nasa da yanayin zazzabi gashi yayi wani irin rama lokaci guda jikin shi kamar ba nasa ba babu kuzari a tare dashi.
Ya dan dade rike da hannuna a jikin shi a hankali yake sauke ajiyan zuciya alaman ciwon na lafawa a lokacin.
Nace yaya tun yaushe ne baka da lafiya haka baka kula har ciwon yai nisa haka a jikin ka ?
Da kyat ya bude ido ya kalleni a sanyaye idon shi da kyat yake iya budan idon yake fadin zainab yau two days ke nan ina fama haka.
Idona na runtse runtse lokaci guda na shiga wani irin damuwa da dan tunanen halin da yake ciki din.
Cikin daurewa nace kaci abinci kuwa yace na dan sha ruwan coffee da safe na mike tsaye ina fadin bari na debo ma wani abu kadanci yanzu.
Sai lokacin na tuna hannun mu yana sarke dana junadashi da sauri na kalli hannun don har lokacin bai sakeni ba na dago na dan kalle shi muka hada ido nayi saurin dukar da kaina kasa.
Nace bari na kara hada ma ruwan dumin ka watsa ko zakaji jikin ya sakema yace to zainab tunda kina son inyi a yanzu.
Tsikar jikina naji ya tashi don irin kallon da yake min a lokaci na zare hannuna dake sarke da nasa na juya ya dan bini da kallo.
Ruwan dumi na kara hadawa wanan karon yafi na farko zafi don zazzabin da naji a jikinshi dazun.
Na matsa mai maclen ga brush sanan na fito na sameshi har lokacin a inda na barshi kwance a kasa.
Murya kasa kasa nake fadin na hada ruwan a bandaki yaya ka tashi kayi wankan ko ?
Jin yayi shiru gabana ya fara faduwa na dauka wani abune ya sameshi kuma lokacin ganin yadda ya lefe baya ko motsi .
Hannuna nakai saman wuyan shi a hankali ina tabawa naga ya dago kai a hankali yana kallona cikiin wani irin yanayi na zafin ciwo nacin sa sosai.
Ya mike yana mai mika min hannun shi na kamashi ya mike tsaye yana dafani har zuwa bandakin saida ya fara alaman tube tofafin jikin shi nayi saurin fitowa naja masa kofan.
Ina fitowa na nufi gadon da yake a yamutse na gyara mai shi tsaf na kara gyara mai ko ina na dakin sannan na daga filo na aje mai kudaden dana gani a dakin.
Saidana shirya komai tsab a dakin na fitar mai da wasu kaya masu laushi na dora saman gadon sa.
Kitchen na shiga nasa julie ta hada mai kalar abincin sa da yakw ci idan baida lafiya a take jiki na rawa ta fara hada mai abincin na koma in gani ko ya fito daga bandakin.
Sai jin kakarin amai naji shi yana yi daga cikin bandakin da sauri na isa kofan bandakin ina kiran sunan shi a hankali.
Da kyar ya amsa min a wani irin yanayi sai can ya bude kofan ya fito yana rangaji ya nufi bakin gado ya zauna.
Da sauri na karaso wurin ina masa sannu ya kai kwance daga shi sai tawul a jikin shi yana maida numfashi a hankali.
Sannu da jiki na kara mai na dan dade a tsaye saman kanshi ina kallon yanayin da yake ciki na ciwon dake damunsa din.
Kafin in juya in fita zuwa kitchen inda na samu julie ta hada abincin tana kokarin dauka takai masa na karba tare da yi mata godiya na bar kitchen din.
Still dai a kwancen yake ya dora hannayen shi saman goshin shi ya rufe fuskan shi dashina aje abincin tare da fadin yaya ka daure ka saka kaya a jikin ka mana sai ka danci wani abu.
Da kyat ya mike yana gyara tawul din dake jikin shi na kawar da idona da sauri daga kallon shi don abinda naga yanayi ban taba ganin namiji tube a haka gabana ba sai wanan ranan.
Da kyar ya iya saka kayan a jikin shi ina mashi sannu a yadda nake kaina na duke ina kallon kasan ties din dakin dake sheki da daukan ido.
Shima hankalin shi na gurina don yana tausaya min saboda ganin yadda na damu cikin dan lokaci kananki da ciwon shi.
Yaci gaba da kallon yanayina bai iya magana ba har ya gama shirin shi ya dawo gaban abincin dana ajemai ya zauna .
Da sauri na mike ina kokarin zuba mai yana kallona yana mamakin yadda na sa aka hada mai wanan abincin don gaskiya shi kadai zai iya ci a lokacin.
Nagama na juya zan bar gurin ya dago kai ya bini da kallo can naji muryan shi yana fadin kada ki fita ki barni ni kadai yanzu.
Jikinane yayi sanyi don jin abinda ya fada nace zan duba halimatu ne in dawo don bata san na bar dakin ba tana barci.
Daga haka na fita na barshi a dakin ina tunanen yadda lokaci guda yayi laushi haka kamar bashi ba.
Tana kwance abinta tana barci har lokacin hankali kwance na kara ja mata abin rufan ta data rufe dashi na shiga bandaki na kara wanka don dan aikin danayi naji jikina ba dadi.
Na fito na gyara jikina na shirya na fito tare sawa kofan key ta baya zuwa part din yaya yana kwance share share saman gadon.
A hankali na mayar da kofa na rufe na karasa bakin gadon ina kallon shi kafin in mayar da kallona wurin abincin dana zuba mai.
Baici komai ba nake fadin yaya bakaci abincin ba ai ya dan dago da kyat yana fadin amai na kara yi danaci.
Allah ya sauwaka nace mai tare da nufa wurin kayan ina hadawa yace ki barsu har da safe a fita dasu bari na fita dashi yanzu kada ya bata dakin na dauka ba tare jiran jin abinda zai fada ba.
Na dawo tare da rufo kofan a hankali na samu gefen gado na zauna tare da tsura mai idanu ki kwanta zainab na gode ya fada a sanyayye.
Zan kwanta a can na nuna sofan dake can gefe daya a dakin naji yace No ki kwanta kawai a nan bari nina koma can yana kokarin mikewa tsaye.
Ni dai ido na kura mai har yakai ya kwanta tare da dunkulewa a wuri daya na dade a zaune ina kallon shi kafin na dan kwanta a hankali don dare yayi sosai a lokacin.
Barci ya daukeni a yadda na kwanta din har bansan a inda nake ba sai can cikin dare cikin barcin nake jin wani irin nishi a gefena.
A hankali nake bude idona na dauka da farko ko mafalki nakeyi saida kara bude idon naji a fili nake jin nishin na fitowa a gefena.
Idon na ware gaba daya sai a lokacin na tuna a inda nake tare da dan dawo da hankalina wurin danake jin nishin nasa.
Ban fahinci halinda yake ciki ba nayi yunkurin mikewa zaune ya kankame min jikina yana fadin please kada ki tashi zainab ki taimaka min in samu relief daga gare ki .
Hakana daure yana kankame dani har lokacin da naji ya sake wani ajiyan zuciya mai karfi kafin naji jikin shi yayi lakwas na dan lokaci.
Nidai ina wuri daya a takure a cikin tsoro da fargaba sai naji ya sakeni ya juya yana gyara kwanciyarshi sai lokacin na sauke wani irin ajiyan zuciya tare da dan juyawa.
A hakan har na koma nayi barci na sai asuba na falka don lokacin tashina sallah yayina sauka saman gadon a hankali don kada na tayar dashi ya falka don a zatona ya samu barci.
Sai na ganshi a wurin sallah shi yana sallah abin ya ban mamaki ganin hakan fasa shiga bathroom din nasa nayi na juya zan fita yake fadin ki shiga nan kiyi mana.
Kamar munafuka na shiga nayo alwala ban dade ba na fito sallah nayi kafin in mike na bar dakin zuwa namu.
Ina budewa halimatu na dagowa take fadin yayan mu har naji tsoro na falka ban ganki ba da dare tsoro ya kamani .
Kai halimatu ina zani yanzu ai gani na dawo na bata amsa ina cire hijjab din dake jikina na nufi bandaki kai tsaye don in kewaya.
Saida na fito ina shafa mai nake fadin jiya jikin yaya ya matsa mai saida ya kirani da dare na sameshi tace da sauri yaya jikin nasa yayan mu ?
Yaji sauki yanzu na barshi yana sallah kafin in fiti na bata amsa naci gaba da abinda nakeyi na bata baya.
Idan zaki koma zanje in gaudashi naji ta fada nace ba tare dana juyoba ki bari idan ya fito falo ku gaisa ban yarda da zuwa part din shi ba.
Nima kinga ai saida ya kirani na tafi aka hada mai abinci nakuma hada mai ruwan wanka shine har ya samu barci.
Na dade ban koma dakin ba har wani lokaci banji motsin shi har kusan sha dayan rana kuma ban koma na lekashi ba.
Na dai yanke shawara a raina in lekashi inga halin da yake ciki yana barci sosai lokacin saidai na kula da baici komai ba tun safen .
Sai kofin dake aje a saman dan table din glass din dake dakin da kwalba a kasa a raina nace Allah yasa dai ba abin yasha ba da sasasafe haka a cikin shi watau giya.
Na juya zan bar dakin ya bude idon shi a hankali ya kira sunana na juyo inda yake kwancen ina fadin sannu yaya ya jikin ?
Naji sauki ya fada yana kokarin mikewa zaune daga kwancen nayi saurin fadin akawo ma abincin ne ?
No ki barshi yace tare da yunkurawa ya mike na bishi da idanu kasa kasa ina kallon shi a yanayin da yake tafiya a cikin rangaji.
A zuciyana nace ka sha ka bugu ina zakaci wani abincin a yanzu Allah dai ya rabaka da wanan halin ga baki daya.
Ya dan jima ya fito ya sameni a zaune can gefe ya samu daga karshen gadon ya dan kwanta ta hanyar daga kafan shi daya yana dan kadawa a hankali.
Gaskiya yaya yakamata ace ka daina wanan abin yanzu na fada kamar am matso bakina in fada mashi hakan.
Ido ya kura min sai na kasa karasa fadin abinda nayi niya kao tsaye da farko don tunanen danayi tayi ke nan dama a dakin.
Don sai nake gani kamar giyance har tayi mai over ya sakashi a wanan rashin lafiyan da yakeyi a yanzu.
Ina jin ki ya fada sai na dago kai na dan kalleshi ya tsura min ido yana kare min kallo cikin wani irin yanayi dana kasa fassarashi kona meye haka yake min.
Kafin inji yace dani me kika daukeni ne zainab kin dauka ban san me nakeyi ba har kika samu matsayin da zaki fada min magana kai tsaye haka yadda kike so.
Ni sa,an kine zainab ko shike nan don ina auren ki yanzu kike ganin kina da right din da zaki fada min maganan da duk yazo maki a baki.
Ganin yadda ya taso yana fada dani yasa na dukar daina tunda ya fara maganan sa ban dago kaina ba.
Wasa wasa saida ya kwana biyu bai fita ko kofa ba yana dakin sa a kwance ni kuma ina faman jinyar shi har yaji sauke ya fara fita .
Gashi ya rame yayi baki dan lokaci guda ya fada sosai ga wanda yasan yadda yake a baya da yanzu din.
Ranan mun fita zuwa school sai gaahi kwatsam ranan mun dawo daga school mun sami anty fadila a gidan kamar a mafalki muka ganta a falon kwance tana barci.
Ga jakkata na kaya ajiye gefe daya da farko ban ganeta ba sai muka kama mata kallon mamaki don ganin mace bakar fata irin mu a gidan kwance tana barci.
Halimatu ne da rigiman ta taje ta dan leka fuskanta a hankali ta sake wani ihun murna daya falkan da ita daga barcin tana fadin lah anty fadilace.
Anty fadila na fada a daidai lokacin da itama ta falka a cikin tsoro dama da tsoro tayi barcin don sai bata gaskanta cewa gidan da muke bane a ciki.
Munyi murnan da ihun ganin juna kafin in shige ina fadin ina zuwa na nufi part dina kai tsaye na bude na shiga da jakkan dake hannuna.
Yau kan yaya ya gama min komai tunda har ya kawo muna anty fadila wanan kasan sai nakeji kamar innan muce yakawo muna a lokacin.
Sai bayan mun gama murnan mu na ganin juna ne aka fara gaisawa da juna tare da tambayan ya bayan rabo ?
Wanan part din dasu hjy suka zauna na kaita dakin a share yake don a kullun masu aikin shara mutum biyune suna gyara ko ina na gidan tsab.
Munyi wanka da sallah kafin mu fito falo mu hadu har lokacin yaya bai dawo gidan ba duk da jikin shi bai gama warwarewa ba a lokacin don zakace yayi wani jinyane a gida.
Fadila kan sai mamaki takeyi a yan watannin da mukayi bama tare da ita wai mun kara girma mun waye haka lokaci guda a nata ganin.
Irin shirmen hjy tayi tana fadin wai ko ciki nake dashi a jikina na koma haka na cicciko nayi fresh dani farina ya karu sosai gwanin ban sha,awa dani.
Murmushi nayi kawai itama dariya tayi tana fadin gaskiya a binciki wanan sauyin naki zainab, don ni gabaki daya kin sauya min ne ai ga sanin danayi baki.
Lafiyanyyen aka shirya muna a dining don haka kai tsaye muka nufi wurin cin abincin halimatu ne ke fadin lokacin dana fara bude abincin.
Anty yau zakici abincin kasan nan kiji tunda muka barku mukai missing din abincin muna gida wallahi kila naman kawai zaki iyaci sai ferfesu.
Ta kalli halimatun tana dan murmushi tare da fadin nima nayi missing din ku sosai sadiya daga inda nake na harari halimatu tagane me nake nufi ta mike batare da cin komai a wurin tana fadi bari je inyi assigment dina ta barmu a wurin mu biyu.
Ga mamakina sai naga taci abincin sosai ba tare da nuna komai ba kamar yadda mu muke nunawa ga abincin don har yanzu ba komai muke iya ciba sosai.
Sai bayan mun gamane mun bar wurin zuwa wurin kujerun falon muka dasa hira yaushe rabo kamar munyi shekaru bama tare.
Da alama dai zainab komai yana tafiya daidai a yanzu tsakanin ki da mijin ki sabanin yadda kuka baro mu gida.
Don alamun sauyawan ki kawai ya nuna min hakan a yanzu don ance labarin zuciya a tambayi fuska naga farinciki sosai yanzu a tare dake.
Wata karfafan ajiyan zuciya na sauke tuni annurin fuskana ya dauke na dan kalleta ina murmushin dole lokaci guda.
Tace haba dai zainab kada kice min komai na nan har yanzu a yadda kuka barmu dashi don ni nayi zaton ai zaman ku wuri daya haka zai kara kawo shakuwa a tsakanin ku yanzu ?
Kai na gyada mata ina fadin kwarai akwai canji sosai yanzu ba kamar baya ba anty don yanzu akwai dan shakuwa a tsakanin mu dashi.
Sai dai wasu halaiya nasa ne na boye dana sani a yanzu suke tayar min da hankali sosai wallahi ban a cikin natsuwa ko kadan anty ga ba wani najikina da zan fadawa ya taimaka min da shawara.
Kina nufin yanzu kin gane abinda na dade ina kokarin fahintar dake game dashi ke nan zainab ?
Kai na gyada mata alaman na gane hakan sai ga halimatu tana fadin yayan mu nikin ban gane me ake nufi da wanan ba.
Na juya gareta cikin kulawa ina karban takardan dake hannuta take nabi komai da akai masu na fara yi mata bayani a tsanake yadda zata gane.
Wanan ne ya dauke min hankali na bar zancen hiran da mukeyi da anty fadila muka buge ga kararu dama aikin mu ke nan idan mun dawo ko kafin mu gama har lokacin dawowan yaya gida yayi.
Nan dai muka gaida shi da dawowa ya amsa muna yadda ya saba karbawa sai fadilace ta gaidshi a karshe yasa ya dan juyo yana fadin.
Af sorry kun iso lafiya ta amsa cikin danjin nauyin shi da lafiya kalau boss mun same ku lafiya ?
Lafiya ya bata amsa a takaice ya bar wurin zuwa part din shi kai tsaye ta sauke ajiyan zuciya tana kallona ko zan mike nabi bayan shi a lokacin sai taga sabanin hakan.
Ina zaune munci gaba da hiran mu da halimatu kafin inji tace mijinki fa yadawo daga aiki zainab kina zaune ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA



Yana zaune yana sauraren wayan da mahaifiyar su takeyi da dan uwan shi tana wani lalashin shi a cikin wayan tare da kara warning din shi kan abinda take bukata.
Daga inda yake zaune yaja wani irin tsuki yana kawar da kai gefe daya wanan yasa mami dago kai ta
Showing 228001 words to 231000 words out of 390011 words