garesu.
Ko taga yadda na danyi da fuskane sai cewa tayi ga ruwa mai sanyi kusha na juya wurin asamu din ina fadin karba an gode anty lantana.
A waje na samu innan mu bakin baranda tana jiran shigowan mu da sauri na karasa jikin inna din sai hawaye suka zubo min lokaci guda don murna.
Sa,adatu na shiga part din mu take fadin inna bani makulin kofan nan na baya a bude a shigo da kaya ta mika mata a daidai lokacin ne aka fara shigo da kayan da muka zu dashi din na tsaraba da ya sayo muna.
Yayin da lantana ta koma ta kasa ta tsare a kofanta taga an shigo da abinda muka zowa inna dashi gidan zuwan mu.
Drivers din basu tsaya ba kamar yadda ya umurce su da sun sauke mu su juyo da mota daya zasu bar daya a gurina a nan don zirga zirgan mu a garin.
Haka yasa suna gama sauke kayan sukai muna sallama duk da nasan ya sallamesu hakan bai hana na kara masu alheri ba da zasu tafi.
Falon na inna ya hargitse da hayaniya lokaci guda kowa sai fadin albarkacin bakin sa yakeyi a lokacin kan mu.
Gyaran muryan da Abba yayi yasa kowa natsuwa a falon nan aka shiga gaida shi da dawowa gida yana amsawa sadiya ce ta taso ta rungume shi.
Farin cikin Abba bai boyu ba ga ganin yadda muka sauya gaba dayan mu yake fadin wai sadiya ce wanan ko yar gidan gwaunan jahan nan ?
Duk aka kwashe da dariya a falon sai lokacin na fito daga cikin daki ina fadin Abba sannu da dawowa ya washe baki don gani na yana fadin a, a Abu kune haka tafe ?
Yaya shi maigidan naki da mahaifiyar shi tare da yan uwan shi shine tambayan Abba a gareni cikin nuna jin dadi da rikon da suke min a can.
Allah sarki ABU CIKIN DUHU SIRRINE yanzu shi Abba yana tunanen zaman mutunci muke dasu a baki daya har nayi wanannsauyin da yake gani a tare dani a yanzu.
Muryan Abban ne yake saka masu albarka kan kokarin da sukeyi damu a can hakan yana fadin wa yan nan mutanen sai godiya kawai Asiya.
Da cewan innan mu ya fadi sunan ta kai tsaye don jin dadin abinda idon shi ya gane mashi bai san na badinin dake a boye ba a lokacin.
An dan taba hira kafin ya mike don fita yana fadin bari je a nemo abinda za ai masu kafin yamma yayi ya fita.
Har kwana biyu ina gida iyakata na fito daga part din mu zuwa wurin Asabe da lantana mu gaisa in dawo dakin mu bazan kara fita ba sai kuma washe gari.
A rana ta uku da zuwan mune na shirya zuwa gidan su maizube don mu gaida su tunda mun saba sosai yanzu dan zaman mu da ita a abuja kafin mu koma chaina akwai shakuwa sosai a tsakanin mu da ita yanzu don lokaci lokaci muna waya dasu.
Don idan nabi ta mutanen dake shigowa ba zan fita zuwa ko ina ba garin nan don tsaraban da ina ta zauna ta rabawa mutane unguwa da yan uwa yasa suke shigowa gaishe mu.
Cikin wani dinkin yan mali na shdda marron colour dinkin har gwiwa yakai min ga farin lace da akai mai kwaliya dashi duk jikin kayan.
Duk da ba dadin daura zanin nake ji a yanzu ba haka dai na daure na daura don sanin gidan da zan tafi wurin malam ne mu gaisa amma da abinda zai kaini kuma a kasan zuciyana.
Mun fito a cikin shiri na tsaya da inna muna magana take fadin idan mun fito mu gangara mu gaida wasu yan uwanta nace to inna.
Ni da sa,adatu ne a gaban motan tana nuna min wasu sabbin gina har na dauki hanyar da zai kaimu gidan malam din.
Muk tsaya a kofan gidan malam din da mota na bude muka fito suka kwaso kayan muka shiga ciki.
Farko munci karo da kishiyar su wace itace amarya a gidan tana ganin mu take fadin shike nan ma yaya ga wace zamu gaidawa anjima tazo har gida.
Nan suka fara fitowa suna muna sannu da zuwa muna amsawa kafin mu zube a dakin maizube ana sabom gaisawa da yaushe rabo ?
Munyi hira sosai dasu kafin kafin su watse suh bar daki ya rage sai mu da ita take tambayana ya bayan rabo ?
Na danyi murmushi kafin nace wallahi maizube sai alheri saidai har yanzu muna nan kamar yadda kika sani.
Ta dafe kirji tana fadin ban fahince ki ba zainab kina nufin har yanzu ba wani abu a tsakanin ku dashi ko me ?
Kallon sa,adatu dake zaune nayi sai na kawar da kai da sauri ta gyara zancen ta da fadin har yanzu ace ba shiri dake da yan uwan shi haka ?
Sa,adatu ta cabe da fadin wallahi maizube nima shedane kan hakan dan zuwan nan da nayi kwana biyu sai dana sheda hakan.
Nan ta shiga ba maizube labarin abinda ya faru tsakanin mu da mami a gidan ta ranan tace ikon Allah wanan matar da karfin hali take ashe.
Zamani na abinda dan ka ya kwaso har idan baida illa akaima sai ka ruguma da hannu biyu tunda ba Allah ya hana hakan ba.
Saidai idan da illa ga abin zaka nuna kinsa gareshi har sai ya gane abinda kake nufi da hakan.
Amma wanan kamar tana jayayya da ikon Allahne hakan shiyasa nake son na bar masu gidan har danta na fada a sanyayye ina dukar da kai kasa duk suka kaleni.
Ki bar mata danta anty ai sai taji dadin hakan tayi nasara ke nan a kanki wallahi ke suka samu sukewa hakan da nice da duk sun gane kuren su har wa yan nan yan matan gidan nata masu yiwa mutane kallon raini din.
Amma kice zaki bar mata danta dama ai haka take so ita ki barshi din tunda dama ba zaman ku a tare take so ba dashi.
Tana fadin hakan ta mike tsaye tare da fadin ni barin kewaya kinji fitsari ya cika min mara tun dazun wallahi ta fita daga dakin.
Maizube ta kalleni tana fadin amma yanzu kun daidaita da mijin naki a tsakanin ku nan ma kaina iya kada mata alaman a,a takaice na dan fada mata abinda zan iya don ta fahinceni.
Hankalin maizube yai matukar tashi a lokacin sai maimaita cewa takai har wanan lokacin kana zaune da mutum kamar dutse ba abinda ke gudana a tsakanin ku haka ?
Gaskiya wanan ba abinda za a kyaleki bane zainabu don a gaskiya kina cutuwa da yawa sai dai dole ki san yadda zaki bulowa mutane da maganan a yanzu.
Maizube wanan ba wani abu bane illa ranshi daya fita ga mata sai yan uwan shi maza yake bi shine matsalanshi kawai.
Jam jam wa,iyazu billahi wanan abin da muke ji dauri a jakkar magori shine ya kawo garemu yanzu ?
Shigowan sa,adatu dakin yasa mukai shiru kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi cikin mu a lokacin.
Anty muje kinsan ba nan kawai zamu tsaya ba gashi malam bai dawo gida ba har yanzu.
Zan dawo na yini a nan na fada ina mikewa don nasan maizube din zata fahinci mai nake nufi da hakan dana fada ai.
Mukai masu sallama muka fito daga gidan zuwa gidajen da inna ta umurce mu da mu tafi idan mun fito gidan malam din har gidan mahaifiyar Lantana nasa muka je mukai mata alheri bayan mun gaida ita sa,adatu ta cika fam dani kan zuwan mu gidan.
Sai bayan la,asar muka dawo gida a gajiye mun samu wai anyi fada da innan mu da anty lantana wai an fake da zuwan mu Abban mu yana shiga lungun inna ko wani lokaci yanzu.
Wanan maganan shi ya kawo fitina har suka kaure da fada a tsakanin su don kishiya bata raina abin fada kullun.
Ana hakane muka shigo gidan a daidai lokacin da Lantana ke fadin mijin yae taki dake yankan kai yana turo maku kudin jini kuna kashewa keda ubansu.
Muka karasa shigowa muka samu ko wace na tsaye cirko cirko rayukan su a bace sunyi shiru don ganin mu.
Kamar ba zan tanka masu ba har na dan wuce na juyo ina fadin haba innan hakan ba girman ki bane yanzu ai shi kadai na fada na shige part din inna abina.
Saidai ina tunanen a raina wanan maganan ke nan ina ga sun san gaskiyan ko waye mijina a gaba me Lantana zata fadawa innan mu ke nan ?
Dakuwan da muka dawo dashi daga gidan wata yar uwan inna na bude ina rabawa kannen mu kan na fara ci na dibarwa yayan lantana nasu akai masu.
Nan sa,adatu ta hau fada ba za a basu ba ai yanzu muna ji ta gama zagin innan mu da mijina tana masa kazafin da ba shi ba a tsakar gida.
Nace naki ne ko nawa sa,adatu duk me tayi don kanta ai itama ta haifa kuma zasu girma ai taji idan da dadi abinda takeyi din.
Inna ta shigo nake mata maganan don Allah ta bar biyewa haukan lantana suna zama daya haka a gaban mu.
Dama shi me son fada maka magana yakan jaka fadane ya samu kafan fada ma magana a cikin fada din.
Yar nan bar wanan matar mara hali ko yaushe ita burin ta shine taga ba, a zauna lafiya ba a gidan nan.
Nan dai na bawa innan mu hakkuri aka bar zancen kowa ranshi ba dadi ga abinda ya faru din ranan.
Sai bayan kwana biyu ina kuryan dakin inna kwance da dare bayan kowa yayi barci inna ta sameni ta zauna a bakin gado inda nake kwance.
Na dago da sauri ganin ta shigo ta zauna a wanan lokacin nasan magana ya kawo ta wurina ke nan.
Yar baba meye damuwan ki da har kika kasa fada min kike shiti yankewa kanki hukuncin da bai dace ba badon sa,adatu taji kudirin ki ba kan hakan.
Wani abu ta fada maki nayi inna na tambaya cikin mamaki don na manta da munyi wanan zancen a gabanta.
Hukuncin da kike shirin dauka don kawai mahaifiyar mutymin nan bata kaunarki da danta har yanzu.
Wani dan murmushi na sake a fuskana kafin na fara silalo da hawayen takaici na dago kai na kalli inna cikin karfin hali na toshe bakina ina fadin .
Inna ba don mahaifiyar shi nake son rabuwa dashi ba don akidarshi ce daya kaucewa addini nake son barin shi.
Wani ka)on mamaki inna tayi min kafin tace dani kin ko san abinda kike fada yar nan mutum kamili kamar wanan zakiwa sheri don kawai bakya son shi ko me zaki mai wanan kazafin ?
Kallon ina nayi nan dan lokaci kafin na girgiza kai ina hade wani kololon bakin ciki daya tokare min makogorona dama nasan za a rina idan na fito masu da wanan zancen ai.


ZAINAB IDRIS MAKAWA




YA ALLAH ALLAH KA JIKAN MAGABATAN MU KA GAFARTA MASU KURAKUREN SU KASA ALJANNAN MAKOMAR MUSULMAI YASA ALJANNA MAKUMAR WANDA YA FURTA KAMAL LA,ILLAH HA,ILLAH MOHAMMADAN RASULULILAH, , , , , , ,


YAN UWA MUSULMAI YA SHAGALGULAN SALLAH DA BANKWANA DA RAMADANA DA FATAN RAMADAN DIN BANA YAZO DA KARA MUNA IMANI A ZUKATAN MU AMIN, , , ,


Ganin da inna tayi na kasa magana sai hawaye ke zuba a fuskana sai kuma ta shiga damuwa lokaci guda ta rude.
Hankalinta ya tashi ta koma fadin ki rufa muna asiri ki rufa min idan da wani abu ki fada min mu san inda zamu bullo ma ko meye matsalan ki da mijin ki yar nan ?
Da kyar na iya budan bakina da yai min nauyi ina fadin inna da matsala a cikin auren mu babba sai dai idan kince na koma mu zauna a hakan zan koma don ke .
Menene matsalan dake akwai tsakanin ki dashi inna ta sake tambaya tana kallona don son jin mezan fada.
Bakina yai nauyi da abinda zan fadawa innan sai kawai naja filo na mayar da kaina tare da sake wani irin kuka lokaci guda mai ban tausayi.
In don matsalan kice da uwar mijin ki wanan ba kanki bane farau ai naji muryan innan na fadi,don da wayau ki kinga irin zaman da mukayi da kakar ku a gidan nan.
Yanzu fa da nayi hakkuri komai ya wuce sai abinda ba,a rasa ba tunda yanzu ta gane gaskiya ita da kanta.
Cikin kukan da nake nayi karfin halin fadi inna matsala ba irin taki bace tawa matsalan daban yake dana ko wace mace inna.
Subbahanallahi wanan maganan babba ke nan ta fada sai kuma tayi shiru na wani dan lokaci can naji ta mike zata bar dakin .
Ta kai kofa ta juyo tana fadin kiyi tunane kafin ki san abinda zaki fadawa mahaifin ku don kin san shi kin san halin sa ta fita.
Ban daina kuka ba sai ma karawa da nayi kan wanda nakeyi da farko don nasan za a rina kan hakan.
Don ba kowane zai yarda da abinda zan fada ba gashi ma ban fada din ba a fahinceni asan akwai matsala akan hakan dana ce.
Haka na kwana ranan tare da dinbin tunane a raina ina nemawa kaina mafita da naga zai dace dani.
Washe gari koda muka tashi inna ta dauki zafi dani sosai ko gaisuwan da nayi mata da kyar ta iya amsa min shi ba cikin dadin rai ba.
Ganin haka yasa nima na nisance ta na koma kuryan daki ban zauna a falo ba yadda muka saba gaba dayan mu.
Kanne na sai shigowa dakin suke suna tambaya ko lafiya nake na zauna a dakin har tsawon kwana biyu muna haka da inna ba wani sakewa a tsakanin mu ni da ita.
Ranan na uku na shirya nake fadin zan je naga maizube tayi min sai mun dawo wanan tafiyan ban yarda na tafi da kowa ba sai karamar kanwa daya dana dauka muka fita tare da ita.
Nayi sa,a na samu malam a gida muka gaisa da matan shi maizube tayi min jegora zuwa wurin malam din.
Ya tareni sosai yana saka min albarka tare da kara ban hakkuri irin na manya kafin maizube tace dashi barin baku wuri ku gana ayi yaushe rabo ko ta fada cikin hikima .
Nace ba sai kin fita ba ai tunda kin san komai tun farko kamar dai yadda kika barmu har yanzu hakan muke dashi.
Ta amsa da fadin eh malam gaskiya kamar yadda dai na fara fada mane zaman nasu ba dadi sai hakkuri.
Ga kuma fannin uwar mijin nata shima dai babu dadi har yanzun din don kiyayyan nata da ita yana nan bai gushe ba.
Nan malam din ya danyi murmushi yana fadin halin ku mata sai ku wallahi mace ko tayi shekaru kamar me bata taba canza halinta na mata.
Ita bata san ke din alheri bace a garesu ke maizube na fada na kara fada maki tun farkon auren yarinyar nan ita din alheri ne a cikin su.
Duk sanda zanyi istihara akan matsalan su ni haske nake gani a lamarin nan banga wani abin aibu ba a cikin auren ta da yaron nan .
Sai dai dan matsala na rayuwa da ba a rasa ba can da ake samu gun ko wasu maurata da suke tare na rayuwa.
Dakin yayi tsit babu mai motsi a tsakanin mu sai can na gyara zama ina sharce zufan dake zubo min a goshina lokaci guda jin abinda malam din ya fada.
A raina ina fadin ta yaya malam zai fadi hakan har in ance malamai suna ganin abinda ke faruwa ga mutum .
Ni tayaya malam zai kira min wani alheri bayan halin da nake ciki muryan malam din ne ya dawo dani daga tunanen dana tafi yana fadin.
Maizube ki bamu wuri in kara ganawa da ita akwai abinda nake son ji a bakin ta don naga akwai nauyi a tare da ita har yanzu.
Take maizube ta mike don bin umurnin mijin nata tana fadin nima dai haka naga yafi don matsalan kawar tawa babba ne don gaskiya malam sai anyi bicike sosai ga matsalan nan.
Ace mace na zaune gidan miji har tsawon wanan shekarun yana kallon ta photo malam ba ko wace mace bace zata iya wanan hakkurin haka.
Hannu malam din ya dagawa mai zube din alaman ya isa tare da fadin ke kuma yanzu zaki zama babban banza ko makin ki yabe ta kan hakan sai kuma ki tunzura ta.
Malam abinne keda daure kai wallahi koma meye Allah na maganin sa ai tana kokari tunda har takai haka dashi yanzu riban ta ya rage ta girba
Showing 315001 words to 318000 words out of 390011 words