kike furta ya sakeki ?
Zata ce hakan dole hjy don jafar mutumin banza ne a yanzu na fahinci dalilin shi na zaben zainab dayayi a matsayin matan auren shi.
Wanda dacan hankalina bai kawo min haka ba sai yanzu dana fahinci waye jafar din don rayuwan jafar baida kyau hjy.
Jafar ya fita daban a cikin yayana da al,umman musulmai baki daya hjy zan iya fadin yau nayi dana sanin haihuwan jafar da cikina wallahi.
Wa,iyazu billahi mami don Allah ki bar fadin haka ko mai yai maki haka mai zafi kiyi hakkuri ki tausa zuciyar ki akan shi.
Idan kaga na yafewa jafar har mun shirya dashi ya daina wanan halin banzan da yakeyi a rayuwan shine zamuyi zaman da uwar shi.
Don haka yau ba sai gobe ba gaba dayan ku ku shirya mu bar masa gidan shi don banga amfanin zaman mu a gidan mai fasadi irin jafar ba.
Wa iyazu billahi iyami dan naki kike aiban tawa haka da bakin ki har kina kiranshi da mai fasadi wani irin aikin asha yake aikatawa mai muni haka.
Please mami don't tell her abinda idon ki ya gane maki don hjy bata da karfin zuciyar daukan wanan maganan a yanzu na fada da turanci.
Gaskiyane ya mamud ya fada shima a cikin harshen turanci sai hjy tace nasan dai ba zai wuce akidan nasara ba da yake yawan dauka kuma ko yaushe mukai waya ina masa huduba da hakan.
Jafar din ne ya turo kofa ya shigo da alama ya danji wani abu daga cikin zancen namu a dakin don kofan a rufe yake lokacin.
Yayi wankan shi fes ba zaka taba cewa shine ba mai mumunan halaiyan nan idon shi akan mahaifiyar su dake darzan kuka saman gadona.
Kafin ya mayar da kallon shi wurin hjy dake tsaye a kan yarta ni kuma ina rusunne a gefe ina hawaye.
Hannun ya mikawa ya jafar yana fadin so you surprise me zuwa haka babu sanarwa duka family baki daya.
Cikin dan basarwa ya mamud di yace dokan mami ne hakan ta hana kowa ya sanar daku zuwan mu saidai ku ganmu kwatsam.
Nayi dana sanin wanan zuwan yafi dubu dana san abinda kake aikatawa a kasan nan da ban taba taka kafana zuwa gidan ka jafar .
Dan murmushi yayi irin na masu karfin hali tare da fadinn haba mami me yai zafi haka kuma da bazaki zo gidana ba .
Ai ko baki zo don ni ba zakizo don yar ki nan ki ganta kiga inda take zaune tunda kin huce damu.
Shidai na gani sai dai kuma kai ja,iri da zuwan uwar taka ka bata mata rai haka me kayi haka da zafi har ka fice mata a raine lokaci guda ?
Dan murmushi kawai ya sake tare da kallon mamud yana fadin ina madam da yaran su ke ko har dasune tafiyan .
Kowa na nan ya mamud ya fada tare da fadin muje daga waje don mami ta huta ya soma tafiya yana fadin hakan.
Shi kuma ya mara mai baya muryan mamine ya dakatar dasu din da wani irin tsawa take fadin mamud na fada ma kafita ka samo inda zamu sauka gobe zamu bar kasan nan da yardan Allah.
Lokaci daya suka juyo gareta da mamaki suna kallon ta hjy ce ta katse su da fadin kekan tir iyami da wanan halin naki na rikau.
Don kawai danki ya bata maki rai zaki fadi haka gareshi idan kinyi hakan ma kanki kika bawa kunya ai.
Kada ki manta wanan tafiyan ba iya diyan ki kawai kikayi shi ba don haka ki shiga hankalin ki tun kan duniya ta saki a baki.
Ki fada muna laifin yaron nan kuki fitowa fili ku fada daga ke har matar tasa sai kwanaye kwanayen da kuke muna a yanzu.
Wanan maganan da hjy tayi yasa jikin mami sanyi amma kuma sai ta sake wani sabon kuka mai tayar da hankalin mutum .
Ya mamud din ne yajashi suka fice daga dakin suka sauko kasa nan ma babu kowa duk suna dakunan da aka saukesu suna mayar da fadi a game dani da kuma irin gidan da muke zaune.
Inda Aisha ke basu labarin ai basu ga kallo ba sai idan sun shiga dakina da nake zaune a ciki a nan zasu sha mamaki wai duk zee ce da wanan daulan haka.
Har suna hada baki wurin fadin ki bari don Allah nan ma din kadan ke nan ashe muka gani bisa ga nata din

ZAINAB IDRIS MAKAWA



YA HAIYYU YA KAIYUMU BIN RAHAMATIKA YA ASTAGIS UBANGIJI KAI HASKE GA KABARIN DUK KAN MUSULMIN DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA ALBARKA KALMAN LA,ILLAH HA,ILALLA MOHAMMADAN RASULILLAH DA SUKA TABA FADA A RAYUWAN SU ALLAHUMA AMIN , , , , ,


Gidan yayi shiru lokaci guda baka jin motsin kowa a gidan sai na,orurin dake aiki kawai na gidan a lokacin.
Mami dake kwance ta mike a hankali zaune taji zaman bai mata dadi don zuciyar ta daya cushe wuri daya a lokacin.
Haka yasa ta saukowa daga saman gadon a hankali ta gyara hulan dake saye a kanta ta nufi kofan fita daga dakin.
Ba kowa falon don haka ta nufi wurin shan iska inda zaka iya tsayawa kaga duk wani abinda wajen gidan ke ciki daga inda kake tsaye.
Jamal ta hango tsaye shi kadai a cikin duhun yana tsaye ya harde hannayen shi guri daya yayin da kafafuwan shi ma suke a harde mashi.
Hankalin shi gaba daya ya mayar dashi gaban gidan jikin shi na jingine da dan bangon wurin yana tunane ga iskan sayi yana huro mashi a jiki.
Jin motsin mutum da yayi lokacin yasa shi dan juyowa inda yake jin tafiyan mutum din mami ya gani don ya sheda ta duk da akwai duhu a lokacin.
Hakan bai hanashi sheda mahaifiyar tasu ba da take tafe itama mami din ta sheda ko waye a wurin tsaye duk da duhun dake akwai din.
Mami baki barci ba ya fada cikin mamaki da tare da juyowa inda take yana fuskantar ta.
Jamal ban dauka zan kara barci da idanuna ba kuma a wanan halin da dan uwan ka ya jefa kanshi a ciki na rayuwa irin wanan.
Mami yanzu kin gani ke nan kema abinda na gani gareshi nake wanan fushin dashi .
Jamal na gani Allah ya nuna min da idona yau naga mugun gani da idanuwa ga dan dana haifa da cikina .
Sai wani irin kuka yazo mata lokaci guda jamal din yace mami ba kuka zakiyi ba don yanzu yaya addua da taimako yake so a garemu don yayi nisa a cikin wanan harkan ko yanzu.
Jamal dole inyi kuka yau jafar ne a cikin wanan halin haka jamal ina zan saka rayuwana dan dana haifa aka bar min amana shine ya zama haka a rayuwa.
Wanan kaddaran bawane, mami duk mai rai baya wuce kaddaran shi a rayu don haka zama ya kamata ayi asan hanyar da za a fitowa wanan maganan tunkan zancen nan yayi bosting kowa yasan hakan.
Sani kuma na yaushe jamal tunda matar tasa ta sani kila kuma yan uwanta nan da suke zaune suma duk sin sanda hakan ko ?
Kai haba mami zainab tana da matukar wayo bazata bar kowa yasan wanan zancen ba rufa min baki wani wayau can.
Zata dai iya yin hakan don ta kare kanta itama tunda take zaune dashi ai kila itama din yar hannun ce ke nan ai yanzu.
Ina mami baki san waye yarinyar nan zainab ba ashe har yanzu don koni danagani da idona kuma a kusan tare zance munga wanan abin amma bata yarda nasan da hakan ba .
Saida na fito mata da zancen da kaina ta yarda tayi min bayanin komai don haka nake ganin ko yanzu ba zata taba barin kowa yaji hakan ba a bangaren ta.
Jamal ke nan duk da kai yaron har yanzu baka tunane ko ita yanzu ya bata ta yasa bata yarda ta tona mashi asiri.
Shiru Jamal din yayi yana tunane kala kala a zuciyar shi kafin yaji muryan mami yaci gaba da fadin nima haka wanan tunanen yazo min .
Don yadda naga tana kokarin rufa mai asiri dole akwai wani abinda itama take boyewa nata don ko hjy dake dakin muna magana da mamud cewa tayi kada a bati taji komai don tsufa.
Sai wanan karewan da takeyi din ya tsaya min a zuciyana na fara zargin itama ta dade da lalacewa ta wanan fannin yanzu.
No mami kada kiyi zargin hakan a dai bincika a ji ai zata fadi gaskiya koma meye ba zata boye maku gaskiyan ba nake tsamani.
Kana wasa da wanan yarinyar jamal ya katse da fadin haba mami yanzu kuma meya saura na zargin zainab gareki.
Ga gaskiya tayi halinta baro baro za a tsaya zagin yar mutane damafa ya J yayi amfani da yarinyar nan zainab ne ya aureta bada yardan ta ba yabi ta wajen iyayyenta ya aureta.
Don kawai ya kawar da idon mutane a kasan ace yana da aure ai ba haka kawai yake zaune ba.
Don kada mutane damu a gano abunda yake aikatawa din wanan hikima yayi yaki yarda da auren hadin da kika so yi masa a baya.
Don yasan idan daga bangareki ne yarinyar ba zata taba yarda ta boye shi ba yadda zainab din ta boye shi na shekaru.
Idan ma cutane mami yanzun dai kingani yar mutane da aka baki amana aka cuta don mutuncin ki iyayyen ta suka gani tun farko suka yarda suka aura mai ita ba tare da wani kwankwanto ba can.
Kai jamal ni kake kokarin nuwa yaran nan kome ina dukkan ku ta dalilina kuka san yarinyar nan dai ?.
Koma meye zan zauna da ita ai in fahinci komai wallahi idan yarinyar nan tana da hannu cikin wanan matsalan gaba daya sai na sabawa rayuwan su.
Don me zai shiga daki haka da wanan katon suna wanan wasan banzan idan ba wani abu suke aikatawa ba hakan ?
Ok mami hakan yana da kyau ai ki bincika kiji komai don zaki gane mai gaskiya a cikin su yanzu ai idan kin bincika din.
Sai dai kuma mami ki sani danki fa abinda kika gani shine gaskiya abinda danki ke aikatawa a kasan nan don shi sam bai damu da diya mace ba a rayuwan shi.
Ga abu kin gani da idon ki mami zaki tsaya kina wani kwanaye kwanaye akan yar mutane ?
Yanzu dai ai abin cikin duhu ya fita fili Allah ya nuna maki wanan sirin da danki ke boyewa sheka da shekaru yanayi.
Ji kawai yayi mami ta fadi kasa a wurin somamiya da sauri ya nufi kanta yana kiran sunan ta cikin tashin hankali.
Gashi su biyu ne kawai a falon dabara ya fado mai na ya yayyafa mata ruwa ya nufi kitchen da sauri ya dauko goran ruwa mai sanyi ya dawo dashi inda take.
Ya yayyafa mata sai gata ta farfado lokaci guda sannu yake faman yi mata sai ta koma luuuu ta kara somewa kuma.
A daidai lokacin fadila ta fito don motsin da take ji tun dazun a gidan idon ta yai arba da mami kwance kasa somamiya .
Ga Jamal a kanta sai faman gurgizata yakeyi ihu ta yanka don tsoro lokaci guda muke bude kofofin gidan muna fitowa daga dakun nan mu.
Kai ranan munga tashin hankali asibiti suka nufa da ita kai tsaye dashi da yaya mamud sai jamal da jalal da suka bisu.
An barmu gida hankali tashe don bamu san halin da mami ke ciki ba a can don duk sun bar wayoyin su a gida tunda ba fitowan girma da arziki sukayi ba daga dakunan su.
Tambayan nasha shi wurin Aisha amsa daya nake bata shine nima ban san dalilin hakan ba nadai ga mami a wanan halin tun bayan shigan ta dakin yaya .
San nan na samu sa,ida a wirin su da tambayan da suke min hjy kan iya damuwa ta damu sosai da yar ta mami a halin data shiga.
Basu dawo gidan ba sai washe gari suke fadin anba mami gadome asibitin da aka kaita tana can kwamce tare da jalal da jamal.
Duk da hankali ya dan kwanta tunda sunce ba wani case bane sosai wai gajiya ne yai mata yawa na hanya.
Nikan a raina nasan ko meye umul,aba,isin hakan da takeyi naja bakina nayi shiru don kada wani ya farga ya gane nasan wani abu.
Gani da test a ranan Maya tana ta kirana dole haka na sance jiki na fice zuwa rubuta test din fadila kawai na fadawa inda zan tafi a lokacin.
Allah ya taimakeni ba a fara ba saura minti biyu za a fara na shigo ban dade ba aka fara test din muna fitowa nayi sallama da maya na tafi.
Na dawo na samu sun tafi asibitin duban mami sai fadilace kadai a gida sadiya bata riga data dawo gida ba daga makaranta don ni nayi saurin dawowa ranan.
Da kaina na shiga kitchen muka hada masu abinci tare da mai aikin daya data saura a gidan don sauran sun dauki hutun sun tafi gida.
Fadilace ke fadin rashin kyautawana da ban je asibiti duba mami ba nace da zuwana da rashin zuwa daya yake a wurina.
Don yanzu jira nake kawai ta ba danta umurnin ya sallameni mu koma gida don shi kawai nake jira yanzu.
Da sauri ta kalloni da mamaki tana fadin kada ki fadi haka zainab don nasan boss bazai taba sakin ki ba ai.
Saboda wasu dalilai nasa kina da rana da amfani a wurin shi sosai wanda ba kowane yasan da hakan ba.
Saki ya zama dole yanzu gareshi don lokaci yayi da zaiyi hakan na gaji da ganin laifina da mahaifiyar shi ke min ko yaushe.
Gara na bar mata danta a zauna lafiya ta aura mashi yar masu arzikin da take so ya zauna da ita.
Ina shima yasani ai zainab babu macen da zatayi wanan hakkurin da kikeyi a gidan nan yanzu.
Don haka ki daina ma wanan zancen zainab don haka ki shirya muje anjima mu dibo ta ko ran mijin naki bazaiyi dadi ba idan bakije ba ai.
Amma anty don ta katseni da fadin please zainab kada kice ba zaki ba din ko rashin zuwan ki a yanzu ai tasan da wani abu a kasa don abin zai iya damun kowa nan gaba.
Nace shike nan anty zan tafi da yamma idan Allah ya kaimu sai ki shirya idan sadiya ta dawo mu tafi dukkan mu.
Sun dawo gidan saidai ba wani damuwa a tare dasu don jikin mami din da sauki sosai sun dai kwantar da itace don ta samu hutu da natsu a can.
A falo suka zube wasu kuma suka shiga yin sallah masu rikon addini ke nan daga cikin su irin hjy tsohuwa da anty Na,ima sai Aisha data shiga itama don laluran ta ba laifi ta tsaya tayi sallah a dakin.
Don na shiga na sameta tana sallah amma su Nuriya dasu Rufaida suna falo ana hiran garin wanda a cikin hiran nasu suke sako habaici a ciki.
Dawowan Sadiya ba ta dade da shigowa ba a lokacin kowa na falo zaune har mazan suna cin abinci duk suka bita da kowa da abinda ke zuciyar shi .
Lokaci ne na mike zuwa daki na samu Aisha kwance tana waya nan daki na shiga ban tsaya ta kanta ba na fara watsa ruwa a jikina.
Nafito nake shiryawa don fitan da zamuyi zuwa duba hjy muryan Aisha ya daki dodon kunnena da farko tsuki mai karfi naji taja.
Hakan baisa na waigo inda take ba don zatona da wanda take wayan take tsukin sai naji muryan ta na fadin tsiyan banza ashe da gaske ake fadin dan talakka bai iya samun wuri ba dama.
To bari kiji wallahi zainab idan wani abu ya samu mahaifiyar mu wallahi ni da kaina zan dauki mataki akanki koda kuwa ya j zai halakani nima.
Na juyo ina fadin au dani kike zance ashe amma dai kafin ki halakani din zai fi kyau shi J din ki fara halakashi don shi musabbabin komai da mahaifiyar ku ke ciki.
Ni meye nawa a ciki don bani nakar zomo ba rataya akabani don haka kowa ya sakar mun mara nayi fitsari .
In laifine jeki gun dan uwanki ki tsure shi donni ba haifana kikayi ba da zaki sakani gaba zaki fada min rubish.
Tunda na juyo na fara magana Aisha ta tsura min ido tana kallona da mamaki karara a fuskanta har nakai karshen magana na juya ina daukan kaya da
Showing 249001 words to 252000 words out of 390011 words