ne kowa na barci da kyat na samu layin gajiye ta fito ta bude min kofan part din mu.
Na fito saye cikin dogon riga purple, yaddin rigan mai mugun taushi da santsi, silk ne kayan sun matukar karban jikina sosai.
A hankali nake takawa na fito daga motan bashir din ina tare dashi ya riko dayan hannu na ina rataye da handbag dina mai kyau da tsada a kafada na.
Kowa yasan da dawowan mu ranan don haka suna jin motsin bude get suka fito don taron maigidan.
Idanuwan su kar a kaina babu wacce bata razana ba da gani na gaba daya na canza masu lokaci guda.
Na koma gefe daya duk da bai saki hannu na ba a lokacin yana rike da ni still ko wace tazo ta rugumay shi.
Balaifi shima yai masu murnan ganin su nan guri yadan rude da surutu duk da dare ne Bashir yai mashi sallama ya juya zuwa gidan shi bayan ya sauke kayan da muka shigo dasu wanda kusan duk nawa ne don shi bai tafiya da kaya haka masu yawa.
Yace dasu kowa yaje ya kwanta kafin gari ya karasa wayewa don karfe hudu saura a lokacin yace zamu dan kwanta mu huta don a gajiye muke.
Basu so hakan ba sai dai babu yadda zasuyi dole suka fice suka bar mu don yaki sake ni na koma part din mu don ita antyna bata fito ba.
Basu bar juna ba sai da sukai gulma na tare hindatu tace Zulfa kinga yadda wanan yar kauyen ta koma kodai ciki ne da ita ?
Zulfa tace nima mamakin da nake ke nan gaba daya ta juye wata iri kamar yar wani da wata ?
Sukace ba dole ba Allah kadai yasan abinda sukayi haka acan hindatu tace kin san namiji muna fuki ne ai.
Bamu tashi ba sai sha dayan rana daddy ya baru na fito part din ko shi sai da naita hada shi da Allah ya bari naje naga anty don yace sai two zan fito wai ina da gajiya kafana duk sunyi wani suntum don zaman jirgi da nasha.
Nashigo part din Anty dake zaune sai ganina tayi kamar a mafalki tace wai da gaske dama kun dawo ne Rama na rugumay anty da sai kallona take cikin mamaki don gaba daya na canzawa idon ta baki daya zaka rantse da Allah kace injin aka sakani na koma haka a lokaci guda yadda na goge na waye nayi kyau sosai kamar wata yar gidan wasu masu fada aji.
Nace miss you anty na ina cewa ina yaran tace sun tafi school ai tunda safe Gajiye ke fada masu dawowan ku sukai ta ihu suna neman ki.
Na zauna ina cewa kin san daddy da son rigima ko yanzu sai da nayi da kyat yabari nazo na ganki tace shi wanan yanzu wake batun shi ai duk ya burge ne gaba daya baijin has.
Nai murmushi don na gane nufinta Fatima tazo da murnan ta muka rugumay juna cikin farin ciki.
Itama ta yi kyau da ita fes kauyancin ta duk ya goge ta zama wata babba a idona.
Na tambaye ta lafiyan jikin ta take cewa dani da sauki nan muka zauna mukai hira sosai da ita tace bari taje dakin maigida su gaisa nima na mike zuwa nawa part din don na huta.
Tana shiga falon shi taci karo da kayyan dana muka dawo dasu a falon tabi kayan da kallon mamaki haka don tasan shi ba gwanin tafiya da kaya bane amma yau gashi yazo da kayya haka duniya juyin juyi ke nan.
Yana kwance barci yake ya dunkule a guri daya kamar maijin sanyi ta dan dade tsaye a kan shi tana kallon shi ta juya zata bar dakin tunda barci yakeyi.
Taji yace Saade karaso mana na gaji da yawa ne wallahi, tai murmushi ta karasa bakin gadon da yake kwance ta samu wuri ta zauna tana fadin an dawo lafiya yace Alhamdullahi.
Yace yaya kuke da yaran ya jikin naki ya juyo yana fuskantar ta da kyau tace duk muna lafiya.
Tace ban dauka zaka dawo yanzu ba ai ko da kace a satin nan zaku shigo yai murmushi yace ba dole na dawo maki da kauna ba hankalin ta nagareki da yara sai karatun ta da ta bari.
Tace Rama ba dai rigima ba kan gashi kuma daga kai har ita tafiyan yai maku kyau sosai wallahi doon kunyi wani fresh da ku kamar ba aiki kaje yi ba ?
Yai murmushi yace kuma ga tafiya anyi nasara sosai fiye da tsanmanin mai tsanmani wallahi don bantaba samun nasara ba irin wanan.
Masha Allahu abu ko yayi kyau wallahi haka muke son ji ko yaushe Rama tai tafiya a sa,a ke nan yace gaskiya kan don ni abin ya ban mamaki wallahi.
Nan dai yai mata bayani kan irin nasaran da ya samu ga tafiyan itama tayi mamaki kwarai kuma tai murna ta mike tana cewa bari ta barshi ya huta kada ta damay shi da yawa.
Ta mike take tambayan shi abinci fa yake cewa da ita zai tashi yai wanka sai yaci.
Tana fita hindatu ta shigo itama sun gaisa take cewa ta hada mai breakfast fa.
Yace saboda may zaki hada min bayan kin san da wacce nai tafiya sai yamma zata fita girki mai dauka ya dauka.
Bataso jin haka ba don ta shirya sosai tana son ya soma cin abubuwan da ta aiwatar akan shi lokacin.
Tace ai ba don wani abu nayi ba don kawai na taimaka mata ne tunda ta dawo da gajiya ba wani abu zata iya yi ba nagani.
Yace No ki barshi ai zasu kawo min daga part din ya mike zai shiga bathroom tabishi da kallon mamaki ina mukaje muka koma hakan harshi ga shi yai wani haske da kiba ya murje yayi kyau ke nan babu abinda yaje yi sai hutawa kawai da wanan shegiyar yarinyar ai zata gane kuren ta yar iska kawai.
Idan tayi tayi idan bata yi bata yi ba don in maggi ya hau kan mage sai tarihi bar yar iska zanyi maganin ta sai dai hange ita dashi a gidan nan.
Ya fito wanka ya shirya cikin kananan kaya ai matukar kyau dashi ya samu an kawo mai abin karyawa daga wurin anty ya zauna yana ci Zulfa ta shigo dauke da yar ta a kafadan ta.
Ya mika hannu ya karbi yarinyar yana cikin mata wasa ta samu guri ta zauna tana tambayan shi yaya hanya yace Alhamdullahi.
Shigowan hindatu ne ya katse masu maganan su itakuma zulfa ta daure fuskan ta don bataso hakan ba.
Itama wuri ta samu ta zauna tana cewa tafiyan wanan karon harda tsaraba haka muka samu ya dan dago yana kai cibin ferfesu abakin shi saida ya hade yace.
Tsaraba kuma yana ina tace gasu ko dauri dauri mun gani aje can yace kayan Rahama ne ni ban ma san may ta sayo ba ciki.
Duk wanan kayan na Rahama ne haka lalai ita ina ta samu kudin sayen kaya haka kuma ?
Yace sai ki tambaye ta ai tana gidan ya mike dauke da yarinyar yana kokarin bin kofan shiga gurin mu yace da su ina zuwa.
Ina zaka da ita kuma miko min ita har ka dawo inji uwar yarinyar tace dashi yace hakan.
Yace doka zaki saka min ni da ya ta ko may Zulfa tacee ba doka bane ina dai kafakafa da abina ne ita nake gani naji dadi a raina.
Bai bata amsa ba ya fice da yarinyar ran uwar ya baci don ita dai tunda ta haifi yarta bata taba shiga da ita wani part na gidan ba sai yau zai daukan mata yarinya zuwa waani gun kuma ?
Wurin anty ya fara shiga tana falon ta zaune tana waya ta kashe wayan tana cewa yau yae rowa ce aka shigo muna da ita nan ?
Yace gata nan yau nazo da ita ashe ko rowan ake muna don ko ni yanzu saida akai min korafi ina zan tafi da ita kuma danayo nan ?
Tace mayar mata da yar ta don Allah kada kuma ace anzo da ita nai mata wani mugun abu.
Humm yace yana tambayan ina yaran basu dawo ba ke nan tace basu dawo ba ai basu san mummy su ta dawo ba ma.
Ya zauna sun danyi hira da ita yana wa yarinyar dan wasa duk da ta nuna tagaji tana son uwarta da ta saba da ita.
Ya mike yana cewa bari na leka wanan nasan tana can tana barcin gajiya tace Allah ya sa indai Rama ne kila dai wani abin take naji ta shiru.
Ya shigo muuna zaune da Fatima kallo take ita niko ina duban waya na nan Fatima ta gaida shi da dawowa ta mike ta fice falon.
Nace a, a baby kece kika girma haka namika hannuna sai ko yarinyar tazo guna na karbeta ina mata wasa.
Yace taso muje ki bani magani Rahama har yanzu jikina yaki walwale min ya juya na mike nabi bayan shi dauke da yarinyar.
Muna shiga falon uwar na ciki zaune ita da hindatu yadda ya barsu tana ganin yar ga hannuna take cewa miko min ita don Allah abinda nake gudu ke nan kabawa wata ya ta wallahi.
Ya juyo cikin mamaki yace waye watan Rahama data dauke ta ko may ni dai na mika mata yarta data lafe a jikina tace ni dai nace abani ya ta don haihuwa wuya gare shi.
Kowa ma ya haifi nashi ya dauka ban hana ba ni nawa na sani don ni na san wuyan da nasha akan abina.
Tana katban yar ta wwuce a hasale tana kallon jikin yarinyar kamar may son ganin wani abu ajikin yar nata.
Murmushi nayi ban tsaya ba nashige don na dauko maimaganin inda na aje mashi su na barshi da hindatu falon.
Na dauko ruwa a fridge na kawo mai tare da maganin batai min magana ba nima ban mata ba.
Ban fita ba don tana ciki na samu dogon kujera na zauna yake cewa kisa a kwashe kayan nan a shiga maki dasu ciki kafin a fara shigowa .
Munyi waya da Tahir yace zai sa a turo maki da sauran kayan zuwa gobe humm naji Hindatu tace cikin mamaki.
Nace wanan kayan kan ai daukan shi sai su Lawali mai wanki don yafi karfin daukan mace.
Mikewa hindatu tayi tana fadin anga banza ba dole ai cin amana a kwaso kaya haka kamar hauka ba.
Da kike kwaso naki banza ba wanda ya hanaki ai don haka dole ki bar kowa da nashi.
Ke Rahama bana son magana har yaushe kika dawo da zaki tsaya wani fitina haka ku baku raina magana.
Hindatu tace idan kin min rashin kunya ni yanzu zaki jini wallahi don ni ban daukan rashin mutunci yarinya.
In ba samun guri ba wa yaa taba tafiya dashi ya dawo da kaya haka sai kece kikafi kowa da zaki ce ba za ai maki magana ba ko may ?
Wanan kuma ai matsalar kice keda abin ya dama a rai, mace baki da aiki sai hassada da bakin ciki a rayuwan ki da kike naki sha, anin waya saka maki ido balle ke ki saka min ido haka ?
Eh lalai ma yarinya wuyan ki yai kauri wallahi samun wuri har yakai ki mayar min da amsa haka ko ?
Nace ke uwata ce da bazan fada maki ba ko mai yadda kika kada girman ki a gareni haka nima bazaan ji kunyan fada maki amsa daidai dake ba daga haka ma namike nakai kwance saman kujera da nake zaune akai.
Haushi ta kara ji kafana da yai fari sol ya fito daga cikin dogon rigar da na saka ko shi abin haushi ne gareta.
Kada fa ku sani magana ko ku fice min yanzu tace yarinya zaki san da wacce kike a gidan nan muje zuwa nida ke ne yar iska kawai.
Na dago zan bata amsa ya harare ni na koma na kwanta nai shiru tafice rai a bace da bakin ciki tab a ranta.
Rahama idan kina biyewa wanan haukan bazamu shirya dake ba na fada maki halin hindatu ne baki sani ba komay ?
Amma daddy kana ji ta take zagina yaya bazan rama ba tunda bata dau girman ta ba ita.
Na gane wanan matar baza, a taba zaman lafiya da ita ba wallahi may nai masu may na tare masu da zasu sakani gaba haka ?
Su basu tafiya da kaine wake masu haka idan sun dawo ko ni da aka raina za, aiwa haka kawai.
Mikewa nayi naji bama zan zauna falon ba yadda, yake son na zauna dashi gurin su lawali na nufa na samu suna wanki nai masu magana sai gasu na shigo nake cewa ga su Lawali zasu shigo su kwashe kayan yace OK kawai.
Sun kwasa suka nufi gurin mu dasu nace su shiga dashi inda anty su aje min a nan nan falon ta suka jibge kayan .
Ba ta dai yi magana ba tabi kayan da kallo kawai sai da na zauna na fara mata bayani da kuma wa yanda suka bani kyauta a can komai dai nai mata bayannin shi.
Sai dai ban fada mata na sayo mata wani abuba na kare da cewa sai su Amira sun dawo mu bude tare da su a gani.
Tacd indai an bude ai zamu gani tunda mu ba, a budewa damu dariya nayi nakai kwance don duk gabobina ciwo suke min lokacin.
Nan na kwata sai barci barci nayi sosai a gurin anty na zaune tana kallona yadda nake barci a gajiye.
Shedan yaso yai galaba a ranta inda yake kiyasta mata cewa ai dole in barci haka tunda banda aiki sai mannewa miji wai kamar Rama tasan yadda zata kwace zuciyan namiji kamar besty.
Sai kuma wata zuciya tace kai Saade ba girman ki bane fa hakan asalima kece kika saka ta yin tafiyan nan da tayi.
Yarinyar nan bata nuna maki komai ba a rayuwan hada miji da watace ai haka bazaki gane komai ba a kan ta.
Amma gashi yanzu ta zauna tagama fada maki komai bata boye maki ba don may zaki yarda daman ki da Allah ya baki a kanta komai fa kece silar shi a kan ta.
Tai saurin fadin astangafurullah Allah na rokeka kaba ni ikon cinye jerabawan nan da nake ciki a cikin nasara Allah kada ka nufe ni da bayar da kaina a gun wanan yarinyar.
Duk da bata son sanyin AC amma sai ta tashi ta kunna min don na kara watsakewa tana jin tausayin nisan tafiyan da nayi dole ne ta gaji haka ai.
Hayaniyar yara da suka dawo ne suka fada min a jiki suna murna suka tayar dani nima rugumay su nayi cikin murna ji nayi kamar nai hawaye.
Anty tace ai yanzu gashi kin tashi amma tun dazun nake tayar dake kiyi sallah kikaki yanzu ba gashi sun tayar da ke ba ?
Na rasa wanda zan taba a cikin su don daukin ganin su duk suka zauna min a jikina muna ta zuba surutu.
Da kyat na mike naje nai sallah suna biye dani ranan kan basuje islamiya ba muna tare sai da mukai sallah la,asar muka fito zuwa part din anty.
Nan muka fara bude kayan tsaraban da nayo masu duk wanda na fitar mai da nashi sai yaran su dauki ihun murna duk mun ruda mata shiya da hayani tana zaune cikin jin dadi na ware na kowa naba gajiye takaiwa sauran mutanen gidan nasu.
Ita Zulfa ta karbi nata dana yar ta amma hindatu taki karban nata har na yar nata tace ace min ban isa ba kuma ban kai ba, bakuma zan taba kaiwa ba nasani.
Ni dai na karba abina nace tayiwa kanta bani ba dama mijin ta yabada a sayo ai bani ba.
Anty tace bari nai wa besty magana ai shi yasa ta karba dole ba wani jayayya akai.
Nace anty kiyi hakkuri ai shi cin tuwon kishiya ranko neAllah ya bamu rai da lafiya kawai.
Dana nunawa anty kayan sayarwa na sai da tai mamakin su run nan ta fara zaba nace anty ki dauka kawai tunda kina son su.
Tace barsu kawai, biya zanyi ba aiwa sana,a haka sai mutum ys tabe idan bai ksrban kudin shi.
Bamu dauki lokaci ba yamma yayi yara sai murna sukeyi na samun tsaraba haka abinda suka dade suna bukatan su gashi na sawo masu shi basu ko fada min ba.
Rayuwa ya ci gaba da gudana a haka da dadi babu dadi a gidan ko yaushe da irin fitinan da zai bullo kai.
Gashi tunda suka fahinci banda komai a tare dani sai gori ya fara biyo baya kuma da anzauna zakaji sun fara habaici suna fadin.
Mutum sai kace juya a gida sai da aci a juye a maza haihuwa ai ba banza bane dama idan mace ta faye mannewa miji yaushe wani ciki can zai tsaya mata a jiki kullun kai kenan cikin zungura.
Wanan gorin da sukw min kan haihuwa har ranan ya dawo kowa na falon don yanzu ya kirkiro a dinga zama a falin na wani dan lokaci bayan la, asar.
Ihisan ta shigo tana fadawa uwar wai na ba su Amira sweet na hana mata ihisan ba
Showing 222001 words to 225000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75 Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153