hasali ma sune kuke sawa nemo muku masu laifin."

A jujjuye ta fahimceshi dan haka tace "ban fahimceka ba yaro? ko zaka iya yimin dalla dalla?"

"Mama ba zan iya fad'a muku komai ba, amma ku aika wasu jami'an na daban ba wanda kuke tare dasu ba, suje unguwar airport daga farkon shiga unguwar a gida mai number 8, suyi bincike da kyau karsu bar komai, ina tabbatar muku zaku samu hojojjin da suke nuna masu laifin anan suke."

Tuni hawaye suka wanke fuskar Mamie tana kallon Umar Faruk tace "jirani ina zuwa kaji yarona."

Tana fad'a ta juya ta shiga ciki da gudu, Umar Faruk na ganin haka shima yayi murmushi kawai ya juya bar wajen, tare da Papa Mamie ta fito amma basu ga Faruk ba, nan Papa ya ciro waya jiki na rawa yasa aka turo mashi wasu jami'an, dan danan asibiti ta cika da jami'an kama daga police soldier da gendarme, nan fa suka basu jawabin abinda Umar ya fad'a musu, ina Papa ma ba'a barshi ba saida ya bisu.

Suna gaf da fita daga k'ofar asibitin motar su Musa tazo shigowa, nan suka tsaya suka fito suka sarama manyansu suma wasu suka sara musu, nan Papa yace su shiga mota su tafi an samu labarin in da mutanen nan suke, ganin yanda ya masu magana bai nuna wani abu ba yasa ransu yayi fari suna tunanin wasu ne aka lak'ama sharrin, amma tunda suka ga ana nufa unguwarsu gabansu ya fara fad'uwa, babu wanda baiji gudawa ba lokacin da aka tsaya k'ofar gidansu.

Duk da unguwa ce da babu mutane sosai amma saida jama'a suka fito kallo ganin yanda jami'an suka cika unguwar, Papa na fitowa ya duba yaga kwatancen daidai ne kawai ya juya ya kalli su Musa da sukayi sukayi sharkaf da zufa, hannu Papa ya nuna musu yace "ku kama min su."

Tuni aka cika aikin yallab'ai akayi ram dasu Musa aka d'aure su , gidan suka shiga nan fa suka fara shiga kusfa kusfa ana bincike, saboda Umar Faruk ya rage musu wahala hakan yasa suka samu hujjojin da Faruk ya gani har dama wanda shi bai gani ba kamar bras d'inta da d'an kunnai, haba su Musa ai tun daga nan suka fara shan duka.

_Kuyi hak'uri jami'an mu, akwai fa zafin rai._


Kasancewarsu jami'an yasa ba'a tausaya musu ba, cikin k'ank'anin lokaci har sun canza kama wai wannan somin tab'i ne kafin su gurfana a gaban kotu, tuni labari ya karad'e gari akan abinda ya faru da Khairat da kuma kama masu laifin, duk mai zuciyar imani ya tausaya mata sosai ace har mutum hud'u.

*02: 40* na dare Khairat ta farka da ihu tana fad'in a taimaketa zasu kasheta, Mamie da Mammie ne suka rik'eta sosai suna tofa mata addu'a harta nutsu, kuka take sosai tana d'aga murya kamar ranta zai fita, haka har suka wayi gari bata daina kuka ba, tunda likitoci suka nufi wajenta ta dinga kuka tana fad'in karsu tab'a ta su saketa ta koma gida, babu abinda suke ji kamar d'orin qafarta dan yafi hatsari, ganin abin ba qarami bane yasa Papa ma yace su sallamesu kawai.

Duk da ba haka aka so ba haka aka sallameta aka koma gida da ita, a d'akinta aka sake mata wani tanadin na ci gaba da jinyarta , amma duk da sunzo gida ma ba'a bari kowa ya ganta saboda kukan da take.


*Bayan sati d'aya* jikinta yayi dama dama sai dai har yanzu bata fara taka qafar ba, qananan raunikanta ne suka warke har akaihunta guda biyu sun toho, in banda shiru da tunani da hawaye babu abinda Khairat keyi hakan kuma na damun iyayenta.

Da farko an fara barin 'yan uwa na zuwa dubata, amma ranar da Mujahhid yazo da abokanshi su uku saita firgita sosai tana fad'in sune sune, tun ranar sai Mammie ta yanke shawarar tafiya da ita india danta samu ta dawo daidai.

Umar Faruk ya ci gaba da zuwa wajen aikinshi sai dai i zuwa yanzu babu wata damuwa a tare dashi, gaba d'aya ma mantawa yake da wata Khairat bare ta dameshi , yayin da d'aya b'angaren kuma yake soyayyarshi hankali kwance da 'yar uwarshi *Zubaida* wacce suka fi kira da *Zuby*, kuma suna jiran hutun 'yan makaranta domin shi zai basu damar zama miji da mata.


An shigar dasu Musa kotu kuma sun samu hukuncin shekarun da doka ta tanadar ga duk wanda ya keta haddin wata, tun akan akan hayarsu ta zuwa sabon gidansu suka fara tuhumar juna suna dorawa Musa laifin, shi kuma yace ba gaskiya bane tunda bai tilasta kowa ba.

_Wallahi ni duk abokin da ba zai anfaneni duniyata da lahirata ba to banga anfaninshi ba, domin kuwa kamar abotar shedan da yan uwata zata kasance, bayan ya ganka cikin wuta zai kora maka jawabinsa, bayan ya muku dogon jawabi da bama fatan jinshi daga qarshe dai zai ce ._

*Karku zargeni ku zargi kawunanku.*

_Allah ka karemu da yayenmu daga fuskantar qasqanci irin wanda Khairat ta fuskanta, Allah ka shirya mana zuri'armu shirin addinin musulunci._πŸ‘


Mamie da Mammie ce suka kama Khairat daga bisa kujerar guragunta suka cire mata kaya sannan suka sata cikin bahon wanka dake d'auke da magunguna na ice kala kala, suna zaunar da ita ta rintse ido saboda zafin dake da ruwan, duk da kullum ake mata tunda suka komo gida amma ta kasa sabawa , a hankali ta bud'a ido hawaye suka gangaro, Mamie ce ta fita daga ban d'akin sai Mammie ta dinga tausarta da kalaman har saida ruwan suka huce sannan ta kira Mamie suka kamata suka fito da ita.

Mamie ce ta shiryata cikin doguwar rigar kantie iya gwiwa sannan suka zaunar da ita akan kujerarta, abinci Mamie ta d'auka ta fara bata a baki, da sun had'a ido Mamie take saurin dauke nata, ganin kuma ta kafeta da ido yasa duk ta tsargu , a raunane ta kalleta tace "akwai abinda kike so ki fad'a ko?"

Lumshe ido kawai tayi ta kawar da kai, Papa ne ya shigo cikin shiri da alama fita zaiyi, saida ya sumbaci goshinta yace "shalele ya kike?"

Da ido kawai ta kalleshi, sake fad'in "ya jikin naki? da sauk'i dai ko?"

Ganin dai ba za tayi magana yasa yace "shaleleta kiyi hak'uri kinji da abinda ya faru, ina tabbatar miki hakan ba zata koma faruwa ba."

Take idonta ya kawo ruwa cikin mamakin abinda ba suyi tsammani ba suka ji Khairat tace "wane mai hankalin ne zai sake sha'awata kuma? akwai wani abinda ya rage min ne da har zan birge wani?"

Maida kallonta tayi ga Mammie tace "Mammie, ki kaini waje dan Allah ina so nasha iska."

A hankali ta tuka kujerarta ta fitar da ita kamar yanda tace, lambun dake bayan gidan ta kaita ta barota kamar yanda ta buk'ata, shiru tayi tana kallon firanni na kad'awa ga iska mai dad'i.


Papa da Mamie ne suka fito daga d'akin nata suna zuwa falo yayi daidai da shigowar manager, bayan sun gaisa ya fad'a musu tare da sauran ma'aikata yake suna so suga jikin Hajia, Papa ne yace su shigo sannan yace Biba mai aiki taje ta taho da Khairat, zaune sukayi suna jiran shigowarta, Mamie kuma ko kad'an bata lura da Faruk ba yaron da take nema danta gode masa, madafa ta nufa domin samo musu d'an abun tab'awa.

Shigowar Khairat a keken guragu yasa kowa maida kallonshi gareta, mamaki al'ajabi duka a tare da ganin Khairat, ita kam ido ta kafesu dashi tana kallon kowa, a lokacin da kallonta ya sauka kan Umar Faruk kuma sai gabanta ya mugun fad'i, duk da haka kuma bata d'auke idonta ba, shima a nashi b'angaren gabanshi ne yayi mummunar tsinkewa ya fad'i, d'auke kanshi yayi ita kuma suka k'arasa shiga falon, sannu kowa ke mata da jiki amma babu wanda ya amsa, Papa ne ya shafi kanta yana kallonsu yace,

"Sai hak'uri fa, har yanzu magana na mata wuya, muma haka muke zaune da ita."

A bazata Umar Faruk ya sake satar kallonta amma sai idonsu ya sake had'ewa , suna haka har Mamie ta fito amma da qyar wasu suka sha ruwa dan ganin Khairat ya girgizasu sosai, tashi sukayi gaba d'aya suka fita, amma Umar Faruk dake daf da barin falon sai yaji kamar muryar Khairat a bayanshi, dan haka yayi saurin juyowa ya kalleta, dama itama shi d'in take kallo dan haka suka kalli juna, d'an sakin fuskarshi yayi daga had'ewar daya mata baisan sanda ya saki wani basaraken murmushi ba, ita kum sai taji haushi ya kamata dan tunaninta yayi farin ciki da abinda ya sameta.


*'YAN TEAM UMAR FARUK.*πŸ˜›πŸ˜›πŸ˜›
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*Raina Fansane gareta*
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_My sweet Heenat, ina tayaki murnar kammala wannan littafi, tabbas ya qayatar tare da nishadantarwa, ga ilima da muka samu a ciki, wannan shine labari ina fatan ubangiji ya yafe miki kurakuranki sannan ya baki ladar dake cikin wannan fad'akarwa da ki kayi._ sai mun jiki a next novel.



_Bismmilahir-rahman-rahim_


1⃣0⃣



*Haka* kwanaki suka dinga tafiya sati ma ya fara shud'ewa har aka fara lissafa abinda ya faru da sati uku, a *sati uku* kuma duk wasu qananan raunika sunyi sauk'i sosai sai qafarta da har yanzu takata ya zama aiki, har yanzu Mammie na gasata a ruwan zafi tare da wasu saiwar magunguna da zai taimaka mata, haka ma an sake maidata asibiti an mata gwaje gwaje amma cikin ikon Allah babu wata matsala har yanzu.

A lokacin data cika wata d'aya sai suka fara shirye shiryen tafiya india, a lokacin kuma Mamie ta matsawa Papa akan ya bata takardarta, shi kuma ya dage ba zai bayar ba, amma ita taci alhwashin tafiya ko babu takardar saki, Mammie bata fahimci komai ba dan basa nuna da wata matsala a gabanta, Papa kam yayi tuba na gaskiya ya daina duk abinda yake yanzu, sai dai akwai barazana da wasu matan ke kawo masa saboda suna samun arzik'i sosai a hannunshi, duk da Khairat bata cika magana ba a yanzu amma dai bata kula Papa sosai haka ma Mamie.

Yau ta kama ranar *juma'a* Papa ya fito cikin shirin massallaci misalin k'arfe *10:00*, zaune suke a falo yayin da suka bishi da ido, durk'usawa yayi gaban Mammie ya gaisheta tare da fad'in "Mama zan tafi masallaci sai a mana addu'a."

Murmushi tayi dan ita har ranta tana ganin d'iyarta tayi sa'ar miji na gari, cikin sakin fuska tace "Allah ya tsare ya kareka daga sharrin masharranta, insha Allah ba zaka tab'e ba, domin kai mutumin kirki ne, duk da ban haifeka ba amma ka d'aukeni tamkar mahaifiyar data haifeka, babu abinda zance sai dai nace Allah ya saka maka da alkairi."

"Ameen ameen Mama, na gode da addu'ar nan Allah ya bar mana ke."

"Ameen." itama ta fad'a sannan ya mik'e yana kallon Mamie yace "ni zan wuce."

Cike da murmushi tace "to abban Khairat Allah ya tsare, saika dawo."

Shima cikin murmushi yace "ameen na gode."

Maida kallonshi yayi ga Khairat ya dafa kanta yace "shalele ni zan wuce, kiwa Papa addu'a kinji."

Sanin ba za tayi magana sai kawai ya wuce, muryar Khairat yaji tace "Allah ya kiyaye, a dawo lafiya."

Da sauri ya juyo ya taho a sukwane ua zube gwiwoyinshi gaban kujerarta, cikin farin ciki yace "Khairat, yau kece ki kawa Papanki addu'a? kai Allah na gode maka."

Duk da hawaye sun fara taho mata haka tace "Papa, duk munin halinka kai mahaifina ne, Papa ku yafe min da duk abinda na muku wanda ya b'ata muku rai, nasan hada hakk'inku dana kasa saukewa da kyau shi yasa haka ta faru dani."

Hannunta ya rik'e da sauri yace "a'a shaleleta, ba laifinki bane, laifina ne duk ni na ja miki, amma ki sani Papanki yayi nadama sosai kuma ya daina duk abinda yake yanzu."

"Khairat yanzu mahaifinki ya rabu da duk wani shirme na maida al'amurana ga ubangijina, shaleleta ki yafe min domin na cutar dake, duk nine...."

"Papa" cewar Khairat tana kau da kai gefe.

Shiru sukayi babu mai magana dan haka Papa ya tashi yana goge hawaye ya fita, Mamie ce ta matso kusanta ta rik'e hannunta tana shafawa tace "Khairat, ki yafe mana a bisa kurakurenmu, nima na taka rawa wajen faruwar komai a matsayina na uwa, amma yanzu mun shirya gyara kuskurenmu."

Da ido kawai ta kafe Mamie ba tace komai ba har Mamie ta gama surutunta ta koma mazauninta, haka suka zauna shiru dan yanayin da gidan yafi zama kenan tun faruwar abinda ya faru.


Bayan Papa ya dawo daga masallaci sunci abinci Mamie taje d'akinsa ta zauna dan kawar da duk wani shakku da zai nuna basa zaune lafiya, yana cire kayan jikinsa ya kalleta ta madubi yace,

"Har yanzu kina kan bakanki na tafiya tare dasu Mama?"

Ba tare data kalleshi ba tace "kana tunanin akwai abinda zaisa na fasa ne, kayana a shirye suke ranar kawai nake jira."

Gabanta ya zo ya tsaya ya kamo hannayenta suna kallon juna, kai ya girgiza mata yace "Na'ima, ke musulma ce kuma mai ilimi, nasan kinsan ba daidai bane aibata wanda ya musulunta, haka ma bai dace ak'i karb'ar yafiyar wanda ya nemi afuwa ba, hakan nasa da dama su kasa shiryiwa saboda tunanin haka, dan Allah Na'ima ki yafe min laifina wallahi ba sani da kika min da bane."

Ganin ta kawar da kai gefe yasa hannu ya tallabo fuskarta yana kallo, a hankali cikin tsoro ya had'ata da jikinshi, 😁wasa fa saita fara canzawa to ni dai nayi nan, bana kallon k'aramar harka bare kuma wannan babbar harka.


Kamar yanda Mamie tayi niyyar tafiya ko babu takarda hakane ta faru, ta shirya itama kuma tace wa Mammie shine yace su tafi tare danta kama mata kula da Khairat, ya gama shirya musu komai amma banda Mamie, in da itama ta shiryawa kanta komai ba tare da saninshi ba.

Sun gama shirin tafiyarsu tsaf ranar talata kawai suke jira ta zo, yau *litinin* da dare Mamie na zaune matashin saurayin nan ya fad'o mata a rai, wayarta ta d'auka ta kira manager ta tambayeshi akan yaron da suka zo tare a ranar, ya fad'a mata sunanshi dama matsayinshi a ma'aikatar tare, ta kuma tambayeshi koda wata alaka tsakaninshi da Khairat yace a'a, amma ya fad'a mata abinda ya shiga tsakaninsu.

Nan tace da safe ya turo mata shi kafin lokacin tashin jirginsu, bayan sunyi sallama ya kira Umar Faruk ya fad'a masa, hakan yasa ya kwana yana tunanin abinda zai faru da kuma dalilin da yasa matar ke nemanshi, haka dai ya wayi *gari* sannan ya shirya ya tafi gidan.

Khairat ce zaune akan kujerarta ta kira Biba, tana zuwa tace mata ta turata ta kaita lambu tasha iska, haka akayi ta kaita can ta barota yayin da ta toshe kunnuwanta da abin sauraro tana sauraron wak'ok'i, Umar Faruk ne ya shigo gidan sai dai kafin ya shiga ciki sai wayarshi ta fara ruri, yana fito da wayar yaga Zuby ce ke kira dan haka ya d'auka ya fara tafiya ya nufi kwanar cikin gidan duk da baisan ina zata kaishi ba, a hankali yake takawa harya riski lambun dake bayan gidan, jingina yayi a bishiyar daya fara gani cikin taushin murya ya mayar da martanin abinda Zuby ta fad'a masa,

"Ina sonki, ina qaunarki , na matsu ranar nan tazo domin a ranar burina na gidan duniya ya cika, na gaji da mafarkinki a kullum, ina so mu fara rayuwar gaske."

Khairat dake sauraren wak'ok'i bata jin me yake fad'a, amma shi duk da yana magana ne amma yana jin wata siririyar murya na tashi a kusa dashi ana rera waka , juyawa yayi ya kashe wayar yasa aljihu tare da rumgume bishiyar ya lek'a kanshi a hankali dan ganin me wakar, yanda ya rumgume bishiyar yasa hannunshi ya d'an shafi kafad'arta hakan kuma yasa ta juyo da sauri, manyan idanunsu ne suka sarke dana juna suna kallon kallo, babu wanda baiji fad'uwar gaba ba a cikinsu amma sai suka basar.

Babu wanda yace wani abu kuma babu wanda ya d'auke kanshi, Khairat ce taja tsaki tare da maida kallonta ga wayarta ta ci gaba da abinda take, yana ganin haka ya tab'e baki shima ya koma hanyar daya fito, Biba ce ta masa izinin zama sannan taje ta sanar da Mamie bak'onta ya zo.

Yana cikin kallon hadadden falon yaji bud'a k'ofa, maida kallonshi yayi ga nutsatsiyar matar mai dattako, tsaye ya mike yana murmushi ita kuma ta masa izinin zama, cike da girmama juna suka gaisa kafin Mamie ta kalleshi a tsanake.


Hakika Umar Faruk ba zaka kirasa da kyakyawa ba ajin farko, amma dai dole ka kirashi kyakyawa na farko a aji na biyu, manyan idanunshi masu firgita mai kallonsu da kuma saka kwarjini, haka kuma bak'i kuma yalwataccen sajenshi ma ya k'ara masa kyau, kana ganinshi zaka san jarumin namiji dan suffarshi ma ta zaratan maza ce, daga tafiyarshi kuma zaka gane ingarman dokine mai tashen k'uruciya a jika.

Murmushi Mamie tayi tace "Umar Faruk, ranar ka taimakemu amma kuma saika tafi ba tare da mun maka godiya ba, kome yasa kayi haka?"

D'an murmushi yayi yace "Hajia ni na taimakeku ne saboda Allah, bana buk'atar ku gode min."

"Duk da haka Umar Faruk muna godiya sosai da irin taimakon daka mana, amma dan Allah tayaya akayi kasan da mutanen nan?"

Kallonta yayi yace "Hajia da mun bar duk wannan maganar, tunda dai masu laifin sun shiga hannu."

"Hakane, amma zan iya sanin meke tsakaninka da Khairat?"

Murmushin gefen labb'a yayi yace "ba komai Hajia."

"In tambayeka mana idan ba damuwa?"

"Uhum, ba damuwa."

"Dan Allah kana da aure?"

"A'a, amma dai nakusa insha Allah."

"Allah yasa alkairi."

Ya amsa da "ameen, na gode."

Kallonshi tayi tace "amma misali, idan nace zan da Khairat, kana ganin zaka yarda ka aureta?"

Kafeta yayi da ido da tsananin mamaki, ba zai iya yi mata qarya ba
Showing 21001 words to 24000 words out of 186119 words