sosai tunda har yai maki wanan hanyan.
Yanzu matsala zai dinga shigo maku sai kiyi ta hakkuri kada ki yarda a shiga tsakanin ku don korafi zai mai yawa idan kuma ke a fannin ki bai samun kwanciyan hankali ba abin mamaki bane kiga canji daga gare shi don mace shuumace.
Nace haka dai Inna ta take fada min kullun mukai waya insha Allahu zan zamo mai hakkuri da juriya daga duk wani kalubalin da zan gani a zama nan tare da shi.
Mun gama waya dashi na kira anty nake fada mata mun gama zaman camp har an yi posting din mu ko.
Banji tai min wani farincikin hakan ba nima dama ban yi tsan manin hakan ba a wurin ta don ba sabon abu bane gare ta.
Sai dai rashi na a gidan ta fara shiga wani hali sai take ganin ashe ba karamin amfani zamana yake mata ba a gidan don gashi dan rashi na da tayi na kwana biyu abubuwa na son jagule mata ko ta fanin yara abin yana son yafi karfin ta yanzu.
Gashi idan ba yar aikin ta ta dan samu zama da ita ba babu wanda zatai magana dashi haka zata wuni zur ita kadai a part din yara suna makaranta.
Sai yanzu ta san ba karamin rana Rahama take dashi ba a gurin ta bata kara tabbatar da hakan ba sai ranan da ta wuni ba lafiya duk gidan ba wanda yazo gaida ita haka ta wuni zur a kwance ita kadai don mai aikin ta irin matan nan ne masu kama da doleye sai dai ta wuni tana aiki ba magana .
Gajiye dai kan shigo su gaisa da safe daga haka kuma sai wani safiyan idan ta shigo gashi ita kanta ba dadin girkin mai aikin take ji ba da nake gari ne wani lokaci idan yaran sunce suna son cin abu kaza zatace kuje ku fadawa little mum tai maku.
Yanzu ko little mum tayi nisa dasu yaran sun dawo daga school Amira ta dawo da ciwon kai haka ta samu uwar ba lafiya babu mai kama wani tun yarinyar na ciwon kai har ta koma mata maleria ta rasa yarda zatayi ta tura Nasir ya kira Gajiye ya samu wai Gajiye bata nan ta fita unguwa.
Abu ya taru yai mata yawa gata a kwance ita babu moriya nan ta tuna halaiya irin na Rahama da ace tana nan ne yau suke haka ita da yarta da yanzu tana nan tana fadi tashi a kan su sannu yana zuwa yana dawowa garesu da kulawa yadda ya dace a kan su.
Rahama ko batace ba idan taga abinda ya dace ita da kan ta zatayi mata shi batare da ta sani ba za, a aikata shi.
Yanzu ne tasan ta rabu da wani babban bangare na rayunwanta yarinya mai matukar alheri a gareta da taimakawa ko sau daya bata taba nufinta da sherin da ada take ganin kamar abinda take mata da wani manufa take mata shi.
Son kai kawai yasa ta ta tsani yar mutanen da tasan kimarta da darajan ta, sam Rahama bata gajiya da kyautata mata dan bata taba gajiya da laluran ta dana yaran ta akanta.
Abinda taiwa Rahama kan graduation din yaran ta ne ya fado mata a rai ta sani sarai Rahama zata iya masu fiye da abinda tai masu a lokacin in har tana dashi amma ta rufe ido saboda tasha zuga tai mata cin mutunci.
Hakan da tayi bai hana taci gaba da kyautata mata ba da yaran ta amma ita da guda daya da Allah yabawa Rahama a gidan taki jinin ta bude ido taga yaton a idon ta tana jin haushi da takaicin yaron kamar ta shake shi.
Tun tana yi a boye har ta bari yarinyar ta fahinci hakan da takewa gudan jinin ta duk abinda take gwadawa yaron bai hana yarinyar taci gaba da so nata diyan ba tsakani da Allah.
Ta gyara kwanciyar ta wasu hawaye masu dumi suka biyo idon ta tace ni Saade wai yaushe na koma haka ne Allah ina rokon ka daka rage min wanan zafin kishin haka a raina.
Ta lumshe idanuwan ta kalamin Rahama ne ke dawo mata a rai da take cewa ba zantaba cutan ki ba anty a rayuwa idan ban soki ba bazan ki ba ko wanii naki don kece silar farin cikina a yau.
Amma sai take ganin a lokacin dadin baki ne irin na yaudara kawai take mata baya ta gama cuta mata mijinta da take matukar so yau yana kokarin nuna ma duniya akwai mazauni Rahama a zuciyar shi.
Yau gashi da ranta tana ji tana gani daga karshe Rahama ta barta kuma tana can tare da mijin zaman ta lafiya ta barsu nan suci kansu a tsakanin su.
Yau da Rahama tana gari da yanzu daga ita har yarinyar sun san abin yi ko gashi bata da wani dabara a hakan.
Idan bako tayi da zaran Rahama ta sani ta shiga da wainiya da shi ke nan har sai ya wuce idan babba ne zata saya mai sunan shi kaikoma saan tane zata girmama duk wanda yazo gareta ta dauke shi kuma da mutunci.
Amma yanzu da bata nan ranan ma da tai baki Hindatu na ganin su tai kamar zata buge su da mota tazo ta wuce su kamar bata gan su ba ma tayi tashige abinta.
Nan take ta tuna da daddin Rahama a gareta tace da Rahama ce da murna zata tare su tana haba haba dasu tana farin ciki da zuwan su harsu tafi.
Tana cikin wanan tunanen ne abin ikon Allah taji wayan ta na ringing har ya katse bata iya dagawa ba can kuma kira ya kara shigo mata da kyat ta iya daukan wayan sunan Rahama tagani a screen din wayan yanuna mata da Rama.
Ta dauka cikin dauri jin Sallaman ta kawai mun fara gaisawa na katse da cewa anty may ya faru baki jin dadi ne ta dan kakaro murmushi da kyat tace hakane Rama.
Nace subbahanallahi kin ko sha magani tace nasha sai dai bai barni ba ciwon har yanzu, ya salam nace anty kije asibiti mana a dubaki .
Tace dare ya somayi Rama nace haba anty ina Nasir abashi waya muyi magana dashi tace yafita baidawo ba.
Nace bani Amira anty, tace wallahi tunda yamma ta dawo ba lafiya ita ma tana can kwance jiki ya gashe mata hankali yai matukar tashi nace anty shine kuke zaune a gida haka.
Kashe wayan nayi take na kira wayan Hamza na fada mai cikin tashin hankali da ya je gida ya dauki anty da Amira zuwa asibiti don Allah.
Bai bata lokaci ba ya isa gidan da shiga ya nufi wurinta inda ya fada mata nice na turo shi ya kaita asibiti.
Bataki ta shirya ita da yarinyar suka tafi asibiti inda likita yai mata fada may yasa tabar Amira har jikin yai mata nisa haka ?
Nan dai akai masu allurai da magani da ita da yar Hamza ya dawo dasu gida mai gidan bai nan yai tafiya kasar Sudan a lokaci wayan shi kuma baya shiga.
Ina sallah ishai ya bugo waya gaisawa kawai mukayi nake fada mai zancen rashin lafiyan anty amma sunje asibiti an basu magani sun sha.
Nan nake fada mashi cewa harda Amira bata da lafiya yace bari ya kirata yaji yanzu mukai sallama ya kashe wayan .
Tana kwance ya kira layin ta sun gaisa yake cewa yanzu Rahama ke fada min keda Amira duk ba lafiya to yaya jikin tace Alhamdullahi mun samu lafiya Rahama ta turo hamza ya kaimu asibiti ai.
Yace yanzu ke idan da batai wanan dabaran ba haka zaku zauna da ciwo a gida yana cin ku sai yai nisa kuma ki sa mutane a wani hali.
Fada yayi sosai bata dai ce dashi komai ba yai mata Allah kar lafiya sukai sallama ya kashe wayan tai tsuki tana cewa kaman ya damu da mutane yanzu.
Kafin ya kira ai saida ya fara kiranta nasan shine take fada mai bamu da lafiya ya bugo min yanzu yana wani fadan karya haka.
Ban kwanta ba sai da nai mata yaya jikin da Allah ya bata lafiya mukai sallama na kashe wayan tana mai bani tausayi a raina.
Da safe ma tun da na idar da sallah na kirata muka gaisa na tambaye ta jikin ta tace taji sauki harta samu barci jiya sosai.
Nace a bani Amira don Allah mu gaisa sai da aka dauki lokaci duk wayan na a kunne aka kaiwa Amira nai mata yaya jikin tace da sauki nace ta karya da wuri tasha magani.
Ta dai amsa min kamar bata so ban damu ba nai mata Allah kara sauki nace ta gaida yan uwan ta tace zasu ji.
Haka na wuni akai akai ina mata ya jikin har dai nagane kamar tagaji da jina na daina kiran nata hakana tunda ta samu lafiya yanzu.
********* ********* *********
Muna zaune a falo gaba dayan mu har helen da kan zauna a tare damu idan ta gama aikin ta don ban matsa mata kada na zo na cutawa yar mutane gata ko banza ba musulma bace.
Karatu muke da Atika da ke assignment din ta don ta fara karatu yanzu har Aisha takan je wurin daukan lesson idan ina up.
Mamakin yadda yarinyar take da saurin daukan karatu nake gashi dai daga sama ta fara amma tana iya hada kalmomi yanzu da kan ta.
Sai nake gani da yanzu tana kauye a haka wanan basiran nata zai tafi ga banza bata amfana dashi ba sai tallan koko kawai da uwayen su ke sanaan yi kullun safe.
Wanda saura yan uwan su shi suke yi yanzu a kauyen babu karatu a tare dasu wanda ko a dakin su ne zai amfane su nan gaba.
Rokon Allah nake a zuciya na akan zurian da Allah zai bani nan gaba su ma Allah ya basu hazaka akan karatu na addini dana bokon baki daya.
Mun gama sai muka dan shiga hiran dasu Aisha da helen keyi wai sun fita sun ga wata mace ta raba sadaka da kan ta a hanya kuma kudi yan dubu take bayarwa.
Nace injin dai baku tsaya karba ba don kun san yanzu duniya ta baci zakkaga mutum da fuska kamar na Annabi ne shi amma yana da wata manufa a tare dashi a zuciyar shi.
Sallaman daddy ne mukaji a tsakiyan falon bai fada min zai dawo ba a ranan sai fanin shi mukayi kawai ya dawo a ranan a kuma wanan lokacin.
Atika ta mike da murnan ta haka ma sauran suna mashi sannu da zuwa shima da murna ya amsa masu taron da suke mashi din.
Duk da ina da kwaliya a jikina don bani zama hakana don bai gari don ban san ko wa zai shigo min ba ya samay ni babu shiri a tare dani.
Kallon shi nake daga inda nake zaune ina jin wani iri sin daddy yana ratsa min jikina har zuwa cikin zuciya na gashi ban iya tashi na tare shi ba sai faman binshi da kallo nake daga inda nake zaune.
Inda baba yake zaune a kasa yana ta wasa da kayan wasan shi ya nufa ya duka ya dauki yaron yana cabewa a sama sai washe baki yaton keyi don yanzu yasan mahaifin shi sosai.
Ko dan muna mu kadai ne sabanin dacan da sai an dauki lokaci bai ganshi ba, ko kuma don yaron yanzu ya kara wayo ne ban sani ba.
Har ya karaso inda nake zaune dauke da yaron yadan lakoto min hanci yana fadin irin taron da zan samu ke nan kuma yau ?
Nai dan murmushi nace to ganin ba zata nai maka mana daddy shine bazaka sanar damu kana tafe ba na shirya maka ?
Murmushi yayi yasa hannun shi daya ya dago fuskana dashi muka hada ido yai murmushi yace bani son ki wahal da kanki ne wurin cewa zaki shirya abin taro na dan nafi son kina hutawa a koda yaushe.
Yace yanzu baga kina zaune ba kina hutunki hankali a kwance da na sanar dake samun ki zanyi kin sha aiki duk kin gaji.
Na dan dago kai na kalle shi nai murmushi tare da cewa aiko yanzu daddy ba zan huta ba tunda abincin da mukayi nasan ba irin cimar ka bane da dare.
May kuka dafa ya tambaya cikin son ji nace dafa duka ne da vegetables a cikin sa kawai yace ke bakin ci ba Rama ?
Nace a sanyaye naci don nice ma ke son ci na zauna na dafa muna shi din da daren nan yace to nima shi din zanci in har akwai saura idan kuma babu sai nasha tea na kwanta kawai.
Nace balle ma akwaishi bamu cinye ba duka ya samu wuri ya zauna tare da gajiya a jikin shi nace Aisha zo karbi yaron nan ya huta please.
Yace haba barshi Aisha nayi missing din babana da yawa mu gana nace dake nagaji da daukan babana ne halan.
Murmushin jin dadi nayi don inajin dadin yadda daddy ke nunawa yaton so da kauna tankar shine din mahaifin nashi ba suna yaci ba.
Sai na tuna da lokacin da yaso sakawa yar wurin Zulfa sunan mama laraba amma taki ta saka sunan da take so ga yar nata wanda nasan hakan yaci mai rai kyalewa kawai yayi a ranshi.
Mikewa nayi na dauko mai ruwa da cup na kawo mai tare da tsiyaya mashi ruwan bai sha ba sai daya dan fara ba yaron ruwan tukun yako sha sosai ashe dama yaron najin kishi ban sani ba.
Yace kai Rahama kina ko kula min da uba wanan shan ruwa haka kamar tun safe bai sha komai ba yana jin kishi.
Atika tace daddy haka baba yake da son ruwa fa shi ruwa baya usan sa yace ai ko a dinga bashi nace dashi ya miko sauran wanda yaron yasha yai burtsatsi a ciki.
Yace haba Rahama baki son muyi zuminci ne da uban nawa nan gaba zuba min kawai ki gani dan Allah.
Na zuba mai ruwan cikin sauran wanda yaron ya rage ya zuke gaba daya na kara mai yadan yi wasa da yaton ya miko shi yace zai rage kayan jikin shi yaii wanka.
Ya mike na mikawa Atika da ta saura a falon yaton nace kaishi wurin anty Aisha tai mai shirin kwanciya kafin nazo tare muka shiga dakin dashi.
Saida na hada mai ruwa bayan ya shiga wanka na tsaya na kara gyara dakin tare da kwashe kayan da ya cire na ciro mai riga mai saukin sawa na dora a saman gado na fita zuwa hada mai abinci kafin ya fito daga wankan .
Tare muka zauna bayan yafito yaja cin abinci muna hira akan tafiyan nashi inda yace dani yaje duban wasu kaya ma adanai ne a can sudan kuma sunyi nasaran samun kayan a can din da suka je.
Nai farin ciki sosai dajin wanan labarin inda na taya shi murna mun kuma koma hiran a kan ciwon anty nan ya nuna min bacin ranshi na akan may zata zauna da yarinya a gida ba lafiya hakana.
Nan dai mukai hiran mu daga karshe muka mike zuwa ciki don na fahinci yana son hutu a tare dashi duk da nasan idan mun shiga din bawai kwanciyan zaiyi ba sai ya samu natsuwa a tare dani.
Washe gari ban tsaya ba na shirya mai abin karyawa don kada na makara har ruwan wanka sai dana hada mai kafin nabar gidan.
Bai tashi ba don gajiyan da yake dashi sai sha daya yafito a cikin shirin shi inda ya zauna ya karya ya mike ya shiga store din mu ya dan duba abinda bamu dashi a ciki yafito ya fice a gidan.
Da wuri na dawo gida dan ina son shirya ma daddy abinci lafiyayye don dawowan shi.
Bendi sa na jawo na ce da Aisha ta wanke min kafin nafito na shiga dakina nai sallah tare da sauya kayan jikina nafito na dora girki inayi muna hira da yaran har komai ya kammala min yadda nake son shi.
Sai dana kusan gamawa ne ya shigo gidan inda yaton shi na na Abuja Sani ya biyo bayan shi da kayan amfanin gida a ledoji niki niki.
Sannu da zuwa muke faman yi mashi ya amsa muna nan yazauna sukai magana da sani na dan lokaci yai muna sallama yatafi.
Ban zauna ba sai da nakawo mai abinsha yasha sai kuma ga kiran waya ya shigo mai ya dauki lokaci yana wayan ina zaune daga gefen shi ba dai sauraren shi nake ba amma kuma sai na fahinci kan business din shi ne yake wayan.
Neman kudi akwai wahala nace a raina don mutum baida lokacin kan shi kullun busy mutum yake naganin yaya zaiyi ya hada ya zama mai kudi.
A yadda na fahinta yanzu kamar daddy yayi watsi ma da aikin shi na filaye da yake a Abujan yafi bada karfi a fanin business din shi nake gani.
Don kamar yafi mai muhinmanci da kawo mai kudi duk dai shi ba mutum bane da ke zama da mace yana fada mai sirin shi kamar wasu mazan can.
Da hannu ya nuna min wasu kayan da Sani ya zube a falo
Showing 282001 words to 285000 words out of 456145 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95 Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153