shiga kace mata na dawa ta zo ta gaisheni."

"Lallai ma, sai dai ka kama layi to harta gama dani, kasan ance in ana dara fidda uwa ake."

Baice komai ba saboda harya fara cire kayan jikinshi, yana fitowa kuma yayi alwala ya shiga d'akinshi, doguwar riga yasa ya kabbara sallah ya fara nafilfili har saida kiran sallah asuba ya riski kunnuwanshi sannan ya dakata, fitowa yayi saboda jin motsin mutane sun tashi suma , tare suka nufi masallaci da yan uwanshi da kuma mahaifinsu, bayan sun idar da sallah suka dawo gida, kuma kamar yanda mahaifin nasu ya koya musu wasu karatun littafi mai girma suka fara, wasu kuma tasbihi da hailala da kuma istigfari, Umar Faruk ma karatu yayi saida 06:00 tayi sannan ya rufe ya d'an kwanta kafin k'arfe 09:00 auren Khairat.


*Daga gobe ne fa*πŸ’ƒ

********************

*Yau ne fa*πŸ˜‚

Yau ta kama ranar *asabar* ranar d'aurin aure, Umariri ma πŸ˜‚baiyi qasa a gwiwa ba wajen shiryawa kamar yanda yaga yayanshi Abbakar da k'annanshi guda biyu *Usman da Aliyu* suna yi dan cika umarnin mahaifinsu, wani abun mamaki shine, haka kawai Umar Faruk kejin wani nishad'i da farin ciki na baibaye mishi zuciya, ga murmushi mai matuk'ar tsada daya kasa barin fuskarshi, duk da yana d'an jin fad'uwar gaba da kuma tsoro, amma dai yafi farin ciki hakan kuma yasa ya ta'alak'ashi da karatun da yayi ne dan yafi komai samarwa mutum da nutsuwa.

Cikin wata shaddarshi gizna fara ya shirya wacce suka d'inkata a bikin abokinsu , kasancewar ba mutum ne mai sha'awar manyan kaya ba yasa tun ranar bai kuma sawa ba, kamar yau ne ya fara saka shaddar saboda yanda take d'aukar ido, dogayen hannuwa ne da ita da kuma wasu da aka aza daga iya kafad'u hakan zaisa kayi tunanin rigar ninki biyu ce, bak'ar hula takalmi qafa ciki bak'ak'e da agogo ya d'aura kamar dai yanda aikin rigar yake, shi kanshi yasan ya had'u masha Allah sai tafiya kawai.

Yana fitowa ya samu duka sun shirya suna tsakiyar gidan, rufe d'aki yayi ya kallesu yace "muje ko."

Duka da kallo suka bishi saboda ganin bak'on al'amari a tare dashi, ganin kallon yayi yawa yasa Umar faruk sake cewa "muje ko."

Baba ne yace "wai Umar faruk kaine da wani murmushin haka mai tsada, meya faru ne haka kake farin ciki?"

Murmushin kawai ya ci gaba dayi ba tare da yace komai ba, Abbakar ne yace "wannan farin cikin dai akwai wani abu a qasa gaskiya, mutumin da kullum fuska a had'e."

Cikin dariya yace "dan Allah ni ku wuce mu tafi, lokaci fa tafiya yake."

*Saratu* matar Abbakar dake zaune tare dasu Mama a tsakar gidan ce tace "wannan sauri da kake Allah yasa ba wani abun kake shiryawa ba."

Kallonta yayi yace "baki iya gaida miji ba amma kin iya katsa landa, to me zan shirya ni kuma?"

Cike da zolaya tace "tona sani ko amaryar zaka sace , ko kuma kasa a d'aura auren da kai."

Dariya duka aka saka saishi daya ce "wata d'iyar robace da kike tunanin haka ta faru?"

Mama ce tace "yarinya fa tsadane da ita tunda ita ta...." sai kuma tayi shiru.

Ke Ruk'ayya uwar d'umi sai kika ce "ita ta tallabeshi da mari fa duk wannan d'acin da yake mana a gida."

Da gudu tayi d'aki saboda biyota da yayi duk da kiranshi da Mama keyi saida yakai , yana shiga ya tallabeta da marin itamaπŸ˜‚ sannan ya kama kunnenta ya murd'e yace "wallahi na sake jin bakinki manya na magana, saina lahira ya fiki jin dad'i."

Kuka take sosai shi kuma yana fitowa ya kalli Saratu yace "ki shirya tarban sabuwar amarya."

Fita sukayi suka hau taxi dukansu suka nufi d'aurin auren, dandazon jama'a manya da qanana masu mulki masu sarauta, masu kud'i na nesa dana kusa ga kuma bak'i daga k'asashe da dama na gida dana waje, ganin irin d'ubbin jama'a yasa Umar Faruk jin haushi ma ya kamashi, haka dai suka samu suka kutsa tare da mahaifinsu harya shiga babban masallacin dake d'an nesa da gidan su kuma suka tsaya daga bakin masallacin.

Unguwar *Presidetielle* tank'am take da mutane har lokacin da shugaban...ya iso wajen, haka aka bud'a masa hanya jami'an dake tare dashi suna kakkareshi harya shiga cikin masallacin, bayan sun gaisa da mutane suka fara qoqarin abinda ya tayasu a wajen, duk da haka Umar faruk baya jin komai sai wannan d'an fad'uwar gaban wanda farin ciki yafi yawa a ciki, Ishaq ma zolayarshi kawai yake manager kuma yana musu dariya.

********************

*A b'angaren* Muzaffar ma farin ciki yake da d'okin zuwa wajen d'aurin auren, ya gama shirinsa tsaf ya d'auki babbar rigarshi zai saka amininshi da suke kira da *Basta* ya kalleshi yace "sai farin ciki kake da zumud'i zaka samu Khairat, amma mu kuma bak'in ciki muke dan koba komai munsan mun kusa rasaka kenan har abada."

Cike da mamaki yace " Basta, yanzu dama bak'in cikin aurena da Khairat kake? amma gaskiya ka bani mamaki."

"Ba haka bane abokina, ina nufin ina bak'in cikin rasaka da za muyi."

"Ban gane ba, rasani kamar yaya?"

"Nasan kasan komai game da Khairat, amma sai gashi ka yarda da aurenta kamar wanda mata quka k'are a gari, baka tsaya kayi bincike ba bare ka tabbatar da lafiyarta, haba abokina kayi tunani mana ka gani, kai da kanka ka fad'a min mahaifin yarinyar nan ne yaje ya samu mahaifinka da maganar aurenku, kenan akwai wani abu a qasa."

Shiru ya d'anyi yana tunani sai dai bai iya tunani komai ba, a hankali ya tambayeshi "kamar me kenan?"

Shu'umin murmushi yayi yace "kasan ko suwaye suka mata fyad'e, ai kuwa ba zata rasa cuta mai karya garkuwar jiki ba, ko kuma dai wata cutar ko kuma ciki."

"Ciki kuma? amma ai ba yau bane aka mata fyad'e, wata nawa aka d'auka da cikin ya kasa bayyana har yanzu?"

"Kai baka san mata ba wallahi, amma idan baka yarda da abinda na fad'a maka ba , to ga wuri nan."

Yana fad'a ya fita ya barshi dan yasan zaifi yin tunani da kyau, haka ne kuwa ya faru ya jima yana tunanin abinda ya fad'a har lokaci ya tafi sosai, agogon daya kalla yasa shi d'aukar wayarshi saboda ganin 08:57, shugaba ya kira yana d'auka cikin sauri yace "Papa an d'aura auren?"

Murya qasa qasa cikin dariya yace "wai saurin me kake? harna bayar da sadakinka fa, d'aurawa kawai za ayi."

"To a dakatar da d'aurin auren."

"Me , kasan me kake fad'a kuwa? akan me za'a dakatar?"

_Hummmmm Haleemat addu'arki ta kama mu._

"Papa kawai a dakatar da auren nan wallahi na fasa."

"Wai kasan me kake fad'a kuwa, baka da hankali ne? yanzu haka fa d'aura auren nan ne za ayi."

"To ni dai nine za'a d'aurawa auren, kuma nace na fasa dan haka ba zanyi ba."

Shugaba ne ya saci kallon Papa da bakinshi ke bud'e sannan tasa babbar rigarshi ya goge zufa, aje wayar yayi yana kallon mutane malam ne yace "to zamu iya farawa yanzu."

Shirun da shugaban yayi yasa aka fara shirin d'aura aure, sannu sannu murya na rawa yace "a dakatar da d'aurin auren."

Kallonshi akayi amma babu wanda yayi magana , "Muzaffar ne ya kirani yanzu, kuma yace a dakatar da auren."

Papa ne da gabanshi ya fara dukan uku uku yace "a dakatar kamar ya, gaba d'aya za'a dakatar ko kuma na wani d'an lokaci?"

"Eh to, nidai yace min a dakatar ya fasa baya so."

Da sauri Papa ya dafe kanshi, yana jin mutanen cikin masallacin na hayaniya amma bai iya cewa komai ba, kusan minti ashirin aka d'auka wasu na waje sun fara qaguwa akan meke faruwa, na cikin masallacin ne da suka tabbatar ba za'a d'aura ba suka fara fitowa, shugaba ma kallon Papa yayi yace "kayi hak'uri Mani, wallahi bansan meya faru ba,amma idan na koma gida zanji meye matsalar."

A wulak'ance Papa ya kalleshi yace "ba damuwa, ba saika takurashi ba, allah zai kawo mana d'auki."

Fita shima yayi ya rage daga Papa da malam sai yaya Suleiman da sauran k'annan Papa, su Umar Faruk dake tsaye k'ofar masallacin ne suka shigo ciki, wajen malam suka nufa suna tambayar lafiya har yanzu ba a d'aura auren ba, a raunane malam yace musu "yaran ne ya fasa."

Kallon kallo suka shiga yi suma har muryar Papa ta daki kunnuwansu yana fad'in "bansan me zance mata ba, tafi kowa damuwa da auren nan, tana matuk'ar son ganin Khairat tayi aure, yanzu gashi ba lafiya ne da ita ba, watak'ila idan na fad'a mata hawan jininta ya tashi, Khairat ma na fama da rashin lafiya, itama zata iya shiga matsala duk da dai nasan biyayya ta mana ta yarda zata aureshi."

A hankali ya furta "Allah ka kawo mana agaji." sai kuma kuka ya k'wace mishi, ganin haka yasa hankalin Umar faruk tashi babba na kuka a gaban idonshi, akan abinda zai iya taimaka masa, dole ne ma yayi wannan *Jihadin* kodan ceton mutunci da rayukan wasu, watak'ila kuma labarinshi da Khairat dama baizo qarshe ba, kuma zai iya yiyuwa akwai wani *b'oyayyen al'amari* dasu basu sonshi ba .

Matsowa yayi kusan Papa ya rik'e hannayenshi yace "yallab'ai, ni ba kowa bane, kuma ba d'an kowa ba, bansan ko zaka iya bani auren 'yarka ba."

Take farin ciki ya lullub'e Papa ya rumgume Umar faruk yana ci gaba da kuka, godiya kawai yake masa yayin da mutane suke mamaki malam kuma yana farin ciki haka ma 'yan uwanshi.

Anan take aka d'aura auren *UMAR FARUQ AHMAD ADAM* da *KHAIRAT MANI BUKAR* Papa da kanshi ya wakilci Umar Faruk, anan ango ya tattara duk abinda yake da aka biya sadaki, malam kuma ya wakilci Khairat.

_Farin ciki_πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ€barkanmu 'yan uwa, musha biki lafiya.
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

*ALHAMDULILLAH KASIRAN, ALHAMDULILLAH ALA KULLI HAL*


_Bismmilahir-rahman-rahim_


1⃣8⃣


Ana gama d'aurin aure sai kuma labari yasha bam bam, amma a wajen Papa farin cikine zalla yake saboda faruwar hakan, Papa ne ya keb'e da ango da Abbakar da kuma Baba yana tambayar lokacin da zata tare, Umar Faruk dai cewa yayi duk lokacin da suka shirya, amma Baba yace a basu sati d'aya, sosai Papa yaji dad'i ya kuma ce ya bawa Umar Faruk kyautar gidan da zasu zauna da kuma mota, murmushi Umar faruk yayi yace "wallahi bana buk'atar komai, shi yasa ma na fad'a maka koni waye dan matsayinmu ba d'aya bane, ba zan bar gidanmu ba, kuma ina da wajen da zan ajiyeta, idan kuma taga hakan bai mata ba, toni banda matsala tun kafin tafiya tayi nisa zan iya sss..."

Bai k'arasa ba saboda taushe mishi baki da Abbakar yayi, Papa ne yace "ba komai Umar faruk, ai ba sai ankai ga haka ba, ko rumbu ka ajeta dole ai zata zauna, mudai muna godiya sosai."

Papa ne yama Umar faruk iso a cikin gida yaga sauran iyaye da kakannin Khairat ya gaishesu, abinka ga idan Allah ya aiko abu, duk uwayen masu hankali idan suka kalli Umar Faruk sai suji ya kwanta musu a rai saboda hankali nutsuwa da kunya, haka suka kamo hanyar komawa gida yana wasi wasi yana ji kamar yayi kuskure hukuncin daya d'auka.

******************

*Khairat* na d'aki tare da k'awayenta tanti (aunty) Safiya ta shigo ta fita da ita bayan ta rufeta ruf da daren amare bleue wacce ta mata kyau, babban falon da Papa ke sauke manyan bak'inshi suka shiga, duk da kanta na qasa kuma cikin dara amma saida taga yawan mutanen dake d'akin, gaba d'aya kannan da yayun mahaifinta ne, Mamie kuma dama ita d'aya ce ga iyayenta, hakan yasa sai Safiya da *Ramlatou* itama cousine d'inta ce, sai kuma matar margayi babansu Papa da kuma Mammie, zaunar da ita tayi a tsakiyarsu sannan itama ta zauna.

*Nan fa* aka fara sambado ma Khairat nasihoji ta ko ina bayan sun fad'a mata yanzu ita ba budurwa bace mai aure ce, kuma ita ba matar Muzaffar bace, matar *Umar Faruk ce*, an jawo mata ayoyi hadisai da kuma karatun *duniya*, sosai nasihar ta shiga jikin Khairat sai gata da kuka tare da bawa kowa dake wurin hak'uri na ayafi juna, dan duk rashin kunyarta bata kai tama mutanen dake wajen ba saboda girma da matsayinsu gareta, haka suka bita da sa albarka bayan ta musu alk'awarin bin Umar Faruk sau da qafa, tanti Safiya ce ta mayar da ita d'akinta.

Tunda ta zauna ta fara wani sabon kuka dan babu yanda za tayi ne kawai ta amsa musu, amma ko kad'an Umar Faruk baya da tsari irin na mazan da take so (a cewarta fa)😎, gashi kuma baya da komai hasalima a qarqashinta yake samu, to tayaya zata rik'eshi a matsayin miji, gaskiya zata hak'ura taje gidanshi danta musu biyayya, amma dole zata dawo dan rainine ma a had'ata da wani wai Umar Faruk, haka dai bayan 'yan d'aurin aure sunsha lagwadarsu wasu har sun tafi da guziri, aka fara biki gadan gadan aka sha casu sosai.


Tun yamma mutane suka fara watsewa zuwa dare kuma babu kowa sai bak'i da suka zo, kowa ya kwanta dan yayi bacci ya huta gajiya amma banda Khairat dake tunanin yanda rayuwar aurenta zata kasance, yanda taga safe haka taga rana ba tare data rintsa ba, kiran sallah asuba kad'ai yasa ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta kwanta rama baccin da bata samu tayi ba.

******************

*A b'angaren* Umar Faruk kuma suna shiga gida yanda duk suka shiga da kazar kazar amma banda shi yasa mahaifiyarshi ta fara tambayar lafiya, fad'a mata yayi ita da yan uwanta (matanshi guda biyu) su sameshi d'akinshi, ba b'ata lokaci suka hallara tare da Abbakar da UmaririπŸ˜‚, nan Baba ya fad'a musu abinda ya faru sannan ya d'ora da "wannan na tabbata itace k'addarar yaranku, kuma wannan abun *rubutatten al'amarine* da ubangiji ya rubutashi tun kafin a samar dashi kanshi Umar d'in, dan haka ku shirya tarbar sarakuwarku ban da rana irin ta yau insha Allah, sannan ku saka musu albarka."

Saida suka gama jimami sannan mahaifiyarshi ta sauke ajiyar zuciya tace "gaskiyane malam, kuma insha Allah ba za'a samu matsala daga garemu ba, kuma muna musu fatan alkairi Allah ya basu zaman lafiya."

"Ameen ameen." cewar malam kafin ya kalli sauran yace "ku kuma me zaku ce?"

Tab'e baki *Sa'a* tayi tace "ah to me zamu ce, tunda kun riga da kun gama yanke hukuncinku."

Mik'ewa tayi ta kama hannun *Maimuna* tana fad'in "nifa ba zan iya zama wajen nan ba."

Itama Maimuna saida suka mike ta kalli Umar Faruk da kanshi ke qasa shi abin duniya ma ya dameshi tace "wallahi dai kayi abin kunya, in banda kwad'ayin dukiya ta uban yarinyar nan, ince kaine nan kazo kwanan baya kana huci akan ta mareka kuma ka rama, shine yanzu dan tsabar rashin zuciya wai kai uban taimako ka taimaketa, kai yanzu ba abin kunya bane a wajenka ace ka auri macen da wasu garada suka raga?"

Sa'a ce tace "ke rabu dashi dan Allah, yana tunanin zai samu abin duniya shi yasa, amma ka sani ba lallai ka mori abinda za'a baka ba, dan cutar da waccen ya guje ma kai zata sama, wannan itace k'addararka."

Bushewa sukayi da dariya suka tafa hannu suka wuce abinsu, ba sabon abu bane wannan dan haka babu wanda ya dama a cikinsu, Baba ne yace "Umar Faruk."

D'agowa yayi ido jawur kamar zai fashe da kuka yace "na'am Baba."

"Kayi hak'uri kaji, wallahi Allah ba zai barka haka kawai ba saiya dafa mata, kuma ni nayi farin ciki da abinda kayi, kuma nayi alfahari da kai a matsayin D'ana, Allah ya maka albarka."

"Ameen Baba."

Mama ce tace "to a ina zasu tare?"

Baba ne ya kalli Umar Faruk d'in shima kallonshi yayi, cikin muryar tausayi yace "Mama ba zan iya barin gidan nan ba, idan sunga nan ya musu, to su kawota idan kuma ba haka ba, to gaskiya sai dai mu rabu, danni dama kawai saboda na fitar dasu daga halin da zasu shiga nayi."

Mama ce tace "haba Umar Faruk, me yasa zaka fara maganar rabuwarku tun yanzu, bana so ka daina, kuma ba komai ai sai a qarasa gyara abinda ya rage, idan har ya musu saisu kawota nan d'in."

Abbakar ne yace "Mama, saida fa mahaifinta yace zai bashi gida da mota, amma yaron nan da taurin kai yak'i amincewa."

Umar Faruk ne yace "idan na amince na amsa kenan me nayi? me kake so al'umma suce a kaina? na aureta saboda dukiya? to wallahi babu abinda mahaifinta zai bani a duniyar nan na amsa, ni taimako nayi *jihadi* nayi na auri 'yarsa, dan haka bana buk'atar komai daga gareshi."

Tashi yayi ya fita daga d'akin Baba kuma ya kalli Abbakar yace "nifa naji dad'i da bai karbi komai ba, dan yanayin haka jama'a za suce dama abinda yasa yayi taimakon kenan, duk da bansan yarinyar ba nasan dai tana da rawar kai, kana ganin idan ya amshi wani abu daga mahaifinta zata yarda ya tank'warata a matsayinshi na mijinta?"

A hankali Abbakar yace "kuma hakane gaskiya, zata rainashi ne ma."

Mama ce tace "nidai wallahi a tsorace nake, dan zamanshi da yarinyar nan fa akwai matsala."

"Wace irin matsala kuma?" cewar Baba.

"Kaifa kasan halin Umar Faruk da zuciyar tsiya, ina jin tsoron yanda zasu zauna gaskiya ba tare da sun samu matsala ba."

"Kinga dan Allah, ki cire tsoro a ranki sannan ki bishi da addu'a, insha Allah komai zaiyi daidai."

"To Allah ya yarda."

Baba ne ya sake cewa "yanzu to me zaku shirya? biki za kuyi ko walima."

"Kuma dai?" inji Mama.

Cikin dariya Baba yace "ban gane kuma dai ba? kina ganin zamu zauna hakane ba muyi komai ba bayan amaryar da muka samu a sauk'ak'e, kema kinsan dole za muyi koda walima ce mu godewa Allah."

Abbakar ne yace "ina ga ayi walimar zaifi, kunga sai ayi wa'azi ma tare da musu addu'ar zaman lafiya."

Mama ce tace "gaskiya kam shawarar tayi, to yaushe
Showing 42001 words to 45000 words out of 186119 words