ya kasa komai sai tunanin wannan daren yake.

*Safiya* nayi ya shirya kamar yanda ya saba ya fita sai dai yau ma'aikatar ya tafi dan jin meke faruwa, da sameshi ko sai yayi sa'ar ganin manager a farfajiyar wajen zai shiga mota da alama fita zaiyi, da sauri ya karasa suka gaisa kafin manager yace "Faruk ashe kana nan ka daina zuwa aiki?"

Kai ya shafa yace "eh yallabai ina nan, nasan ko nazo ba zata barni ba shi yasa ma bana zuwa."

"To yanzu meya kawoka?"

Nan ma kai ya shafa yace "yallabai nazo ne naji meke faruwa anan? dan jiya Baba ya sameni yana fad'an wasu maganganu da ban gane ba."

"Kamar me kenan?"

Shiru ya d'anyi sai kuma ya kalli saman ginin yace "Hajiar tana ciki?"

Da mamaki yace "Umar Faruk, kar dai kace min baka san meke faruwa ba? Hajia Khairat ai yau kwananta hud'u bata fitowa."

Dammm , yaji gabanshi ya tsinke ya fad'i, saida ya had'e yawu yace "to meya sameta?"

Ajiyar zuciya manager ya sauke yace "yanzu dai kaga ganinta ne zanje, idan zaka iya mutafi tare mana?"

"Ganinta kuma, a ina?"

"Asibiti."

Ji yayi duk ba dad'i sai kawai yace "ba damuwa muje."

Zagayawa yayi ya shiga motarshi suka d'auki hanya tare, amma ya rasa dalili sai yaji zuciyarshi na bugawa d k'arfi ga gabanshi dake ta fad'uwa babu gaira babu dalili, a haka suka isa asibitin jami'in dake tsaron k'ofar d'akin yana ganin manager ya kauce masa ya wuce amma saiya hana Faruk, manager ne yace "dan Allah abokina ka barshi ya wuce, dani dashi duk d'aya ne."

Cewar jami'in "gaskiya ba zai wuce ba wannan doka ce, kayi hak'uri ka koma."

Papa ne yaji maganarsu daga cikin d'akin dan haka ya lek'o duk da baiga ko suwaye ba amma kawai sai yace "barsu su shigo kawai."

Da sallama suka shiga amma sallamar Faruk saita tsaya cak saboda ganin Khairat a wani hali na daban, cikin sanyin jiki da rauni ya k'arasa gaban gadonta ya tsaya yana kallon fuskarta dake d'aure da bandeji , Papa kuma d'akin kusa dana Khairat ya shiga in da Mamie take kwance, a hankali ya kalli manager yace "meya sameta haka, hatsari tayi?"

Kai kawai ya girgiza masa, sake maida kallonshi yayi gareta yana k'ara jin tsoron ubangiji na shigarshi, wai wannan matashiyar mai tsiwa da girman kai da raina mutane yau gata kwance, ta sauya kamanni kamar ba ita ba duk kusan rabin jikinta bandeji ne sai jini, bin qafarta yayi da kallo wacce tayi sumtum da ita ta kunbura , kallon yatsun qafar yayi wanda suka sha akaihu da kalar pink, kallon fuskarta yayi idonta rufe gashin idonta duk ya kwanka luf kamar na kanti, wata har sharasharar rigace fara aka lak'aba mata.

Suna haka wayar manager tayi k'ara dan haka ya fito da ita ganin mai kira yasa ya fita daga d'akin dan amsa wayar, kujerar dage gaban gadon Faruk ya zauna yana kallon k'afarta dake rataye da gado tasha k'arafa saboda dorin da aka mata haka ma hannu, sosai zuciyarshi ta karye saboda ganin halin da take ciki, sama sama ya fara jiyo murya daga d'aya d'akin ko ba'a fad'a masa ba yasan muryar iyayenta ne, tsaye ya tashi saboda ji da yayi muryoyin na sake sama kuma kamar zasu fito daga d'akin.

Juyawa yayi da nufin barin d'akin kawai yaji har sun fito, muryar Mamie ce ta fara magana cikin tsananin kuka da fitar hayyaci ta nuna Khairat dake kwance tace "ka dubi yarinyar nan dake kwance waya ja mata shiga wannan halin? kaine duk kaine sila."

"Ka sani wallahi jira kawai nake 'yata ta samu sauk'i mu raba kanmu da kai , dan in har zamu ci gaba da zama da kai , to ya zama dole sai mun shirya karb'ar bala'en da suka fi wannan, bansan me yasa nayi wannan kuskuren ba duk da na karanta cewa bai hallata ba zama da fasik'i ba, yau gashi abinda ka shuka yarka ta fara girbarshi, gashi gyaran kuskurenka zai zama alhakin 'yarka, to sam ba zan yarda ba wallahi, dole ka sakeni nayi nesa da kai da yata dan mu tsira da rayuwarmu da lafiyarmu."

"Ka dubi k'ask'ancin da aka mata, nasan ko kai baka tab'a shigar da 'yar wani a wannan halin ba, amma yau gashi yarka mutum d'aya d'aya har guda hud'u ne suka keta mata haddi , yanzu haka ya maka daidai kenan? kaji dad'i?"

Duk da kuka yake amma cikin dakakkiyar zuciya yace "Na'ima, wai me yasa kike da taurin kaine? me yasa baki da yafiya a rayuwarki? tunda abin nan ya faru nake baki hak'uri amma kinki hak'ura, na rantse miki da Allah Na'ima nayi nadama kuma na tuba ga Allah, wallahi ba zan sake aikata sab'o irin wanda nayi a baya ba, dan Allah Na'ima ki sake bani dama mu sake sabuwar rayuwa, muyi fatan ganin Khairat ta samu lafiya, ni kuma na miki alk'awarin saku farin ciki sannan zan samar ma Khairat miji na gari na had'ata dashi, kuma wallahi daga yanzu duk abinda ki kace nayi zanyi Na'ima amma banda rabuwa dani."

Murmushi tayi tace "oho , kenan sai yanzu zaka fara maganar yi mata aure, kenan yanzu ne kake ganin Khairat ta isa aure? to kai a ganinka waye zai yarda ya aureta a yanzu bayan ta rasa kimarta , ai kowane namiji yana alfahari ace shiya fara sanin matar daya aura, wallahi Mani duk wanda kaga ya auri Khairat a yanzu to abu d'aya ne, shine dukiyarka, amma duk wanda ya auri Khairat dan Allah to ka sani wallahi taimakonta yayi kuma *JIHADI* yayi."

Juyawa tayi ta zauna kusa da Khairat ta fara shafar kanta tana zubar da hawaye, shima Papa hawayen yake yi yana kallonsu, Umar Faruk kuma ya kasa motsawa saboda tunanin kamar basu lura dashi ba ma a wajen, baya baya ya fara ja yana so ya sulale daga wajen kawai yaji an bud'o k'ofar an shigo, ya dauka manager ne ashe Kakar Khairat ce ta zo daga India, maida kallonsu sukayi gareta da sauri duk suka tashi kowa na fad'i "Mammie, yaushe kika zo?"

Hannu ta d'aga musu tana kallon Khairat dake kwance a tsananin mamaki, bata d'auke idonta akan Khairat ba tace "meya samu gimbiyata? me kuka mata?"

Mamie ce ta fara kame kame tace "Mammie babu komai fa, ta samu wani d'an hatsari ne."

Cikin d'aga murya tace "wane irin hatsari ne wannan? zaku fad'a min gaskiya ko saina tsine muku albarka."

Da sauri Papa yace "a'a Mama, dan Allah kiyi hak'uri, wallahi..."

Kuma sai yayi shiru, ganin Mammie ta kafe Mamie da ido yasa ta fara i'ina tana fad'in "Ma...ma wa...sune..suka , wasu ne....suka, suka mata fyad'e." ta k'arasa da fashewa da kuka.

A nitse Mammie ta k'arasa gaban gadonta ta durk'usa tana shafa kanta tana zubar da hawaye, kuka suke sosai babu wanda yake bawa wani hak'uri a cikin wannan hali Umar Faruk ya sulale ya fita, a farfajiyar wajen ya samu manager yana waya , saida ya jira ya gama suka shiga mota suka wuce in banda tunanin halin daya ga Khairat da abinda yaji mahaifiyarta ta fad'a babu abinda yake, a haka har suka kai ma'aikatar manager yace kawai ya shigo yaci gaba da aikinshi kafin Allah ya bata lafiya.

Nan ya shiga ya kuma zauna mazauninshi, abokinshi Ishaq da wasu ma'aikatan mata da maza ne suka taru suna tattauna abinda ya faru da Khairat d'in, d'aya daga ciki ne yace,

"Koda dai har yanzu babu tabbas, amma duk mai hankali ai zaiyi zaton wani abu."

"Gaskiya ne, wallahi abar tausayi, nasan tana cikin wani hali ne shi yasa ma ba'a bari a ganta."

Wata matashiya ce tace "wacece abar tausayin? Khairat d'in, ni kuma wallahi ko kad'an banji tausayinta ba, dan nasan ba wani mummunan abu bane a wajenta."

Faruk ne ya kalli matashiyar ya taso ya tsaya gabanta, duk da yana k'ok'arin tausar kanshi, amma haka kawai yaji zuciyarsa na masa zafi akan abinda suke fad'a, basu san da zuwanshi ba sai muryarshi suka ji yace "wannan maganar bata dace ace ta fito daga bakinki ba a matsayinki na mace, tausayi da jimami ya kamata a gani a tare dake, kamata yayi ace kinji cewar an tab'a kimarki kema saboda 'yar uwarki mace aka tab'a, ki tuna fa kema macece kuma bana miki fata, amma kema kina cikin wannan k'alubalen dan haka zata iya faruwa dake, dan Allah ku dinga kyautatawa juna zato."

Tab'e baki tayi ta kau da kai tana fad'in " ni dai nasan ina zaune da kowa lafiya, kuma kamar yanda na fad'a a baya bana jin Khairat wani sabon abune ya sameta bare kuma taji zafinshi."

Sake gyara tsayuwa yayi cikin b'acin rai da d'aga murya ya fara magana "bata jin zafi kike cewa? kinsan me fyad'e yake nufi? shin kin tona zuciyarta kinga me take ji? shin kin tab'a kwatanta me zaki ji a zuciyarki ace namijin da baki had'a komai dashi ba ya tursasaki ya kusanceki? kefa macece, ki misalta kona second goma kiji me zaki ji a zuciyarki."

"Shin kinsan halin da take ciki? kin ganta da idonki bare kisan me take ji? kije, kije kiga halin da take ciki, kina gani nasan dole ki yarda tana cikin wani hali, kinsan zafin karaya a hannu bare kuma a qafa? shin kin tab'a yin hatsarin da yasa kika ji raunika? to ita a sanadiyar abinda ya faru tana can kamar wacce babbar motar ta bige, dan Allah ki sawa zuciyarki tausayi kodan kasantuwarki mace."

Yana fad'a ya bar wajen ya fita farfajiya zuciyarshi in banda tafasa ba abinda take, ji yake kamar zai fashe da kuka amma kuma ya kasa, a hankali ya tambayi kanshi "wai me yasa ka damune? Khairat ce fa."

Saida yasa hannu ya goge idonshi da yaji sun cika da k'walla sannan yace "rashin imanina bai kai na kasa tausaya mata ba."

*Haka* Faruk ya kasance cikin wannan damuwa da tunani har yaje gida, haka ya dinga tunanin abinda idonshi suka gane mishi a ranar, kai da kawo yake a tsakiyar d'akinshi yana fad'in "rigarta, wannan saurayin, matashin da yazo daga baya, d'aukewar wuta, dawowar wuta bayan qanqanin lokaci, b'atan Khairat, sai kuma....sai...sai kuma me?"

Ci gaba yake da kai da kawowa har saida ya tsaya cak baki bud'e ido waje, a hankali ya furta "wannan motar, wannan *CRV Honda* d'in, tabbas akwai alamun tambaya akan wannan motar, me yasa take gudu a cikin wannan daren, sannan ina suka nufa da suka ratsi wannan jejin?"

"Dole nasan wani abu a game da motar nan, dole na koma wajen nan."

Wata zuciyar ce kuma tace "to wai akan me? ka barsu da matsalarsu mana."

"A'a, ka tuna fa kana k'annai mata dayawa, ya zaka ji idan d'aya daga cikinsu ce? koda namiji d'aya ne ba zaka ji dad'i b bare har hud'u saboda rashin imani, zanyi wannan taimakon a matsayin *jihadi* fisabilillah."

_To Umar Faruk Allah ya bada sa'a._
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ
_Farin ciki auntynmu ta dawo, *ASMA'U GALADIMA* (ummu Maryam), marubuciyar *Dijah Qaya* ina miki barka da dawowa._


_Bismmilahir-rahman-rahim_

_Allahumma antas- salam, waminkas-salam, tabarakta ya zuljalali wal- ikram._


9⃣



Har gaggawa yake gari ya waye, alwala yayi ya fara tsayuwar dare kamar yanda ya saba, ya jima yana sallah har aka kira asuba sannan ya nufi masallaci tare da sauran 'yan uwanshi, saida gari yayi haske suka dawo yana zuwa shiryawa yayi ya fita ko kari baiyi ba, kai tsaye asibiti ya nufa dan yana so ya d'an samu wata makama da zai iya dafawa a matsayin k'warin gwiwarshi.


Sammakon da yayi yasa ya tarar da Papa a k'ofar d'akin da Khairat da Mamie suke tare dasu Musa bayan sun fad'a masa har yanzu basu samu wani abu ba, cikin b'acin rai da sassauta murya yace,

"Wannan ai maganar banza ce, ba zai yiwu ba, ku dubi Khairat nan fa kwance har yanzu bata farka ba, me kuke so nace mata idan ta kalleni? to kuji wallahi ku shiga duk in da zaku shiga ku nemo min 'yan iskan nan, idan ba haka ba ranku ne zai b'ace, kunji na fad'a muku."

Yana fad'a ya koma cikin d'akin su kuma suka jiyo Musa na fad'in "kaji d'an wahala, to ya zaiyi in bamu samosu ba? dole dai a qarshe ya hak'ura tunda ba mik'a k'anmu zamuyi ba muce mune muka mata fyad'en."

Da sauri Faruk ya juya yana binsu da kallo matuk'ar tsoro ya bayyana a fuskarshi sosai, yana kallo har suka shiga motarsu CRV Honda, hannu yasa ya rufe bakinshi yana fad'in "inna lillahi wa'inna ilaihir-raju'un."

Juyawa yayi ya koma ya hau mashin d'inshi dan baya da hujjar da zaice sune kai tsaye dole ya samu wata makama da zai nuna eh sune, saida ya koma har club d'in nan sannan ya fito ya d'auko hanyar, a hankali yake tafiya yana dube dube har saida ya kawo wajen da motarnan ta shiga kwana, nan yabi yana waige waige yana dubawa ko zaiga gida da makamantansu, wasa wasa dai bai samu komai ba har saida hanya ta b'illo dashi kusa da unguwar airport, ganin idan ya koma baya zai maida kansa baya ne kawai saiya shiga kwanar da zata sadashi da titi, zai hau titi kenan motar su Musa ta shigo kwanar suka nufi hanyar daya fito, da sauri ya taka birki ya juya yana kallonsu, bai b'ata lokaci ba yabi bayansu har suka tsaya k'ofar gidan da Papa ya basu duk lokacin da suke bakin aiki.

Nesa da gidan ya tsaya da tunanin ko zasu fito, amma shiru shiru su Musa basu fito ba har suka kwashe awanni uku, tun yana gyara zama akan mashin d'in har ya kai gayin kwance a sama nan ma ya gaji ya sauka ya aza takalminshi ya zauna qasa.

Su kuma suna ciki dama duk lokacin da Papa ya matsa musu lamba nan suke dawowa suyi kwancinsu su huta sannan su koma suce masa babu labari, _(rainin wayo)_, sai lokacin suka fito suka shiga motarsu sukayi gaba abinsu, anan ya bar mashin d'in ya nufi gidan, ganin k'ofar rufe take amma katangar gajera ce yasa ya tuna yarinta d'araf ya haye katangar ya haura gidan.

🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣


Ganin k'ofar falon itama a rufe take kawai yasa ya dinga bangazar k'ofar har saida ta bud'e da k'arfi, nan ya shiga d'akuna hud'u ne a ciki, kowane d'aki b'alle k'ofar yayi ya dinga bincikawa ko zaiga wani abu amma shiru, d'aki na qarshe daya shiga ganin bai samu komai ba yasa ranshi ya b'ace ya daki armoire (wradrob) d'in da k'arfi, abinka ga d'akin maza ba'a kimtsa komai, kayane suka zubo daga ciki.

Durk'usawa yayi zai kwashe kawai yaga wata bak'ar mask ta fuska, d'auka yayi ya kalleta da kyau yana tunanin ko meye anfaninta, zai mayar da kayan saiya sake ganin wata, dan haka ya sake dubawa saiga guda hud'u ras sun bayyana, kai ya girgiza ya mayar da kayan har da mask d'in sannan ya rufe wradrob d'in fito ya daga d'akin, maida k'ofar falon yayi ya rufe duk da bata rufu ba.

Har zai wuce kuma ya tsaya yana kallon poubelle (abun zuba shara) d'in wajen, cike da mamaki yasa hannu ya ciro rigar da koba a fad'a masa ba yasan ta Khairat ce dan itace a jikinta a ranar, duk rigar ta yage sosai ga jini a jikinta har da pant dinta da kuma takalminta duk a cikin sharar, ji yayi idonshi sun kawo ruwa amma saiya aje rigar ya da kayan ya fita ya bar wajen, gudu yake sosai akan mashin d'in har saida ya kai asibiti.

Ya samu 'yan uwa dayawa a wajen wanda ba'a bari shiga ba, mai tsaron k'ofar Umar ya cewa "dan Allah ko zan iya ganin yallab'ai?"

"Lafiya ko? yallab'ai yace kar a takura masa fa."

"Kaga wallahi magana ce zamuyi mai mahimmanci, dan Allah ka barni na ganshi."

"Ka fad'a min ko miye saina fad'a masa." cewar jami'in yana d'auke kai.

"Maganar nan sirri ce, dan Allah kace ina son ganinshi."

A hassale jami'in yace "kai, wai kai wane irin mutum ne? nace maka yace kar a takura masa ko, kai baka ga yan uwa ba duk gasu nan amma ba'a bari sun shiga ba sai kai, dallah ka b'ace min da gani."

Ganin fa ba zai barshi ba yasa dole ya yanke shawarar fad'a masa, d'an sassauta murya yayi yace "kaga abokina, wata masaniya na samo akan mutanen da yallab'ai yake nema, dan Allah ka barni na ganshi kar lokaci ya qure mana."

Ido ya zaro yace "kenan kasan mutanan da ake nema? to su waye, kuma me sukayi?"

Kallon rainin wayo ya masa yace "kana nan kace baka san akan me ake nemansu ba?"

Cike da son jin gulma yace "wallahi ban sani ba, ba'a yarda kowa yasan meke faruwa ba."

Cike da k'osawa yace "yanzu zaka iya yimin magana dashi d'in ko kuwa na tafi?"

"A'a jira ina zuwa."

Yana fad'a ya shiga d'akin dan fad'a ma yallab'ai Papa, zaune ya samesu shiru dasu abin tausayi suna kallon Khairat, sunkuyawa yayi kusan kunnen Papa yace "yallab'ai wani saurayine a waje kesan ganinka, kuma yace akan maganar mutanen da ake nema ne."

Kallonshi yayi da sauri yace "ka tabbata?"

"Eh to, haka dai yace min."

Tsaki yayi yace "yanzu haka d'an jarida ne yayi basaja ko kuma masu son sanin meke faruwa, kawai kace masa ina wani uzuri ba zanga kowa ba."

Duk abinda ya fad'a a kunne Mamie dan haka bata ce k'ala ba ba ta mik'e zunbur ta fita daga d'akin, tsaye ta samu Umar Faruk yana jira, saida ta kalleshi da kyau tace "sannu bawan Allah, kaine kake son ganin Alhaji?"

"Eh nine Mama."

Cikin muryar tausayi tace "ka fad'a min wani abu da zaisa naji dad'i dan Allah."

Ajiyar zuciya ya sauke tare da gyara tsyuwa yace "kiyi hak'uri Mama, bansan taya zaki fahimci abun ba, amma dai tabbas anci amanarku, wanda suka ketawa yarku haddi suna nan tare daku,
Showing 18001 words to 21000 words out of 186119 words