bude motar na zagaya zuwa dayan gefen na zauna tare da rufo kofan bai tsaya jiran komai ba yaja motan muka bar gidan.
Tafiya mukayi mai nisa da gidan hankalina yana gun motocin danake gani tankar masu shi suka kera abinsu don kyau kafin naji yace may kika fadawa hjy har take tambayana zaman mu dake ?
Da sauri na juyo na dan kalleshi tankar bashi yai maganan ba don hankalin shi gaba daya yana ga tukin da yakeyi lokacin.
Kaina na mayar a wurin window motan naci gaba da kallon da nakeyi na motoci da gidajen su har ma da al,umman garin da nake gani kamar aljannu a idona.
Yaci gaba da fadin na dauka kina da wayau da farko ashe abin ba haka bane don na manta ke din karamar yarinya ce da bata iya rike siri a cikinta ashe ?
Daga cikin tsakiyan kaina nake jin sautin kalaman shi wanda babu tamtama idan nace zan bashi amsa a lokacin bazan fadi daidai ba.
Barin fada maki kiji daga yau sai yau ba hjy ba ko mami data haifeni kika kara fadawa magana na sai kin kwamce da baki sanni ba wallahi.
Wani irin juyowa nayi tare da kallon shi lokaci guda ina fadin kana dai wahal da kanka domin ni banga riban fadawa wani abinda kake aikatawa ba bayan Allah.
Allah kadai ya kamata nakai kukana gareshi ba wanin Allah can ba don shi daya halice ka kuma ya kawoni karkashin innuwan ka na zauna shi yasan yadda zaiyi dakai.
Naci gaba da fadi cikin muryan dake son nuna kuka nason zuwa min bakaji tsoron mahalincin kaba nawa zakaji yaya ?
Ya dago kai yana kallona ido da ido tare da sauraren abinda nake fadi babu kuma alaman tsoron shi a fuskana ko kadan.
Da sauri ya maida kanshi ga tukin da yakeyi zuciyar shi yana tafasa tare da jerowa kanshi tambayoyi wanda basu da amsa gareshi a lokacin.
Wani irin fisgan motan yayi lokaci guda saida tsoro ya kamani a zuciyana amma a fili saina dake da hakan ban yarda na nuna mashi hakan ba.
Fuskan shi kawai zaka kalla kasan rayuwan shi a bace yake wani babban moll ya packer motar sai daya dan sako iska daga bakin shi ta hanyar furzoshi da karfi lokaci guda alaman hade bakin ciki ya dan fadi a dake ki fita mu shiga nan ba tare daya kallo inda nake zaune ba.
Fita nayi kamar yadda yace dani din shima ya fito muka jera zuwa cikin wurin inda mutanene birjit wasu na shiga wasu na fita da kwalaye mai kama da jakka a hannun su.
Bai tsaya ba sai fannin kayan mata naga ya danyi magana mai kama da yare kafin matar ta nufoni tana washe baki.
Kaya take daukowa sai ta zaba tana gwadawa a jikina tare da yaba yadda yayi min kyau nidai ina tsaye kimkyam kamar an dasani a wurin muka koma fannin takalma nan ma tana biye damu a baya da taimakonta har saida yace sun isa.
Halimatu ma ta samu nata rabon don sayayya sosai mukai mata su man shafi da turare masu tsadan gaske ya saya muna .
Bayan ya biya mun fitone ya biya wani shago a nan ya barni ya shiga naga ya fito da shigen jakar da aka sako muna kaya a wancan shagon sai dai ya riko daya a hannun shi yana zuwa wanan din ya saka a gaban mota kusa da kafan shi sauran aka sa a bayan mota.
Hanyan gida ya dauko a lokacin har magariba ya dan gwauta ga yadda yanayi ya nuna na garin don wuri ya fara duhu ko.
Mun shigo gidan babu kowa nasan sun shige yin sallah a lokacin don haka nima na nufi dakina don sauri in gabatar da nawa sallah kada lokaci ya kara kurewa
Idan kin tafi kayan ku fa wazai shigo maki dashi dakin naji muryan shi yana fadin haka a bayana.
Naja na tsaya wuri daya ba tare dana juyo ba ban kuma wuce part dina danayi niyar tafiya ba duk da ina sauri.
Naji takon tafiyan shi sai muryan shi naji gap dani yana fadin banyi wanan maganan dake ba don ki fadawa hjy munyi.
Ba halina bane fallasa sirina wanan abune daya shafeni a yanzu ni daya har in baka tuba ka daina ba nasan watarana idon su zai ganan masu kamar yadda Allah ya nuna min nima .
Don Allah ba ai masa wayau ga duk wani abinda mutum yake ganin yana boyewa dole akwai wata rana da Allah zai fallasa shi ga mugun aikin sa.
Allah ya baka ikon ganewa ka tuba ka daina don kan ka juyoni yayi da karfi har saida na dan firgita don ban zaci haka daga gareshi ba a lokacin.
Da sauri nayi kokarin ja baya daga rikon dayai min din saidai na kasa hakan don ba karamin riko yai min ba a lokacin.
Wani zafi hakan naji har kasan raina.
Na dago a fusace don mashi kashedin hakan da yai saidai muna hada ido dashi kwarjinin shi da zatin shi ya hanani hakan gare shi.
Kaina na mayar kasa da sauri don ba zan iya jurewa irin wanan kallon da yake min ba a lokacin wanda na kasa fassara hakan a raina.
Shiru na dan lokaci kafin muryan mama ya shiga kunnuwan mu tana fadin kuma nan kuka tsaya ina dai lafiya na ganku haka ?
Lafiya mama muna dan maganane a nan yana fadin haka ya sakeni da sauri na juyo ina fadin sannu mama tace har kun dawo ashe ?
Mun shiga yin sallah ne yanzu ma wayana na manta dashi a nan inda na zauna nazo dauka shiko a lokacin har ya kai kofan part din shi don haushi.
Don ba haka yaso ba yasone ya ban wahala sai na raina kaina sai ga mama din ta kwafsa mashi don fitowan ta a lokacin.
Kayan da yake maga wani daga cikin yan aikin gidan ya fara shigowa dashi niki niki a cikin dan guntun turanci na ce dashi ya kai part dina mama tabi kayan da kallo.
Tace ashe ku sayayya kuka fita waini wanan abin naku na daure mun kai yau ina antyn mu dake fadin sai kuma tayi shiru ganin haka nace banyi sallah ba mama.
Jeki ki sallah kada ki makara don lokaci yaja sosai na juya da sauri na barta wurin na wuce zuwa part dina.
Sallah nayi kafin na samu wuri na zauna a dakin ban fito ba don injin nauyi da kunyan mama a yadda ta samemu dashi a falon dazun don haka nai zamana a dakin kawai.
Wanka nayi na shirya kwanciya na saka hijab saman kayan dake jikina na nufi part din shi har na shiga falon nasa .
Sai naga wanan dan jakkan daya riko da kanshi aje saman kujera har na dan wuce wata zuciya tace na koma naga meya sayowa kanshi ne haka bai bari wani ya dauko mashi ba.
Saida na kai zaune na bude ledab a hankali idona yai arba da kwalaben dake ciki kwalban kawai abin kallone.
Zuciyana bai yarda da hakan ba ina kkkarin karata ko meye a cikin kwalban naji an fisge kwalban a hannu na tare da fadin get out from dis part stupid yana nuna min hanyar fita.
Har abin naki yakai kiyi min bincike who give you dis right da zaki taba min kayana a hasale yake magana kamar zai mareni ko me ya tuna kuma oho.
Ya duka ya dauki saurab kayan nasa nima mikewa nayi da sauri na fice daga part din sauri zuciyana cike da zargin shi.
Ina shiga dakin na rufo kofa tare da saka ma kofan key na nufi gado na fada saidai ban kwanta ba ni ban kwance kuma bana zaune sai tunane nakeyi a raina.
Dama wai haka aure yake ne nake ganin mata suna walwala ko wani lokaci kaga kamar basu da damuwa a tare dasu.
Meyasa ya jafar yake min hakane koba komai yakamata ya rikeni tankar kanwarshi ta jini a gidansa tunda yasan yadda mukai aure a tsakanin mu.
Tunane kala kala nayi shi a wurin karshe na mike na dauro alwala don barci ya kaurace min gaba daya a idona ranan.
Sallah nayi raka,a hudu na dade wurin ina addua ina mika kukana ga Allah kafin naji sanyi a raina har barci ya daukeni.
Naso makara ranan don ban kwanta da wuri ba a gagauce nayi sallah na koma na kwanta sai barci kuma.
Kodana tashi shadaya na safe wanka nayi na fito bayan na shirya na fito don gaida hjy don nasa zata damu da rashin ganina da batayi da wuri ba ranan.
Da sallama na shiga dakin ta saidai ita daya na sama tana zaune tana nafila na samu wuri na zauna harta idar bandade da zama ba naji tana fadin zainabu kin fito ?
Eh hjy ina kwana ta amsa min a cikin fara,a tare da fadin ai mijin ki daya shigo nan nake tambayan shi yace jiya baki kwana da dadi ba.
A raina nace makaryaci ke nan shikan ya hada duk wani abin ki da Allah ya hana Allah dai ya shiryoshi ya daina wanan hakin .
Saidai a fili dan murmushi nayi ina fadin ciwo kaine kawai ai hjy kuma nasha magani ya bari.
Dole ki ciwon kai jiya kun fita kun dade tunda baki saba fita irin haka ba dama kin dai kara cin wani abuko yanzu bayan kin tashi.
Zan daici hjy na fada a cikin ladabi to kinga ga wanda suka kawo min niba dadin abincin su nake ji ba ki tashi ki diba kici yanzu.
Dole haka na mike na dan dibi kadan na zauna nan gabanta kinga da haka zaki ta kamo zuciyar shi don kinga yanzu shi na masa fada ya nuna min yayi biyayya ga magana na yanzu .
Don haka kiyi ta hakkuri bana son har uwarku ta gane wani rashin jittuwa yana shiga tsakanin ki da mijin ki ta yadda zata dara muna.
Kinga Ramatu da kike gani diya tace nasan halin abinna kamar me yanzu tana zaman idon uwarku ne a gidan nan nasan duk abinda suka kitsa kan zuwa nan da ita .
Don baki san yadda tafiyan ya wakana bake ta nuna idan bada Ramatu ba saidai a fasa tafiyan dole mijin ki ya yarda da hakan mukazo tare.
Don haka nake son kafin mu tafi ta koma ta fadawa uwartaku zaman lafiya kukeyi tare dashi kinga duk wani shirin su sai ya tafi a banza ke nan.
Saidai abindake wakana tsakani shi da dan uwanshi na rasa ko menene ya hadasu haka a yadda nasan su a tare nasu yafi zuwa daya.
Sai gashi yanzu naga suna wasan kura da kare kamar wani abu na faruwa a tsakanin su ko kinsan meya hadasu haka wanan abin ke faruwa ?.
Da sauri nace nima hjy haka na fahinta don ranan ma naji mama nawa ya jamal fada kan hakan yace da ita ba komai .
Saboda na gane hjyn tana son tayi min wayau manya taji wani abu daga gurin yasa na fasa mata hakan don ta barni.


ZAINAB IDRIS MAKAWA



Akwana a tashi ba wuya a wurin Allah sai gashi har hjy ta gama shan maganin da aka bata suka koma da ya jamal don shi yayi tafiya wata kasa a lokacin yasa yabar komai a hannun jamal din.
Suka bata sallama da sharadin zata dinga zuwa checkup duk bayan wata uku lokacin da naji hakan nayi murna kwarai don a zato zata zauna damu nan ke nan ga baki daya har lokacin da asibiti zasu sallameta baki daya.
Saidai me ranan daya dawo daga tafiya baiko shiga dakin shi ba ya zarce wirin hjy sun gaisa tare da dan taba hira dashi har ta sako mashi zancen da asibiti sukayi.
Shima cewa yayi da ita ashe zama chaina ya kamaki ke nan yanzu zaki shakara tare damu a nan ke nan ?
Da wani irin sauri ta dago kai tana fadin ai in kaga na kara sati daya a kasan nan to bansan hanyar gida ba kenan idan kuma har ban sani ba sai in buga gida suzo su dauke ni.
Hjy kamar wace dai ake kora ya fada a dan galabaice yana dan mika don zama cikin jirgi da yayi yasa shi gajiya don har dubai suka je bayan sun gama meeting.
Hjy ta kalleshi tana fadin jeka ka huta mana tunda ka debo gajiya haka da yawa ni bance kuma da kai ana korana ba a nan.
Iyakar gata dai kan aikun nuna min shi a duniyan nan nikai na godewa Allah na godewa haihuwa don yai min albarka.
Ya mike yana fadin ni dai kan baki haifeni ba uwata dai ta iya haihuwa tunda itace ta haife ni ai hjy tace ja,iri waya haifi uwar taka da kake yabo da ban haiho ta ba har zata haifeka.
Yau dai na gane fitina wanan tsohuwar kike ji dashi zuwa Nigeria kuma baki zuwa sai ranan da likita yace ya sallameki kwata kwata mama ce kadai zata koma ke ko kina nan tare damu.
Dakai da likitan kunci gidan ku na gane abin naku hadin baki ne ni ko da kafa sai in karasa gida ba matsala bane a gareni.
Zakiko hadu da kura dasu zaki hanya in takaman ki zuciyana ya fita yana dariyan yadda ta takankare tana masifa dashi don yace ba zata tafi ba.
Ance sabo turken wawa bansan dan zaman mu tare ba har akwai sabon da ya shiga tsakanin mu hakan sai bayan tafiyan nan nasa .
Duk ko da yatafi bamu cikin dadin rai dashi don har lokacin akwai fushin daukan mai kaya da nayi ina dubawa ya dauki fushi dani sosai a gidan.
Har tafiyan nan ya kamashi yana cikin fushin haka dani ko zancen tafiyan a bakin hjy na farajin zaiyi tafiya wai.
Na nuna mata nasan da zancen sai dai na manta da sunan kasan don yana da wuya mama Ramatu ke fadin ni dai yar nan kada wata rana ki ba dana kunya da wanan kauyancin naki.
Hjy tace haka yarki tayi kafin ta waye itama aishi jafari ya mai da tarihin ubansa ne a rayuwa don haka ku bar ganin laifin shi haka.
Da zai tafi kuma sai safiyan ya shigo min daki bayan ya shirya har an fita mai da kayan shi ina zaune saman dan stol din mirrow dakina ina shafa mai da nayi wanka.
Ya shigo dakin ba tare da tsayawa ba yake fadin zaiyi tafiya zai kwana biyu a can idan muna da wani matsala in kira Samuel in fada mashi ko menene .
Daga haka ya jiya zai fita a dakin na samu na bude bakina da kyar ina fadin Allah ya kai lafiya Allah yasa abinda akaje nema a samu .
Na gode ya fada ya fita da sauri nabi bayan shi da kallo tare da sauke ajiyan zuciya na mayar da kaina ga mirrow ina kallon kaina a cikin madubin dake gabana .
A hankali na raya a raina wai ina nake da matsalane a jikina da ya jafar bai min kallon mace ne har yanzu yadda naga wasu maza sunawa matansu dai ?
Nidai banga inda na kasa ba da bai ma son ko ya kalleni idan har ya tsura dani haka a dakin da sauri kuma na kawar da wanan tunanen a raina ina fadin .
Kenan har na damu da ya tabeni ke nan kamar wata jarababba dani nikan ina zan yarda da wani tabi kazami dashi yana shan giya kuma ya dawo ya tabani.
Yau ma daya dawo ina kwance ina tunanen shi ashema yana cikin gidan ko a lokacin ban sani ba saida zai shiga part dinshi ne kamshin turaren da yake amfani dashi ya bugo hancina don kofa a bude halimatu ta barshi da zata fita .
Saida naji gabana ya fadi sosai shiru na saurara banji motsin shi ba a dakin na sauke ajiyan zuciya a hankali tare da gyara kwanciya naci gaba da karatuna da nakeyi.
Har wani lokaci hankalina bai kwanta da rashin ganin sa ya leko ba kuma ban daina jin kamshin sa a hancina ba saina dauka kewan shi kawai ke damuna nake jin hakan.
Karshe dai waya ta na jawo na fara gamen a ciki tunda layin da nake dashi na Nageria ne bai zuwa ko na kira dashi.
Nayiwa ya jamal magana ya saya min da zai fita ranan mama ta hana ya sayo min wai kila mijina baida bukatan na rike wayane a nan yasa bai sayo min ba don haka kada ya soma ya sayo min su samu matsala dashi.
Don haka ya jamal din yaki sayo min layin da zanyi amfani dashi amma bayan wanan duk abinda mukace muna so idan zai fita yakan sayo muna yazo muna dashi.
Showing 219001 words to 222000 words out of 390011 words