?
Yace wanan kuma maganan ki ne ai ni dai sadakan da ta bayar na abin amfani yakai ga mahaifina nakewa magana yanzu.
Ta bayar ko ka bayar sau ka fadawa wanda bai san komai ba anan duk banbancin da kake gwadawa sai kai tayi tunda bazaka iya bari ba ya zama ma hali.
Ba yau na na sani duk abinda zai haska Rahama a udon duniya muko muyi baki shine gurin ka ko yaushe.
Hindatu tace niko a nan banga wani abin fitina ba don ya fadi haka don kowa yasan halin kowa a cikin mu ba wanda aka hana yi sai dai in ba kaso ba.
Ko yanzu ai bai baci ba zaki iya kaiwa massalatai a bada ai tunda itama da ta raba ba ita da hannun ta take bawa mutane ba kuma kin gani da idon ki ai.
Hindatu idan ina magana bana son ana min saurin katsewa tace may ye na katsewa a nan tunda nima zancen ki ya shafe ni ai.
Fada ya kaure masu a wurin sai gori ya tashi tace ni nasan rayuwa na kike nema Raliya tunda kika iya sani haihuwa dole a zaton ki cikin zai zube ban haifa ba ko ?
Tace wanzan ai don anmaki ranawa ne don kema haka kokaiwa wata ai ko kina nufin ban san yadda kikaiwa zulfa ba a baya.
Daddy yace lalai abin naku akwai samun wuri sosai don kunyi ban dauki mataki ba har kukewa junan ku fade haka.
Hindatu tace ita Zulfan ra fada maki hakan zulfa tace ai gata idan mun taba wani zance makamancin haka
May ma zai kaini wana magana tunda ta hannun damarki ne sai Raliya take cewa baki fada min may ba munafuka ko Rahaman da kuke tare kin barta ne halan.
Ina nan kwanaki kike cewa ta baki maganin daukan ciki don kyeta kika bata na haihuwa diya mace.
Murmushi nayi daga inda nake zaune sai dai ban yi magana ba don nasan ba wanda yasan zancen na bata magani ko shi maigidan.
Tace munafuka bake kika kawo zancen wai maza take haihuwa shiyasa yaya ke son ta ba haka nace anya ba hakana bane itama tana son diya mace sosai gashi ni dake son namiji da tavan magani sai na haifi mace.
Daddy yace yanzu dai na gane komai a nan ita Rahama dai itace mai hakkuri a cikin ku don har yau ba a wanan zaman kaji ance ga zancen Rahama ga dayan ku.
Haka kuma lalurar ku zai zo tayi tsaye akai yana cikin fadin maganan ne aka shigowa Raliya da yar nata da take muna boyen ta kada mu ganta.
Kanta yai kato ga idanuwan ta a waje saboda nauyin kan ta daya rinjayi jikin ta da komai.
Fada take tana kokarin bawa yarta nono tana boye ta na mike daga inda nake zaune zuwa wurin ta tsam na dauki yar daga hannun ta na shiga dubata a hankali.
Sai duk suka bini da kallo auna girman kan nakeyi na duba yarinyar da kyau nace surgyry za aiwa kan yarinyar nan daddy.
Yace kina ganin haka zai yuyu kuwa nace may zai hana tace aiga uwarta nan idan ta amince sai take cewa wallahi bazan yarda ba wa zakiwa bakin ciki don kinji zai fita damu waje zaki kawo wanan issue din yanzu.
Nace to Allah ya baki hakkuri ni kinga tafiya na ma na juya inda sauran suke nace na barku lafiya Allah ya sauwaka.
Sai naji daddy yace na dama kin amince don wanan abar ba inda zan kaiku na fada maki.
Nan sukai ta jidali kuma yace ai tunda ga sauki ya samu har gida tace bata so sai waje to ki zauna da ita hakana kina kallo.
Sunyi fada sosai washe gari nikan na shirya na bar garin don zan tafi sokoto wani aiki a can da mun koma.
Wasa wasa sai da suka share sati uku suka dawo duk lokacin ina sokoto kebbi zamfara muna aiki dasu.
Na dawo garin a jike dan irin wanan fitan ba karamin alheri muke dawowa dashi ba idan munyi shi.
Tsaraba sosai nazo masu dashi naba kowa dake gidan ban bari na dauki loiaci ba dama ina shayar dasu yan biyu na don sunyi saurin samun kafa sosai yara sun taso gwanin ban sha, awa dasu.
Daki na shige nai barci sai biyar na yamma na tashi nai wanka nai sallah dana gama na dauko abinci don naci.
Ranan nice zan yi girki har su Aisha sun kammala min komai ko gyaran wurin daddy nayi da yan wasu aiyuka.
Na fito daga part din ina zama falona yara suka rufe ni kowa da irin korafin da yazo dashi ina biye masu nan daddy ya samay ni dasu yake min sannu da zuwa.
Mun gaisa ne yake tambayana sokoto nan nake bashi labarin yanayin wurin da yadda aiki ya kaya muna a can da muka tafi.
Amira ce take fadin wai idan zan koma tana son ta bini taga yabayin garin itama nake cewa zafi ko zai kusa karki ai don weather su akwai zafi sosai .
Nan nake fada masu in two weeks zan tafi ibadan akwai wani seminer da zamuyi a can na kwana ukku ne kawai zamuyi.
Daddy yake cewa shifa gaskiya wanan yawon nawa ya fara isar shi a rayuwa nace nima va da son raina ai nake barin yarana haka ba na tafi aikine ya zo da haka .
Da sannu komai ke tafiya har tafiyan nawa yazo na samay shi don na tuna mai da zancen sai ga Raliya tashigo falon taji yaja fada akan tafiyan nawa.
Aikin kan tunda kana auren likita mace ai sai kai hakkuri don mijin likita dama da hakkuri aka san shi ai tunda aikin su ba tsarin addini a cikin sa.
Allah ko hakane ashe kike daukana ban san addini ba shiyasa nagan ki malama ai ke Raliya ban son shigan tsugula ke take aure ko ni da zaki zo min da wanan magana haka ke naki aikin tsari gare shi kullun cikin rikici ga yaudara ba gunma wanan na taimakon al, umma ba da irin aikin ku.
Jin amsan da daddy ya bata yasa na yi shiru na barshi yai mata tas yana fadin shi bai son abin musgunawa mutum ina ruwan ta da zancen mu
Nai tafiya na tare da Aisha da yara na daga can muka shiga lagos nai masu sayayya sosai na aure muka dawo gida.
Washegarin dawowan mu ne muna falo zaune da yara sai ga helen ta shigo tana kuka nake tambayan da ke lafiya may ya faru ne wai ?
Ta ce mummy wanan yaron ne ina shanya kaya ya rungumay ni haka ma ranan ya taba min nono na nace wake nan da karfi tace Ahmad.
Mikewa nayi tana gaba ina bayan ta har inda yake zaune daga shi sai singlet a jikin shi da gani ma shaye shayen shi yayi a lokacin.
Ina zuwa ban tsaya jiran komai ba na kwashe shi da mari zaiyi magana na sake azamai wani marin a tsakiyan fuskan shi yace akan wana yar kafiran zaki mare ni.
Nace ashe kasan kafira ce kake son kyeta mata hadi to bari kaji akan wannan matsalan sai nasa an daure min kai a garin nan idan halinka ne kuma ka sake yin hakan.
Na juya na barshi a wurin tsaye yana mamakina ban dade da zama ba sai ga uwarshi ta shigo har part dina da fada akan kafira zan mara mata da ita bazata yarda da wannan ba.
Raliya ban taba sanin ke kamar dabba kike ba ashe sai yau keda zaki tayani mu yake shi a kan wanan dabiar banzan zaki zo har kina fada akan na dauki mataki kan shi.
To ki sani helen zaman amana take a wurina ke koba helen ma yaiwa haka ba naji irin matakin da zan dauka ga dan banza ke nan mara tarbiya.
Ashe kece mai daure mai yana lalata yaran mutane tunda har kika iya zuwa fadan na mare shi yanzu.
Idan kuma kika kawo min rashin hankali yanzu zanyi maganin shi a gidan nan ha sai anjima ba ma.
Fada sosai mukayi da ita ranan abinda ban taba tsayawa yi da wata ba a gidan ke nan irin haka bayan fitan ta ne daddy ya dawo tun a waje Nasir ya tare shi yana fada mai abinda ya faru tsakanin mu.
A hasale ya shigo gidan wurina ya nufo yana fadin may ya kawo fitina a gidan nan ?
Shiru nayi don har lokacin raina a bace yake yace bake nake tambaya ba ne kin kyale ni da kyat na bude bakina nake cewa dashi.
A kan Ahmad ne yake son ketawa helen shine ya kawo fadan don uwar shi ta nuna bata yarda da matakin dana daukarwa dan taba tunda ba gida na bane haka kuma ba gidan uban helen bane.
Yana jin haka ya juya a fusace sai part din Raliya tana zaune falonta tare da yaran ta shi ko Ahmad yana zaune daga shi sai singlet a jikin shi a haka ya wuni tun rana kamar wani dan iska uwar bata kwabe shi ba da zama hakan.
Ya juya a wurin yaron yace kai gobe idan Allah ya kaimu ka shirya ka koma gidan uban ka ba zan zauna da kai haka a gidana ba fitinar yau daban na gobe daban.
Har ta fara tafiya ya juyo tare da cewa kaji na fada ma gobe kada na samay ka a gidan nan zan fadawa masu gadi da kada su bari ka shigo min gida again.
Ya fara tafiya Raliya ke cewa ai wanan ba adalci bane ka dawo an fada ma karya da gaskiya sai ka hauka zauna a kai.
Yace may kike son na bincika cin mutuncin da kikaiwa matana akan dan ki da baida tarbiya ko may kike son naji ?
Ai dama nasan karya da gaskiya zata fada ma don kawai tana bakin ciki da zaman yara nan a gidan nan kawai.
Yace cikin mata wani irin kallo amma baki da adalci ko a kan ki tunda kuke abun ku kin taba jin Rahama tai magana akan diyan ki gidan nan.
Ko yanzu ma daya tabo ta ai bata fada min sai yaran da akayi a gaban sune suke fasa min ita bata ce dani komai ba.
Ya juya yana jin tana fadin ba inda zaitafi tun da ba a gurin uban shi yake ba inda nake nan zai zauna.
Yaron yace ni mama ban san may yasa wanan mijin naki yake min haka ba nifa zan ma daina gaidashi ne wallahi.
Tace rufa min baki mara kunya kawai ai duk kaika jawo wanan tsiyar ka sani sarai daga shi har Rahama ba su da wasa a kan yaran su.
May ya kaika ga yaran ta kasan yadda ta zamawa kowa kamar ciwon ido daga ita har yaran ta a gidan nan.
Mama kan yar kahiran nan ne fa ta mareni for god sake wallahi wallahi idan ta sake sai nayi maganin ta a gidan nan .
Kada ka soma wallahi don Rahama da kake ganin ta nan tafika bura uba wallahi sannan kuma kana ganin ta nan tasan kanta fiye da tsanmanin ka.
Aikin ta yasa tasan mutane fiye da yadda kake zato don dai bata da yawan hayaniya ne sai idan an tabe ta.
Smma tafi min wa yan nan munafukan ko dazun na daiyi fada ne kawai amma ba wai gaskiya ne da kaiba ko nice haka zan ma.
Ya mike yana gunaguni yabar falon ran shi a bace a lokacin da safe naji suna rikici sosai kan barin yaron gidan.
Ban so saka masu baki ba sai dai sam bana son a samu matsala a saboda ni tare muka shiga da su Zulfa da kyat muka samu daddy ya hakkura da zancen.
Sai dai ban fadawa kowa manufa na ba naja bakina nai shiru haka rayuwan yaci gaba kowa na harkan gaban shi ba mai yarda da wani kowa tashi ta fisheshi akeyi.
Bayan kamar wata uku da case din mu da Raliya sai ga wani sabon rikici kuma wai yaron ya shiga wurin yar aikin hindatu kuma again.
Wanan karon kan tsaye daddy yayi sai da yaga yaron ya kwashe ya bar gidan haka ya kawo tashin hankali sosai a tsakanin su da uwarshi.
Har yakai daddy ya furta ya saki Raliya ba karamin tashin hankali ta shiga ba don a zaton ta irin asirin da takeyi ba zai iya taba furta kalma haka ba a gare ta.
Barin ta gidan ya dan kawo kwanciyan hankali don baka jin wani hayaniya ya auku kuma kowa na kokarin hade kishin shi a tsakanin mu.
Haka yasa har yaran suka dan fara samun kwanciyan hankali ranan aka aiko yar wurin Raliya din ta rasu ba wanda yaje mata gaisuwa daga cikin mu.
Ni ban ma da lokaci don haka ban damu da abinda akeyi a gidan ba hindatuce taso tayar da halinta itama daddy yasa mata waigi dole ta daina ta zauna lafiya da kowa.
Sallah muka tafi kano gaba dayan mu can ma mun samu anyi muna gyaran gida yadda ya dace gyaran yayi kyau sosai.
Na roki daddy don ya barni nayi sati daya a kauyen mu amma ya hana kwana uku kacal ya bani haka naje nayisu na dawo kwanan mu shida kano muka dawo Abuja ni da yara don Nasir zai zana jerabawa shi na karshe a jamia.
Ga zancen auren Aisha dake gabatowa duk abin ya rikice min akaina yanzu duk da nasan cewa banda wani matsala sosai don dai sai dai nace Alhamdullahi don Allah ya buda min sosai yanzu.
Ban san yaya akayi gulma ya shiga tsakanin zulfa da hindatu kan auren da zanwa Aisha har suka samu daddy don jin idan shi yayi kayan dakin da naiwa Aisha din.
Bai basu amsa ba sai da yai wani tafiya ya dawone ya tara mu yake cewa dama don tafiyan dake a gabana yasa ban baku amsa ba a kwana ki.
Falon yai shiru muna saurarwn shi yace Zulfa da hindatu kunzo kun samay ni da zancen akan kaya dakin da kuke ganin Rahama na wa yar uwarta.
Da sauri na dago kaina ina mamaki yace gata zaune a gaban ku sai kuji idan na bata wani gudun mawa akan bukin nan ko.
Yace zargin ku akan wanan yarinyar yai yawa wallahi ina son ku sani yanzu Rahama ba yadda kuke daukan ta take ba.
Ko da can baya ba damuwa tayi da kawo min korafin ta ba wai nai mata.
Balle yanzu da take amsan daruruwan kudi duk wata a matsayin albashi a gare ta bata rasa komai ba a gidana na biyan bukata.
Kuna gani yadda sauran ma,aikata suke fifita kan su a gidajen su da sauran abokan zaman su.
Amma ni ina mamakin ku yadda duk hankalin ku ya gushe ajan abu daya ko yaushe ni dai a sanina Rahama ba mace bace dake zama tana min korafi a kan ku duk da tasa cewa ina taimaka maku lokuta da dama takuma sani amma batai min korafin yin hakan gare ku.
May yasa ku baku daurewa ne daganin tana abu baku zargini ba ko ita alhalin kun san tana da hanya yiwa kan ta abu a rayuwan ta.
Yadda take da hali ai muma muna dashi ba sai ka tara mu kai muna tozarci ba inji hindatu ita ko Zulfa cewa tayi.
Magana mukai maka ba don komai ba sai don bi namu hakkin akan hakan don muma muna da yan uwa ai.
Yace wani ya hana ku jawo su a jikin ku yadda ita take jawo nata take zama dasu har suke samun karuwa irin haka don duk yaron da ya zauna a wurina dole ne yana karkashina na taimaka mai idan harkan shi ya tashi balle Aisha data kwashi shekaru a wuri na bata da gajiya da dawainiya damu ba.
Take dai dawainiya da wacce take wurin ta ko inji hindatu yace idan tayi da yarana kamar dani tayi ai.
Daddy don Allah abar wanan zancen haka ba zargi sukeyi ba to abarwa Allah don shi yasan komai don haka ni ban da lokacin irin wanan maganan haka.
Mikewa nayi daddy yace dani koma ki zauna na koma ba mussu na zauna ina sauraren shi yake cewa damu.
Wanan halin ya isheni haka wai ku yaushe ne zaku san kun girma ku dai na haka a tsakanin ku kullun hali daya.
Yau ma ace nine ke wannan abin may ye na damuwa a cikin sa balle in dai Rahama ce bata da rayuwan yawan roko na ko yi min ko yaushe na fada maku.
Ana zaton girma yazo maku zaku daina abubuwa amma abu sai karuwa yake maku haka to ku sani hakan ya isheni kada ku mai dani karamin mutum ko yaushe.
Duk wacce ta karamin wanan halin ta kuka da kan ta don ni ban son yawan zargi nan yana bata min rai sosai wallahi.
Zulfa ce ta iya cewa dashi anyi kuskure za a gyara nake cewa dashi Allah ya kyauta namike na basu wuri raina a bace.
Watau ita dai kishiya ba yarda ko amana a tsakani ke nan ji Zulfa da wasu abubuwa
Showing 408001 words to 411000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137 Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153