koma gida.
Yakai kamar sati daya da dawowa sai gashi dakina da yamma ya shigo ina zaune ina waya da Amaya kawata ya shigo.
Wuri ya samu ya zauna ganin haka nima na natsu ga sauraren shi do jin abinda zai fada a lokacin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA



ALLAH YAI MUNA DAUKI YA KAWO KARSHEN WANAN TASHIN HANKALIN DAYA ADDABI AREWA DAMA SAURAN KASASHEN MUSULMI NA DUNIYA ALLAHUMA AMIN 👏🏻👏🏻👏🏻

DON ALLAH YAN UWA KUYI HAKKURI KU KAI ZUCIYA NISA KAN SHIGA HAKKIN WANI KI DAURE KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALLAMA ALLAH YASA MUFI KARFIN ZUCIYAR MU AMIN, , , , , ,

Juyuwa nayi na kalleshi a hankali yana zaune kamar mai tunane ya harde hannayen shi a guri daya kanshi na kasa sade.
Banji tausayin shi ba sam ko kadan a raina saboda yadda nakejin shi a raina illa shirun da nima nayi na dan lokaci ina sauren shi.
Gyaran murya kafin ya fara magana murya ciki ciki naji ya furta kalman sunana da zaina....b .
Ban dago kai na kalleshi ba saidai yadda na natsu yasan ina sauraren shi a lokacin maganane kawai banyi ba lokacin .
Magana nake son muyi dake a tsanake dan wanan zancen na ranan ya daure min kai a ranan saboda ban fahinci abinda zancen ki ke nufi ba.
Don naji kina kokarin kafirtani yasa na fice na bar dakin nan ko kuwa kina tsamanin don har yau ban dubeki a matsayin mace ba kike dauka wani abu nakeyi na daban.
Da farko naji tsoro da kunya don jin abinda ya fada sai dai a cikin karfin hali nace yanzu fa yaya na wuce daukan da kake min na yar kauye kuma diyan talakawa.
Wani kallo yai min don jin abinda na fada hawaye na zuba min a idanuwana shar shar naci gaba da fadin kaji tsoron Allah yaya .
Kada mutuwa ya riskeka acikin sabon Allah kai musulmine kuma musulunci ya haifeka gaba da baya yaya.
Kasan irin hukuncin da Allah ya tanadarwa wannan abin saboda wanan ubangiji ya kifar da mutanen wani zamani mai tsawo kana sane da ukuban kabari ga bawa mai sabawa fadan Allah.
Yaya bayan wanan yau idan mahaifiyar ka ko wani yaji wanan ko daga kasan ka na haihuwa aji abin ashan da kakeyi a nan yaya da wani ido zaka kallesu.
Wani dauka kake son duniya tayiwa duk ahalin ka saboda kai yau idan Allah ya baka zuria nan gaba a duniya yaya duniya zata daukesu yaya ?
Kasa cigaba da maganan nayi dan sheshekan kukan dazo min bazan iya furta komai a bakina ba ga lokacin.
Shiru yayi yana sauraren sautin kukan nawa yana dan girgiza kai a hankali tare da dan buga hannayen shi cikin juna.
Bai hanani kukana ba shima din a lokacin na zuciya yake yi don ya gama fahinta na ganeshi baro barone kawai ban fito fili na fada mai hakan ba.
Lalai mutum abin tsorone tunda har wanan abar da nake rainawa ta san yadda zata fahinci komai game dani .
Duk taka tsantsan din da nakeyi wai ace yau yarinyar nan sai data gano hakan ina ga mami idan har labarin nan yaje mata sai yaya ke nan.
Idanuwan shi ya runtse a hankali yana jin wani abu yana tokaro mashi kan zuciyarshi lokaci guda.
Cikin muryan kukan naci gaba da fadin ina rokon ka katai maka muna ka mayar damu gida wurin iyayyen mu don Allah.
Koda kuwa ta hanyan wani mumunan kazafine ko sheri zaka lakaka min ta hanyar da duniya ni zasu tsaneni na yarda da hakan yaya matukar zaka mayar damu hannun iyayyen mu din Allah.
Nayi ma alkawari har abada ba maijin wanan zancen daga bakina don ba abin alheri bane da zan fada har wani yai ma kallo dashi a duniya.
Yau nima laifin ka yaya ya shafeni don abinda ya taba mutuncin gidan ku a duniya ya taba rayuwana nima don alherin ku gareni ba abin mantawa bane.
Nasan kayi nisa a cikin wanan akidar fitan ka a yanzu sai Allah daya halicce ka yaya zan taya ka da addu,a Allah ya rabaka da wanan halin ga baki daya dakai da sauran yan uwa musulmai da suka bace suka makance a wurin sabawa Allah da munanan aiyukan da ubangijin mu yafi tsana ga bawa.
Yaya yau idan mahaifiyar ka ta samu wanan labarin da wani ido zaka iya kallonta a yadda mami take da mutunci da kima a idon mutane.
Ya isheki zainab ya fada da karfi a cikin wani irin yanayi na bacin rai yana min kallon ido da ido daga inda yake zaune nayi kasa da kaina kawai don ba zan iya jurewa kallon shi ba ko kadan.
Zaki iya fada min komai a yanzu amma kada ki yarda ki jefa sunan mami a wanan zancen wurin nan .
Zan iya sauraren don abinda zaki fada banda wanda kike fada min game da mami din yanzu wanan tsakanina ne da mahaifiyana.
Ni mutum ne mai yancin kansa kamar kowa ina da daman da zanyi wa raina duk abinda ya dace dani a rayuwana.
Ki sani ban auro ki don ki zaunar dani kina min guntun wa,azin ki ba a nan don tun kan ki sanda hakan na sani.
Kasa daurewa nayi don jin abinda ya fada na dago da sauri ina fadin yaya ka sani kake aikata abinda Allah ya la,aci maishi.
Ina zaka da wanan nauyin mai yawa a kanka ka tuba ma Allah shi mai karban tuban bawan sa idan har bawa zai tuba tubana tsakani da Allah har abada.
Nidai ina maka adduan Allah ya taroka yasa ka gane gaskiya ka daina wanan halin kafin mutuncin ka da kimar ka ya zube a idon duniya don Allah ba zai taba boyeka ba ga abinda kakeyi yanzu.
Saurarena yake yana mamaki yadda nake fitar da lafazi kamar wata tsohuwar mace a zuciyar shi.
Ki ci gaba da min adduan tunda har kin gane abinda nakeyi din mara kyau ya fada yana mikewa amma gida ba zan mayar daku gida ba kamar yadda kika bukata.
Bayan shi nabi da kallo lokacin da yake fita dakin sai dai a yanzu ba kamar yadda ya shigo yake tafiya ba.
Don yanzu a dan hasale yake takawa ya fice daga dakin rayuwan shi da hankalin shi a tashe don bai taba zaton zan gane hakan gareshi ba da sauri.
A tunanen shi wayau na da hankalina ba zai kai har in fahinci abinda yake aikatawa ba haka da wuri.
Sai gashi a bazata na fito mai a fili dana nasan da abinda yake ciki wanda bai taba kawo hakan a ranshi ba.
Mace mace ka barta komai kankantar ta ta wuce yadda mutum yake daukatan watau don wanan yarinyar yar kauye da yake gani gidahuma har ta iya zaunar da mutum kamarsa tana jero mashi zance haka.
Part din shi ya shiga ya mayar da kofan garam don ba mai kara bane kofan da kowa na gidan yaji sautin bugawan da yayi a lokacin.
Oho god ya fada yana sasauta kwalan rigan shi sai zufa ke sharto mashi ta ko ina a jikin shi lokaci guda.
Zaune yakai ya mike kafa tare da dafe goshin shi ga wayan shi na kara ana kiran shi ya kasa dauka a lokacin.
Don yadda yake jin kansa na juya masa ya dade bai sha cocaine a rayuwan shi ba badon baidashi ba sai ranan yaji shi kawai yake son sha a lokacin.
Mikewa yayi ba tare daya tsaya kula wayan shi dake ruri ba a lokacin ya nufi inda yake aje kayan aikin shi ya dauko ya dawo tare da jawo dan table din dake gaban shi.
Ya zuba a gurguje ya fara shaka yana daga kai kamar kadangare kafin ya mike zuwa kitchen din dake part din ya nufi wurin fridge ya bude ya dauko kankara da cup ya saka tare da dauko kwalban giyan shi ya dawo ya zauna.
Bai daga ba sai da yayi tatil ko dagawa bai iya yi a wurin nan ya zube babu shirmen da baiyi ba a dakin shi kadai a cikin dakin.
Kamar zai buga yake jin kanshi a lokacin ya manta da inda yake balle maganan dake damun shi har safe mai gyaran gida ya shiga ya sameshi kaca kaca a dakin shine yazo ya kirani hankali tashe.
Ranan nayi kuka kamar Allah ya aiko ni karshe dai haka na daure na kamashi da kaina na kaishi bandaki na tubeshi haka kawai dabara yazo min in watsa mai ruwa masu sanyi a jikin shi .
Ruwan na sauka a jikin shi yayi firgigit tare da ajiyan zuciya wanan katon ma kukan baizo min ba juyawa nayi na fita daga bandakin.
Dakin nasa na fara gyarawa kafin na koma falo na gyaro na na saka kamshi a ko ina saboda amai da sauran najasan daya sake.
Na koma dakin zaune na sameshi da tawul daure a kugun shi ya zauna ya hade hannayen shi wuri daya tare da dukar da kanshi kasa kamar mai tunane.
Ina ganin shi haka a zaune nayi saurin juyawa zan fice dakin sunana naji ya ambata har lokacin mayer bata gama sake shi ba nake gani.
Kizo ki dauko min kaya na saka a jikina ya fada kanshi yana duke bai dago ba dan jin nayi kafin na juya na nufi wurin kayan nasa na bude.
Rasa wanda zan dauka nayi dayake nasan kayan nasa farare ya faye sakawa na dauko wani wando fari da riga shirt fara na kawo mai.
Under fa ya fada bayan na aje mai kayan a gefen shi na juya na dauko singlet da box dake jere a wurin.
Ina ajewa na fice dakin ban tsaya ba daki na koma na haye gado dama na shirya zan tafi school ne yanzu kuma na makara da zuwa school din.
Nayi kuka har na gaji kusan awa daya ya leko part din nawa ya sameni a kwance na kifa ciki yasan ba barci nakeyi ba a lokacin.
Yau ba zaki shiga school ba ke nan ya fada yana tsaye sai kamshi ke tashi daga jikin shi kamar bashi bane dazun a cikin najasa hakanan yanzu ko yasha wanka yana kamshi.
Ido na dago da sukai min ja dan kuka ya gani yayi kamar bai gani ba wani kallo na watsa mai ya juya da sauri ya fita daga dakin.
Nan ya barni kwance na dasa sabon kuka a fili tare da dinbin nadama da dana sani yafi dubu ina blaming din kaina da iyayyena.
Nayi sati bana yarda mu hadu dashi a gidan idan na dawo ina dakina ko wurin su fadila na daina shiga ga damuwa da yai min yawa.
Da ka ganni zaka gane hakan saboda ya nayina daya nuna hakan lokaci guda Fadila tayi tambayan duniya nace babu komai karatu ne kawai yai zafi ya sakani komawa hakan.
Kyaleni tayi ba don ta yarda ba bata kara tanka wanan maganan ba ta saka min ido amma a ranta tasan akwai abinda ke damuna dana koma hakan lokaci guda.
Tsakanina dashi kan kamar sarakai muka koma don shi baison mu hadu ni kuma ban son gani shi sam don na tsaneshi har kasan zuciyana a yanzu.
Ranan na manta da wayana a dakin fadila don haka wayan a can ya kwana dakin nasu tun da asuba kafin nayi sallah asuba na bude daki na fito don in buga masu su bude saboda maya zata turo min wano sako a wayan tunda dare nake jira.
Ina budan kofa mukai kicibis da wasu samari biyu suna fitowa daga part din yaya ko shigan su ma abin tsorone dan da gani su tantiran matasan kasan ne.
Wani irin kallo suka bimu dashi sai da tsoro ya kamani don ganin su wayan da ban dauko ba ke nan na koma daki da sauri na rufe wasu hawaye suna zuba a idona.
Sai zance nake kamar mahaukaciya a daki ni kadai da sauri na mike tsaye dan karamin jakkana dake aje tun zuwan mu kasan.
Kaya nashiga hadawa lokaci guda a gurguje na fito da dan troler dina zuwa part din su fadila na buga masu kofa suka bude.
Anty ku dauko kayan ku mu bar gidan nan tun kan gari ya waye muna a nan gidan kallon mamaki fadila ke min.
Saida na kai karshen magana take fadin kanki daya kuwa zainab ina kike nufin mu nufa da wanan safiyan haka yanzu.
Duk inda muka samu na bata amsa ina fadin ba zan zauna gidan wanan mai sabon Allah ba kuma.
Kiyi tunane zainab nan fa ba kasan mu bane muna a garin mutanene yanzu ina kike son mu tafi yanzu idan mun bar gidan nan.
Hannun halimatu na jawo tare da daukan akwatina ina faman ja muka fice a gidan tana tsaye tana kallon mu da mamaki a fuskanta.
Ganin da gaske mukeyi yasa ta nufi part din yaya jafar dake kwance shame shame saman gadon shi ko sallah safe baiyi ba ta shiga dana mashi door bell babu kakautawa lokaci guda.
Tsuki yaja yana mamakin waye wanan da safe haka yake damun sa dan nawan da yayi kafin ya bude kofar yasa har muka samu taxi muka shiga muka bar unguwan.
Yana budewa tana tsaye a cikin damuwa tace sir kazo ga madam can da sister ta zasu bar gidab nan sun dauki bag din kayan su sun fita.
What ya fada tare da kallon jikin shi daga shi sai bathrobe din dake jikin shi daya dauko yasa da zai fito kofan.
A hakan ya fito abinda bai taba yi ba tun kan ya fito yake fada da fadila don me bata fada mai ba da wuri ta bari muka fita daga gidan.
Babu kowa wajen gashi ba ranan aiki bane sai yan tsiraru mutane dake zirga zirga a unguwan.
Kai ya dafe da hannu daya tare da fadin shit yarinyar nan tana son caza min kai a garin nan how come zata bar gidan nan ya fada a fili.
Sai kuma ya juya wurin fadila ya hauta da fada don me zata bari har mu fita bata sanar mashi ba yanzu gashi mun doshi wani wajen da ba,a sani ba.
Nan ya barta ya juya cikin gidan a gurguje ya dauki key din mota da kanshi yai driving ya rasa inda zai tafi sai tafiya yake a unguwa yana dube dube ko zai ganmu.
Muko mai taxi ya tambaye mu wani wurin shakatawa da muke yawan zuwa nace ya kaimu lokacin ya ajemu na biyashi kudin shi.
Sai lokacin na fara wiki wiki da idanu na rasa abinda zanyi a lokacin abu na farko shine na fara tambayan ko halimatu zata ci wani abu don nasanta bata wasa da ciki ta ko kadan ita.
Wurin masu hada irin abincin su a bakin titi din nan naje aka hada mata taliya da tarkacen su don ita tana iya cin abinci su yanzu.
Wuri muka samu muka zauna taci saida ta koshi niko ina ta faman tunane a raina na inda zamu sai dabaran zuwa hotel ya fado min a raina.
Tana gamawa muka bar wurin don kallon da ake muna yayi yawa a lokacin munyi sa,a mun samu hotel mai dan saukin kudi muka kama bayan na nuna masu ID card dina na karatu.
Dakine mai dan gado da tv a ciki sai ban daki da sauran tarkace a cikin dakin wanka halimatu tayi ni kuma ina zaune ina faman tunane a raina.
Yaya ina zamu daga nan halimatu data gama shiri take tambayana nace gamu dai tukunna halimatu gida nake son mu tafi daga nan idan mun samu hanya.
Abin kurciya sai ta hau murnan jin wai gida zamu tafi tausayin kan mu ya kamani a hakan barci mai nauyi nayi sosai a lokacin daga ni har halimatu data kwanta a gefena tana danna laptop itama tayi barci.
Da wani irin matsakacin yunwa na falka ina neman abinda zanci a cikina lokacin fita nayi na nemo muna abincin na dawo dakin dashi .
Na samu halimatu falka a dakin tana wuri wuri da idanu sai gani na shigo ta sauke ajiyan zuciya tare da tambayan inda naje ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA



MASHA ALLAH ANOTHER FRIDAY AGAIN MAY ALMIGHTY ALLAH ACCEPT OUR IBADA FOR THIS FRIDAY ALLAHUMA AMIN, , , ,

YAR UWA TUNI GAREKI KI BIYA KI KARANTA WANAN LABARIN KARUWAN DA ZAKI SAMU A CIKI YAFI ABINDA ZAKI BADA YAWA UBANGIJI ALLAH YA TSARE MUNA ZURI,AN MU AMIN, , ,


Kwanan mu biyu a dan karamin hotel din ga wayana na kashe tun fitowan mu gidan wayan yake kashe ban kunna ba.
Haka yasa duk kokarin yaya wurin gano inda muke baiyi nasaran gane komai ba hankalin shi ya daga ga baki daya har yakai rahoton batan mu
Showing 240001 words to 243000 words out of 390011 words