danayi a fuskana riga kawai na zura a jikina na fito falon na samu har sun fita waje ko da uwar zumudi sadiya.
A mota na samesu zaune na bude baya da nufin shiga ba tare daya dago kai ya kallon in da nake ba yace dani.
Amma kinga ni zan tukaku ai da zaki shiga baya yafada yana gyara zaman shi cikin ko in kulla na dawo gaban motan na zauna na rufo kofan a hasale.
Don ni harga Allah wanan fitan haka kawai zuciyana naji baison fitan da zamuyi dashi a lokacin.
Juyowa yayi yadan kalloni ya girgiza kanshi don shigan nawa bai mai ba a lokacin sai kuma naji ya furzo iska daga bakin shi tare da shafo suman kanshi da hannu daya ya tayar da mota muka fice gidan.
Kida ya saka a motan kamar na yare bandai saurari mai ake fada ba balle na gane haka muke tafiyan har wurin wani taro don na gane hakan ne saboda motacin dana gani a wurin .
Saida ya tsayar da mota yake fadin zamu shiga wurin tarom nan ba zamu dade ba don abokinane ke bukin zagayowan haihuwan shi yau.
Kai na dan gyada ba tare da in kula dako ya kalloni ba muka fito daga cikin motan zuwa cikin inda ake taron .
Sune yan kasan birjit a wurin tun daga waje zaka gane hakan sadiya dake wani shige mai na finciko da karfi tayo baya duk da yajimu bai juyo ya kalle mu ba nace a hankali wallahi ki natsu ki kama kanki a wurin nan kin dai san kasan nan naman mutum sukeci.
Sai mu nemeki mu rasa a wirin sun daukeki sun yanka ba wani aiki bane a wurin su don haka kafana kafan ki idan kinji.
Na fadi hakane do yadda naga tana zumudin shiga ga wurin sam ban yarda dashi ba tun daga ganin irin mutanen dake wajen da nayi.
Take ido ya dawo a wurin mu nasan ba komai ya jawo hakan ba sai kasancewan mu bakaken fata kuma musulmai don abaya na saka sama na rufe kaina da gyalen shi shigar musulunci nayi kamar nasan hakan zai kasance idon ta ya jafar ne baiki na fito kamar sauran matan dake wurin suna shiga kamar tsirara dasu.
Tun a kofa aka fara bashi hannu wani irin gaisuwa da akeyi wurin zai daurewa mutum kai don in dane sai ince gaisuwan kasan ke nan a hakan .
Amma yanzu na fahinci komai ba wai dabi,an yan kasan bane wanan gaisuwan haka muke tafiya har zuwa inda taron yake duk wanda nayi katari ya gaida mu sai dai na dan dukar da kai yadda naga yan garin na gaisuwan su.
Idanuwa a kanmu sai kuskus da keyi kan shigowan mu din hannu philip ya miko wai mu gaisa na girgiza kai tare da mai gasuwan su na koma bayan yaya na labe sai ya bini da kallo.
Duk inda ya saka kafan shi muna biye dashi a baya har wani yazo ya jaye shi ina hangen su suna gaisawa da wasu da nake ganin kamar bakine suka zo saidai shigan su tantiran yan iskane ga sarka ga dankune duk sun saka a jikin su kamar mata.
Ganin hakan na kara shan jinin jikina ga sadiya tana makale a hannu na ban yarda na saketa ba.
Wani ne ke nufo mu a cikin murmushi har ya karaso inda muke ya miko min hannu yana fadin sunan shi Sam hannun nasa na kalla nace mai thanks kawai ina kokarin kawar da kai sai ji kawai nayi ya rungumoni a jikinshi.
Ban tsaya jiran komai ba na daga hannu na kwasheshi da mari kayauuu a fuska Allah ya ban sa,a na samu fuskanshi da kyau ya dafe wurin yana kallona.
Haka ya dawo da hankalin mutanen taron kan mu yana fadin pretty kika mareni do kinyi sa,a na kulaki kina mace ?
Sai zaran idanu nake a hasale nace dashi how dear torch me ina musulma zaka rungumeni haka kaiba mijina ba ba wani dan uwana ba ?
J dinnne ya karaso inda muke wanan maganan ya kalli mutumin yace me ke faruwa ne a nan ?
Ya dago idanun shi da sukai ja yana fadin don kawai ta burgeni nazo mata shine ta daga hannu ta mareni kawai yana murza wurin da alama marin ya shigeshi sosai.
J din yace kasani ai ita ba karuwa bane ko wata mai zaman kanta addinin mu kuma bai yarda dayin hakan ba don me zaka rungume ta ?
Just a hug nayi niyar mata don tana pretty girl ta burgeni kawai amma ban san hakan zai bata mata rai ba ai har ta mareni ?
Zuwan abokan shi su uku wurin ya hana J din bashi amsa don har ya dago idon shi jajaye da niyar fadin wani abu suka iso suna rungumar shi.
Tare da fadin mai zai sa kayi mata haka kaiko ai kaga shiganta kasan su musulmai ne basu yarda da hakan ba ai dakayi.
Yace naga J din kamar shi bai damu da addinin nasu ba don naga baya abinda sukeyi na dauka itama yar hannuce ya dauko .
Wani irin hawayen nadama ne suka zo min lokaci guda a idona a hankali na juya na fara tafiya da hannun sadiya dake makale da nawa har lokacin.
Fita mukayi daga cikin dakin da ake birthday din ba tare da nasan inda muka dosa ba a lokacin sai tafiya mukeyi babu ko waigawa.
Nake jiyo horn din mota a bayan mu sai sadiyane ta iya juyawa naji tace ga yaya nan a bayan mu da mota shi.
Hakan baisa na tsaya ba saida naji yace ina zaku tafine ana maki magana kina wucewa naja na tsaya .
Ya tsayar da motan yana fadin ku shiga mu koma gida sannan na taka na zagaya na shiga motan ba tare dana kalleshi ba muka fara tafiya bamu san yadda suka karasa a wurin taron ba .
Ga wayan shi nata ruri tun dauka daya dayayi ya duba bai kara duba mai kiran nasa ba lokacin sai tsukin da yakeyi kawai lokaci lokaci.
A wani babban shago ya tsaya tare da waigawa inda sadiya take zaune yake fadin ku fita kowa ya dauki duk abinda yake so a nan .
Shiru motan yayi ba wanda ya motsa a cikin mu ya kara fadin ku fita mu shiga nace daku ko bakuji bane ya fada a dake.
Bana son komai gida nake son zuwa kawai na bashi amsa ba tare da juyo inda yake ba sadiya fito mu shiga ciki.
Da sauri sadiyan ta girgiza kai tana fadin a, a yaya muje gida kawai nima ban son komai .
Kallon mamaki yayi mata kafin yace tsoro kike jine har yanzu sadiya ta gyada mai kai alaman eh.
Dama tunda bakiso fita ba nasan fitan ba zai muna dadi ba don kamar na tursasakine kika fito ai da sai ka barmu gida zaifi tunda ka fahinci hakan.
Na fada a hankali wasu hawaye na zo min a idona kai ya girgiza tare da bude motan yana fadin da zai fita ko ku fito ko kuma na mayar daku wurin taron nan don ba zaki hanani zama ba .
Kizo nan kuma ki tauye yar uwanki dani zabi ya saura gareki yanzu ya fada yana karasa fita daga cikin motan.
Dole na fito don ranan ji nake kamar duk zunubi a kaina ya kare don abinda dan arnen nan yayi mun a wurin.
Yana gaba muna biye dashi har muka hau lifter zuwa sama ya juyo yana fadin yau kan Sadiya ba zan tayaki zaben komai ba don fushi nake dake.
Kayi hakkuri ya jafar tsoro naji kada su kashemu a wurin kaga su arnaku ne duka wurin cewa da abinda na fada mata da zamu shiga wurin birthday din dazun shi ya tsorata ta ashe ta natsu badon Allah ba.
Balle taga abinda ya faru dani a wurin ya kara daga mata hankali take ganin kamar gaskiyane abinda na fada mata din.
Naji yace tsoron may kike ji kuma Sadiya ba gani ba ba abinda zai same ki ai muna tare kinji.
Mun shiga wurin ban dauki komai ba a shoprite din sai faman yawatawa da sadiya sukeyi karshe ma na dawo na samu wuri na zauna har suka gaji suka fito lokacin dare yayi sosai koda muka shigo gida.
Sallah nayi bayan nayi wanka nayi ta darazan jikina don ina jin kamar har lokacin indaya tabani wurin yatsunshi dun manne mun a kafada na.
Ko a school haka nake komai sukuku dani ba sakin jiki yasa har maya ta fahinci hakan gareni ina zaune cikin zurfin tunane .
Naji an dafa min kafada na nayi firgigit na zabura ina sauke ajiyan zuciya ta zauna gab dani tana fadin meke damuwan ki haka zee ?
Tun da safe ina hankale dake baki cikin hayacin ki ko kun kara hadewa da mutumin naki ne kuma har kike tunanen hakan ?
Kaina girgiza tare da dan dago kai ina fadin abinne ba dadi sister nan dai na labarta mata duk abinda ya faru dani a weekend din .
Dan guntun murmushi tayi tare da fadin matsalanki sai kinga native doctor din mu na gargajiya suke da herbal medicine dake kawo karshen wanan case din nasu da sauri harma a manta mutum yayi shi a baya indan an dace.
Amma yana da mata kai da zakubi don kada maganin ya baci amma nasan idan kinga kakata akwai yadda za ayi don wani dan uwan mu ya taba fadawa irin case din nan a baya yanzu kuma ya daina ko cigari baya kaunan gani balle giya.
Case din homosexual kuma sai dai idan kinje don na bata labarin ki tunkan kizo tana dakon ki a ko wani lokaci don ta tausaya maki sosai kan hakan.
Nagode maya da kullawan ki a kaina zanyi kokari na samu time da zamu tafi kauyen tare dake amma sai idan na shiryawa hakan zan fada maki.
Haka muka rabu na dawo gida da wanan maganan a raina ba abokin shawara fadila na kira da dare bayan mun gaisa na kwashe yadda mukayi da maya din na fada mata.
Saida ta nisa kafin tace zainab wanan damane sosai Allah ya baki kan hakan sai dai gaskiya akwai matsala ga hakan baki ganin idan aka samu akasin hakan abin zai iya dawowa kan ki ?
Kindan fa yadda kike da uwar mijin nan naki don haka nake shawarta ki da kidai kara tunane akan hakan gaskiya.
Anty ta yaya zan fara tunkaran mami da wanan zancen ai saita dauka ni din watace data iya irin wanan abubuwan tun a gida kamar yadda takan fada min cewa .
Nida iyayyena mun iya shige shige muna kammale mutum da dan sa tun kan mu shigo birni wanan zancen ba zan taba mantawa dashi ba a raina don ido da ido tasha fada min hakan.
Idan na tuna yana min zafi sosai wanan kalman yanzu kuma in fito mata da wanan zancen ai sai tace hakan gaskiyane dama.
To yanzu ke wani shawara kika yanke ga hakan don gaskiya kada wanan daman ya wuce ki yanzu zainab .
Don idan kika baro kasan baki gwada sa,an ki ba daga baya hakan zai dameki sosai kuma kinga abin nasa sai gaba gaba yakeyi yanzu.
Na sauke ajiyan zuciya tare da fadin zan kara tunane in gani abinda zai yuyu zan kiraki in fada maki abinda zuciyana ya yanke min kan zancen.
Dan tsuki nayi don wanan shawaran da fadila ta bani din din kamar ta famamin wani miki dake zuciyana ne lokacin.
Don sam ban kawo wanan tunanen ba da farko sai yanzu da ta fito min da zancen fadawa mami din nake tunanen hakan.
Kawai banda mafita saina share zancen a zuciyana naci gaba da abindake gaba na.
Kowa sai harkan gaban shi yakeyi don ba ganin shi nakeyi ba shima baya ganina sai idan zamu gaisa da safe bayan hakan sai kuma wata safiyan kuma idan yayi zamu gaisa.
Ranan ba school don haka na fito don nasha iska saman benen part din mu ina zaune a gurin wanda ba kowa ne zai sanda hakan ba.
Da takarda a hannuna wayana na gefe daya aje sai cup din drink's dana aje daga dayan gefen ina dan kurba kadan kadan.
Na dauki cup din drinks din na dan kurba kadan na aje kamar ance na dago kaina na kalli kasa sai na hango ya je suna fitowa da Taju daga cikin gidan.
Wani irin faduwa gabana yayi yaba da ras ras lokaci guda ban san lokacin dana mike tsaye ba ina mai furta innalillahi wa inna alaihim raju,un.
Allahuma Ajirni fi basibati wa,akalillif hairan min ha , .
Ina mai runtse idanuwa na kafin in bude in kara fadin La,illah ha illa anta subbahanaka inni kuntun minal zalumin har ban san lokacin da hannuna yakai saman cup din dana aje saman table din ba ya fado ya tarwatse a wurin.
Kai ya J ya dago daga inda yake tsaye yana kokarin shiga mota ya hangoni ina shigewa ciki hannuna yana dafe a bakina don kuka.
Sam shima baiji dadin hakan ba don bai kaunan in ganshi yana aikata wani aikin da bai dace ba shiyasa ma raba part din da akayi yanzu yai mashi dadi sosai don mun rage samun rikici dashi yanzu.
Motan ya fasa shiga ya juya zuwa cikin gida da sauri taju wanda ya riga ya shiga mota ya bishi da kallo kafin ya dago yana kallon saman benen part din mu baiga kowa ba.
Haka yasashi mamakin mai kuma ya mayar dashi cikin gidan a wanan lokacin bayan yasan inda zasu a yanzu yana da muhinmanci a garesu sosai.
Nikan ina shiga dakin na fada saman gado kife na fara rusa kuka mai tsuma zuciya naji an turo kofan da karfi an shigo dakin nawa.
Hakan baisa na dago don ganin wanda ya shigo min saima kamshin turaren shi mai mugun tashi daya ziyarci hancina a lokacin daya yasa na gane shine a dakin.
Zainab meke damun kine har zaki so halaka kanki da glass haka baki da hankaline kome ?
Ban dago ba sai kukan da nakeyi naji yaja wani irin uban tsuki yana tako zuwa inda nake kwance ina rusa kuka.
Jinayi kawai gaba daya ya ficikoni na kwanto a jikin shi lokaci guda nayi saurin kokarin jayewa ina fadi cikin muryan kuka.
Kada ka tabani don kai ba cikakken musulmi bane har abokan hurdan ka sun sanda hakan don sun fada a gaban ka suma.
Ni din ya nuna kamshi cikin mamaki yana kallona nace kai mana Allah ya kara min tsari da duk abinda kake nufi da daukoni dakayi zuwa wanan kasan na kafirai.
Idan har kana tunanen zaka iya juyani na koma kamar yadda kake fasiki ne Allah ba zai taba yarda kaga hakan ba a rayuwan ka, , ,
Wani irin mari yaso kaimun Allah ya taimakeni na kauce bai sameni ba na samu na kwace a jikin shi ina ja da baya baya.
Zainab ni kike kallon idona kina fada min haka ya fada kamar zaiyi kuka ba tsoro nace mene marabinka dasu yaya ?
Ai gara fasikin dake neman mata da kai yaya wanda ke fasadi da namiji dan uwan shi ta inda Allah mahalici mu ya hanemuyi koda matayen kuna aurene kuwa.
Amma kai don rashin tsoron Allah da karancin addini dake yawo akanka shine ka mayar abin tunkaho a gurin ka kamar ba zaka mutu ka koma ga mahalicin ka ba saboda rudin duniya dake damun ka.
Ya kara kaimu cafka a hasale na kara ja baya har na samu na sauka daga saman gadon muka fara zagayan dakin muna fadawa juna bakaken maganganu.
Ranan kan yayi mamakina matuka don idan wani ya bashi labarin hakan zai iya karyatawa don ban raga mai komai ba ban kuma ji tsoron shi ba.
Karshe nace dashi zan bugawa mami waya tazo ta daukeni don duk abinda ya sameni kaine na kuma riga da na fadawa iyayyena hakan da yan uwanka .
Don nasan gab kake daka kasheni a kasan nan don kawai kana ganin ina takura maka kan harkan ka.
Ido waje yake kallona yana nunani da yatsan shi yana kallona ido waje ya iya furta zainab ashe dama haka kike baki da hankali da wayau.
Ina maki komai da kike so ban ga na rageki da komai ba don kema ki amfana daga gareni tunda nasan kinyi hakkuri da ba kowa zai iya irin sa ba.
Ka daina idan ma kana mun ne don yaudara don ni na dade dagane manufan ka a hakan don ka auroni ne nan don ka kawar da idon
Showing 267001 words to 270000 words out of 390011 words