ganin ko wanene yasata zube qasa tana gaisheshi, saida yayi qaramin tsaki sannan yace "ina Mamie?"

Murya na rawa tace "tana d'akinta bata fito ba."

"Khairat fa?"

"Itama bacci take."

Kamar mai ciwon baki yace "ok, jeki."

Tashi tayi ta nufi madafa tana fad'in "ikon Allah kenan, sai kuma Allah ya had'ata da daidai ita."

Shima sama ya haura d'akin Khairat, a hankali ya bud'a k'ofar yana kallon gadon da yake da tabbacin tana nan, (kunsan mutuniyar dama ba kwana take da manyan kaya ba) hakan yasa Muzaffar ya kusa kallon rabin sadakinshi😂, saboda wata irin riga ce bata da maraba da bras, sai kuma wandon rigar kad'an ya wuce mazaunanta, takowa yayi harya tsaya gaf da ita yana had'iye yawu masu nauyin gaske, da qyar ya lumshe idonshi sannan ya sake bud'ewa ya saukesu a kanta, hannu ya kai zai daddab'ata ta bud'e ido tare da juyawa, karaf idonsu suka sark'e dana juna, a zabure ta tashi zaune taja dara ta rufe jikinta tana mashi kallon tuhuma.

"Wannan wane irin jahilci ne, miye haka Muzaffar, ya zaka shigo min har cikin d'aki kana tab'ani?"

K'ara matsowa yayi yana fad'in "kinga Khairat dan Allah kiyi shiru, karki tara min jama'a, wallahi bada wata manufa na tai tab'aki ba."

"Dallah ni kamin shiru, ka fice min daga d'aki."

"Haba Khairat w...." katseshi tayi da fad'in "dallah ni nace k...." kuma sai tayi shiru saboda tuna abinda Hibba tace mata.

Hararanshi tayi ta turo baki gaba tace "to dan Allah kawai ka shigo min haka duk ka bani tsoro."

Ajiyar zuciya ya sauke yace "kiyi hak'uri kinji. "

"To naji, wai mema ya kawoka nan? bayan nace maka ba zamu had'u ba har sai an fara shirya shiryen bikinmu."

"Kiyi hak'uri my Khairiri, wallahi na kasa hak'ura ne shi yasa, matuk'ar so nake na ganki sosai."

"To naji ni dai yanzu ka fita ka jirani falo zanyi wanka na fito."

Cikin wani shu'umin kallo yace "to muje na miki wankan mana."

Pillow ta dauka ta jefa masa tare da masa kallon kai shashasha kuma hamago ne, amma da yake hamagon ne na gaske saiya kasa fahimtar kallon, hannu ya mik'o mata tare da sake fad'in "kizo na rakaki to idan ba zaki yarda na miki wankan ba."

Saida ta had'e fuska sannan ta mik'a masa hannunta ta sauko daga kan gadon, ci gaba yayi da k'arewa surarta kallo ita kuma ko a jikinta, har saida ya kaita bakin ban d'akin sannan yayi murmushi yana cewa "insha Allah nan da rana kamar ta yau kin zama tawa, kuma daga wannan ranar ni zan dinga miki wanka."

Itama murmushin tayi tace "zaka dinga min, ko zamu dinga yi tare?"

Sunkuyawa yayi yace "yanda kike so gimbiya."

"To ka jirani falo ina zuwa."

Tana shiga shima ya bar gidan gaba d'aya ba tare daya jirata ba dan akwai abubuwa gabanshi, itama kuma ta jima bata fito ba bayan ta shirya ta fito falo, bata sameshi ba kuma bata damu ba, harkokin gabanta ta shiga yi bayan Mamie ta had'a mata kayanta tasha nasha taci naci, foyer ta nufa wajen gyaran jiki kamar kullum.

***************

Cikin farin ciki ya fito daga gida zuwa wajen aikinshi, tunda ya shiga yaga gungun su Ishaq sunata hira, saida ya tsaya bayanshi bai sani ba ya kai masa duka yana fad'in "iskancin banza, wajen neman kud'in naku kuka mayar kamar kasuwa?"

Dariya Ishaq yayi lokacin daya juyo ya kamo hannunsa yace "kai haba zo ka gani kaima."

Matsowa yayi shi kuma ya d'auko wata had'add'iyar shadda gizna kalar ruwan qasa ya bashi, hannu yasa ya karb'a yana kallo yace "na miye wannan?"

Saida ya kalleshi yace "ankon Hajia Khairat ne ta aiko manager ya kawo, kuma tace duk wanda bai siya ba to yasan sauran, dan tace tana buk'atar ganin kowa dake wajen nan ya hallara duka shagulgulan da za ayi."

D'orawa yayi da "kuma kasan halinta dai, k'aramin aikinta ta tsige mutum daga aikin nan, dan haka kayi sauri ka siya dan kwana hud'u ya rage a fara shagulgulan bikin."

Wata uwar harara ya zabga masa tare da jan tsaki ya cilla masa shaddar a qirji ya fita ya bar wajen, saida ya hau mashin d'inshi ya tambayi kanshi "ina kuma zaka je?"

"Gida." inji wata zuciyar.

Ai kuwa gida ya nufa da tunanin samun sauki, yana shiga a soro ya aje mashin d'in ya shiga ciki, duk da mutanen daya gani a farfajiyar gidan bai kula kowa ba yana shirin shiga d'aki mahaifiyarshi tace...

"Kai Umar faruk, lafiya ka dawo gida yanzu?"

A wahalce ya kalli Mamar yace "ba komai Mama, bana jin dad'i ne."

Zai wuce ta sake cewa "Umar faruk, ashe yarinyar nan za tayi aure wacce kuke aiki a masana'antarta, shine kuma baka fad'a ba, kuma kaga ko mahaifinka bana tunanin ua sani dan daya fad'a min."

Rai b'ace ya kalli Mamar yace "Mama kuma waya fad'a miki maganar nan?"

Kallon budurwar dake gefenta tayi tace " *Ruk'ayya* ce."

A zafafe ya kalleta yace "ke kuma gidan uban wa kika ji?" ya tambaya a harahen zarma.

Tuni Ruk'ayya ta fara rawar jiki saboda tsoro tace "wallahi yaya Umar nima a Whatsapp ne na gani ana d'ora photonta da akwati talatin da makullin mota,amma ni bansan komai ba."

Sama da qasa ya harareta ya rangada dogon tsaki sannan ya kalli Mama yace "wallahi shi yasa banso aka bar yarinyar nan ta rik'e wayar nan ba, kawai salon yara su lalace."

D'akinshi ya wuce zuciyarshi kamar zata kama da wuta, wani irin haushin kanshi ne yake ji daya takura kanshi akan tunanin wata banzar Khairat (a cewarshi), bai sake fita ba har saida Ishaq yazo gida ya sameshi da yamma.

Gaishe da matan gidan yayi kafin ya d'ora ma Mama da "Mama mutumin kuwa yana ciki?"

"Yana ciki Ishaq, yana sabon d'akinshi."

Dariya yayi ya mike yana fad'in "mutumin fa ba dama, kamar gobene auren nan."

Itama dariyar tayi tace "ka barshi kawai, a doleshi k'uryar d'aki yake so a fitar masa, kuma wuri ba zai isa ba, in dai baso yake na fita daga d'akina ba dan yayi k'uryar d'akin."

"A'a Mama ki barshi, dole zai hak'ura ai."

Yana shiga ya sameshi cikin falon d'akin wanda ke shafe kayane kawai babu, falon babba ne sosai amma babu wani d'aki a ciki, d'an k'aramin kewayene daga waje sai matsakaiciyar ban d'aki , gaisawa sukayi Ishaq ya d'ora da "kai haka ake? kawai saika sa kai kayi gaba kuma baka komawa, shi yasa ai na fad'a musu wallahi son yarinyar nan kake, dan inba...."

Katseshi yayi da fad'in "kai kai kai, dakata dan Allah, wacece nake so d'in?"

"Khairat mana."

"Mtssss, yanzu wannan sakaryar kake had'ani da ita, wannan mahaukaciyar yarinyar? gaskiya ka cuceni Ishaq, wallahi da zan san zuciyata na sonta, toda babu abinda zai hanani hukunta kaina ta hanyar da tafi kowace hanya zafi."

"Wace hanya kenan?" cewar Ishaq.

Shiru ya masa ya ci gaba da kallon d'akin shi kuma yace "to aini banga wani aibunta ba yarinyar, kaifa kasan *wacece ita*."

"Sanin wacece ita yasa ba zan iya yarda na bari zuciyata ta fara sonta ba, da bansan ita yar d'an giya bace ko kuma manemin mata, da ace bansan ita fiysararriyace wace bata d'auki cud'anya da maza ba a bakin komai, da ace bansan ita mai wulak'anta mutane bace, da ace bansan tana soyayya da arne ba, sannan da bansan itace yarinyar da namiji majiya k'arfi guda biyar suka sauke sha'awarsu a kanta ba, to da zan iya tunaninta."

Da mamaki Ishaq ke kallonshi dan b'acin rai ne kawai ya gani a idonshi da tafasar zuciya, girgiza kai yayi yace "wallahi wannan ba Umar Faruk d'ina bane, tabbas akwai abinda ke damunka kuma baka shirya fad'a min ba, Umar d'in dana sani yana da ilimin addini dana zamantakewar rayuwa, wannan maganganun bai kamata su fito daga bakinka ba, amma saboda b'acin ran da kake ciki yasa ka fad'esu, amma duk da haka ni ban yarda baka son Khairat ba, sai in har ka siyi ankon bikinta kuma ka halarci taron sannan na yarda."

"Wannan shi zai tabbatar maka bana sonta?"

"Sosai ma."

"Muje, muje ka rakani na siyo yanzun nan."

Kamar wasa Umar faruk ya shiga d'akinshi ya k'wamuso kud'ad'enshi suka fita, tare suka siye kuma suka biya suka bada d'inki, Umar harda siyan takalmi 😏kaji sai kace shine angon.

Saida dare yayi suka dawo gida, dama kuma gida biyu ne ya raba gidansu, k'arar mashin d'inshi yasa Baba dake zaune a d'akinshi dake farkon shigowa gidan yasa ya kira sunansa , bayan ya shigo nan ma dai maganar d'aya ce akan aure Khairat ne, sai dai shi Baba Papa ne yazo da kanshi ya gayyaci malaminshi a matsayin wanda zai wakilceshi ya bada auren Khairat, a tsorace Umar Faruk ya d'ago kai yace "Baba, wai kai zaka d'aura auren?"

"Eh, da wata matsalane?"

"A'a, zan iya shiga ciki? kaina ke ciwo."

"Ba damuwa kaje, amma ka sani dole zaku je wannan d'aurin auren, na fad'awa duka yan uwanka maza masu wayo , zamu tafi tare daku."

"K....kkk....kuma dai?" cewar Umar faruk.

"Eh, akwai damuwa ne?"

"A'a, saida safe."

Da qyar yakai kansa d'aki yayi kwance yana ji kamar yayi kuka, amma kuma yana tambayar kansa to kukun me kenan zaiyi😆😆😆.

*****************

*Komai* na tafiya yanda suke tsarashi a haka kuma Khairat ta fara d'aukan haske saboda k'unshi da gyaran kai mai masifar kyau da aka yanyara mata gwanin sha'awa, ranar *laraba* aka fara da indian night, a ranar an rak'ashe sosai shagali yayi shagali, yayin da ya tara dubban mutane manyan yara da manyan mata, kusan kowa yayi qoqarin yin shigar indiawa, amma kana ganin amarya zaka ganeta saboda kayan data d'auka jar kala da golden, riga da siket ne hannayenta sun sauko akan damatsenta amma ta kamata sosai, sai k'aton siket d'in da yake jan qasa yasha duwatsu ga walk'iya, mayafin kayan ne aka d'ora mata akai, ba laifi gana gani zasu birgeka dan had'insu yayi, sai dai duk kyan Muzaffar Khairat ta takeshi ta shanye, haka akayita walima har aka buk'aci da amarya da ango su shigo fili su d'an taka, sai lokacin kad'ai nida ma chérie Hakeema da sister Chappa muka tsagaita da rawa muka ba Khairat d'inmu fili dan munsan tanan b'angaren gwanace ta qarshe.

Ai kuwa bata bamu kunya ba, dan kuwa wata waqa ce aka baza mata d'aya daga cikin film d'in *dilwale* mai taken *janam janam*, Muzaffar tsaye yayi amma fa amarya ta taka ba laifi sai lik'i da tafi da aka dinga mata, a haka aka tashi taron ango ya maida amarya gida shima suka wuce gida kowa yayi baccin gajiya.

_Har yanzu kunkumina ciwo yake😂 can naga yan team d'in Umar faruk ta taga suna lek'enmu muna yagar kaji, ah to ai dama na fad'a muku dan babu alfarma a wannan ranar_.


*Washe gari* ma sabon shiri aka d'auka na arabian night, abayar da Khairat ta zanawa kanta ta saka, sosai rigar ta dace da ita, dogayen hannuwa kuma matsatsu hakama ta kamata wajen qirki abinda yayi kunkuminta, sai dai daga nan kuma saita bud'e sosai har tana jan qasa a baya, kwalliya akama rigar sosai ga d'an kwallinta ma, tana d'orawa ta fito kamar balarabiyar gasken, dogayen takalmi aka d'auko mata zata saka kawai taga ba zata iya ba, in da take ajiyar takalmin ta bud'a sai idonta ya sauka akan wasu tapet masu kyau masu kamar na maza , murmusawa tayi data tuna ranar farko da manager ya shigo tare da Umar Faruk suka gabatar mata da takalmin kuma tace su bar mata su, tana sawa suka tsaya a qafarta d'aram gwanin sha'awa dasu, haka suka nufi hall d'in taron amma idon Khairat sun kasa barin takalmin nan, yau ma haka akayi wannan taro aka ci aka sha baja baja (an samu na banza ba), 22:15 kowa yasan in da dare ya masa, sai dai tun kafin abar taron photon amarya da ango suka rigasu fita daga wajen, masu d'orawa a fecebook, Whatsapp, Instagram, kai da sauransu, cikin qanqanin lokaci sai photunan suka shiga duniya, maganganu iri iri wasu na yaba dacewarsu, wasu na yaba kyawun matar, wasu na yaba kyawun namijin, wasu na fad'in ai an mata fyad'e, yayin da maza suka fara tabka mahawara a shafukan sada zumunta iri iri, wasu na cewa ya kyauta kuma yayi jarumta tare da *Jihadi*, wasu kuma suna ganin ba zasu iya ba kuma shima da yayi bai birgesu ba.

*Al'amarin aure kenan, dole sai ace nan yayi daidai, nan baiyi daidai ba, mutum d'ari na iya maganar aurenka, amma da wuya ka samu goma da zasu ce Allah dai ya sanya albarka, kashi saba'in masu kushewa ne, ashirin masu yabawa, goma ne masu addu'ar fatan zaman lafiya, Allah ka rabamu da sharrin mutane da aljanu , Allah ka bamu ikon yin komai da kai.👏*

A cikin haka Allah ya had'a Umar Faruk da videon Khairat a Indian night tana rak'ashewarta, wanda anan ma mahawarar ake , wai idan kaine ya za kayi azo party amaryarka na wannan rawar kamar baindian gaskiya, wasu na fad'in kafin a d'aura auren zasu ce sun fasa, wasu kuma na cewa aiba komai bane zamani ne, yayin da Umar Faruk ya sake jin haushin Khairat sosai a zuciyarshi, tunanin yake yanda zaije partyn gobe da aka ce dole suje kuma gashi manager ya rok'esu akan suje danshi.

Photo d'aya ya zubawa idanu shine in da take cikin abaya ta yane kanta, meuk-up d'in da tasha ta sake canza mata kammani tayi bala'in kyau, saika santa zaka iya ganeta abinka ga farar fata, da alama bata san an d'auki photon ba saboda babu murmushi a fuskarta kuma bata kallon mai d'aukarta, kanta na kallon qasa baka iya ganin idonta sai golden da pink d'in eyshadow d'in dake saman idon, zoom d'in photon yayi yana kallon kyawun fuskarta, a hankali furta "dama labarina dake gajere ne, gashi ya datse tun bamu kai ko ina ba." da kallon wannan photo har bacci ya d'aukeshi.


A b'angaren Khairat kuwa har tayi shirin kwanciya bacci Mamie ta shigo da 'yan tame tamenta, tun kafin tayi magana Khairat tace "ohh Mamie, wai dan Allah abun nan ba zai qare bane? nifa wallahi na gaji da shan kayan nan suna takura min."

Cikin dariya Mamie tace "kiyi hak'uri kinji, keda nake tunanin na had'a miki su idan ki kaje can kiyita anfani da kayanki."

"Wa, ni? ba zan iya Mamie, na yanzu ma wallahi komawa za kiyi dasu."

Kafad'arta ta dafa tace "Khairat, burin kowace uwace, taga yarta tayi rayuwar farin a gidanta, kiyi hak'uri nasan ba zaki ji dad'i ba amma ya zama dole na tuna miki, 'yata, akwai wani abu mai mahimmaci da kika rasa wanda ba zaki iya yiwa mijinki tink'aho dashi ba, amma duk da haka ina so naga kin samu kyautar da ake samu a daren farko."

"Kinsan wace irin kyauta ce?"

A hankali Khairat ta girgiza kai alamar a'a, murmushi tayi tace "wasu na bada kyautar kud'i, kadara ko tasa albarka, amma ni ina so a daren farkonki , mijinki ya mallaka miki kanshi ke kad'ai, ina so ya mallaka miki zuciyarshi ki zama mai alhakin kula da ita, duk abubuwan da kika ga ina baki, wannan ne sirrinsu, ki rik'esu da kyau su zama sirrinki, duk in da mijinki zaije to wallahi zai dawo matuk'ar kin rik'esu, natural ne ga lafiya a jiki ga dad'i a baki, kuma zasu dinga tsumaa jikinki koda kin zama raguwar mace, to zasu jima a jikinki ba tare da kin rage d'and'ano ba, idan kuma kina yi akai akai, to kullum d'and'anonki zai dinga haukata mijinki tamkar qaramin yaro ."

Kumatunta ta dafa tace "kinji ko 'yar albarka?"

Kai ta sake girgiza alamar eh, Mamie na bata ta amsa ta kifa kai saida ta shanye sannan ta ajiye cup d'in Mamie ta d'auka sukayi sallama ta bar d'akin zuciyarta fari qal.

*Mamie nima na rik'e sirrin nan, shi yasa ban fad'a musu ba😎, nifa har kyautar yaran da zan haifa aka min😁.*


*Washe gari* haka aka tashi da sabuwar hada hada kasancewar gobe d'aurin aure, bak'i na nesa dana kusa sun hallara kuma kowa na shirin tafiya partyn da za ayi na kowa da kowa, yamma nayi aka fara tafiya bayan wankan da amarya ta d'auka cikin shadda irinta ango, sunyi masifar kyau masha Allah, yau kam hall d'in cika yayi sosai dansu Umar Faruk ma na hangosu da sauran ma'aikatan, da qyar ake iya ganin amarya da ango saboda masu d'auka da waya nayi masu camera ma nayi, haka ake taro har mc ya kira amarya da ango suka yanka babban cake d'in da aka masa siffar amarya da ango , suka ba junansu a baki sannan suka shigo fili suka fara d'an rausayawa, naira tayi kuka domin wasu kamar a cikin shara suka deb'ota yanda suke zubawa ango da amarya, Umar Faruk ya kasa d'auke idonshi akan Khairat amma da kallonshi ya kai ga Muzaffar, 🤣sai naga ya bishi da harara da dogon tsaki, wannan tsakin ne ya ishi Ishaq yace su tafi su tafi tunda dai an gama ai, ko ruwa baisha ba bare jus sai Ishaq yayo oder abinshi a leda ya taho dasu.

*Can naga yan team d'in Umar Faruk suna kokawa wajen d'aukar kwalban jus d'aya, amma da yake team d'in Khairat akwai imani, haka muka cika musu jakunkunansu da kayan k'walam😁*

_Grp JIHADI FAN'S._
_Grp Queen Bee_
_Grp Qanin miji fan's_
_Grp Nida yayah Al'ameen 1 & 2_
_Grp Beneficiale writers_
_Grp yan Baiwa_
_Grp sharhi da tambayoyi_
_Grp Na baki rayuwata_
_Grp BK fan's_
_Grp Raheenat m kk fan's_
_Grp Online writers_
_Ummu Fatima conversation_
_Grp Mom sultan novels 1_
_Grp rayuwar gidan kawuna_

*Hak'ik'a kun min kara, dan kun cashe sosai fiye da tunani na.*

🤝🤝🤝🥰 *ANA TARE FAN'S*

******************

Koda ya shigo gida kai tsaye d'akin mahaifiyarshi ya nufa sai dai tuni sunyi nisa a bacci, kamar yanda ya sani dama ko yayi dare to abincinshi na gefen mahaifiyarshi, kwanan ya d'auka ya zauna kusa da ita ya fara ci yana kallonta tana baccinta, sai dai baici mai yawa ba ya barshi ya fito daga d'akin, d'akinshi ya shiga ya cire kayanshi ya fito zai shiga wanka, yayanshi ne *Abbakar* ya shigo shima bayan ya yiwa mashin d'inshi wajen zama, hannu ya bashi suka gaisa yana fad'in "yadai abokina, ina ka shiga ne haka?"

Cikin sanyin jiki Umar Faruk yace "wallahi abokina ina nan, kai dai ka b'ace, waccen matar ta b'oyeka."

Nunashi yayi da hannu yace "kai ka fita idona, ina ruwanta kuma."

Bokitin ya d'auka ya nufi ban d'akin yana fad'in "idan ka
Showing 39001 words to 42000 words out of 186119 words