son taji a rayuwan tane.
A yadda ra san shi miskili bata taba zaton zai iya yin haka ba amma sai gashi ita da idon ta ta gan shi kuma ya basar to may yake nufi da hakan ne wai ?
Amma kuma ko ma may ye ai ai yarinyar dai ta fada min in ma har wani magana ne yai mata ai da Rama ta fada mata.
Kawai don kana son jin lafiyan iyalinka shine kuma sai ka munafunce ni don girman kai irin na besty nasan dai ba wani abu a tsakanin su sai tambayan lafiyan su kawai da zai yi, amma yana jin girman kan fada min hakan.

********* ********* *********
Abu kamar wasa sai gashi irin matsin da Ibrahim ke yawan kirana dashi a waya yasa har na fara dan sake jiki dashi a lokacin.
Don zai kira waya yace na bawa kowa su gaisa har gajiye da muke tare sai sunyi waya da ita idan ya kira.
Sai dai a waya kawai nake bari yaji ni bana yarda mu hadu a fili dashi don warning din anty da daddy da sukai min a kan shi.
Hakan bai damun shi bai kuma hana shi kirana bayan dan wani lokaci shi dai kokari yake ya samu ya kafa gwaunatin shi gareni kawai.
A haka har muka sharare kwanaki kwanki ya koma makwanni makwani ya share watan ni muna shakuwa tawaya dashi kawai.
Sai faman shiri muke na dawowan mutanen gidan komai mun wanke mun goge munyiwa shiyan kwalla ni da gajiye gwanin ban sha, awa dashi.
Dawowan nasu a lokacin ya samu nasaba ne da aiken da Alhajin shi ke mai na aurar da yaran yan uwasu da za, ayi.
Ciki harda sisters din Ibrahim su biyu da zaa auran a lokacin dinkin duk event din da za, ayi Ibrahim yai muna shi har Gajiye da anty da bata kasan.
Dawowan dare sukayi muna duk da dare ne bai hana mutum ya fahinci sauyin rayuwan da suka samu ba gaba dayan su.
Abu ga yanayi ba guda ba da nan sun yi kyau sun koma freshen dasu ga lissafina dai watan su na shidda suke ciki dan dama daddy yazo dubai a lokacin suna can.
Muma mun samu labari ne don matan gidan da suka tafi can bamu sani ba saida aka bugo waya ana tambayana ko an bar husna a gurin mu gida kamar yadda daddy ya bukata ayi.
Nace husna anty maman ta bata nan ne take cewa ai basa nan yau kwanan su uku da zuwa Dubai don besty ma yana can wani aiki ya kaishi.
Nace to gaskiya bata nan amma anty shine daddy bai kawo muna ke ba nan tace Rama kiyi hakkuri lafiya na yafi komai a gareku likita nake gani anan akwai magani da alluran da ake min duk karshen wata ne.
Kinga idan nace nadawo na kuma koma akwai wahala haka a gareni nace hakane gaskiya tace to kuyi hakkuri ai na kusa dawowa din.
Sai gashi bayan wata biyu din Allah ya dawo muna dasu lafiya muna zaune falon anty kunnuwan mu yana sauraren isowar su mussanman ma danaga an hada hadari basu iso ba sai nai tunanen haka din ne kawai bazasu dawo a ranan ba ashe sun tsaya clearing din kayan su ne a lokacin.
Da murna mukayi waje da gudu don jin dirin motar su data tsaya sai dana dan tsaya don naga ta bangaren da zanga farin cikin rayuwana tafito a ciki.
Dayan bangaren nagane ta ta bude mota tafito da gudu na kwasa nai gurin ta da murna na na rugumay ta duk wani dadi ya kumay ni sosai a raina.
Gaba dayan su sun yi matukar kyau dasu na karbi jinior dake barci muka shige ciki ni ban ko tsaya gaida daddy ba ma.
Hakan ya matukar ci mashi rai danayi nan muka baje a falo tare da gabatar mata da abinda muka shirya mata don bamu sa daddy zaici anan ba tun da ga matan shi a gida.
Hira ya dauke muna hankali anty bata ko ci abincin ba shigowan daddy part din yasa mu natsuwa a lokacin.
Ya sauya kayan jikin shi zuwa doguwar rigar jallabiya mai laushi da santsi daganin shi a galabaice yake a lokacin.
Kujeran three seater dake falon ya nufa ya zauna tare da dan kishingidewa yana kallon yaran shi.
Sai yanzu dana gan shi abinda ya faru a cikin waya ya dawo min sabo a raina.
Muryan anty naji tana cewa dani Rama kin ko gaida daddy da dawo don banji kin gaidashi ba ni ?
Sai lokacin ya dago daga ruguman da yaiwa Amira yana fadin ta gaidani ko ta shake ni tunda bata kauna na a duniya.
Mikewa nayi tare da tsugunnawa kusa dashi ina gaidashi anty take cewa haba besty aiko Rama mai kaunarka ne jifa yadda muka samay su hankali a kwance ba matsalan komai.
Kaina na sadda a kasa nace sannu da zuwa daddy yaya hanya kokarin kauda kan shi yake kamar bai son ganina a lokacin.
Balle ni dake ji a lokacin kamar kasa ya bude in shige don kun ya
Gaba daya hankalin anty yana akaman ga kunya ya rufeni na rasa abinda zan dafa naji sauki a lokacin.
Banda zabi banda na kwashi tsuman kafana na shige daga ciki don takuran da nayi a gurin.
Ina kuma zaki baki bani abinci ba Rama naji muryan ta tana fada min hakan.
Dole na dawo na shiga jawo kayan abincin a gaban su take cewa zuba ma daddy nasan baici komai ba kila.
Sai lokacin na dan kalleshi don inji may zaice akan abincin yayin da anty sai faman kashe mu da idon ta takeyi kawai.
Na bude kulolin tare da dan tambayan may zan zuba masu kallon shi tayi tana cewa dear may zakaci ne wai ?
Duk abinda aka zuba min zanci yunwa nake ji sosai wallahi ko barci na kasa kwanci nayi don ban samu an hada min komai ba a gidan.
Haka ya sauko suka zauna kasa shi da anty ba su ko hau dining ba suka shiga loda abinci a cikin su.
Sai da anty ta cika cikin ta take cewa dashi kan shi na duke yana faman kai loman tuwo a bakin shi ina nan ina kwasan kaya zuwa dakin ta dasu.
Rama zo mana ki zubawa daddy fruit's ya kara dashi, don nasan yana matukar sha, awan shi sosai a ran shi.
Wani irin faduwan gaba naji irin mai shirin tarwatsa zuciyar bawa a lokacin.
A sanyaye na karaso gurin da suke tare da durkusawa gaban kayan ba abinda nake tsoro kamar ya tayar da zancen kuma again.
Har na bude zan fara zubawa naji yana cewa No tabarshi zan diba kata ta turmujeni dashi kamar yadda tace zatai min ranan.
Dukar da kaina nayi kasa kamar nace wayyo ni Allah a lokacin saboda gigicewa namike da sauri simi simi na bar falon na shige dakin ta ban fito ba har sai lokacin da naji ya fice.
Anty ta shigo daki ta samay ni ina rikici da jinior wai shi ya manta da mu ko duk wanda ya tabashi sai ya sa kuka wai bai san mu ba.
Tace kai jinior kada fa kaiwa Anty Rahma butulci kaine kuma yau kake mata kiuya nace ai barshi in yazo ya sauko nima nace ban san ka ba.
Nace akwashe kayan kingamane a falo tace kwashe kedai Rama daddyn ku ya hanaki tsaya ko ?
Nace cikin shagwaba ai wallahi anty duk kece kin san yana kusa kika barni ina ta zuba surutu ni yanzu ma wani ido zan kallesshi wallahi duk na shiga rudu.
Tace akan may fita batun shi ki basar da zancen kin ji yayi ya gama ya dawo hanya ai baison gaskiyya ne ai shiyasa.
In bashiba may ye na tsayawa mutane wani kwanaye kwanaye can kuma kan gaskiya.

********* ********* *********
Tun ranan bani yarda na hadu da da daddy agidan Allah kuma ya taimakeni bamu ma haduwa koda zai shigo nina fita ko kuma ya fita nina shigo gidan.
Ga bukinsu ya kusa lokacin da anty ta dawo ta fahinci rawan kan da Ibrahim yakeyi a kaina amma takawo ido ta saka min taga gudun mu dashi tun da ban fada mata komai ba gamay dashi din data dawo.
Nadai nuna mata dinkunan dayai muna na event din da zasuyi a gidan su harda nata a cikin tai godiya kawai.
Ranan da yazo gaida anty bana gida shine take mai godiya kan dinkin da yai muna yai dariya yana washe bakin jin dadi.
Tace amma Ibrahim ban son yar haka dakai fa bayan kasan akwai wacce zaka aura
Showing 123001 words to 126000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42 Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153