amma zainab tayi kankanta da irin wanan rayuwan haka da takeyi a gidan nan tunda da kurciyar ta.
Ace miji ba ruwan sa dakai ba zaya kalleka da sunan mata ba a idon sa saidai ayi ta labta ma kayan alatu kana hasaka gari ?
Tsohuwar ta gyara zama a rude tana fadin nikan kun barni a cikin duhu har yanzu don na kasa fahintar inda kuka dosa.
Sai ta mike tsaye wanan zancen bana kyalewa bane barin samu uwar nasa idan itace me sakashi cutawa yar nan haka a zaman su.
Duk kiran da fadila kewa hjy ta fice bata juyo ba gashi da kyat take tafiya yanzu ajiyan zuciya na sauke don nasan ko banza yanzu za ayita ta kare tunda har hjy taji wanan zancen duk da bataji duka ba ma.
Fadila ke fadin banso tsohuwar nan tafita haka a cikin fushi ba don yanzu komai zai iya faruwa har wa yan nan yaran su ji.
Dakin da mami ke ciki hjy ta dosa suka hade da ya jamal a kofa ta wuce shi tana fada haka kawai ka tasa yar mutane a gaba da duka .
Gara dai a kashe wanan auren kamar yadda iyami ke so tun farko kowa ma ya huta da wanan alkakan hakana.
Aure ba haihu bada ba jika amma fitinan shi har yau yaki karewa mutane a rayuwa gara akashe kowa ya huta.
Jin hakan yabi bayan ta zuwa dakin kusan a tare suka shiga mami na zaune ta jingina bayan ta da gado kafafuwan ta a mike da gani ba sai an tambaya ba tana cikin damuwa ko tashin hankali walau ciwo kuma.
Yau dai ayita ta kare a gidan nan ku sakarwa yar mutane mara ta huta mami ta dago kai da sauri tana fadin hjy kedawa kuma ?
Ni da dan nan naki jafari ya kama yar mutane da duka haka duk ya bata mata fuska da shartin yatsun shi ina yar nan ina daukan dukan bawan Allah nan.
Ko ya fara shaye shaye ni kan don sai magana take min bayani a dunkule mai nuna ABU A CIKIN DUHU SIRINE.
Mu muna mata kallon ta samu gida tana yadda ranta keso jiya jiyan nan na gama ji yaran nan wanda basu da aiki sai hassada da kyashi suna fadan haka da kunnuwana naji su sai gashi yau Allah ya nuna muna sirin dake boye.
To gara dai kisa ya sallami yar nan tunda abin ya kai ga duka haka tun muna nan ke nan inaga bama nan Allah kadai yasan ukuban da yake nuna mata tunda kin riga da kin masa huduban shedan ya dauka gara dai kowa ya huta da wanan auren itama ta kama gaban ta taje ta samu daidai da ita a can.
Saida ta kai aya ta dago kai don duban mami data kyaleta tana ta zuba haka sai taga mami din na hawaye mawuyacin abu ga mami din duk yadda ranta yakai ga baci kuwa.
Cikin muryan kuka mami ke fadin hjy jafar kasheni yake son yi ya huta a yanzu ina dana sanin ma haihuwan jafar a duniyan nan .
Hjy tayi tsaye sororo tana kallon mami din cikin mamaki don ganin yanayin ta dakuma abinda take fadi din don yadda tasan tana son dan nata fiye da duk yan uwan shi.
Haba mami ki daina fadan haka ki masa addua jamal ya fada daga bayan hjy inda yake tsaye a kofa ranshi bace.
Jamal dole in fada don jafar so yake ya konani a duniya bayan ya kona kansa saboda rudin duniya.
Fita yayi zuwa waje ashe ya mamud zai kira a waya ya kirashi ba a jima ba sai gashi yazo da saurin sa suka shigo tare.
Har lokacin mami kuka takeyi sosai itama hjy sai ta kama kuka duk da bata san abinda ya saka mami din kuka ba haka ?
Da sauri ya turo kofan ya shigo jamal na bayan shi ya maida kofan ya rufe don ma ginan su irin na kasan da wani bsijin wani da dole sauran mutanen gidan hankalin su ya dauku garesu.
Wai me kuma ya faru ni wanan abin gara mu koma gida zaifi mami fon wallahi hankalin kowa dai a tashe yake da wanan maganan.
Shi kanshi jafar din ai in kin kula baya cikin kwanciyan hankali duk tsiyat shi yanzu da yasan an gane me yakeyi ana nuna mai kyama.
Haka yasa ya tozarta ga baki daya baya cikin walwala duk da karfin halin shi kuwa wanan karon ya sare don bai zaci haka abin zaizo mai lokaci guda ba tunda ya maida mutane wawaye,
Yanzu ba wanan ba ya mamud zainab ya kama ya doka waya sani ko yayi shaye shayen nasa ne kuma ko ta kamashi yana harkan banza.
Sam ya manta da hjy tana dakin don idon shi ya rufe a lokacin yake faman dake maganan da ba a son taji din taji sai ji sukayi ta fadi saman gado Allah ya taimaka a zaune take lokacin.
Ihun kiran sunan ta da sukeyi yasa hankalin a gidan ya koma kansu da gudu aka nufo dakin mami din.
Gaba daya dakin suke shiga dan ihun da mami din keyi ina daki ban leko inda suke ba don hutun nasu ya zama muna tashin hankali ga baki dayan mu daga mu harsu a yanzu.
Ya mamud ya kira jafar a waya yana fadin kana inane kazo ga hjy ta some muna bata numfashi.
What hjy din meya same ta kuma yanzu muka gaisa da ita na fita to kazo dai yanzu ya fada ya kashe wayan.
Shike nan kun kashe min uwa kun huta saura ni ku kasheni mami ta fada a cikin kuka goran ruwa mai sanyi jalal ya dauko a fridge ya bulbula ma tsohuwan ta sauke ajiyan zuciya saidai bata bude ido ba.
Lokacin ne jafar ya shigo gidan a rude yana fadin ku dauko ta ga motab asibiti nan waje yanzu zasu karaso .
Yana kokarin daukan tsohuwan kakan tasu uwar ta daka mai tsawa da fadin kada ka taba min tsohuwa.
Tsayawa yayi cak bashi ba da wanan zancen ya daki zuciyar shi duk wanda ke wurin saida zancen ya taba mai zuciya.
Ya mamud ne ya matso ya sukuci tsohuwan dake kwance zuwa waje sauran suka mara mashi baya a cikin sanyi jiki.
Allah ya gyara daga Nuriya har yaran ta babu kowa a wurin lokacin suna part din su sun kulle don har yanzu bata bari yaran su sake jiki a cikin yan uwa.
Muna daki bamu san wainar da ake toyawa a gidan ba fadila tana ban hakkuri har muka koma hiran hjy da take nuna min kauna kamar ni din jinin tace.
Na,imace ta shigo part dina tana fadin hjy fa ba lafiya an tafi da ita salati muka saka fadila na fadin yanzu fa muke nan tare da ita.
Falon muka fito muka samesu zaune zugun zugun anan suke labarta muna dan abinda ya faru muna jimame tare da tamtaman hakan.
Allah ya taimaka ba a kwantar da ita ba bayan yan aune da sukai mata suka bata magani da sallama.
Bayan sun dawone kula da hjy ya dawo kaina nake kula da ita da komai dani da fadila yayin da shi kuma bai zama gidan sai dare sosai yake dawowa.
Ranan naji yaya mamud na fadawa hjy zasu koma Nigeria jibi jin hakan danayi yasa nima na fara shirya muna tafiya.
Fadila ta fahinci hakan ta sameshi ta fada mai don kada tayi laifi a wurin shi bai iya min magana ba don abinda ya faru mami ta kara daukan fushi dashi sosai da bai taba tsamani ba don ko ya gaida ita yakai bata karbawa yanzu ko gaban waye.
Don haka yaje ya samu yaya mamud don yai min magana ina daki zaune sai ga ya mamud din yazo nan dai yake ban hakkuri yana fadin.
Tunda yace da zaran na gama karatu zai zo damu Nageria don haka nayi hakkuri idona ya kawo hawaye nake fadin ya mamud kasan ya dai fada ne kawai .
Sau nawa yake zuwa gida bai je damu ba sai ya dawo muke sanin gida ya tafi ai dolen shi yazo gida don mami dake fushi dashi yace .
Muddin yana son albarka ya gama da duniyan nan lafiya dole yazo su shirya da mami din.
Dole ba don na yarda ba na bar zancen tafiyan muna kallo suka kwasa suka koma bayan ya cika yan uwan shi da abin arziki kaf da suka zo sai mami da jamal ne sukaki karban komai nasa.

ZAINAB IDRIS MAKAWA





LITTAFIN NAN NA KUDINE DON ALLAH KI BIYA MU FITA HAKKIN JUNA DANI DA KE YAR UWA, , , , ,

Gidan shiru kamar ba kowa tun bayan tafiyan su ashe mutum rahamane sosai don duk yadda nake dasu sai gashi na koma ina kewan su.
Ina dakina kwance don tafiyan dare sukayi ranan tunda muka dawo daga rakiyan su na shige daki ban kara lekowa waje ba har dayan rana.
Yunwa ya fitar dani na sauko nan ma babu kowa wurin a lokacin dakin su na nufa na tura na shiga.
Na hangosu saman gado kwance ba barci sukeyi ba sai dai sun kwanta shiru a lokacin ba wai hira sukeyi ba.
Sadiya tana kallo a wayana ita kuma fadila tana kwance ta kurawa rufin dakin ido tana tunane.
Kin tashi Fadila ta fada tana dagowa daga kwancen da take nake fadin eh dama ba barci nakeyi ba ina dai kwance ne.
Abinci fa ta tambayeni nace shina sauko ci zama nayi a dakin ta kawo min abincin na dan ci muna hira.
Itace ta sako zancen su tana tuna yadda hankali ya tashi da ciwon hjy kafin ta koma hiran yadda hankalin mami ya daga akan su koma gida alhalin basu gama kwanakin da zasuyi ba a nan.
Bandai yi magana ba sai murmushin da nakeyi kawai ina jin raina yana matukar baci sosai ga hiran da take min din a lokacin.
Nan dai na zauna a dakin har lokacin sallah yayi na mike na koma dakina bayan na idar da sallah kuma ba sake fitowa ba falon saida dare da zamuci abincin dare.
A takaice dai bamu hadu da yaya ba sai bayan kwana biyu da tafiyan su ranan ya samemu a falo zaune duk suka shiga mai sannu da zuwa.
Yanayin shi kawai na kalla nasan a buge yake yashawo maye don ko wurin hawa sama saida ya dan tsaya kadan kafin ya daure ya hau sama din.
Binshi nayi da kallo zuciyana tana wani irin tafasa kafin in mike zuwa part din na sameshi a yadda ya shigo din kwance shame shame saman kujera yana barci.
Saida na kare mai kallo na duka wurin kafan shi ina cire mai takalman dake kafan shi saye baiko tsaya ciresu ba.
Ya dan bude idanun shi a daidai lokacin dana fara cire mai takalman a kafan shi yana fadin wai meye hakane kin dameni fa yarinyar nan.
Kai na girgiza ina zare mai safan kafafuwan shi na mike dasu zuwa inda yake aje takalman daya saka kafin a goge mai a mayar.
Wanan ba aikina bane yana da mai gyaran dakuna a gidan yasa ban wani damu da inje in masa wani aiki ba a dakin nasa.
Na sake mai gudun AC din falon don yayi saurin farfadowa da wuri sanan na ja masa kofan na fita zuciyana na cike da tsanar sa.
Daki na na shiga ina tunanen zancen hjy a gareni da take fadin yar nan ki taimakawa mijin ki don Allah badon mu ba ko uwarshi dake nuna maki rashin kauna taimako zakiwa addini ki zauna dashi.
Zan samu lokaci mu zauna dashi kan matsalolin ku saidai hakan ba zai samu ba sai kin hada da hakkuri cikin al,amarin.
Hawaye ne yazo min dana tuna da wanan nauyin data dora min wanda ta rantse datun farko tasan da halin sa ba zata taba yarda ya aureni ba.
Yanzun kuma data sani din iya taimakon da zamuyi mai shine addua da saka ido ga wasu abubuwan da yake aikatawa koda yin hakan zai ja mana matsala a tsakanin mu.
Shine dalilin gwada hakan da nayi yanzu bayan na fahinci a buge ya shigo gidan ke nan don baida niyar daina hakan alama ya nuna.
Haka na kwana a cikin bakin ciki washegari inda na idar da sallah nan na kwanta sai barci don ban samu barci da dare ba saboda da tunane.
Haka ya shigo dakin ya sameno kwance kasa ina barci a takure ya dan dade tsaye yana kallona kafin ya juya zai fice daga dakin.
A lokacin na bude idanuna don nauyin mutum danaji a kaina tare da gyara kwanciyana shi nagani zai fita jin motsina yasa shi juyowa.
Baiyi magana ba ya sa kai ya fice dakin da sauri kamar wanda aka kora yayin da ya barni da mamakin abinda ya kawo shi dakin lokacin.
Saida naga fitan shi na mike da sauri na zauna ina dan dube dube a dakin banga komai ba na sauke ajiyan zuciya.
Wayana dake saman gadone ya dauki kara lokaci guda na mike zuwa inda wayan ke ruri na dauka bakon lamba daga Nigeria ake kirana dashi da mamaki nakai wayan a kunne na.
Muryan mami ne ya daki kunuwan nawa tana amsa sallaman da nayi saida na dan daga wayan daga kunne na a cikin mamaki.
Na mayar ina sauraren ta tana fadin mun sauka lafiya zainab nace Alhamdullahi mami ya gajiya ya sauran yan uwa da gajiya ta amsa a sake da lafiya lau zainab.
Ya kowa nan wurin ku kuna dai lafiya ko nace a cikin dan dari dari da ita lafiya muke to ki kara hannkuri don Allah zan kara kiran ki idan mun huta muyi magana a kan mijin naki kiji ko ?
Nace to mami nagode kiyi hakkuri kinji komai yai farko yana da iyaka insha Allahu ta fada a sanyaye na kara fadin na gode mami.
Bayan ta kashe nabi wayan da kallon mamaki ina rayawa a zuciyana yau ni mami kewa magana a tsigar lalashi haka ?
Nan ta barni da tunane barkatai a raina karshe na mike na shiga bandaki na watsa ma jikina ruwa cike da mamakin mami a zuciyana.
Don koda zata wuce wanan kalman ne muka rabu dashi na don Allah na kula na kara daure koma zai zo da sauki insha Allahu.
Ina zaune gaban mirrow nake wanan tunanen sai ga wasu hawaye masu dumi suna gangaro min a fuskana nasa gefen hannu na share a hankali.
Ina ayyanawa a raina cewa ni kuma nawa kaddaran ke nan auren dan luwadi mai bin jinsin shi ya gane me a hakan da yakeyi wai.
A take naji wani itin ysanarshi ya kara mamaye min zuciyana na mike zuwa wurin kayana ina dauka naji an shigo dakin.
Dan juyowa nayi shine ya shigo dakin a cikin shirin shi yayi wanka yasa tufafi a jikin shi yayi wani irin kyau da kamala zakace wani musulmine da tsoron Allah ya gama ratsashi.
Kallo daya nayi mai na kawar da kai daga kallon shi hakan bai hanashi karasowa inda nake tsaye ba.
Saida yazo gab dani ya ja ya tsaya yana fadin zuwa gobe ku shirya zamu bar gidan nan mu koma wani unguwa.
A raina nace at list ai zaka fada min da wuri don mu shirya amma ba haka kwatsam na inji wai gobe zamu bar wanan gidan zuwa wani wurin.
Saidai a fili ce mai nayi Allah ya kaimu kawai ya juya zai tafi sai kuma ya kara juyowa yana fadin uafin ku kawai da kuke so zaku dauka .
Naji na fada yasa kai ya bar min dakin na sauke ajiyan zuciya ina mai godewa Allah dayasa na rage kayana da yawa na tura gida.
Don hjy nabawa ta kai min gun innan mu don ita sakon zaifi saukin kaiwa a wurin don a kaduna take zaune.
Saida na gama shirina na fito falon zama nayi don inci abinci na samu irin girkin mu na yan Africane aka girka don girkin fadila daban yake da nasu idan tayi.
Zama nayi naci abincin sosai na turo ban kai ga dagawa ba fadila ta fito daga daki su tana fadin ashe kin fito yanzun nake zancen ki a raina ai ko kin tashi ?
Na tashi na bata amsa, sai ta dago kai ta dan saci kallon idanuwana da sukasha kuka tun a dare don tana saurin gane hakan idan har nayi kukan .
Zama tayi a gefena tana fadin kuka dai ya zama maki sana,a madam ya kamata zuwa yanzu kin saba da halin mijin na
Showing 258001 words to 261000 words out of 390011 words