suna da haihuwa biyu ko ukku wasun su ?
Sadiya naso ace kin girma a gaban su inna da wanan wayau naki bazai dauki garin naku ba mema sunan kauyen naku ?
Lah yaya har ka manta da sunan garin namu niko ko barci na tashi akace min meye sunan garun mu zan ce Anchau da gudu.
Yau hausa suke a tsakanin su sosai don bai faye mata magana a cikin yaren hausa ba nice dai koda yaushe hausa nake mata a tsakanin mu don kada mu manta da yaren mu mu koma gida ai muna dariya wata rana.
Idan ba haka ba sai ince da yanzu sai turanci da yaren yan garin da take ji a yanzu don saurin daukan yare dake ga yaro ko ni ba a barni a baya ba wurun daukan yaren su don ina jin wasu masu saukin dauka a yanzu duk da ban mu,amula da kowa sosai kamar maya da yanzu naje gidan su yafi a kirga don kaina .
Gashi duk zuwa kakan maya din sai ta hada min maganin irin nasu ta ban wanda ban san irin amfanin su ba a gareni ina dai karba ina sha don sanin ba masu cuta min bane.
A zancen da yakeyi da sadiya din kuwa raina yakai kololuwar baci a lokacin dashi don fadin wai ya manta da sunan garin mu a cewan shi yanzu.
Ba abin mamaki bane don ka manta da sunan mahaifan mu ai yanzu tunda ka biya bukatan da kake dashi akan mu.
Murmushi ya sake tare da fadin ai ban isa in manta dasu ba a rayuwana sunan garin kawai na manta kuma sadiya nake tambaya ta fada min ba wani ba.
Ai gata nan sai ta fada ma da bakin ta kafin ma na rufe baki sadiya tace dashi ANCHAU ne sunan garin mu yaya.
Gaskiya sunan garin akwai dadi sosai kuma gashi garine da ya tara manyan yan boko da suka san kansu a tahirin kaduna kaf.
Yanzun ma ga wasu karin an samu harda yan scientic a cikin su mata masu kera fasaha da kansu don wanan matar tawa nan gaba .
Sai lokacin na gane zolaya yazo dashi akaina na neman jin bakina kawai yasa ya fadi haka akan garin mu.
Nace gara dani nasan asalin garin mu wasu ko kauyen su basu san hanyar shi ba har yanzu sai kame kamen garin wasu sukeyi da sunan nasu.
Sadiya ke kinji akwai wanda zaice bai san asalin garin su ba ko ga suna idan ba karya ba.
To idan nan sani din a tafi mana in ba tsoro ba na fada ina kwashe kafafuwana ina dorawa saman kujera tare da kawar da kai a gare su.
To zamu gani idan mun je Nigeria idan wani zai nuna min hanyar asalin garin mu lokacin da nake zuwa ke kina ina ?.
Zamu gani idan an tafin ai in ba burgan aiki ake muna ba a nan don banga alaman an sanda yan kauyen ba sai yan birni.
Wai yaushe zamu tafi gidane yaya sadiya ta tambaye shi da saurin don jin yace idan mun tafi Nigeria zai kaimu garin nasu.
Zamu tafi idan ki samu hutu sadiya har in yayi daidai da lokacin banda aiki sosai zamu tafi.
Ko yanzu dai ba wani amsa mai karfi na fada a raina ina dan tunane kafin naji sun buge da hiran gida shi da sadiya din fitan da basuyi ba ke nan a ranan sai washe gari muka samu fita dashi ya kaimu yawo cikin gari tare da yin sayyaya mai yawa muka dawo gida dashi a cikin farin ciki iyakar abinda ke tsakanin mu ke nan dashi ko yaushe.
Da irin wanan har muka shirya fada ya kare a tsakanin mu a yanzu mun koma daidai a tsakanin mu yakan shigo mu dan taba hira da yakan yi kamar na dole wani lokaci.
Wani lokaci zanyi zargin bai daina komai ba a cikin halaiyar shi don ba wani canji da nake gani dake nuna ya daina din.
Abinda ban sani ba shine abune mai wuya ashe koda mutum ya daina wasu halaiyar shi ya dawo daidai lokaci guda kamar yadda nake tunane ni.
Abin ba haka yake ba don shima yaya din yana fama da kansa ne sosai boye hakan yakeyi kada mu fahinta da hakan.
Haka zai ta fama da ciwon ciki wanda bai san kanshi ba sai da kyar zai samu ya lafa mai ko kuma wani kumfa mai kauri ya dinga fita mai a baki zai wuni yana fama da wanan laluran yana faman shaye shayen abinda zai lafa mai da ciwon .
Ranan ya fita wurin aiki sai gashi zuwa karfe daya sai gashi ya dawo ina dakina kwance ina barci .
Dakin shi ya nufa a gigice ya fada saman gado a yadda ya shigo din ko takalman kafan shi bai cire ba don zafin ciwo.
Kamar a mafalki nake jin wayana yana ringing da kyat na bude idona na kai ga wayan na dauka muryan shi babu dadi yake fadin.
Wanan maganin da kika taba bani nake son ki bani yanzu idan akwashi a wurin ki har yanzu ?
Kana ina yanzu yace part dina kwance banda lafiya tun daren jiya da kyat na samu na fita yau dama.
Maganin na dauka na jika kamar yadda tace na nufi wurun shi wani irin juyi na sameshi yana yi shi kadai a dakin da sauri na karasa inda yake din ina mashi sannu.
Ya tashi da kyat yana karban maganin ya kafa kan shi saida ya shanye ya cire baki sa yana miko min cup din daya sha maganin.
Zaune nakai gefen shi tare da kura mashi idanu na dan lokaci sannu a hankali na fara ganin yana karya zufa a goshin shi sai barci.
A cikin dabara na cire mai takakman kafan shi sai ya bude idanu shi ya sauke a kaina tare da fadin nayi barci ne ko ?
Wai da takalman zan cire ma ko zaka ji dadin barcin nan wurin ne yake yawan damuna sosai sai yayi kamar ya bari kwana biyu kuma sai naji ya motsa min ba dadi wallahi ya fada yana bata fuskan shi.
Da zaka daure ka sha maganin na yan kwanaki mu gani ko Allah zai sa a dace a hakan zan sha ya fada a dan maraice yana lumshe idanun shi a haka barci ya daukeshi yana sake ajiyan zuciya kamar karamin yaro.
Tagumi nayi ina tunane ni kadai a dakin sai bin ko ina na dakin nakeyi da kallo amma a can kasan zuciyana sai tunanen kada fa wanan abin ya halaka wanan mutumin ta dalili na.
Don yanzu kan na yarda da cewa maganin kakar maya ce ke bashi wanan matsalan haka yake hanashi sukuni da sakashi yawan ciwon mara da ciki da yake complain ko yaushe .
Lalai idan haka din ne kuwa ya zama dole in koma wurin kakar maya in mata bayanin komai dake faruwa kan abinda ta bani na bashi din yasha .
Don ni har yanzu ba wai naga wani canji bane a gurin shi banda wanan matsalan dake taso mashi na yawan ciwon mara din.
Gashi har shi kanshi ya fara zargin hakan don wanan zancen daya taba fada min a gaban mami din ya nuna yasan na bashi wani abu yasha da yake zargin hakan.
Kwana biyu yana shan wanan dan abin mai kama da kankara da nake jika masa yasha yana kuma dada kara samun sauki don idan ya sha sai wani irin zufa ne zai dinga karyo mashi a duk kafofin jikin shi lokavi guda sai ya tube yana neman sanyi a jikin shi.
Haka yakanyi duk tsawon kwanakin nan da yake shan wanan maganin dan hakane ma baya sha yanzu sai da dare idan zai kwanta.
Na gama bashi maganin na juya zan fitane naji yana fadinn wai zainab waya baki wanan maganin da kike bani ne ?
Na tambayeki ranan baki ban amsa gamsashiya har nake zaton ko mami ce ta aiko maki dashi ki bani tace bata san zancen ba ?
Dan shiru nayi kafin na dago kai nace mai na fada ma dashi nazo garin nan dama ina dashi a wurina nakan yi amfani dashi idan cikina yana ciwo.
A zaton ki zan yarda da wanan maganan da kike fada ne ko kin mata farkon zuwan mu kasan nan kiyi ciwo mara saida aka kaiki asibiti ?
Baka yarda ba ke nan dani ai da kada kasha tunda zuciyar ka yana baka zan iya cutama ne da maganin .
Ban ce hakan ba amma kin san dalilin da yasa kike min amfani dashi wanda yasa nake zargin hakan a kanki sai yanzu na kara tabbatar da hakan.
Kada ki dauke ni karamin yaro da baisan abinda yakeyi ba zainab na kallo shi da sauri don jin abinda ya fada yace eh.
Na dade da sanin komai shiya har da farko nake zargin ko mami ce ta baki kiyi min amfani dashi ashe tunanena bai bani daidai ba.
Kece don kanki kika ga daman yi min amfani dashi ai da saiki fada min tun a Dubai da kika fara saka min nasha wahala kamar zan mutu.
Kin ko san kwana na kawai ke gaba a wanan lokacin dan da zan iya mutuwa a wanan lokacin.
Hawaye ne yazo min masu dumi kan maganan da yake fada min din na kasa furta komai sai hawayen da nake zubarwa kawai.
Babu abinda zan iya fada tunda har ya gano hakan a yanzu nace dashi don kawai yana wanan halin na bashi magani ya daina ko don ina son shi nayi masa hakan bai sani ba tunda gashi yana fadi da bakin sa ya san na bashi wanan maganin kan wani dalili nayi hakan zan bashi amsa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA



YAN UWA MUSULMAI BARKAN MU DA SHAN RUWA UBANGIJI ALLAH KA YANTA MU CIKIN YANTATTUN WANAN WATAN MAI ALBARKA AMIN YA ALLAHU.
ALLAH KA KARFAFA MUNA ZUKATUN MU MU ZAMO MASU KASKANTAR DA KAI A GARE KA AMIN YA ALLAHU, , , , ,

LITTAFIN KUDINE YAR UWA DON SAYA SAIKI KIRA WANAN LAYIN 08036959257 KO 09026931792 DARI UKUNE KAWAI KUDIN SA ALLAH YA BADA IKON BIYA YAR UWA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DA YARDAN UBANGIJI, , , ,


Rayuwa haka ya kasan ce ba tabbas a tsakani da yaya akan cewa ya daina duk wani halaiya nasa mara kyau a yanzu.
Ni dai tunda yace yace ya daina na dauka din ya daina ko ya rage don ba yarda nayi da hakan har kasan zuciyana ba.
Sai dai ba wanan zancen a tsakanin mu ban sani ba ashe yaya yana nan yana shirin tafiyan mu zuwa Nigeria a asrince.
Don daga gyaran gidan da zamu zauna har suturo da duk wani abinda zamuci ko amfani dashi an gama hada komai a can Nigeria din ya tura wasu daga nan wasu kuma an saye a wani kasan an tura can Nigeria din.
Ko mami bata san da wanan shirin nasa ba balle wani dan uwansa ya sani dama dai jamal ne wanda nasu yazo daya da jafar din .
Yanzu ko sun raba gari a tsakanin su do ma mahaifiyar su na tsaye a kansu ne yasa basu kai inda ba,a so ba a tsakanin su din.
Don shi jamal din ga baki daya ya tsani jafar gaba daya a rayuwan shi ya tsani duk wani abinda ma ya fito daga hannun jafar din.
Tun yana iya boye hakan a zuciyar shi har yakai mami ta kai ga fahintar hakan duk abinda ya fito daga jafar din shi jamal baya amsa baya ko kallon abin.
Ranan a gaban kowa mami ke masa fadan hakan sam ta manta da cewa sauran yaran basu san halin da dan uwan nasu ke ciki ba a lokacin.
Take fadin Jamal ina kula da take taken ka kan dan uwanka kana nuna kyama da tsana akan komai nasa.
Duk halin da jafar ke ciki a yau ko ma ya zama abin kyama ne a gun wasu banyi tsammanin ku zaku iya guje masa ba ai.
Tsit sukayi falon kowa na kallon su kafin shi jamal din yace mami nifa ba tsanan shi nayi ba ina dai koyi ga abinda sunna ya koyar da mune ga masu wanan halin kawai.
Hali wani hali kuma kega ya J da har zai fadi haka mami kawai kila hassada ya jamal ya fara a kan dan uwan shi .
Amma meye matsalan da har zai fadwa dan uwan shi haka ni dai a gareni banga wani abin kushewa gun ya j din ba sai dai wanan bakauyiyar yarinyar da yake aure kawai wace bata san kanta ba balle na wasu .
I realy totally hate dis zainab yanzu wallahi ji irin dukiyar da shegiya ke ciki amma bata san yadda zata juyashi ba dan gidadancin dake damun yar iska.
Wani kallo jamal din ya watsa mata tare da fadin dan Allah gafara can ki rufawa mutane baki gada na balla ki a wurin nan.
Tunda bakya son ta ba sai ki kasheta ba ko ki fitar da ita cikin daulan da kike kyashin zaman ta din a yanzu.
Zainab da kike gani tafiki hankali da wayau sau dubu dan ita tasan ya kamata ba wai daula ko arzikin shi ke gaban ta ba ita.
A,a,a ke Aisha ki kyale bakin ki fa akan zainab don bata taba laifi a gaban bros tun asali kin sani .
Ta sani mana tunda yafi son ta sama ga dan uwan shi tunda ta iya makirci har ta gaji a rayuwa har yana wani son ririta ta yanzu a gaban kowa.
Mikewa yayi tsaye don fita daga falon yana fadin gaskiyane dai baki so mami amma yarinyar nan ai bata cancanci irin wanan ba a wurin ku yanzu tunda kunsan zaman da takeyi dashi itama.
Sakarai kawai mara hankali zanga yaushe zakayi hankali ka daina wanan halin wai kai mai ra,ayin rikau hakan.
Fita yayi bai juyo ba yana fita jalal ke fadin mami wai me ya J yakeyi ne da kullun jamal ke nuna baya son shi haka ?
Kyale mara hankali da baisan me yakeyi ba dan kawai dan uwanka na wani hali mara kyau zaka nuna masa tsana haka ?
Ni dana haifeshi ince me yanzu don yanzu dani duniya zatayi kwatancen shi idan an tashi fada ai.
Wani irin kallo yaran kewa uwar cikin rashin fahintar inda maganan nasu ya dosa a lokacin kafin Aisha tace wai mami nafa kula kamar akwai wani hali da ya J din keyi wanda ba a son mu sani.
Wata kila dai mata yake nema ko tunda naji jamal na fadin ko zainab na hakkuri dashi ai.
No kai ina ba dai ya J ba kan akan mata don da munga alaman hakan tuni a gareshi ba wanan bane mami basa son muji daine nake gani.
Dan Allah ku rufa min baki koma me yakeyi ku tayashi addu,a Allah yasa ya daina ta fada a cikin bacin rai tana kawar da kai a garesu baki daya.
Ranan wanan zancen da yaran sukayi ya hana mami din shakat a rayuwan ta dashi ta kwanta can dare kamar yadda ta saba tashi a cikin dare tayi nafila hakama ranan ta tashi tana mika kukan ta ga Allah.
Tun tana yi a cikin zuciyar ta har yakai ta fashe da kuka a fili tana rokanwa dan nata sauki a wurin Allah.
Tare da kaskantar da kanta ga Allah ta daga hannayen ta sama duka biyu tana hawaye tana addu,a tare da mika kukanta a kaskance wurin ubangiji.

Zaune nake ina bitan kur,anina da yanzu na koma gare shi sosai fiye da komai da nakeyi don ina son na kara saukewa duk da banda wanda zai karani a lokacin.
Sadiya ta fito daga dakinta tana saye a cikin dan wando pink daya tsaya mata iya gwaiwan kafanta sai yan aninaiya biyu da akaiwa wandon ado dashi sama rigace fara mai shaka shaka da rigan ta fito dashi a jikin ta.
Zama tayi kusa dani tana kokarin lalaban wayana dake gefena ajiye sai lokacin na dago kai na kalleta na tsayar da karatun da nake ina fadin .
Amma dai kinga abinda nake zaki zo min kai babu hula ko dan kwali ki zauna a kusa dani haka ?
Ba zama zanyi ba ai waya nake son dauka dama ta fada a cikin harshen turancin da yanzu dashi take iya magana ko a gida sosai.
Kallon ta nayi mai kama da harara ina kawar da kaina gefe ta gane may nake nufi yasa ta juya ta koma dakin.
Naci gaba da abinda nakeyi ban tsaya bin ta kanta ba sai can ta fito saye da hula a kanta ta zauna nisa dani tana kumbure kumbure na fita batun ta.
Shine ya shigo part din saye da farar jallabiya zakace balarabe ne shi din yadda rigan ya karbi jikin shi kusa dani ya zauna daya shigo .
Sai dai hankalin shi yana gun sadiya
Showing 291001 words to 294000 words out of 390011 words