laifi ta samu lafiya a lokacin.
Mun dawo gida dakina nashiga nayi wanka har lokacin ina jin jikina ba karfi kamar nayi watani a kwance ina jinya nake jin jikin nawa.
Karfe shida sai ga maizube da malam an shigo dasu gidan wanan ya ban mamaki don ban san zasu zo garin ba a lokacin.
Basu huta ba malam ke fadin a kaishi wurina yana son ya ganni a lokacin aka kaisu har dakin ina kwance duk da yamma yayi a lokacin na kwantane don zama bai mun dadi a lokacin .
Yana shigo da sallama a bakin shi bai min magana ba ya fara bin dakin da addua kuswa kuswa na dakin kafin ya dawo ta kofan dakin ya tsaya ya dade yana adduan da bamu ji abinda yake fadi a lokacin.
Yasa hannu ya ciro wani dan gora da rubutu a cikin aljihun babban rigan shi tare da wani fifiken wani dabba mai dan girma yana bin ko ina yana dan yayyayafawa a dakin ko ina har zuwa wurin gado.
Sai daya gama yazo inda nake zaune din ya mikowa maizube wani gora yana fadin ku shiga bayi ki mata wanka da wanan zamu samu abin yin hayaki ko a gidan nan ?
Burner muke dashi na bashi amsa tare da yimai bayanin yadda yake yace zaiyi ai tunda yana fitar da hayakin a jikin shi.
Nayi duk yadda yai min bayanin ayi min koda muka fito basu dakin shi da yaya jafar din hakan ya bamu daman yin yadda yace ayi din maizube na fadin ai da yardab ubangiji komai zaizo karshe ke nan yanzu don sai da malam din yaje Damau yaga aminin shi kafin muzo nan.
Ni da kaina nace aban abinci inci a lokacin ina ci sai barci mai nauyi ya daukeni ban falka ba sai cikin dare sosai koshi fitsarine ya tayar dani a lokacin.
Da safe koda na tashi jiki wasai dashi kamar bani bace a jiya ban ko iya daga hannuwana a lokacin.
Kwanan malam ukku a gidan mu yana burgan gidan damai gidan gaba dayab mu har mami da ya mamud sunzo ya zauna dasu sunyi maganan siri da jafar din dasu .
Wanda ban san abinda suka tatauna ba a lokacin nidai naga mami ta canza min yanzu tun a asibiti naga wani canji a gareta a yanzu gareni.
Washe gari su malam sukai min sallama suka tafi bayab yaja mun kunne koda wasa kada in fada wa wani a gida cewa sunzo nan Abuja .
Kuma haka din nayi duk da inna na kirana mu gaisa ban fada mata ai malam yana wurina a abuja ba.
Duk da malam ya tafi haka baisa mun daina maganin daya bamu inayi ba a kulun har kwanakin daya diban muna din muyi a tare dashi mukeyin maganin kullun kafin mu kwanta barci zamuyi wanka da hayaki sai adduan kwanciya din daya bamu safe da yamma.
Alhamdullahi zance a yanzu banda wani damuwa a jikina ko na tsoro a yanzu tun bayan zuwa malam wurin mu din.
Ana sallamo Hjy gidan mu akayo da ita don can tace a kaita kafin ta koma gida idan ta dan murmure jikin nata.
Mami bata so hakan ba saidai ba yadda ta iya da hakan dole ta barta taje gidan namu ta zauna hakana yayin da mu kuma hakan yai muna dadi sosai don son da mukewa tsohuwar.
Sabon zancen daya taso muna kuma a kan zuwan hjy gidab mu shine dawo da kwanan mu wuri daya da yaya a yanzu don zuwan hjy.
Don tun faruwan hakan ban kara komawa dakin na kwana ba sai yanzun da hjy tazo gidan namu zata kwana biyu damu.
Don sa idon tsohuwar duk da a daki take zama nan take wuni bata fitowa ko falon gidan sai dai kuma suna tare da mama Ramatu a gidan namu.
Wace mami tasa ta biyo mahaifiyan nasu su zauna nan tare da ita don halin jikin nata da take ciki a yanzu.
Hakan yasa a yau dole mu hada daki da yaya din wanda kowan mu na cike da tsoron hakan a cikin zuciyar shi tunda bamu san mai hakan zai haifar muna daga baya.
Na shiga dakin da sallama yana kwance yadda ya saba kwanci wani lokaci ya daga kafa daya ya dora hannu saman fuskanshi ya kare da hannu daya.
Yana jin sallamana ya dan dago kadan ya kalleni ya mayar da kanshi a yadda yaken na tako a hankali zuwa bakin gadon kamar a tsorace nake.a lokacin.
Zama na danyi a baki gadon ban karasa hawa ba gaba daya yake fadin idan kina ganin hakan da matsala ki koma part din ki ko hankalin ki zai kwanta nima ina dauting din hakan a yanzu ban son a kara samun matsala again.
Kada su mami su kara zargina don mun kwasa dasu wacan satin suke fadin wai nine na bayar da jinin ki a wurin tsafina.
Jin hakan yasa na juyo da sauri ina kallo inda yake kwance din yana nan yadda yake yake maganan shi hankali kwance.
Waya fada mata hakan na tambayeshi da mamaki a fuskana shine abinda ya ban mamaki don maganan yana kama da wanda muka sani din don haka yaya akayi suka san da zancen.
Nasan baki fada masu komai ba kan hakan saidai idan zargi sukeyi ko kuma sunji a wurin malaman su don nasan kowa na shige shige a kaina a yanzu.
Wanda ni nasan da hakan ba yau ba sai dai duk bata lokacin su sukeyi ga hakan don hanya fita ciki dayane nina sani idan lokaci kuma yayi zan daina din da yardan Allah.
Wani irin kallo nayi masa na tuhuma duk da bai kalloni ba yasan nayi masa sai naji yace yes matakin da basu so zan dauka shi zai rabani dasu lafiya.
A hankali na jingina bayana saman filon dake gefena nakai kwance ba tare dana iya furta mashi komai ba a lokacin.
Don a yanzu ya daina bani tsoro ko mamaki don sai nake ganin a gadarance yakeyin abinsa kai tsaye duk da yasan hakan ya sabawa addinin mu sosai.
Sai dai maganan malam ce da yake fadin in bishi a sannu don bayin kansa bane hakan zanga kamar komai yana yinsa a cikin sani ne saidai asirine dake aiki a kansa kawai ba a gane hakan ne ko shi kanshi bai gane hakan kai tsaye.
Sai idan an bishi a sannu zai zo ya daina komai wanan ne suka tatauna da mami da malam din ashe da zasu tafi bayan malam din ya fada mata komai akan dan nata da a yanzu ta yarda da komai da ake fada akanshi.
Ba wanda ya sake wani magana a cikin mu har barci ya dauke mu a hakan ko dadin barci ne ya kawo mu kusa da juna kowan mu ya dora hannu saman jikin dan uwa oho.
Sai dai mun tashi da asuba mun samemu a hakan nice ta farkon falkowa nayi mamakin gani shi rungume dani yau abinda bai taha faruwa a tarhin mu cikin jin dadi irin hakan.
Ban gama mamaki hakan ba ya falka shima da sauri ya dan ja baya ya zabura wanda hakan yasani na kara mirginawa gefe daya.
Ganin na matsa yasa shi sauka da sauri ya zauna a bakin gadon na dan wani lokaci kafin ya mike ya shiga ban daki nabi shi da kallon mamakin yin hakan.
Bai dade ba ya fito daga bayin na shiga wanka nayi na daura alwala ina mamakin wanan bakon yanayin yau da nagani a garemu.
Har na fito ban daina mamaki hakan ba ina idar da sallah na koma na kwanta don gari bai gama waye ba a lokacin.
A cikin barcin ne nayi mafalkin ga wasu nata kwasan kayan su suna tafiya kamar masu barin gari ina tsaye ina kallo su sai da suka gama suke dago hannayen su na duba sai banga kowa ba kuma.
Kakan maya na gani tsaye da abu kamar sanda a hannun ta tana min murmushi na mayar mata itama din tabi bayan su suka bace mi tare.
Tashi nayi firgigit ina kallon ko ina na dakin sai lokaci na gane inda nake kwance a dakin yaya nake har lokacin kwance .
Juyawa nayi shine zaune yana aiki a cikin laptop din shi ga tea a gefen shi yana tashin turin hayaki.
Na mike na saka hijab gaidashi nayi na nufi hanyar fita daga dakin naji ya dakatar dani yana fadin mafalkin me kikeyi kuma haka da safen nan.
Dan kallin shi nayi ban furta mai komai ba nasa kai na fice daga dakin kai tsaye zuwa dakina .
Idan ka ganni a yanzu zaka gane ina a cikjn damuwa don yadda na rame na danyi duhu ba sosai ba dai.


Don Allah ayi hakkuri da wanan din ba yawa sosai yar uwa dare yayi sosai ba zan samu karasa shafin nan ba yau.



ZAINAB IDRIS MAKAWA



ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI UBANGIJI ALLAH YA BAMU WUNI LAFIYA MARASA LAFIYAN MU ALLAH YA BASU LAFIYA MASU LAFIYA ALLAH YA KARA MASU LAFIYA .
YAN UWA MUSULMI DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA UBANGIJI ALLAH YAI MASU RAHAMA ALBARKACIN KALMAN LA, ILLAH HA,ILLAH MUHAMMADUN RASULILLAH ALLAHUMA AMIN.

NOVEL DIN KUDINE NA FADA BA HAKKI A TSAKSNINA DAKE RANAN TAMBAYA NAGODE ALLAH BADA IKON BIYA A KATANTA LAFIYA, , , ,

Zaman hjy a gidan mu zance kamar alherine a garemu baki daya don tsohuwar duk da tsufa da yai mata yawa a yanzu haka baisa ta barkace ba ga komai.
Wanan shi ake kira da tsufan mutunci zakaga tsofo a kamile komai nasa a cikin mutumci da addine yakeyin sa ubangiji Allah kabamu irin tsufan nan idan tamu tazo Allahuma amin.
Yau ma ina fitowa mukai kicibis da mama Ramatu da tafito kitchen yiwa mai aiki magana ta kawowa hjy ruwan zafi tasha shayi kafin tasha maganin ta.
Tana dawowa ina bude kofan yaya jafar din zan fito a lokacin mukai kicibis da ita jin karan kofan yasa ta dago ta kalli part din .
Nice ina rufe kofan ta dan sake dan murmushi a fuskanta daga can nisa inda take tana fadin har kin tashi ashe.
Ban iya bata amsa ba don nauyi da kunyan hakan a gareni ashe shigan ta take cewa hjy din ikon Allah koda ake cewa yaran nan basu damu da junan su ba auren nasu na gashi nayi kane sukayi ashe zancen ba haka yake ba hjy.
Nikan nasan cewa lokacin haihuwan nasu ne baiyi ba koda yaya ke fadin dama dai ai auren yinsa yayi don kada a matsa mai yarinyar ba sonta yakeyi ba har yanzu.
Tunda babu soyayya a tsakanin su da yarinyar yasa bai kulata har su samu fahinta nikan nayi mamakin hakan da yaya take fadi ai.
Dan murmushin manya hjy ta sake kafin tace da yar nata shin Ramatu kin taba ganin inda akai sharia kan mata da miji irin haka ?
Kyake yar ku kawai da halinta nina dauka kawai lokacine baiyi ba don Allah ba ai masa dole sai lokacin daya dibarwa mutum yayi.
Yaran nan duk kansu hankali ke garesu don basu fita fili suna fitsara irin na yaran yanzu yasa take fadin hakan amma ai mai hankali yana gane wani abu a tsakanin su shi.
Ina nan kuke hiran yadda ya rude da ciwon ta a asibiti har kuna masa sherin hakan kawai dai ku barta da halinta jinin sune bai hadu da yarinyar ba a yadda na dauka.
Sun dauki lokaci mai tsawo suna tataunawa akan mu da mami kafin su juya hiran zuwa hiran Nuriya matar ya mamud.
Nafito wanka na shirya kafin in fito dakin na nufi dakin da hjy take don in gaidasu da kwana a zaune na samesu suna hira ga abin karyawa da suka karya dashi a gefe daya.
Da sallama a bakina na shiga dakin suka amsa min nakai zaune ina fadin hjy ina kwana ya karfin jiki take fadin lafiya yar nan .
Ya naki jikin ina da sauki i yanzu nace Alhandullahi hjy na juya wurin mama Ramatu ina gaida ita ta amsa min a cikin fara tana fadin ya dare zainan an tashi lafiya Alhamdullahi na bata amsa.
Daga haka nakai zaune a gefen carper din da suke zaune suna hiran ga abinci nan ki karya hjy tayi min tayi.
Kafin inyi magana mama ke fadin a, a hjy da mijin ta suke karyawa fa yanzun kuma kyace ta zauna nan tace aiko zaku hadu dashi idan ya fito.
A daidai wanan lokacin yayi sallama ya shigo dakin saida ya kalli hjy kafin ya juyo ya kafeni da idanun shi har saida na tsargu.
Mama ya fara gaidawa sabanin ni dana fara gaida hjyn a lokacin dana shigo din dakin hjy ce tace kin gani idan na nuwa yar nan so da kauna kuga laifina a hakan kuna fadin wai nafi son ta da kowa.
Yanzu ki duba ina zaune amma dan nan keya fara gaiyarwa daya shigo shi dakin nan matar shi ko datafishi sanin muhinmanci na ai kinga ni ta fara gaidawa data shigo.
Bai bata amsa ba sai da yakai zaune kusa dani yake fadin wai mama mai wanam tsohuwar take fada ne haka tun dazun ?
Fada takeyi da kai ka fara gaidani kafin ita ya juyo inda take zaune yana fadin da me kike nufi in bar uwata da take zaune in fara gaida ke ?
Ai idan ina da rana ka fada randa babu ni yace baga iyayyena ba ina gani ta mere bakin ta tana fadin ke dai kawata kada ki biyewa wanan butulun mijin naki nayi murmushi kawai ina dukar da kai kasa ina dan wasa da hannuna.
Ta sake nunani tana fadin ka gani Allah ya baka mata mai.alkunya ba irin ka fitsarare ba mara kunya.
Haka ma wancan kanin naka mai irin zubin ka yazo jiya yana min huci kamar wani tsohon kimarci wai am bata masa rai.
Wa ke nan keda zubina ya tambaye ta take cewa masu suna irin dayan nan wanda yaso kwaso farin ka da tsayi.
Mama Ramatu tace jamal take nufi fa kasan ita hjy bata da gwani a wurinta jiya kuma kai aka yaba akan jamal din gashi yau kuma ana kushema.
Barta kawai ai idan mun tashi tafiya chaina da ita zamu tafi wanan karon hjy na fadin kadai je da uwarka gata zaune ni kuma ina dago kai ina kallon shi.
Don jin zancen komawa chaina da yayi a lokacin don na tsani inji zancen tafiyan nan namu a bakin kowa a yanzu.
Balle yanzu da nake ganin can din yake da babban matsalam rayuwa data shafi halin da yake ciki a yanzu yasa gaba daya na kara tsanar kasan a rayuwana.
Amma kai kadai zaka tafi wanan karon ko hjy ta tambaye shi ya kai hannu ya dauki wayanta dake gefe yana bin shi da kallo kamar yana nazarin wayan.
Ba tare da ya dago kaiba yace ita matar tawa gunki zan barta idan ban tafi da ita ba can din ?
Ni dai in tawa ce kabar yarinyar nan a kasan nan kusa da gida zaifi idan ka tashi kazo ka ganta yafi sauki wallahi.
Wayan dake hannun shi din ya aje mata a gefe inda ya dauka da farko yana fadin wanan sabon zance kike son dauko min hjy.
Yaushe zan iya zuwa in wani dawo nan kasan kuma yanzu banda wanan lokacin gara dai muna can din hankalina zaifi kwantawa ai.
Budan bakin mama Ramatu sai cewa tayi nima abindana fadawa yayan mu ke nan da take wanan maganan wai ba zaka koma da zainab din ba wanan karon.
Kamar ba hjy ce ta tsokalo maganan ba a yanzu dana dauka zata goyi bayan zaman nawa a nan sai ji nayi tana fadin.
Ku barshi ya koma da matarsa yafi mai kwanciyan hankali hakan ita lokacin da mijin ta yake raye ina can suke da zama gaba daya shekara da shekuru kuwa.
Ai kawai ku barta tabi mijin ta shi yafi, na fadawa mami hakan ba zai yuyu ba tun ranan don haka abar wanan zancen don Allah ya fada yana bata rai ya mike don barin dakin a lokacin.
Mama Ramatune ta tsayar dashi tana fadin nace ko zaka leka gidan yayane da safen nan ina son zuwa yau din akwai sakon da zan bayar akai min gida a can.
Haka yasa yaja ya tsaya yana sauraren ta kafin yace da ita ba yanzu zan tafi ba mama amma idan zaki tafi akwai driver a waje sai ya kaiki ai.
A lokacin na mike don barin dakin nima don idanuna ya riga da ya cika da hawayen takaici a lokacin nakai kofa yaja ya ban wuri tare da bina da kallo.
Yaki kawata hjy ta fada ban iya juyoba a
Showing 351001 words to 354000 words out of 390011 words