zai tashi.
A rude na dago ina fadin subbahanallahi har ciwon yayi serious hakane sosai yace ance sosai ne ciwon suna can dai sun tafi su dubo.
Ya na fadin haka ya juya ya fita daga dakin nan ya barni ina jimame akan tsohuwar har wani lokaci kafin in mike in fara shirin tafiya .
Bayan sallah la,asar ya shigo yana fadin ba zamu tafi din ba mami tace mu dakata zasu zo da ita nan Abuja yau din nan.
Sai naji hankalina ya kara tashi sosai ba abinda nakeji sai rashi zuwa ganin ta da banyi ba gani har kaduna amma ban samu leka wurinta ba har na dawo.
Tunda ya fita bai dawo ba ranan har dare sosai haka yasa nasan yana can wurin su hjyn ke nan a lokacin nasan sun iso da ita Abujan kenan tunda yakai wanan lokacin haka a waje.
Har na gama komai na shiriya zuwa dakin shi na kwanta ni kadai a dakin ina addu,in dana iya a bakina.
Barci ne ya daukeni na dan lokaci sai gashi ina mafalkin wasu mutane masu bakaken kaya duk jikin su sun saka hulunan kayan saman kawunan su.
Wanda duk yazo ya wuni a inda nake tsaye ina kallon su din cikin mamakin me ya kawo ni nan kuma su din su waye ?
Fuskan dayan abokain shi philis na gani na gane a lokacin ya daga hannu kamar yana warning dina Allah ya taimakeni na furta Au,zubikalamati min sheri min halak .Lah illa ha in,llah anta subahanaka inni kuntun minal zalumin ya wani yanka ihu duk sauran suka kallo mu sai na juya da sauri nabar wurin.
A daidai lokacin kuma na falka daga barcin sai wani irin zufa dake fita a jikina don wahala na mike zaune a firgice ina bin dakin da kallo a tsorace.
A daidai lokacin kuma kiran wayan jafar din ya shigo wayata saida na dan zabura don tsoron da nake ciki a lokacin.
Na kai hannu da kyar na dauki wayan yana fadin kina inane haka nace dakin ka na kwanta ki koma dakin ki yanzu har in dawo ya fada a cikin comand ya kashe wayan.
Wayan nabi da kallo tare da kallon lokaci karfe biyu na dare da wasu yan mintina a lokacin.
Na mike da sauri zuwa dakina banko rufo kofan dakin da kyau ba wurin sauri don ba karamin tsorata nayi ba a lokacin gaskiya.
Ban kwanta ba na shiga ban daki na dauro alwala na tayar da sallah na dade zaune ina karatun kur,ani naji dawowan shi gidan uku da darabi koda ya shigo.
Dakina ya fara shigowa tun daga kofa yake jin kira,a na har ya karaso tsakiyan dakin inda nake zaune yana fadin.
Mesaya kikaje dakina ke kadai a wanan lokacin na dan dago kai na kalleshi na mayar naci gaba da abinda nakeyi shima ya juya ya fice a dakin da saurin shi.
Kafin asuba wani irin zazzabi mai karfi ya rufeni lokaci daya haka nayi sallah a dadafe na koma saman gado na kwanta.
Rufe nake ina nishi da kyar sadiyace ta shigo ta sameni a wanan halin hankalinta ya tashi sosai ta juya da sauri zuwa part din shi ta fada mai halinda nake ciki.
Tare suka dawo dashi yana tambayan ya nake ji nace zazzabine kawai nakeji a lokacin ya fita sai gashi da magani ya kawo min nasha yana zaune har ya dan fada min.
Sai lokacin nake tambayan shi jikim haji yace taji sauki daya barsu jiya da dare yanzu zai koma yaga jikin nata kuma.
Wani asibiti take na tambaya a cikin karfin hali ya fada min tare da fadin kada kice zaki a wanan halin ki bari sai kinji sauki ya fita.
Bayan fitan shi zazzabin ya taso min sosai na ce sadiya ta ban ruwa na karanta fatiha a ciki nasha sai barci ya dan daukeni a lokacin.
Mafalki marasa kyau na dinga yi a wahalce dai nayi barci sosai a lokacin koda na tashi na dan samu sauki har nayi wanka.
Na fito na shirya don zuwa duba hjy don tana raina a lokacin sosai mu uku muka tafi da sadiya da fadila zuwa duban ta sai abinci da kayan marmari da muka saye a hanya don mu kai mata.
Kusan kowa na asibitin a lokacin don bayan sallah la,asarne lokacin mun shiga mun gaisa dasu tana kwance an daura mata ruwa ana kara mata.
Mama Ramatu ke fadin dazun mijin ki ke fada muna baki da lafiya ai nace naji sauki ne na taso gashi a lokacin wani zazzabi nakeji da sanyi a jikina.
Mami dake gefe zaune tace ya dai fadane kawai don ya kareta wani zazzabi kika gani a nan don Allah.
Kai haba yayan mu kika sani ko alherine ya samemu ake wanan zazzabin yanzu haka ai wasu haka suke laulayin cikin su dama.
Dakin yai shiru ba wanda yai magana a lokacin mamice ta sake fadin ai bata da niyar baku jika ta zauna suna jin dadi idan suka hadu da fushina watarana maganin su zanyi ai.
Da yafi mami tunda ita bata iya haihuwa ai hara a kawo wace zata haihu muna Aisha ta fada fadila ta karba da fadin Allah ne bai kawo ba hjy komai dan lokacine ai.
Wanan kina min shishigi da yawa mami ta fada abin mamaki a lokacin hjy akaji muryanta tana fadin iyami ko bayan raina kikasa jafari sakin yarinyar nan ban yafe maki ba.
Dakin yayi tsit ana sauraren hjy kafin Aisha tace dama na fada maku ai ji wanan tsohuwar da kowa ya rude a kanta tun jiya batayi magana ba yanzu take fadin haka.
Sai aka kwashe da dariya hjyn da take kwance take fadi cikin karfin hali zo nan kiji kawata inji dumin ki kusa dani tana kokarin mika hannun da ake mata karin ruwa dashi gareni.
Kai hjy da zainab sai Allah a tsakanin ku Na,ima ta fada tana fadin to mu din da baki damu da jin dumin mu ba sai mu tafi tunda zuwan mu baida amfani a wurin ki.
Ni dai na taka zuwa bakin gadon na riko hannun tsohuwar ta rike gam tana fadin zauna a nan kinji ko suna so ko basu so kin shigo cikin mu ke nan.
Muna zaune a haka sunawa junan su sheri suke fadin albarkacin bakin su kan hjy mazan suka shigo ya jafar yana ganin mu a dakin yake fadin.
Zainab kin iya tasowa ne yanzu naje gida bakwacen ake fada min kunzo asibiti ya mamud ne ke min sannu da jiki yana gaida ni har su jamal din kasa nayi su lokaci guda akaga na sunkuya kawai dama ni kadai nasan yadda nake ji a lokacin karfin haline kawai nakeyi a hakan.
Tsale daya ya jafar yayi ya kai gareni ya rungumoni na some a lokacin ban sab inda nake ba kuma sai hankalin su ya fara tashi.
Da sun dauka pretending nakeyi a lokacin har mami tana jan tsuki jamal ya fita da sauri ya kira likita yazo dashi dakin likitan ya duba yake fadin dama bata da lafiya ne haka har jinin jikin ta yana batun konewa duka.
Lokaci daya mami ta mike tsaye cikin furgicin jin abinda likita ya fada a game dani yana kiran nurse da sauri yana fadin a shirya daki a kaini ciki nan hankalin kowa ya tashi kuma.
Mami da kanta ta rikeni har dakin da aka kwantar dani duk bansan wainar da ake toyawa ba a lokacin sadiya kan kuka ta saka masu tana ihu ganin halin da nake ciki.


ZAINAB IDRIS MAKAWA



FATAN ALHERI GARE KU DUKKA MASOYANA NAGAISHE TARE DA FATAN NASARA GA DUKKAN AL,AMURAN KU NA YAU DA KULLUN, , ,

KISAYA YAR UWA KI KARANTA A CIKIN LAMUNA KADA KIJI KYASHIN BIYAN DARI UKU DON KARUWAN DA ZAKI SAMU A CIKI YAFI KARFIN HAKAN ALLAH YASA MU GANE HAKAN AMIN, , , ,


A rude suke sama kaina saida likita ya zo ya rokesu dasu fice a dakin su dubani suka fara fita daya bayan daya tare da tarin tambayoyi a zukatan su.
A bangaren ya jafar sai fuci yake yana fitar da iska a baki da hanci don takaici irin yadda yake ji a zuciyan shi lokacin don yasan abinda ke damuna a lokacin.
A bangaren mami kuma ita a nata zaton tunane takeyi kodai jafar din ya samu lafiyan da har na samu ciki a yanzu ne .
Hakama yan uwanshi da suka san da zancen suke zargi suma sai dai ya jamal ne da hankalin shi bai kwanta ba sam don zargin bai dauke shi da muhinmanci ba sam.
A karshe fita yaya jafar din yayi zuwa bayan don yai waya a kuma daidai lokacin Aisha taji tausayin sadiyana dake ta rusan kuka ta jata zuwa bayan.
Da farko bata dauka shi bane yana fadin na fada maku tun farko kada ku taba min yarinyar nan kuma kun sani.
Ta dan dago daga inda take zaune ta hango shi din daine ke magana a waya a hasale saidai bata san da wanda yake wayan ba a lokacin .
Yaci gaba da fadin duk wanda ya tabi lafiyan ta na rantse maku gaba daya dangin shi sai naga bayan su haka yai ta fadin maganganu kafin ya juya ya bar wurin bayab ya kashe wayan nasa.
Jinkin kanwar tasa Aisha har wani irin bari yake a lokacin ta mike tsam tare da jan hannun sadiya suka bar wurin ta hanyar canza hanya.
Kasa zama tayi asibitin take cewa mami ita zata koma gida a lokacin mami tayi mamakin hakan kuma ga yar nata a rude yanayin ta ya canza lokaci guda sai ta dauki hakan ga tsorone kawai yasata hakan yadda ta ga nayi a gaban su.
Har ta fara tafiya ta juyo tana fadin mami kema zanso kizo muje gida akwai abinda nake so zan fada maki .
Aisha kanki daya kuwa ya zan bar asibitu muna cikin wanan halin haka ai saiki sa a zageni idan na wuce.
Haka Aishan ta tafi tabar sadiya tare da fadila a asibitin hankalin kowa a tashe lokacin likita yayi iya binciken shi baigano ciwon komai da yaja min konewan jini ba haka lokaci guda .
Dole wai sai an kara min jini akace a lokacin yace aje a dibi nasa mami tace kai har yaushe ka tashi a ciwo a dai duba na sayarwa a gani.
Kai sam mami ba za,, a kara mata jinin sayarwa ba gaskiya ya fada daga inda yake tsaye cikin tashin hankali kafafuwan shi a harde ya dora hannayen shi saman weast din shi duka biyu.
Jamal yace a je a dibi nawa ai zan iyabawa kowa jini na mami ta kalleshi ta rasa abinda zata fada dole ta kyalesu kawai suka tafi.
A can ma jafar din yaki yarda sai nasa aka diba aka kara min mami tayi fadan hakan sosai don ta nuna mashi bacin rai akan haka har tana fadin idan shi baisan ciwon kanshi bane yake neman kashe kanshi saboda mace su sun dani
Likitan da ya shigone yasa su fita ya fara kara min jinin a jikina sai lokacin na dan farfado har ina gane inda nake ina bin mutane da kallo.
Har dare sosai su mami basu je gida ba sai sha biyu saura na dare suka sauketa a gida don tunda Aisha ta tafi da motan driver bai dawo ba.
Ga mamakin mami ta zata Aisha ta dade da barci a lokacin sai ta iske su a falo zaune suna kallo da yan uwanta.
Tana ganin mami ta mike suka shiga daki tare a gurguje mami tana sauri tana cire kaya a jikin ta zata shiga bayi.
Aishs tace mami ya jikin zainab din da sauki ko tace tana shigewa ban dakin da sauki zainab zaki tambaya banda hjy.
Mami na fada maki da magana wlh kin ki ki saurareni tun dazun wallahi mami akwai matsala akan ciwon zainab din nan.
Ja mami tayi ta tsaya tana fadin wai ban gane ba me kike nufine da magana sai ta kalli kofan dake bude ta mike ta rufo kofan kamar wani zai ji abinda take fadi a lokacin.
Ta zauna ta kurawa mami dake tsaye kofan bayi ido fadi mana ina sauraren ki mami tace ga mamakin mami sai taji yar nata na fadin mami kizo kusa don Allah kiji kada wani yaji mu a waje.
Ikon Allah Aisha meke damuwan ki hakane yau bayan kin rufe kofa wa kike tunanen zaiji kine wai yanzu.
Me kike son fada min har jikin ki ke kyar ma hakane wai tace mami is something serious daya shafe ki wallahi.
Jin haka mami din ta karaso gaban ta yana faduwa don gani yadda yar nata ta tsoroce a lokacin.
Zama tayi a gefen yar nata tana fadin ki fada min gani nazo kusa dake Aisha sai Aishan ta dago kai ta kalli mami din gaban mami ya kara faduwa ganin idanun yar nata tab da hawaye lokaci guda gaba daya hankalin ta ya tashi
Mami ko kinsan ya j yana cikin kungiyan asiri kuwa what mami ta fada da karfi kafin ta fara girgiza kai tana fadin No No No Aisha kin san abinda bakin ki ke fada game da dan uwanki kuwa ?
Kai Aisha ta fara dagawa kafin tace a cikin kuka mami na sani ba zanwa ya J sheri ba ko da kuwa ba dan uwana bane shi.
Wallahi mami ciwon nan na zainab da sanin ya j wallahi ke Aisha mami ta fada da dan karfi ki san abinda kike fada kada in saba maki yanzu a wurun nan.
Wallahi mami naji abinda yake fada a waya da kunnuwana da banji wanan bakin abinba bazan taba fadin hakan ba mami.
Nan ta fara bata labarin yadda abin ya faru har zuwan shi yana waya da abinda taji ya fada a wurin lokacin game da zainab din.
Innalillahi mami kawai ke fadi kafin kuma tazo ta fashe da kuka tana fadin jafar sai kuma ta girgiza kai a cikin takaici.
Can ta juyo kamar tababa tana fadin bayan kanwar zainab din ke dawa ke wurin mu kadai ne ta bata amsa.
Ita kanwar zainab din fa taji abinda yake fada tace ban tsamani taji don kukan da takeyi a lokacin saboda shi najata zuwa bayan wurin filawowi.
Innalillahi Aisha jafar ya kasheni idan wanan maganan gaskiya don ko mu ba zai bari ba wata rana.
Wallahi mami najine ya fada exactly abinda naji na fada maki mami ban kara masa ba ni yanzu tsoron da nake ji shine kada su kashe ta a sanadiyar shi fa.
Ki bar wanan zancen Aisha zanga mamud mu tatauna a kai zuwa safe don yanzu nasan ya shiga gida ko tunda ya saukeni.
Mami a nan zan kwana tsoro nakeji wallahi ba zan iya kwana dakina ba yau ta fada a cikin dan shagwaba.
Mami bata tsaya ba ta wuce zuwa ban dakin da tayi niya kai tsaye zuciyar ta cike da tunanen dan nata.
Har ta fito bata bar jin abinda take ji ba a lokacin don haka ta samu wuri takai kwance Aisha na gefe kwance taji mami din ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Haka yasa ta mike zaune tana fadin mami ki bar kuka please kada ki jawa kanki matsala don Allah addua ya kama ayi masa yanzu please.
Aisha jafar yana son ya kasheni me yar mutane tayi masa yake son bada jinin ta a sh haka ?
Mami ni godiyana ga Allah daba zarah bace yake aure haka ya faru da kinsan iyayyen ta ba zasu taba yarda da hakan ba sam.
Tunanen da nakeyi ke nan yanzu Aisha da ace itace a gidan nasa yau ina zan sa kaina a kasan nan inji dadi.
Yanzu ne na kara tabbatar da kalami da ya keyi idan nayi mai maganan aure sai yace zainab ce daidai dashi ya aura.
Ashe abinda yaron nan yake nufi ke nan ban fahinta ba har hjy tsohuwa ta rigani fahintar manufar sa din .
Haka suka kwana sai kusan asuba mami din ta tashi ta fara nafila ana fitowa sallah ta kira wayan mamud tana neman shi idan ya tashi.
Hankalin ya mamud ya tashi yana zaton ko hjy ko nice wani abu ya faru damu.
Ya amsa da fadin mami gani zuwa yanzu Nuriya dake gefen shi ta dago da sauri tana fadin lafiya dai ko yace ban sani ba sai na tafi.
Kodai zainab din ce ta cika ta tambaye shi tana kure shi da ido don jin amsan da zai bata a lokacin yace itace damuwan ki a duniya dama ?
Kai ba a maganan arziki dakai dama
Showing 345001 words to 348000 words out of 390011 words