Wani lokacin ma idan bamu ce ba zai sayo din tundawa halimatu da take mai oyoyo idan ya dawo tkan zauna ta mai surutu sai ya gaji ya barta.
Shikan gaskiya bamu da matsala dashi ko kadan don a kannensa yake daukan mu wani lokacin ma har ya tsawata wa halimatu idan tana wani abin.
Hankalina ya dauku sosai ga game don haka banji shigowan shi dakin ba sai dai kamshine ya sanar dani hakan yasa na dago kai da sauri na sauke a kanshi.
A lokacin yana tsaye daidai kaina ya sanya fararen kaya a jikin shi farin wando da wani riga mai kama da t shirt din maza saidai yadin shi mai laushi sosai saidai hannun rigan bai sauka har kasa ba.
Saida na dan firgita dan ganin shi girshi hakan a gabana cikin rawan baki nake fadin yaya sannu da zuwa ya hanya ?
Idon shi akan wayan dake hannu da nake game ya amsa min tare da fadin ina sadiya banganta part din su hjy ba dana shigo.
Ban san inda ta shiga ba na basa amsa yasa yai min wani kallo kafin yace kila suna tare da mamane don itama ban ganta a dakin ba.
Kokarin sauka daga kan gadon nayi ina ganin ya juya zai fita don hankalina ya tashi da cewa da yayi halimatu bata gidan.
A daidai lokacin da muka sauko falon ne kuma naga ana shigowa da kayan da ya dawo tafiyan dasu yana tsaye yana magana da Samuel akan kayan.
Dan ganin Samuel di na kallon direction din daya fito yasa shi dan juyowa yana kallon wurin nice nake kokarin gyara daurin gyalen dana rufe kaina dashi lokacin.
Na karaso ina jin yana fadin ku kai wanan part din ta wanan kuma ya nuna part din hjy da nufin su kai can sauran yace su shiga mai dashi wurin shi su adana.
A kawo abinci ko fita zakayi na fada cikin karfin hali da daurewa yace ba yanzu ba sai da dare zanci daga haka ya juya zuwa part din shi ni kuma na shiga wurin hjy don jin abinda ya fito dani.
Na samu hjy tana kallon kayan da suka aje a gabanta tana mamaki nayi sallama take fadin ni wanan menene kuma a ciki suka shigo muna dashi haka ?
Ya jafar yace su shigo dashi nan na bata amsa ina zama zan tambayi su mama sai gasu sun shigo mama na fadin ashe jafar ya dawo yanzun muka ganshi a waje zamu shigo .
Ya dawo yana tambayan ku nake fada mashi kun fita mike kafa da jamal yake fadin ku rage fita a garin nan sosai.
Da gajiyane man kullun mutum yana guri daya a zaune mama Ramatu ta fada tana kaiwa zaune fuskanta a abinda ta gani daure.
Wanan kuma fa hjy ta tambaya tana kallon mahaifiyar tasu hjy tace miskilin danku yace a shigo dashi bai min bayanin ko meye a cikin sa don baima shigo ba tunda ya fita dazun.
Fita halimatu tayi sai gata ta dawo dauke da cup cike da milk a cikin sa sai snack a dayan hannun nata.
Allah yagani ina jin kunyar wanan rawan kan na halimatu a gaban su duk dako nayi mata fadan haka a dakina don ban manta da gorin da mama tayi muna ba a farkon zuwan mu gidan kan abinci.
Yanzu ko tana nuna muna ba komai saidai ni ban yarda da hakan ba tunda har hjy ma data haifeta tace min nayi hankali da mama din ke nan ba sona da gaske takeyi ba.
Shiyasa a kullun nake cikin jawa halimatu kune da ita din kada taje tana sake maganan gidan mu a gunta watarana a samun abin mana gori dashi.
Nikan mikewa nayi da niyar ficewa daga dakin sai naji mama na fadin ai jafar din naga ya fita ina kuma zaki ana zaune ana hira.
Ikon Allah ke haka kikeyi a gidanki idan mijin ki yana gida wanan saka idon har ina kuma Ramatu ?
Haba dai hjy don na fada mata ya fita ai laifine kuma hakan yanzu gani nayi dai ko ta fita baya gidan ai .
Ki barta ta tafi nace maki bana son wanan saka idon tsiya akan yaran nan bansan dalilin ku nayin hakan ba ko kukan mata kuma kuna da diya mata ne a gaban ku.
Yanzu kuma hjy meya kawo wanan maganan daga fadin baya nan ta zauna shine na wanan maganan haka ?
Ramatu ina dai horon ki da wanan dabian ko ita wace kike tayawa din wata rana zatai nadaman hakan mujuri zuwa rafi dai akace inji hausawa.
Tashi kije mama ta fada a dan hasale tana kallona nace dama daki zan koma in dauke kayan dana bari a gurin.
Jeki kawai ban tanbaye ki ba kada kuma kija min wani laifin gun hjy yanzu nikan jikina yayi sanyi haka na fita na bar masu dakin.
Ashe hjy taji wayan mama Ramatune da mami da take fada mata ya jafar baya garin yai tafiya sai mami kecewa da ita.
Ta kara saka ido a kaina ta kula da kyau kada ta bari in samu wani sakewa ko kadan dashi don ta tsani ta bude ido taji muna tare da danta wallahi.
Ta kare da fadin sai yanzu nake yarda Ramatu da ake fadin asiri sukai min ita da iyayyenta tun kan tazo ki duba fa.
Yadda na dauki yarinyar nan kamar ba yar aiki ba a gidana tankar wata jinina na jiki na mayar da yarinyar nan wai lokaci guda jafar yazo ya birkice min a kanta.
Yau itace a kasan chaina zaune abinda ke kara ban haushi da takaici muga namu yayan zaune a gida Ramatu yau wa yaki nasa yasamu miji kamar jafar wai ?
Mama Ramatu tace shine abin da nake fada maki ai anty lokacin nace irin yaran nan ba abin yarda bane wallahi kinki ki gane hakan a lokacin.
Sam ban yarda ai tayi wani abin sakewa ko kadan tana nan yadda kika santa har yanzu saima dawowan hjy gidane ai ta dan sake jikin ta.
Sun dauki lokaci suna magana a kaina itako hjy tayi kamar tana barci ne a lokacin basu sani ba don ta dade da kwantawa a lokacin yasa mama ta dauka barci takeyi har lokacin.
Jin hakan shine dalilin da hjy take samata burki ga duk abinda tayi ta gane da manufa take min shi sai ta taka mata burki a take.
Kayane na ban mamaki na shiga tsara saidai duk kyausu nikan basu min ba don sai na dauka shigan yan iska yake son mu dinga yi kawai a kasan nan yanzu duk da dogayen rigunane basuyi kama da wanda na saba amfani dasu ba masu gyale da nake yafa gyalen a kaina wani lokaci.
Haka na halimatu dana gani a ciki suma dai din masu tsadane sosai daganin su na tattara na saka muna a wardrobe hakama takalma da jakkunan na aje a gurin ajesu.
Sai da dare na shiga part din bada niyar kwana ba kamar yadda na saba shiga yana zaune na sameshi da waya a hannun shi sai cup din daya rike yana shan abu a cikin wanda bansan ko meye ba yake sha a lokacin.
Har na karaso inda yake zaune yana kallona a cikin tsarguwa da daure fuskan shi gareni nima duban kofin nayi na kawar da kaina tare da kaiwa kasa na rusun na ina fadin munga kaya mun gode Allah ya karawa dukiya albarka.
Ya gyada min kai yana zaune yadda yake saidai wanan karon ya mayar da kanshi a makarin kujeran yana mai lumshe idon shi a hankali.
Ina fadin haka na mike ba tare da wani jinkiri ba na juya na fito daga part din zuciyana cike da zargin abinda naga yana sha din a lokacin .
Ya Allah ka kawo wa wanan bawan naka dauki ka rabashi da wanan hali da duk wani abin hani daka hani al,umman Annabi ka dashi ya Allah.
Na fada idona yana mai cikowa da hawaye haka na kwanta na dunkule a wuri daya zuciyana yana min tunane kala kala lokaci guda.
Yanzu koda ace muna kwana a tare ne nayi fushi dashi haka yaya zai barni cikin rashin kulawa ko damuwa da hakan?
Ashe da gaske ne da yake yawan fadin shi mace bata gaban shi asalima saidai yai mata kallon yar uwa ko abokiya kawai a idon shi.
Idan ko har hakane akwai aiki ja a gabana don ba zan zauna a rayuwa haka da miji kamar kurman maza ba.
Shin wai shi wani irin mutum ne haka koko shan giyar dayakeyi ne ya mayar dashi hakan ba,a sani ba ko kuma wanan dalilin ya zabeni a matsayin matar shi don ya cutawa rayuwana haka dai nayi ta faman tunane barkatai har barci yai gaba dani.
Bayan kwana biyu da faruwan hakan nake jin zancen tafiyan su hjy wanda hakan ya tayar min da hankalina sosai.
A cikin hakan ne ranan sai gashi ya shigo muna da takardun karatun mu wanan abin ya ban mamaki matuka.
Duk ina karama haka bai hanani fahintar hikiman shi na kyautata min a gaban su don kawai su dauka kwai fahinta a tsakanina dashi.
Idan ka gani zakacd duk dadin duniya ya kare a guna yadda yakan sayo min abu mai tsada ko ban kulawa a gaban su.
Nikan da abin yakanzo min bambarakwai bana iya boye mamakina a fili ko rashin sabo da haka daga gareshi.
Na samu hjy a daki ita kadai muna hira nake fadin hjy tafiya zakuyi ke nan idan kun tafi nasan rayuwana yana cikin garari a gidan nan.
Hjy ta dago kai tana fadin akan wani dalili har zaki shiga garari yar nan sai lokacin na farga da kato baran da naso yi a gaban ta ashe.
Da sauri nace hjy idan ba wani da zan dan dinga hira dashi haka ai sai damuwa ya kamani ko tunda shi yaya ba zama yakeyi a gida.
Tare da fadin kuma din yace karatu zaku soma ai bada dadewa ba saidai tunanen gaskiyane don nima ban amince na barku haka daga ku sai wa yan nan yan arnakun ba a gidan nan gunda shi din dai bai zama.
Zan kara mai magana kan wace zata zo ta zauna daku nan don kwanaki nayi mai bai ban amsa ba kan hakan.
Barshi dani nasan yadda zan fito masa a yanzu dole ya yarda da hakan ai tunda dai ba zama zaiyi ba daku a gidan.
Ana gobe zasu tafi dagani har halimatu mun kasa tsayar da hawayen mu kuka sosai mukayi ranan saida muka ba kowa tausayi.
Shi da kanshi yaya ya rarashi halimatu don tace ita bin su hjy zatayi ta koma Nigeria da zama daya tambaye ta dalilin ta tace nan din yaya ba a fita kuma bama jin yaren su ai suma basa jin namu kuma.
Da kyat ya samu ya rarashe ta hanyar cewa muma bada dadewa ba zamu je Nageria yanzun ta bari su hjy su fara tafiya don kada tayi fadan zuwa damu.
A airport ma ban iya tsayar da hawayena ba sai faman kuka nakeyi hjy ma hawayene yazo mata tana sharewa da gefen gyalen dake jikin ta.
Ta dan dafani tana fadin zainabu wanan shine aure dakike ji ana fada a rabaka da iyayyen ka da kowa naka zuwa inda baka taba rayuwa a ciki ba sai halin da kaje dashi.
Shiyasa kike jin ana fadin aure yakin mata don idan ba mace ba babu namijin da zai iya barin gidan su har abada sai kadan da suke shigewa duniya.
Gidan ya koma muna ba dadin zama mu biyu kawai ke rayuwa a cikin sa haka zamu suni zungun a gidan idan dare yayi kuma kafin ya dawo ma mun shiga kwana koda kuwa ba barci zamuyi ba a lokacin sai mu zauna muyi ta hira ko labarai a tsakanin mu muna dariya.
Har ranan da zamu fara fita zuwa school din yayi a zatona shine zai kaini school din sai gashi driver yasa ya sauke mun don an gama biyan komai a lokacin.
Sai gamu a bakon wuri muna faman robon ido don ganin bakar fata a wanan wajen sai can ba a rasa ba zaka gansu jefi jefi kuma ba yanayin musulunci a tare dasu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA



Karatu kab zance ba dadi gaskiya da farko har ina shawaran fasawa a raina don kalubalin launin fata na farko da nake gani.
Sai nabiyu yanayin shigana da ya zama masu abin kallo a can don na kasa amfani da kayan da yaya ya sayo min ko guda har wanan lokacin.
Sai na uku shine karatun gaskiya ba fahintar shi nakeyi ba gashi dai turanci ne amma sai yake min kama da yare sukeyi idan suna bayanin su.
Wanan dalilan yasa na saka damuwa a raina sosai har nake shawaran na daina fita kawai idan yayi magana nace dashi fasa kawai.
Wanan shawaran na yanke a raina bazan kara zuwa daukan lectures ba shike nan nasan ma ba zai tambaya tunda baida lokacin mu sam.
Itama dai halimatu kusan wanan matsalan take fuskanta sosai a karatun ta tana yawan min korafi kan challenges din da ake mata a school din da take zuwa din.
Ranan da nake wanan tunanen a ranan ne ya shigo muna dakin mu har mun kwanta ya buga min kofa misalin karfe takwas na dare kenan a kasan.
Da mamaki a fuskana nake kallon kofan kafin inyi karfin hali na mike daga inda nake zaune a kasa ina bitan karatuna don banson a tambaye ban sani ba yasa nake kwakwafewa da bita duk dare.
Kofan na bude a hankali yana tsaye har lokacin sai dai yanayin shi ya nuna ya gaji da tsayi a wurin don bugun kofan.
Zan iya cewa kwana kusan uku ke nan bamu hadu dashi ba a gidan do lokacin da muke fita bai fito daga part dinshi ba da safe.
Ko idan mun dawo har dare bai shigo ba don haka bama haduwa kuma bana gane meke faruwa a kidan da dare.
Ina wuni nace a sanyayye daga can cikin daki kuma halimatu ne ke gaidashi ya barni a tsaye wurin ba tare da amsa min gaisuwa na ba yana kokarin shiga dakin.
Da sauri na jaye jikina na bashi hanya ya karasa shiga daga ciki yana fadin sadiya karatu ya boyeki yanzu ba a ganin ki ko ?
Dan dariya tayi ta kara gaida shi na juyo zuwa cikin dakin daga inda ya barni a tsaye yana tambayan halimatu din I hope karatun dai sauki ko ?
Tace ba, ba dadi yaya don bana fahintar me suke fada sosai dan dariya naji ya kwashe dashi kafin yakai tsugune yana fadin.
Sadiya in kin daure zaki fahincesu ai kin taba ganin wanda ya samu a cikin sauki kowa kikaga ya zama wani abu a duniya jajircewan shi ne takaishi ga hakan.
Ki daure ki fahinci me ake koyar dake zaki gane watarana har kizo ki fisu ga baki daya ajin ko baki son inna da Abba suyi alfahiri dake wata rana .
Kai maddala da haihuwan da sukai maki yan uwa su huta ta gareki bakiga mamina yanzu itace abin kwatance a dakin su.
Kai halimatun ta daga mai kamar tasan komai yace good wata rana kema sai kin fita a rayuwa amma fa hakan bai samuwa sai kin daure kin natsu zaki gane hakan.
Ilimin mace ko da bata aiki bai taba tafiya a banza don zata waye tasan mai duniya ke ciki har ta taimakawa yayan ta itama .
Halimatu ne ta katse shi da fadin ai yanzu yaya na fara ganewa kuma sun daina tsokana na da sukeyi da tunda na fasawa wata baki a cikin su ranan.
Yace subbahanallahi sadiya ki daina fada fada ba kyau nan ba ruwansu sai su kulleki ba matsala bane a garesu nan.
Alaman tsoro karara ya baiyana a fuskanta lokaci guda don jin abinda ya fada tace na daina ai yaya bazan kara ba.
Kada ki kara kinji tashi kije falo zakiga wasu kwalaye da komai saman kujera ki kwaso kizo dasu nan ta mike da sauri zuwa inda ya aike ta kafin shima ya dago kai ya juyo gareni yana fadin.
Baki dai da matsala wurin karatun ki ko na dan girgiza kaina a hankali alaman a,a ga sytem nan na sayo maki don su nan komai saida shi sukeyi zakiji saukin karatu.
I hope kin san yadda ake amfani dashi dai ya tambaya nace eh duk da ba iyawa nayi sosai ba gana Anty Aisha da nake gidan mami takan dan bani in jagula kafin matsala ya shiga tsakanin mu dasu.
Halimatu ta dawo dakin dauke da kwalaye niki niki ba bita da kallo ya karasa bakin gado ya zauna ta zubesu a gefen shi zata juyo yace dawo nan ki zauna .
Showing 222001 words to 225000 words out of 390011 words