ya nemeta tunda itace a gabanshi yanzun, wannan shawara da Mama ta bata bata anfaneta da komai ba sai k'unci, shareshin da tayi yasa shima zuciya ta d'ebeshi ya shareta, idan ya shigo kwanciyarshi kawai yake yayi karatu daga nan bacci ya daukeshi, sam ya daina nemanta tsakaninshi da ita kawai gaisuwa, sai maganar ci abinci ko sannu da zuwa, duk da hakan na damunta amma bata nuna masa, kuma gashi an horeta akan karta kulashi ita shine zai kulata, shi kuma yana ganin ai shine namiji kuma yayi iya qoqarinsa amma bata bashi had'in kai, hasali ma nuna ya gundureta take shi kuma baya jin dad'in hakan.

Ana cikin hakane kuma ta koma Γ©cole, shike ajeta kafin ya wuce wajen aiki, kasancewar ranar juma'a ce hakan yasa ya biyo ya daukota, kuma tun safe ta fajimci yana cikin farin ciki, kuma tasan yana farin ciki ne saboda yau kwana uku, a lissafinta yau Khairat zata dawo, to amma ba komai tazo duk da haka ai kwananta bai qare ba, a fa tunaninta.


Har yamma Umar Faruk na gwada kiran wayar Khairat amma bata shiga, hankalinshi ne ya fara tashi amma daya tuna dama ita ke kiransa bashi ba saiya kwantar da hankalinsa.


***************


Tashin dare jirginsu zaiyi, tare take da Mammie da Mamie da Papa zasu shiga acessaire (lift), mutane suka samu sun shiga, ganin sai sun jira yasa Khairat kama hannu Mammie cike da karsashi tace "kawai muje a matakalar haba, kinga saimu motsa jiki."

"Ke ke, rabu dani dan Allah, ba zan iya ba, jiri nake gani idan na hau." haka Mammie ke fad'a tana bin bayan Khairat data ja hannunta.

Haka suka fara takawa a hankali, ganin yanda Mammie ke rik'e da wajen take takawa a hankali yasa Khairat sakin hannunta ta fara takawa da sauri tana sauka tana fad'in "saimun shekara bamu kai qasa ba in muka bi ta taki."

Tana kusa da sauka taji qarar Mammie, da sauri ta juyo ganin Mammieta fad'i qasa yasa ta jefar da jakar hannunta ta ruga a guje ta qarasa, "Mammie, lafiya, meya faru ne Papa?"

Suna cikin jajen abinda ya faru saiga ambulance har ankira musu saboda anan ba wasa da lafiya, babban asibiti mai kyau aka kaisu, bayan duba Mammie aka basu izinin zasu iya tafiya, amma tana buk'atar hutu sannan ba'a so ta taka qafarta, kuma gashi bayanta ma ya bugu shima an d'orata akan magani, wayar Umar faruk ta fara kira danta fad'a masa halin da ake ciki, bugu d'aya biyu ana uku aka d'auka.

"Hello baby." cewar Khairat cikin taushin murya.

A gadarance Zuby tace "baby dai, waye babyn to, ke yanzu wannan ya miki kama da qaramin yaro? to yana hutawa kuma yace baya buk'atar takurawa bare a tasheshi daga bacci, dan haka ya bani ikon na d'aga wayar duk wani qare da jaki daya bugu masa."

Tana fad'a ta kashe wayar ta aje tana dariyar mugunta, da sallama ya shigo d'akin yayi wanka tare da d'auro alwala, bai kula da komai ya fara shirinshi tana zaune tana kallonshi, har saida ya gama shirinsa cikin wani farin yadi shara shara mai kyau wanda ya amshi jikinshi, machette ya d'auka tare da hula da agogo ya nufi inda Zuby take ya bata, karb'a tayi tana kallonshi shima ita yake kallo.

"Me zan maka dasu?" ta fad'a cikin rashin fahimta.

"Ke yanzu har saina fad'a miki me za kiyi? saka min za kiyi to, tunda naga ke baki tab'a tunanin tayani shiri ba bare nasa ran wata rana zaki min shirin da kanki ma."

Aje kayan tayi a saman gado tace "oho, kana fad'a min yanda waccen karuwar take maka ne? to ba zan iya ba, saika jira idan tazo saita maka har wanka ma idan kana so."

Wata irin tafarfasa yaji zuciyarshi nayi, a qufule yace "Zubeida na fad'a miki karna sake jin kin kirata da karuwa ko, kuma idan ma karuwar ce ai tawace, dan haka karna sake ji, idan ba zaki iya abinda na saki ba ki bari amma ba sai kin fad'a min magana ba."

Tsaki yayi ya d'auki kayanshi ya fara mak'alawa ita kuma ta d'ora da "ba zan daina kiranta karuwa ba tunda ai karuwar ce, dama kasan ina da haushinka wallahi shiru kawai na maka, bansan dame waccen karuwar ta fini ba da har kafi sonta a kaina ba."

Rintse ido yayi yace "karki sake fad'a mata karuwa."

"Saina fad'a d'in, me zaka min?"

Wata zuciyar ce ta d'ebeshi ya kifeta da wani marin da saida ta fad'a kan gado, duk da ta fashe da qara amma sam bata ji ba saboda jinta ya d'auke, da hannu ya nunata yace "wannan ba d'abi'arki bace, ki sake hali inhar kina so mu zauna lafiya dake, ke kinfi kowa sani na bana d'aukar raini, amma na lura dake tun ranar da kika ganni ba kaya a gabanki, kika rainani ko kuma nace aka saki kika rainani, to wallahi ba zan d'auka ba, ke kinsan waye Umar Faruk."

Ko sallaya bai d'auka ba ya fita ya bar gidan, kuka ta dinga rerawa har Ruk'ayya dai taji abin yayi yawa ta shigo ta sameta, daga tsaye ta dafa kafad'arta tace "Zuby, yaya ne ko?"

Shiru tayi dan haka tace "dan Allah kiyi hak'uri ki daina kuka, idan Mama taji ba za taji dad'i ba kema kin sani, kuma ya kamata ki dinga bin yah Umar a hankali, tunda ke kinsan halinshi da zuciya da hushi ga kuma saurin hannu, dan Allah ki daina kukan nan kiyi shiru ki rabu dashi."

Ko motsawa ba tayi ba bare ta amsa mata, dan haka ta fita daga d'akin tana mamakin Zuby, dan bata santa da haka ba kuma duk da bata shiga harkarsu, amma dai ta d'an fahimci akwai matsala a tare da ita, dan ko zaune suke tsakar gida yah Umar ya shigo, sai dai ya wuce d'aki shi kad'ai ita kuma sai dai tace sannu da zuwa daga nan inda take zaune, ba zata tashi ba inba wani babba yace ta tashi ba, haka ko d'akin ta shiga idan suna tare, sai dai ta sameta ita akan gado shi akan kujera, koshi a kujera ita akan gado sam ba zaka gansu kusa da juna ba, sab'anin Khairat da zata samesu daf da juna wani lokaci ma ko qafafunshi akan jikin Khairat d'in ko ita nata qafafun, da wannan tunanin dai ta shiga harkar gabanta.


***************

Yana fita ya fad'a mota dan yanzu ya barwa Aliyu motonshi, kasa tayar da motar yayi saboda zafin da zuciyarshi take, ji yake kamar ya d'auki mataki marar dad'i akan Zuby, danshi baya son matsala ko kad'an, ganin yake akan me Zuby da quruciyarta zata lalata kanta ta zama kamar wata tsohuwa, yana nan inda yake wayarshi ta sake ruri, yana dubawa yaga farin cikinshi ce, itama kuma ta maido kiran ne dan bata yarda da abinda Zuby ta fad'a ba, yana ganin lambar ya d'auka jiki sanyaye ya d'ora a kunne.

Shiru tayi saboda tana so ta tabbatar dawa ya d'auki wayar yanzu, jin shiru yasa yace "Hello."

Jin amon muryarshi ba karsashi ba kamar yanda ya saba ba yasa tace "baby, meya faru, waya tab'a min kai ne?"

D'auke wayar yayi daga kunne ya kalla sannan ya sake mayar da ita yana fad'in "me kika gani?"

"Baka cikin farin ciki, ni kuma ba haka nake so ba, fad'a min waya tab'a min kayana, yanzu shima ranshi ya b'ace."

Wata tambaya ce zuciyarshi ta wurgo mishi _"anya kuwa Zuby itama tana sonka?"_

Basarwa yayi yace "tabbas, bana cikin farin ciki, amma ki barshi kawai."

"Haba dai, bana da hankali ne da zan barka a wannan halin, kaga ina zuwa, yanzu kayi connectΓ© kaga abin mamaki."

"A'a Khairat, ba yanzu ba, masallaci zanje yanzu."

Cikin d'aga murya da raha tace "a'a ban yarda ba, kawai kayi abinda nace, ba zan tab'a barinka kaje masallaci cikin b'acin rai ba."

"To naji." ya fad'a ba annashuwa a tare dashi."

Yana d'orawa Khairat ta kirashi appel vidΓ©o, d'auka yayi amma a take ya lumshe idonshi, ganin haka yasa Khairat bushewa da dariya tace "bud'e ido malam Umar Faruk."

Bud'e ido yayi ya sauke akan qirjinta daya fito yayi fam, saboda wata qaramar bras ce tasa wacce ta matse qirjinta ya fito sama, sai kuma qaramin wando iya cinyarta shima, ga gashinta data baza a bayanta ba zaka tab'a rabata da larabawa ba ko india, d'an yatsanta tasa tana yawo dashi akan fuskarta harta saukar dashi akan bakinta sannan tasa yatsu biyar ta sumbata tare da kashe mishi ido ta kuma watsa mishi sumbatar.

Wani irin narkewa yayi a kujerar motar yana d'an cije lips yana marairaicewa kamar zai fashe da kuka, ganin ta fara kamashi yasa ta tashi tsaye ta aje wayar yanda suke kallon juna da kyau ta fara taka rawa irinta india cikin qwarewa da iyawa tana rera wak'ar *humsafar*.

_Mere tu sare savere._

_Baho me tere tehre._

_Mere tu sare shave._

_Mere sat nahi hai_

Da irin haka ta dinga karairaya jikinta tana rawa (in baku manta ba gogagiyar 'yar rawa ce ko a india), saida ta gama ta koma ta kwanta Umar Faruk kuma wata azababbiyar sha'awarta ce ta taso mishi, da qyar ya fizgi muryarshi yace "baby....yaushe...zaki dawo..gareni?"

Kafin ta bashi amsa wayarshi ta d'auke babu caji, dole ya hak'ura ya lik'a wayar a cajin dake motar a haka ya tayar da mota ya matsa k'ofar gidansu Ishaq ya fito suka wuce , duk da ya shiga farin ciki, amma kuma ta barshi da ciwo.

Haka yaje masallaci ya dawo ba qwarin jiki, saida Ishaq ya shiga gida ya fito suka sake wucewa wajen aiki tare, babu abinda yayi sai ganin Khairat a wannan yanayin, shi dai kawai ya sani koma karuwanci ne Khairat ke masa, to tabbas yana son wannan karuwancin, a haka suka tashi yana tunanin idan ya koma zai sameta tazo, amma kash yaje ba Khairat, hakan yasa tunda yayi sallah magrib ya fara kiran wayarta amma shiru.


Khairat kam na d'akin Mammie suna hira har saida tayi bacci, sannan kowa ya koma d'akinshi, tana zuwa kuma bacci itama ya d'auketa....


**************

Saida safe yana wajen aiki ta kirashi take fad'a masa abinda ya faru, cikin rashin jin dad'i yace "ayya, dan Allah ki gaishe min da amaryar, kice ina mata sannu."

"Zan fad'a mata insha Allah."

"Yanzu kenan yaushe zaki dawo?"

"Ai tare zamu taho idan taji sauk'i."

"To, ya zanyi? sai hak'uri, Allah dai ya bata lafiya."

"Ameen."


*************

Mamie kuma naci gaba da koya mata girki da kalan jus da wasu abubuwan tab'awa, a haka suka qara kwana biyu kuma a ranar suka sake shirin tafiya, Khairat ce ta fita tace zatayi siyayya kafin su wuce...

_Me kuka ce fan's?_

😍😍😍
14/08/2019 Γ  15:32 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


4⃣2⃣


Tunda ya shigo haka ya gama duk abinda ya saba amma babu wanda ya kula wani tsakaninshi da Zuby, ganin babu ko plate akan tebur yasa shima ya shareta bai mata maganar abinci ba, akan kujerar ya kwanta yana latsa wayarshi, a hankali yake duba photunan da suka d'auka da Khairat musamman wanda take sanye da hularsa, haka ake kwance abinshi har gari ya waye.



Washe gari ma tare suke shiri da ita amma babu mai kallon wani, har saida suka gama ta d'auki jakarta zata fita a daqile yace " haka zaki fita baki karya ba?"

Saida ta harareshi tace "kana da matsala da cin abinci nane? "

"A'a, kije."

Yana fad'a yayi wuf ya fita daga d'akin ya barta tana rufewa, kosu Mama bata kalla ba ta wuce, su kuma da kallo suka bita yayin da sukansu suke tunanin, yaushe Zuby ta zama haka marar kunya, suda suke zaton wuta a maqera sai kuma su ganta a masaqa, k'ofar gidan ta sameshi ya paka motar da alama ita yake jira, d'auke kai tayi ta kama hanya ta nufi bakin titi, kallon kan bala'i ya bita dashiπŸ˜‚ da tsananin mamaki, yana kallo harta kai bakin titi tana jiran taxi, kai ya girgiza ya taka motar da k'arfi, yana kaiwa kusanta ya kawar da kanshi kamar baisan da wata halitta ba a wurin ya wuce, ganin ya wuce yasa ta bishi da kallo baki bud'e, dan tunaninta zai biyota ne kuma ya bata hak'uri, a ranta tace "anya Mama ta bani shawara mai kyau, karfa na tsaya jan aji da hauka Umar Faruk ya sub'uce min."

Da qyar ta samu taxi hakan yasa taje a makare, ta kuma yi niyyar idan aka tashi kai tsaye gida zata je ta fad'awa Mama, dan ba zata iya da wannan shawarar ba, gashi duk da ta saka mishi magani a abincin amma bata ga wani canji ba, kuma itama tayi wanka da wanda aka bata amma shiru, na wajen Khairat ne kawai ya rage tayi aiki dashi, kuma duk kusantar da yake mata bai nuna yana wani jin dad'in da zai iya kasheshi, a tak'aice dai bata ga wani anfanin abubuwan da take yi ba.

************

*13:20* ta shiga gida, zaune ta samu Mama akan tabarma tana cin wake da shinkafa, jefar da jakarta tayi har tana neman buge Mama sannan ta zauna tana cire hijab da d'an kwali, Mama kallonta take harta d'auki ruwa tasha kafin ta aje tace "Mama, akwai matsala fa?"

Cikin harara Mama tace "to ke kuma dan ubanki, baki gajiya da matsala ne, me kuma ya faru yanzun?"

Cikin turo baki tace "Mama, sam shawarar da kika bani ba tayi ba, haka ma wannan magungunan naki babu abinda suka qara mana, yanzu haka maganar da nake miki yah Umar jiya marina yayi, kuma har yanzu bama magana ko kulani baiyi ba."

"Mtsssss." shine dogon tsakin da Mama tayi.

"To shine me, dama wannan ce matsalar, waike yaushe zakiyi hankali? kina mace amma sam ba kyada aji da kama kai, to yanzu me kike so na miki da kika zo nan so kike nace kije ki masa magana ko? to kiji yarinya, kamar yanda nace karki yarda ki kulashi, ki barshi zaiyi ya gaji ya dawo gareki , kuma karki qara cewa magungunan dana baki basuyi ba, sai dai in kece ki kayi ba daidai ba."

"Mama, wallahi duka nayi yanda ya dace, kawai dai ba sa'a ne wallahi, nifa gaba d'aya na rasa me yake damun yah Umar, wallahi ni harma na fara tsanarshi, kwata kwata bana son zaman gidanshi ma duk na fara takura."

"Ke! fita idona wallahi, ke kinsan me kike fad'a kuwa? to kima cire wannan tunanin a ranki, dan aurenki dashi mutu ka raba ne takalmin kaza, wallahi kina gidanshi har sai yayi kud'i kuma mun moreshi."

Da mamaki tace "kud'i kuma Mama, an fad'a miki zaiyi kud'i ne?"

"Ke kuma a tunaninki nan zai zauna baiyi kud'i ba?

"Aina jima da sanin zaiyi kud'i, shi yasa ma na shiga na fita na had'aku aure."

"Tohh, lallai, nidai yanzu kawai kisan ya za kiyi dani wallahi, danni rainin hankalinshi ya fara isata."

Cikin sassauta murya Mama tace "yana kusantarki kuma?"

Cikin jin kunya tace "Mama fa tun ranar da waccen karuwar ta tafi bai qara neman wani abu wajena ba."

"Bai nema ba kodai baki bashi ba?" ta fad'a cikin d'aga murya.

Sosai kai tayi tace "eh to, amma aike kika ce na dinga jan aji, kuma ni wallahi bana ma son yana kusantata, saboda...."

"Saboda me?"

Cikin yamutsa fuska tace "kefa Mama baki sanshi ba, wallahi jaraba ce dashi, baya da aiki sai lagudar mutum, gashi inya fara baya dainawa sai yaga ya maka liqis, gashi da tsinannan k'arfi, ga...."

*Wal'iyazu billah, towana miji asiri irin haka, abin yayi muni yan uwa, kuma ace uwar ta kasa kwab'arta , nidai ba zan iya fad'a ba gaskiya* 😏

"To kinsan me za ayi? yanzu zan sake komawa wajen malam na fad'a mishi komai, ina tabbatar miki wannan karan, ba sauk'i a al'amarin dan aiki zansa yayi sosai."

Shiru tayi hakan yasa Mama cewa "waini ke kad'ai ke zuwa ecole d'in?"

"A'a Mama, shi yake kaini, yaune na tafiyata saboda bama magana."

"Da motar tashi yake kaiki ko motar waccen karuwar?"

"Haba Mama, nice zan shiga motarta, da tashi muke zuwa."

"Hum, aini fa wannan tsinnaniyar motar ma saina sa an faffasata kafin ta dawo."

"Mama rufa min asiri, jiya fa saboda nace mata karuwa ne ya mareni , idan kin fasa mata mota kuma sai dai ya sakeni, dan wallahi na fahimci yafi sonta a kaina."

"Ai kuwa za kiga me zanyi, kuma wallahi saina raba tsakaninsu, ni na fad'a miki wannan maganar."

Kiran Umar Faruk ne ya shigo wayarta, dan yaje gida abazata bai sameta gidan ba, hakan yasan ya kira dan yaji ina taje....


_Kafin muji me za tace mishi, zamu waiwaya baya muji tarihin mahaifiyarsu Zuby ._


*WAIWAYE ADON TAFIYA*


*Fatima* shine sunan mahaifiyarsu wato kakarsu Umar Faruk, mahaifinsu kuma *Mamman*, sun haifi yara biyar hud'u mata *Khadija, Asma'u, Maryama, Zeinabu* sai kuma autansu namiji mai sunan *muhammad Sani*, yaran sun samu tarbiya da kuma ilimi na boko da addini, kasancewar mahaifinsu yasan anfanin ilimi, kuma cikin ikon Allah sun sameshi yanda ya kamata, sai dai matan basa wani zuzzurfan karatu ake aurar dasu.

Suka yaran suna aiki da tarbiyar da iyayensu suka basu amma banda Asma'u, tun tana yarinya iyayensu suka fahimci bata da kirki kamar sauran yaransu, sam bata da ragowa ga yan uwanta gata da masifar fad'an tsiya, ga kuma son kud'i da tijara akansu, saboda son kudinta yasa ta kasa fitar da mijin aure har saida ta samu zabinta , a lokacin kuma har qanwarta Zeinabu ta isa aure, dan haka aka had'asu tare aka aurar dasu.

*Hamza* shine wanda wannan hau ta fad'a ma, a waccen zamanin yana d'aya daga cikin masu kud'in da ake ji dasu, amma aurenshi da Asma'u saiya zama silar tarwatsewar komai, ta samu ragama da akalarshi tana juyawa yanda ranta yake so, bata d'aga masa qafa ba wajen rabashi da yan uwanshi dama mahaifiyarshi d'aya da yake da ita a duniya, hatta fita sai taga dama take bari ya fita, hakan yayi sanadiyar raba alak'arshi da abokan harkokinshi mak'ota da abokan arzik'i, sannu sannu kuma sai arzik'inshi ya
Showing 114001 words to 117000 words out of 186119 words