min ke din ai kin haramta a gareni yanzu .
Don tsawon dadewan da mukayi a tare ban sauke hakkina a kanki ba da kuma manufan da na aure ki akai a yanzu wani matsayi aurena dake yake ga Allah ?
Da sauri na daga na kalleshi kafin na mayar da kaina na dukar a sanyayye wani irin harbawa kitjina keyi lokaci guda don sam wanan tunanen banyi a lokacin ba.
Tunanen hakan sam bai taba zo min ba don ban dauki hakan a wani matsayi ba can na daban da zai iya kawo shamaki a tsakanin mu.
Tsam na mike daga yadda muke zaunen na dan gusa nisa dashi ina jin faduwan gaban nawa na tsanan ta.
A yanzu wani iri nake ji azuciyana da yayi wanan maganan dan jinyasa kawai ya kara saka shakuwa sosai a tsakanin mu wanan lokacin.
Shima din da alaman hakan ke damun shi cikin zuciyan shi a lokacin na sameshi yayi shiru dana shigo yana tunane.
Karshe mikewa nayi don ba zan iya jure zama a falon ba a lokacin bina yayi da kallo har na fice ya mayar da idanun shi yadda suke yana maijin tausayin mu a zuciyan shi .
Ina shiga daki na fada saman gado na sake wani irin kuka lokaci guda kukan da bazan ce ga dalilin yin shi ba a lokacin shin kukan bakin cikine koko na murna nakeyi a lokacin.
Abin mamaki nida na dawo Nigeria da zuman rabuwa dashi har abada a zuciya sai gashi yau abin mamaki ina sake hawaye akan ya furta zaman wata kila dashi a yanzu ya haramta.
Don wasu dalilai dabai cika ba na sharia tun yin aurena dashi dana zauna a tare dashi a matsayin nazo aure gare shi.
Ni kadai a dakin na kasa samun natsuwa a tare dani zuciyana ina jin ba dadi a yanzun tun bayan wanan maganan da mukayi dashi a part din shi din.
Haka na wuni sukuku dani da damuwa cike tare dani na rasa sukuni a wanan wunin ba abinda ke min dadi a zuciyana.
Bayan na sallame sallah isha,i ne na jawo wayana na tasa a gabana ina kallon lokaci a wayana ina dakon time din da nake tunanen malam ya shiga gidab shi a lokacin karfe tara ke nan na dare.
Saida na dan bada lokaci kafin na dauki kiran na danna maaa kira kamar kiran zai katse ya daga da sallama muka fara gaisawa dashi.
Yake tambayana jikin jafar din na fada mai yadda yanayin jikin nasa yake a lokacin yayi masa fatan samun sauki a tare dashi har abada.
Kafin nace da dashi malam tambaya nake dashi yace na,am ina sauraren ki zainab nan na jefo mashi tambayan sai naji yayi murmushi ya fata min bayani tiryan tiryan yadda zan fahinci yadda maganan yake a addinance.
Saida ya gama min bayanin nayi mai godiya mukai sallama na kashe wayan a hankali na kai kwance a wurin ina lumshe idanuna.
Dare yayi ban iya lekowa ko falo ba balle nace zan tafi na duba shi don yanayina ya koma kamar na mara lafiya yin yau.
Ina kwance a kasa a inda nayi sallah kuma nayi waya da malam ya wayar min da kai kan maganan kamahin turaten jikin shi ne ya ziyatci hanncina a lokacin.
Jin hakan duk dana gane shine ya shigo dakin a lokacin amma hakan baisa na daga ba daga yadda nake kwance a kasan dakin saman salayan.
Tun da ya shigo idon shi yake a kaina ya karaso yana dan kiran sunana da zainab ko barci kikeyi ne wai ?
Na dan daga tare da fadin idona biyo banyi barci ba ya kalleni ya dan sake murmushi a fuskan shi yaja jikin shi zuwa bakin mirrow ya tsaya tare da jingina da jikin mirrow din yana face dina.
Sake ambatar sunana yayi yana fadin zainab meke damuwan kine yau ko bakya jin dadin jikin ki ne yau din ?
Sai lokacin na dan dago na zauna a hankali ina kallon shi kafin na mayar da kaina na duka ina fadin lafiya ta kalau nake.
Kin manta da kina jinya ne baki lekani ba tun dazun ya sake tambayan yana hakan sai dan sake murmushin dole ina dan gyara hijabin dake jikina nace.
Ban manta saidai naga majinyacin nawane a yanzu ya samu sauki yasa na nisanta kaina dashi har zuwa lokacin da za a warware matsayin zamana da kai.
Shima dai dan murmushin yayi ya gyara tsayi yana fadin au kan wanan maganan yau yasa ban samu kula yadda aka saba min ba kullun ?
Ko kema bakya son rabuwan namu ne a yanzu kamar yadda nima nakeji idan hukuncin hakan ya hau kanmu ?
Na danyi murmushi tare da girgiza masa kai ina fadin a, a ko daya saidai kawai ina jiwa sabone da juna da mukayi da kai a yanzu.
Amma nasan ko mun tafi kai baka da wani kewa ko damuwa ai irin wanda mu zamuji na rabuwa dakai a yanzu.
Don dama a shirye ake da a aura maka wace ta dace dakai a rayuwan ka don farin cikin kowan ka koni a yanzu nasa ba sa,an ka nake ba.
Ya dan kalloni da mamaki a fuskan shi kafin yace wanan shine tunanen ki a kaina zainab ?
Har kina tunanen akwai wata macen data dace dani a yanzu kuma bayan ke ? ke dince zabin da Allah yayi min koda akadara hukuncin rabuwa a yanzu ya hau kaina sai dai in zauna hakana ba tare da aure ba a gareni.
Aiba kai zaka aurawa kan ka ba wanan karon aure za aima kamar kowani da dan gata a duniya irin naku na yayan attajirai a kasan nan don duniya tasan da auren ka.
Murmushi kawai yayi ya dago tare da fadin idan kin gama fadin abinda ke zuciyar ki yanzu saiki hado min magani nasha na kwanta.
Daga haka bai tsaya ba ya fice daga dakin na sauke ajiyan zuciya ina maijin daci a kasan zuciyana kamar ya fashe a lokacin.
Ban bita yadda nake ji a zuciyana ba na mike na hada mai maganin nakai masa na samu har ya kwanta saidai ba barci yakeyi ba a lokacin.
Ina tsaye har ya mike zaune yasha ya miko min cup din na juya na fita daga dakin bai kara ganina ba sai washe gari dana kai masa maganin yasha ba tare da yai min magana ba har na fita.
Yasan dai dalilin hakan a yanzu kan wanan maganance da yayi min da yanzu yake daya sanin furta hakan a garebi.
Don ya fahinci zan juya maganan ya zama wani manufa ta daban a gareshi saboda ya fahinci kawai wani aure nake zato a gareshi a yanzu.
Ya tambayi kanshi dama ina jin shi a zuciya har hakane ashe don gashi na fara nuna kishin shi da wata mace a duniya a fili.
Niko ina komawa dakin hjy na nufa na samu tana zaune tana dan kirga kudin ta tana jin na shigo dakin tayi maza zata boye kudin sai kuma ta fasa tana fadin .
Ai kece na zata ai wanine zai shigo dakin bake ba har abin yaso ban dariya na dan dara kadan ina fadin.
Hjy duk wanan kudin nakine haka tace ba kaji ba shiyasa bana son a gane su haka kada a saka min baki tana kokarin daure kudin cikin jikinta.
Sai kuma ta fasa tana fadin ko na dan baki wani abune ki rika dama dan kudin da bayin Allah dake zuwa gaida nine nake tarawa kinga dana koma sai in taimakawa kawun ku Amadu dana cefane kome kika gani yar nan.
Kinsan shi Amadu baidashi kuma ga tarin iyali Allah ya bashi kullun a cikin wahala yake na iyali shiyasa nake dan tausayin shi a cikin su.
Kaina girgiza jin takai aya ina fadin hjy bar kudin ki kaiwa kawu ya fini bukatan kudi a yanzu ni nan babu abindana nema na rasa a rayuwa.
Tace wanan nake maki fata yar nan ko yaushe gashi har kina fadi da bakinki a yanzu hakan shine shedan kwarai wurun mace ga mijinta.
Ni kaina naga alaman hakan a tare dake a yadda kika koma din nan kamar a tabaki jini ya fita din nan hakkuri ke nan idan ka yishi kana da riba sosai a wurin Alllah tun a nan duniya.
Ki kara rike mijin ki dakyau yar nan irin mazan ku yanzu tsadane dasu a duniya ba kowane ke samun su ba a rayuwa na dan murmusa na ciki na ciki ina fadi a zuciyana.
Kedai tsohuwa ayi sha,ani an cuci na kauye baki san komai ba don ABU CIKIN DUHU SIRINE namiji ko tallakane indai halinsa yana da kyau shine dace.


ZAINAB IDRIS MAKAWA




ASSALAMU ALAIKUM YAR UWA ALLAH YA BAMU WUNI LAFIYA ALLAHUMA AMIN ALLAH YA TAIMAKI MUSULMI A DUK INDA YAKE AMIN YA ALLAH, , , ,

Yanzu sai kuma zaman namu ya dan sauya don wanan kalman daya furta min din sai nake ganin ai
kawai a yanzu na haramta a gare shi .
Zuwa wurin shi din bai zama wajibi a gareni ba kada muzo mu aikata wani zunubi a hakan do gashi yanzun da dabi,an son rugumeni a jikin shi ko yaushe .
Wanda hakan nakewa tsoro tunda ban san matsayina a zuciyar shi ba kamar yadda malam din yayi min bayani.
Don haka a yanzu ya zama dole a gareni na nisanta kaina dashi don ina ganin rashin dacewan hakan a garemu baki daya gujewa afkawa ga fushin ubangiji a kan mu.
Gashi a yanzu duk wani laifi nasa dake zuciyana a baya na daina ganin hakan illa zalla tausayin shi dake cikin raina a yanzu.
Ba komai nakewa tausayin ba na farko dai ko dadin bakin mazane da yaimin daya nuna shima kamshi baisan lokacin daya fara wanan harkan ba.
Haka zalika badon kudi yake irin rayuwan ba kawai dai don giyar kurciyane dake diban mutum a ganuwan kurciyar sa.
Malam kuma ya fada min cewa akwai asiri a kanshin tunda kurciya akaso ya lalace saidai da yake a lokacin mahaifin su yana nan bai zauna hakana ba yasa asirin a lokacin baiyi tasiri a kanshi ba.
Amma yanzu da uwar suce kawai wace tafi maida hankali ga aiki da neman duniya kawai bata da lokacin tambaya da neman taimako akan zuri,anta a yanzu.
Sai uwa uba irin nuna min da yayi shi a yanzu ko ance ba auren mu don irin dadewan da mukayi da taimakon dana bashi baiga wata macen da zai kara zama da ita da sunan aure ba a duniyan nan bayan ni.
Wanan hujojin yasa na hauna zauna a kai ina jin tausayin mu a zuciyana don yanzu in ma haushine nafi jin haushin mami fiye dashi don ganin da nake kamar ita duk munanan halaiyar sgi ba dame ta ba ita.
Bata dauki hakan abin kyama a gareta ba kodan rayuwan turai da tayi ta saba da ganin hakan har yasa take daukan abinda karamin zunubi a wurinta oho ?
Idan nace bata damu ba ba laifi bane duba ga yadda wasu mata a yanzu suka ba aikin su muhinmanci sama ga zama su ba yayan su tarbiya da kansu inganttace .
Nasan wasu na da lokacin hakan saidai kosu ba yadda ya dace din bane akeyi a yanzu don ya zama dole a gareki ke uwa kisan a ina kike barin yayan ki idan zaki fita koda kuwa ba wuein aiki bane a yanzu.
Cusawa yaro tsoron Allah tun yana karami a zuciya da irin azabobin da Allah ya shimfida ga wanda ke masa sabo.
Wanan idan uwa tana hakan yana kawo yaro ya tashi da tsoro a cikin zuciyar shi sabanin wasu uwayen na yanzu da yaro zai ga abin asha a tv yana kwakwayo uwaye su zauna suna dariya ga abinda yaron ke koyo na bata tarbiyan shi.
Zama da dan ki walau namiji ko mace kuna hiran abokan sa tanan zaki fahinci dawa danki ke mu,amula a bayan ki.
Yawan dafa kai ko a cikin wasa kina sakawa dankin albarka tare da adduan kariya yana sa yaro ya kara imani yaji tsoro da tausayin ki ke uwa azuciyar shi koda bayan kine kalan irin yabon da kike masa zai tuna ya fasa aikata wani abin.
Idan kinga da ko yar wata ta lalace bakin ki ya saba da fadin ubangiji Allah ya shirya muna ku kiyi shi a cikin jam,i kada a zauna dake ana gulman dan wani dan sheri jifane dawo kan maishi yakeyi komai dadewa ubangiji ka bamu ikon gyara halayen mu da zurian mu Amin.
Naga abinda nakeyi tsab na shirya kamar yadda na saba samun shi a dakinshi in mashi ina kwana idan yana bukatan wani taimako nayi mai a gurguje in fito.
Yau ma hakan nayi na nufi dakin sai kamshin oud din jikina ke tashi duk inda nabi don a cikin gida nake nakan shafa abina son raina don gasu nan aje kala da kala a dakin wani ma ban taba amfani dashi ba.
Da sallama a bakina na shiga dakin nasa zaune na hangoshi saman gado ya mike kafafun shi ya harde su a wuri daya tare da hade hannayen shi suma ya saka a tsakiyan cinyar shi yana aikin tunane.
Kallo daya za kai mai ka gane yana a cikin wani yanayi na damuwa a lokacin duk gaba daya ya fita a hayacin shi a yanzu.
Kai ya dago a hankali yana kallon kofan tare da amsa min sallaman ya mayar da idon shi kasa wurin kafafun shi yana kallo.
Ina kwana yaya na fada tare da jan in tsaya daga dan abin zaman bakin gado da ake ajewa a yanzu gaban gadajen kasan waje a yanzu.
Ba tare da ya amsa min ba Kai ya sake dagowa a hankali ya kalleni da kyau kafin inga ya dan sake murmushi a fuskan shi can kuma ya girgizan kan nasa a hankali.
Zainab na gane yanzu guduna kikeyi bakya kaunan zama a kusa dani ko kadan a yanzu ko kema kin koma kyama nane a yanzu abinda bakiyi min ba lokacin da nake cikin aikata sabon da nayi a baya.
Ko kuwa har yanzu kina zargina a rankine akan ban daina abubuwan da nayi a baya bane a yanzu ?
Idona kura mai a inda nake tsaye ina kallon shi tare da sauraren abinda yake fadi a lokacin har sai daya dakata na dan gyara tsayuwana ina fadin.
Ba haka bane yaya ina gudun mu fadawa fushin Allah ne ga hakan tunda kayi wanan furcin a gareni nake tsoro da taka tsantsan a zaman mu yanzu.
Me zaisa na gujeka a da can ban guje maka ba balle yanzu da nasan kafi bukatan a zauna dakai zan fara gudun ka kuma ?
Laifi Allah kawai ai yaya yanzu tsakanin kane da ubangijin ka kanemi gafara a aurin shi mu kuma na tare dakai mu taya ka.
Murmushin da yanzu ya kara zama dabi,an shi ko yanzu shiya sake min din don abindana fada a lokacin gefen shi ya dan bubuga alaman in zauna a wurin.
Kallon wurin nayi kamar mai nazari kafin nayi ajiyan zuciya na kai zaune a hankali kamar mai tsoron hakan.
Zamana dan shiru dakin yayi kafin yace dani banyi tsamanin za a samu matsala a kan zaman namu ba a yanzu sai dai shi tambaya yana da amfani don yanzu ban kaunan wani abu da zanyu wanda zan sabawa ubangjji na a yanzu.
Wanan yasa nake son nayi tambaya akai dan kada muzo mu tabka sabon Allah kema in jefaki a cikin fushin ubangiji.
Ni kaina zainab nasan na cuta maki na tauye maki hakkin ki daya rataya a kaina kuma kikayi hakkuri ga hakan bawai don abin hannu yasa kikai hakkurin zama dani di ba a a .
A yanzu na kara fahintar kawai dai Allah yayo ki mai tausayine da jin kai na tare da ita tun a zamanin zaman ki gidan mami na fara fahintar haka.
Saidai ban gaskantan hakan ba sai zamana dake a yanzu na kara fahintar hakan akanki any way anjima ki shirya zamu fita sha biyu zuwa gidan mami akwai malamin da za a kira jan matsalan namu a can yau.
Gabana ne naji ya fadi lokaci guda har yakai ba dan dago da sauri ina kallon shi ido ya dan lumshe tare da kada min kai alaman eh.
Nayi karfin halin fadin Allah ya kaimu a sanyayye ko dan ya kawar da zancen ne a lokacin ya jefo min tambaya da maganin nawa ya kare ke nan naga kin daina ban.
Ajiyan zuciya na sauke tare da fadin iya
Showing 363001 words to 366000 words out of 390011 words