mu.
Da tsoro na dawo cikin dakin ban kwanta ba abandaki na shiga nayi alwala nazo na tayar da sallah na dade a zaune ina addu,a da rokon Allah kan ya tsaremu ya karemu daga halaka.
Zancena da taju ne yake dawo min sabo saka sunan iyayyena da yayi yafi komai tsaya min a zuciyana.
A karshe wani dabara ya fado min a raina a hakan har aka kira sallan asuba na mike na gabatar sai lokacin na koma barci.
Da yake na sa abu a zuciyana sai banyi wani barcin sosai ba don kada yaya ya shigo ban sani ba.
Dakin ya shigo kuwa bayan mun gaisa dashine yanawa sadiya sherin wai ta fara zama yar lukuti tana dariya.
Yaya yau ina son shiga ruwan can don haka idan ka fita kada ka dade ka dawo mu shiga na fada kai tsaye ba tare da shakkan komai ba.
Bashi ba har sadiya tayi mamakin jin wanan maganan daya fito a bakina lokacin yace a cikin mamaki dama kin taba shiga ruwane ke nan ?
Ban taba ba yau dai nake son in fara na bashi amsa da hakan ya gyara tsayuwa yana fadin idan aiki ya barni zan dawo din Allah dawo dakai lafiya .
Yana fita na bishi da kallo tare da mamakin kaina nayin wanan karfin halin haka da nake son gwadawa a yanzu.
Tun lokacin na fara shiri na na fita har zuwa bakin shagunan dake layin hotel din na sayo wasu irin kaya masu matukar kyau ga tsada.
Kwalliya mai daukan hankali na tsarawa kaina don ban taba sanin na iya ba haka tun dan koyon da nayi zamanin zama da yan matan mami a gidan ta ina jin zancen su a wurin yin kwaliyan su zakaji suna gardama wanan yayi yawa wanan bai ji ba.
Kodana dauko rigan zan saka saida na runtse idanuwana kafin na bude na daure na saka kayan hakanan sai gani na koma kamar wace zata wurin fashion.
Ni kaina saida na gigiza dan ganina haka ba komai bane yasani hakan sai daukan irin shawarwarun fadila da yau nayi a zuciyana.
Don ina son in gwada in gwada sa,ata da hikimana na diya mace da fadila ke yawan fada min ko yaushe da takace.
Mu mata makamine gun da namiji komai taurin da namiji da cijewa ko gagara a duniya sai mace ta juya shi a wata tsigar nata wata rana.
Ta hanyar yaudarar ta ko kisa ko kuma kisisina da kutungwila irin na mata da maza basu taba gano hakan sai mace yar uwarta zata gane mai take shiryawa.
Wanan baiwa ne irin na mata da Allah ya halicci diya mace wanda su matan bayan addu,a wanan ne makami na biyu da suke amfani dashi a wajen mazanjen auren su ko hurda.
Ranan turare yasha kashi don duk wanda na gani har wanda ke cikin jakkana nayi amfani dashi a irin hakane na dauko wanda idan baki matan ba fadilace ta banshi da dadewa lokacin da zamu zo chaina tace ta karbo min nayi amfani dashi.
Uku da rabi na fara wanan shirin kafin karfe hudu don saida nayi sallah la,asar na zauna yin kwalliyan nawa na kammala komai daidai lokacin daya dace in kammala din.
A nasa bangaren kuwa yana tune da hakan yasa ya baro abin da yakeyi zuwa masaukin namu don shi ba mutum bane mai saba alkawari duk halin turawa shine akidar shi.
Don da hakan bai samuwa da bai mun alkawari ba tun farko dakin shi ya fara yadda zango yayi wanka ya shirya already yayi booking din wani haddaden jirgin hotel din da zamu shiga ruwan dashi.
Dakin ya turo wanda kamshi ne ta ko ina ya fara taron hancin shi ya fara raba ido a kan mu Allah ya taimake mu ina zaune saman gado ina zaman jiran tsamani ya shigo.
Duk da kusan wata biyun da suke shige idan ya kalleni gaban shi sai ya fadi ko yaji wani bakon yanayi a kaina yana ziyartan shi .
Wanda hakan yakan daukeshi don kawai yasaba da mune kwarai a yanzu yasa tausayine ko wani abu yakan ziyarci zuciyar a kaina don yasan badai feeling bane wanda maza kanji akan wata mace.
Shiya dauka hakan sabone kawai da tausayina da yake ji ayanzu ne don yasan bayai min daidai yasa yana jin wanan akaina idan ya kalleni wani lokacin.
Don saboda wani lokacin yakan zauna yana yin tunane mai zurfi kan matsalan namu tunda mami ta sakashi gaba yanzu don da kyat take daukan wayan shi koshi sai ya bi ta hanyar ya mamud yake samu su gaisa saboda Allah ya aza mai son mahaifiyarsu a ranshi.
Don hakane yakan zauna yana neman way out kan matsalan nasa da yake da wuya ya bari shima ya sani saboda yasha gwada barin ya kasa yin hakan.
Sai yanzune yasan ya fada tarko mai wuyan fita a cikin rayuwan shi wanda zaice kurciyane da zugin abokai sukai tasiri a ranshi a lokacin don kawai duniya ya fada halaka.
Gashi arziki da suna duk sun samu a duniya saidai shi gareshi a yanzu wanan duk banzane a wurin shi tunda har mahaifiyar shi da uwar cikin shi suna kyamarshi saboda halin shi.
Da wanan ya shigo dakin namu sai dai yau din muna hada ido dashi daga inda nake zaune nayi wani irin zama kamar wata Queen of manshion saman gadon.
Wanda nima dai haka kawai yanayin zaman yazo min bawai nayine da ganganba don kawai kada kayan jikina ya baci ne na zauna hakana.
Ras ras yaji a gaban shi wani abinda bai taba ji ko hangowa a gareni bane ya hango tare dani yau din daya shigo ya tsinkayeni hakan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA




LITTAFIN NAN NA KUDINE YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA A CIKIN SALAMA NA FITA HAKKIN KI NA FADA MAKI YAR UWA ALLAH YASA MU DACE DA RAHAMOMIN SA AMIN, , , ,


Ina zaune saman gado nayi zaman balance irin na goggagun mata yan duniya na wani harde kafa rabin cinyana duk a waje yake.
Na bude baki a hankali cikin wani yauki da yatsune ina fadin sannu da dawo tare da kawar da kai kamar shigowan shi ba dameni ba yadda na nuna.
Amsawa yayi da mamaki karara a fuskanshi yana kare min kallon irin shigan da nayi a lokacin don fitan da zamuyi din dashi.
Yayan mu na shirya muryan sadiya ya daki kunnuwan mu lokaci daya tana fitowa wani dan lungu dake dakin don dakin babbane an masa part part kamar kana cikin babban gida mai dakuna da yawa.
Mayar da hankalin shi yayi gareta har ta kara fitowa yake fadin Wa, Wooo wai wanan sadiyace kanwata dai dana sani ko idona ne ke mun gizo haka ?
Dan murmushin jin dadi ta sake a fuskanta ya mika mata hannu tazo gareshi yace kanwata kinyi kyau sosai wallahi .
Tace har na kai yayan mu yin kyau kuwa ya J har kin fita ya furta tare da jawota yana mata rada a kunnen ta kafin ta juyo ta kalleni a inda nake zaune bakin gado.
Idan kun gama gulman sai mu tafi na fada ina mikewa tsaye na dauko handbag dina dake gefen inda na zauna.
Ina gyara gyalen dana yafa saman hullar daya rufe min kaina da kyau ido ya kara bina dashi na turu baki ina fadin wanan kallon ai sai mutum ya kware haka.
Ina mamakin wanan kwalliyan ne haka don ban taba ganin kiyi irin sa ba duk da ruwa zamu shiga amma kika chaba ado haka dake ?
Nayi ne don daga ni sai kai sai Sadiya zamuyi tafiyan da ace wurin mutane da yawa zamu shiga bazanyi shi ba.
Hanya ya nuna min da hannu na kalli sadiya ina fadin shige mu tafi ta fara hanya na mara mata baya ya rufo dakin da makulli bayan mun fita.
Dan tafiya ne ya sadamu da wurin ina bin ko ina da kallo sai gamu bakin ruwa nidai har cikin raina dama ina son shiga ruwa koda bai kai haka yawa ba a rayuwa .
Sai gashi yau zan shiga ruwa irun wanan jiragene a wurin jere da juna muka tun kari wurin nomban da aka bashi.
Bamu sha wahala ba don jirgin yana da matakala kamar a tudu muke a wurin shiga cikin jirgin kuma a kwai komai kamar yadda muke ganin sun shiga a cikin film.
Bayan shigan mune kamar ance in daga ido sama ina dagawa na hango taju a tsaye saman bene yana kallon mu.
Dan murmushi na sake tare da daga mashi hannu alaman bye kafin na karasa shiga cikin jirgin ga baki daya a lokacin har jirgin ya soma tafiya damu ko.
A gaskiya masu kudi suna jin dadin su sosai a duniyan nan don idan ka dace da rahaman ubangiji gaskiya ka huta .
Allah yasa mu cika da imani na fada a raina kafin na kai zaune ina mayar da idona rufe ba komai ya sani haka sai tunawan da nayi da irin rayuwan da yaya yake ciki.
Ya haka kuma keda kikace jirgi kike son shiga kika rufe idanun ki yanzu kuma ?
Jin hakan da nayi yasani bude idanun nawa na sauke a kanshi yana zaune ya bude system ko har ya fara aiki a cikin sa yake wanan maganan.
Duniya nake tunane yaya na bashi amsa don nasha alwashin sakewa dashi yanzu a kan taju duk yadda zanyi sai naga na raba wanan alakan nasu koda kuwa yin hakan bazai sa yaya ya daina ba sai dai ya canza wani katon bashi ba.
Tunanen me kikeyi na duniya nace a daidai lokacin da nayi wani irin zama na yan barikin mata ina dora kafana daya saman daya.
Wanda yin hakan har ya baiyanar da rabin cinyana a waje wanda dama rigan nada tsaga har kasa idan mutum yayi irin hakan zai baiyana sosai a gani.
Duniya aljanan kafiri lahira kuma ta mai rabo duk wanan jin dadin naga iyakar shi duniya za a barshi ba a zuwa lahira dashi nagani.
Yaji maganan sosai har cikin ranshi sai dai bai kara magana ba yaci gaba da abinda yakeyi a cikin computer din shi ya kyaleni.
Tsawon wani lokaci wurin yana shiru jirgin sai tafiya yake damu a cikin ruwa hannu na mika na dauki dayan cup din dake saman table din dake tsakiyan mu ina tsiyayya ruwan enabi na fara kurbawa a hankali.
Yana sane da sabon halin dana tsiro dashi don yasan ba haka nake ba da rashin kunya sai dai yana bina yaga iya guduna kawai.
Daga inda nake zaune na kara daukan kofi na tsiyaya drinks din na mike a hankali zuwa gefen da yake zaune na zauna gab dashi ina mika mai abin sha.
Dan juyowa yayi ta miko min bakin shi da zuman wai in bashi don shi wanan ba komai bane a gareshi.
Don ko Aisha da take kanwarsa watarana ina gani itace ke basa a baki yana sha tun ina zagin su har na saba da ganin hakan na daina.
Tunawa da hakan da nayi banyi sanyi a gwiwa ba na mika masa ya kurba a hakan har ya shaye cup din.
Na aje na dan jiginu da jikin shi tare da daukan jaridan dake saman table din wanda aka aje don mu na fara karantawa.
Matane sexy girls gasu nan iri iri ko wace da irin nata shigan ciki computer ya rufe tare da fadin ki tashi mu leka waje kuga ruwa.
Don ita sadiya tana nata aikin kallo a cikin wayan ya dauke mata hankalin ta garemu tana jin hakan tayi saurin dago kanta tana son jin amsan da zan bashi.
Batare da yin magana ba na mike zaune shima mikewa yayi muka fita sosai muke jin dadin wanan fitan namu don sai da gari yai duhu muka dawo masaukin mu a cikin an,nashuwa.
Tun fitan shi dakin ko washe gari bamu kara jin duriyan shi ba saida yamma ya shigo muna ruwan saman da akeyi a garin ya dan dukeshi.
Don ni a lokacin har zuciyana ya fara wasi wasin din ko dai taju shima ya nuna fushin shi kan fitan mune yasa bai shigo dakin namu ba yau ya fita .
Tunda taju din da ire iren su sune kishiyoyina a yanzu wurin shi yasa na fara wanan tunanen haka sai gashi ya shigo dakin da yamma.
Gaidashi din dai mukayi yake tambayan sadiya ko zamu koma ruwa ne yau din ma Sadiya mu kwana a cikin ruwan.
Da sauri tace a,a yaya j bazan koma ba jiya ma banyi barci da dadi ba wallahi don da zaran na rufe idona ruwan nake gani saina bude.
Matsoraciya yace yana juyawa ya fita dakin yakan shigo da dare kafin mu kwanta sai gashi bai shigo dakin ba ranan.
Hakama washe gari bai lekomu ba sai wajajen karfe biyu aji wayan dakin na ringing na dauka.
Muryan shine a cikin wani irin yanayi yake fadin zainab sun kawo maku breakfast ki hado min ruwan zafi ?
Nace eh yace ok black tea kawai zaki hada min ki kawo min yau ban fita ba bana jin dadin jikina ne kadan.
Subbahanallahi nace hope dai da sauki yace ciwon kaine kawai ke damuna har nakai wurin kayan breakfast din sai wani tunane yazo min a rai.
Da sauri na koma na dauko wanan maganin ba tare da nabari sadiya ta kula da abinda nakeyi ba na nufi wurin da zan hada mai tea din da jakkata.
Na hada kamar yadda maya tayi min bayani na dauka na kai mai dakin da shine farkon shigana tun zuwan mu Dubai din duk da bamu da nisa dashi.
Yana kwance saman mamakeken gadon dakin jikin shi saye da dogon wando ash colour sai farar singlet daya saka a saman jiki ya kife cikin saman gadon yana kwance na shigo dakin.
A hankali na taka zuwa bakin gadon saida na kai zaune nake fadin ga ruwan tea din nan yaya na gado maka gaba sai faman faduwa yakeyi kamar nayi laifi za a kamani.
Dan dagowa yayi sai ya koma kwance yana tsuki kafin kuma ya dago da karfi ya tashi gaba daya yana fadin a daidai lokacin da nake mashi sannu, da jiki yace.
Ina ganin ruwan daya dan dukeni ne jiya yaja min ciwon kai dama jikina bai shiri da dukan ruwa ko kadan.
Kasha magani yace nasha don dashi nazo ban faye yarda da magani su nan ba shiyasa nake tafiya dashi duk inda zani.
Ya shiga ban daki ina ganin baki ta wanko ya fito har lokacin ina zaune a wurin dana zauna din ya dauki ruwan shayin yana kurbawa daga tsaye.
Dan kai na dago na saci kallon shi na dukar da kai shiru muke bayan ya gama kurban ruwan tea din ya aje cup .
Ganin hakan na mike na dauki cup din na fita dashi da zan fita nace Allah ya sauwa yake fadin ai barci zanyi na dan lokaci ko zan tashi inji saukin shi.
Nakoma daki da fargaba a ciki zuciya do dai kam na kada na bashi ya kuma sha saura in jiran hukuncin ubangijin mu yanzu kam a kan wanan lamarin.
A cikin wanan tunanen ne har barci ya daukeni ban sani ba barci sosai na samu nayi a lokacin a can cikin barci nake jin wayan dakin yana ringing alaman kira yana shigo min lokacin .
Da kyar na iya bude idanuwana da sukai nauyi saboda barcin na mike da kyat din kuma na jawo kan wayan dake gefen gadon.
Muryan yayane baya fita da ji yana cikin tsananin ciwo a lokacin yana fadin zainab kizo kada in mutu .
Gabana ya bada ras ras lokaci guda da sauri na sauko saman gadon ban tsaya jiran komai ba na nufi hanyar fita waje zuwa dakin nasa.
Ina shiga yana wani irin nishi da kakari kamar zai mutu ya dafe cikin shi da hannun shi daya yana mulmula a kasa.
Da sauri na karasa inda yake kwance saman ties din yana wanan gurjin kamar karimin yaro.
Gaba sai faduwa yakeyi don tsoro don ni su maya basu fada min zaiyi wanan wahalan ba haka.
Tsugunne nakai saman kamshi ina dan kiran sunan shi da yaya yaya me ya sameka haka ina fadi a rude tare da kai hannuna saman jiki shi ina taba shi.
Bai iya dago kai ba ba kuma magana sai kokarin nuna min cikin shi da yakeyi da hannun shi na kara rudewa sosai.
Magana yake son yi ya kasa haka yasa na mike a rude ina kuka zan fita daga dakin naji ya rike min hannu na a cikin nasa.
Na dawo inda yake din yana son kara yin magana yai wani irin yunkuri sai ga amai yazo mai lokaci guda wani irin bakin amai da ban taba ganin irin saba a duniya.
Showing 279001 words to 282000 words out of 390011 words