da kayan hannunta ta shak'o wuyan Zuby, kafin ma Zuby ta fahimci meya faru Khairat ta dasata a qasa tabi kanta da duka , ihu ta fara tana kiran sunan Umar Faruk dake gyara parking d'in mota, sosai Khairat take bugun bakinta harya fara fitar da jini, gashi girman jiki ba d'aya ba ta kasa qwatar kanta, jin kururuwa ne yasa mutanen dake d'aki duk suka firfito, da azama kowa yayi soro ya fara qoqarin rabasu, lokacin kuma Umar Faruk ya shigo, sosai ta rik'e rigar Zuby harta keta mata rigar, janyota Umar Faruk yayi a lokacin Zuby itama ta rik'e rigarta sosai, hakan yasa zip d'in rigar cirewa har rigar ta zame daga jikinta, ganin haka yasa mazan wajen komawa mafakarsu suka bar mata, cike da takaici da b'acin rai Umar Faruk ya fizgi hannun Khairat daga wuyan rigar Zuby yana fad'in "ba zaki saketa ba?"

"Ba zan saketa ba, wallahi saina ci uwar yarinyar nan, akan me zata rainani, ni tsararta ce?" duk tayi maganar nan cikin neman d'aukewar numfashi.

Duk maganganun da mutanen wajen keyi ko jinsu basuyi, da k'arfi ya b'abb'are hannayensu ya nuna Zuby yace "wuce ciki."

Juyawa tayi tana kuka tana d'yangasa qafa tana tofar da jinin dake bakinta, Khairat ma a tsawace yace "maza wuce ciki."

A hassale ta qarasa zame rigarta ta jefar ta wuce nata kewayen, zaune tayi akan kujera saboda makullin na cikin jaka kuma ta jefar da ita, Zuby na kaiwa qofar d'aki ta durk'ushe tana dafa ciki tana qara tsananta kukanta, da sauri kuma sukayi kanta ana tambayar lafiya, Mama ce da Saratu suka kamata danta shiga ciki, sake lanqwashewa tayi tana dafe ciki, Mama Sa'a ce ta kalli Umar Faruk tace "Umar Faruk tana da ciki ne?"

Kai kawai ya d'aga mata alamar eh, Mama Maimuna ce ta qara da "Allah yasa dai ba b'ari za tayi ba."

Jin haka yasa Zuby sake fashewa da kuka tana kiran cikinta cikinta, a hanzarce yace "to Mama mu tafi asibiti mana."

"A'a bari dai mu gani." cewar Mamanshi, d'orawa tayi da "bud'e mana d'akin."


Umar Faruk d'in ne ya bud'e musu d'aki suka kwantar da ita akan gado, duk wannan murqususus da take har yanzu shiru ba alamar jini ko wani abu, da qyar suka rarrasheta tare da bata baki, sannan Mama ta dora "in ki kaji wata matsala kiyi sauri ki fad'a masa kinji."

Bata amsa ba su kuma suka kama bansu, tashin hankali Umar Faruk ya ganshi a daren nan, kuka kawai take tana fad'in cikinta, sam bata barshi yayi bacci ba, kuma duk kururuwar nan da take akan kunnan Khairat dake cika tana batsewa, duk yanda taso tayi banza dasu abin ya gagara saida ta zubar da hawayen bak'in ciki ,itama dai ba tayi wani bacci ba sai karatunta data kwana tanayi.


Tunda asuba Zuby ta fahimci illar da Khairat ta mata, kallon kanta tayi a madubi taga yanda bakinta ya kumbura, ga masifar ciwon da hannunta keyi ko motsashi bata son yi, a haka Umar Faruk ya dawo daga masallaci ya sameta ba tayi sallah ba, nuna mishi hannun tayi yana gani ya kece da dariya yace "wallahi gotaki tayi, kawo na gyara miki."

Cike da jin haushi ta bashi hannu danya gyara mata, amma yana tab'awa ta fara ihu da kururuwa tana qwaqwumeshi, taji jiki sosai yayin da Umar Faruk yaki sakin hannun har saida ya gyara mata dan gwanine a wannan fannin , hawaye majina da yawu babu wanda bata had'a ba, saida ya shafa mata magani kafin ta kwanta na d'an lokaci shi kuma ya fita gaishe da iyayensu daga nan ya wuce d'akin Khairat.

Tsaye ya sameta gaban madubi tana shiryawa, dan wajen aiki take so ta tafi da wuri dan zaman gidan Umar Faruk ya fara fitar mata akai, sam akwai abinda ba zata d'auka ba ko daga wajen Umar Faruk d'in ne bare banzar matarshi, a daqile ta amsa sallamarshi ba tare data kalleshi ba, takawa yayi har yaje inda take ya kwanta akan bayanta wanda Allah ya wadatashi da tarin nama, hannu yake kaiwa cikin rigarta yana tattausa ko ina na jikinta yana sauke numfashi, yayin da wata sabuwar kewarta ke qara mamayeshi, shiru ta masa tana ci gaba da shirinta harta juyo da nufin d'aukar d'an kwalinta ta d'aura, janye jikinta tayi daga nashi ta d'auki d'an kwalin ta d'aura ta d'auki hijab ta saka, jakarta ta d'auka tasa takalmi zata fita ta rik'e hannunta, marairaicewa yayi yace "bako gaisuwa, me yayi zafi haka, kuma ina zaki je da safiyar nan? koni gani a gida ban fara shirin fita ba saike."

"Saboda kana da qarancin abinyi ne shi yasa, ni kuma akwai abubuwa masu mahimmanci dake gabana wanda suka fi zaman haka."

Janyota yayi ta fad'a qirjinshi Kutsawa yayi cikin hijabint ya manna kanshi a tsakiyar wuyanta yana sumbata, qoqarin fito dashi ta fara yi amma ya cije, jin ya fara birkicewa har yana neman zare mata rigar yasa ta turoshi da k'arfi ya fad'a kan gado, gyara jikinta tayi zata wuce ta kalleshi tace "Khairat fa ba tayi shiryuwar da zaka raina mata hankali ba, ina da 'yancin da zan iya qwatarwa kaina 'yancina da kaina, kuma wallahi ko kaine ka d'aukar min abu zan iya nuna maka b'acin raina, kamar yanda ko kai ka b'ata min ba zan gagara nuna maka hushina ba."

Banka masa harara tayi ta wuce abinta, wani irin iska ya furzar yana jin ba dad'i, tashi yayi ya koma d'akin Zuby ya samu tana bacci , shiryawa yayi shima kawai yabi bayan Khairat ba tare damu daya tashi Zuby ba, abin mamaki da d'aure kai shine, umarni da Khairat ta bawa Habeeba kan cewar bata son ganin kowa, kuma haka akayi Umar Faruk ma yazo ganinta Habeeba tace yayi hak'uri Hajia tace tana aiki, bai wani ja da tsayi ba dan yasan jiya ta dawo Khairat d'inta, kuma zai iya jawa Habeeba matsala a nata aikin inhar ya shiga da k'arfi, haka ya koma ya zauna mazauninsa ya kasa yin komai sai tunani da rashin walwala, abinda ya qara d'aga maishi hankali shine har suka tashi kowa ya kama hanyar gida Khairat bata fito ba, wacce bata iya rabin wuni a wajen, saida yaga har Habeeba ta tafi sannan ya nufi office d'in nata.

K'ofar rufe take dan haka ya dinga bubbugawa yana kiran sunanta, saida ta gama had'a kayanta zata fita tazo ta bud'e k'ofar, yana shiga ita kuma ta fito ta kama hanya, da gudu ya biyota kamar wani matashin zaki ya tari gabanta, yanda suka had'a ido yasa ya d'auke idonshi daga kallonta, wani tartsatsi yaji da rabon daya jishi tun zamanin shed'an na d'an qauye , ma'ana tun tana Khairat d'inta ta ainihin, kasa magana yayi ya kuma kasa kallonta, rab'ashi tayi ta wuce abinta tana fita ta shiga motarta ta kama hanyar gida a lokacin ana sallah magrib.


*Muje da sauri 'yan uwa*


A kwana biyu abubuwa sun faru, daga ciki akwai jinya da Zuby tayi da kuma zuwansu Zulfa'u gidan, sunzo suka tayar da hayaniya akan cewar sai sun d'aukar mata fansa, ganin basu samu wannan damar ba yasa suka ce zasu kai qararta, duk ban maganar da Umar Faruk ya dinga yi basu ji ba, har saida ya fad'a musu itace tasa aka kama Mama, kuma in suka kai qararta tofa magana zata iya yin girman da ba za'a iya tsayar dashi ba, sai lokacin sukayi shiru da bakinsu suka bar maganar qararta, a kwanankin nan aka hana kowa ganin Mama dake d'aure wacce wahalar duniya ta isheta, kuma a kwana biyun nan Umar Faruk ya had'a Khairat da Zuby ya musu qwaqwaran kashedi, ya kuma fad'a musu zai iya rabuwa da kowace in suka sake mishi tashin hankali a gida, kuma yaja kunnan Zuby sosai aka fita harkar Khairat, ya kuma nuna musu rashin jin dad'i akan haka sosai, a lokacin ne Khairat tace,

"Ka fad'a mata ta daina aibatani, wani yana da asali na qwarai, amma wani asalinshi ko waiwayarshi ba'a so ayi, kace ta bini a sannu inhar bata so na b'allo mata ruwan da ba zata iya taresu ba, wallahi wallahi tayi wasa saina tona mata asiri kuma na tonawa mahaifiyarta, mummunan aikin da mahaifiyarta aikata shekarun baya, to ni nan Khairat zan fallasa wannan ajiyayyan sirrin marar dad'in ji, tana wasa dani sosai kuma tana yawan fad'an bak'ar magana akan mahaifina, ni ba zan raina asalinta ba duk da nasan ita wacece, amma dai taci gaba da harzuqani to zata tsinci kanta a wahalalliyar rayuwa, tana wasa da ajina, bata san matsayi da girmana ya wuce duk inda take tunani ba, idan naso yanzun nan zan iya canza miki wajen zama, ba kuma wajen zama kad'ai ba harda sunan uba ma."

Tana fad'a kuma ta koma d'akinta ta barsu cike da juyayin maganganunta...

Umar Faruk ne ya kalli Zuby yace "kin gani ko, kinga abinda halinki ya ja miki, Zuby kin kasa gane cin zarafin mutum ba dad'i bare kuma iyaye, baiwar Allah nan ko kallonki ba tayi ba tare da dalili ba, amma ke kullum burinki kici zarafinta, ire irenku ne kuke saka wanda suka tuba su koma ga ci gaba da aikata laifukansu na baya, kuma irinku kuke saka wanda ba musulmi ba shakku da tamtama akan ya shiga addinin ko karya shiga, na tabbata mahaifinta yayi tuban gaskiya, amma ke sai tozartata kike ta hanyar anfani da kurakuran mahaifinta na baya, kin manta da cewa d'an adam ajizinie, yanzu gashi bakinki yaja miki kinci dukan tsiya harta kaiki ga jinya, abinda nake so na fad'a miki yanzu shine, Khairat ta dage ba zata saka a saki Mama ba har saita san yanda akayi ta samu sarqar, bana zarginki , amma dai ina fatan Allah yasa babu hannunki a ciki, dan in haka ta faru a gaskiya zanji kunya, dan ko babu aure a tsakaninmu, mu yan uwane na jini, dan haka abinda ya shafeki ya shafeni, kuma inya tabbata akwai hannunki a ciki babu abinda zan iya yi miki, dan maganar milyoyi ake, ni kuma ba zansa kaina a matsala ba saboda haukanki, gashi yanzu kinsha shegen duka a banza a wofi saboda shegiyar masifarki, ina fatan zaki kiyaye gaba."

Cikin kukan iskanci ta fara magana "lallai ma yah Umar, yanzu duk da abinda tamin amma ba tayi laifi ba?shine zaka d'ora min laifi, shikenan na gode."


D'akinta ta koma tana tunanin mafita akan Mama, shima d'akin Khairat ya nufa dan yau yana d'akinta ne, samunta yayi ta juya baya ta yanda baya iya ganin fuskarta, da alama har tayi shirin kwanciya bacci ne danta rufe da zanin rufa, saida yayi wanka yayi shirin kwanciya kafin ya haura kan gadon, jikinshi ne ya bashi akwai matsala dan tunawa da yanda Khairat ke tarbanshi idan ya shigo d'akinta, tabbatarwa da yayi ba za'a iya rik'e kanshi ba yasa ya rumgumeta ta baya yan shinshinar k'amshinta, shiru tayi kamar mai bacci sai dai tana ji kamar hawaye zasu taho mata, juyowa yayi da ita ya fara sumbatarta, tureshi tayi daga jikinta ta tashi zaune, a raunane ya kalleta yace...

"Haba baby, laifin me nayi kike min wannan hukuncin? na dauka ban cancanci haka daga gareki ba."

Cikin d'aure fuska tace "wannan shine *kuskuren da nayi*, ba kuma zan sake maimaitashi ba."

Hannunta ya kama ya rik'e yana sumbata yace "amma ai bana da laifi ko, me yasa za'a zab'i hukuntani to?"

"Baka da laifi kake cewa? taya za kace baka da laifi, bayan kana magana na fito da surukarka daga magarqama, bayan kana jin irin iskancin da matarka take min amma ban tab'a ganin ka d'auki matakin daya dace ba, kuma a hakane kake cewa baka da laifi."

Saida ta mayar da hawayen da suka zubo mata sannan tace "naji ni mahaifina yana shan giya kuma yana neman mata, amma ai yanzu ya daina kuma ya tuba ga Allah, duk da haka ina son mahaifina kuma ba zan lamunci cin zarafinshi ba a gabana, kuma ko yanzu ta fad'i bak'ar magana a kanshi, wallahi saina karyata."

Juya mishi baya ta sakeyi ta kwanta ta rufe, lalabarta ya fara yi amma ta juyo ta nunashi da hannu tace "bana so ka takura min, raina a b'ace yake har yanzu."

Cikin rawar murya yace "K..ha..ira...t, dan Allah karki min haka a wannan lokacin, Khairat ina neman taimako da tallafinki, wallahi zan iya shiga wani hali in ki kak'i kulani, dan Allah Khairat."

Banza tayi dashi haka ya dinga lallab'a amma ta shereshi, sam kasa bacci yayi ya fara karatu amma ya cije mishi, sai daf da asuba ya kabbara sallah ana kiran sallah kuma ya nufi masallaci, itama tana gama sallah d'akin Mama taje Ruk'ayya ta d'ora mata karatunta, suna gamawa ta fito ta shiga d'akin Mama Maimuna sa Mama Sa'a ta gaishesu, zata shiga kewayenta Zuby ta fito daga d'akinta da kumburin hannu har yanzu bai gama warkewa ba, tsaki taja tace "aikin kawai, sai iyayi da kurin tsiya kamar ba *Jihadi* akayi ba aka aureki."

Cak Khairat taja ta tsaya tare da juyowa ta kalleta, yayi daidai da shigowar Umar Faruk tare dasu Abbakar Aliyu da Usman, kasa tausar zuciyarta tayi saida hawaye suka wanke mata fuska, kallon Umar Faruk tayi ta d'an matso kusa dashi tace "Faruk, kai ka fad'a mata Jihadi ne kayi ka aureni?"

Kai ya girgiza mata yace "karki saurareta Khairat, kema kinsan ba zan tab'a fad'a mata haka ba, kawai tana so ta b'ata miki rai ne."

Jin haka yasa Zuby jin dad'i tace "kai yah Umar kaji tsoron Allah, yanzu ka manta da abinda ka fad'a min jiya kafin ka shiga d'akinta? tabb'."

Ta fad'a tare da tab'e baki, matsawa yayi Faruk yayi wajenta zaiyi magana saisu Mama suka fito, Baba ne shima yace "me yake faruwa ne kuma?"

Karaf Zuby tace "jiya nefa yace min shi jihadi yayi ya auri Khairat, daga na fad'a yanzu shine kuma yake cewa qarya nake yi."

Jin abinda ta fad'a kowa ya fara tamtama akan abinda ta fad'a, Khairat da kuka ya qwace mata ne ta matso kusan Umar Faruk tace "dan Allah Faruk ka sakeni, ka sakeni na koma gidanmu, wallahi ba zan iya jurar wannan wulaqancin ba saboda ban saba ba, da nasan *jihadi* kayi ka aureni wallahi da ban shigo gidanka ba, dan Allah ka sakeni."

Rud'ewa yayi ya rik'o hannayenta yace " Khairat karki yarda da abinda ta fad'a, wallahi bana daga cikin irin wannan mazan, ban tab'a magana mai kama da wannan ba da ita, Khairat ba zan iya sakinki ba."

Fizge hannayenta tayi cikin daga murya tace "qarya kake, ba zan sake yarda dakai ba Faruk, kai mugu ne azzalumi kuma marar adalci, wallahi na tsaneka na tsani ganinka, ba zan tab'a yafe maka ba abisa cutar dani da kayi."

Juyawa tayi da k'arfi zata shiga d'aki taji muryar Usman yace "kar kiyi haka kema, inhar za abi maganar gaskiya ai Umar Faruk jihadi yayi, amma kuma na tabbata bashi ya fad'a mata haka ba, kawai tana son rabaku ne."

Murmushin takaici tayi tace "ok , amma ai idan bai fad'a mata ba ai kai ya fad'a maka, tunda gashi ka sake maimata min jihadi yayi ya aureni."

Zata wuce Umar Faruk ya rik'o hijabinta, juyowa tayi a hankali ta kalleshi saita ganshi akan gwiwoyinshi yana zubar da hawaye, kasa magana yayi saboda tafarfasar da zuciyarshi keyi, haushi ne ya kama Ruk'ayya saboda soyayyar dake tsakanin 'yan uwa, rufe ido tayi ta matso kusanshi ta raba hannunshi da hijabin Khairat ta d'agashi tana fad'in "ka barta ta tafi mana yah Umar, saime, zaka kasa rayuwa ne? ai kowa yasan jihadi kayi ka aureta , dan babu wanda zai iya auren macen da namiji hud'u suka yiwa fyad'e."

Kallonta Khairat tayi sosai hawaye na safa da marwa a fuskarta, juyawa tayi ta wuce d'akinta Umar Faruk kuma a hassale ya d'auke Ruk'ayya da mari, sannan ya juya ya kalli Usman yace "ba dan ka sulhunta tsakanina da ita ba ka fad'i abinda ka fad'a."

Zuby ya nuna da hannu yace "kin jima kina yimin abinda ki kaga dama ina qlayeki, kiji da kyau, wallahi Khairat ta bar gidan tare zaku fita, bawai saboda sonta da nake ba sai dan qazafi da qaryar da kika min."

D'akin Khairat ya nufa yaci karo da ita da akwatin kayanta ta zubo wanda ya sawwaqa, rik'e akwatin yayi yana fad'in "dan Allah Khairat karki tafi, wallahi tallahi babu wanda na tab'a fad'a ma haka, rabamu kawai suke so suyi."

Mama ce ta qarasa inda suke itama cikin taushin murya tace " 'yata, kiyi hak'uri dan Allah karki sauraresu, babu gaskiya a cikin wannan maganar na tabbata."

"Mama, bana so kiga rashin kyautatawata , dan Allah ki barni na tafi."

"A'a Khairat, haka bai dace ba, dan Allah kiyi hak'uri ki koma d'akin mijinki."

Baba ne ya matso shima yace "ki koma d'akinki kinji, zan daidaita komai."

"Kuyi hak'uri, ba zan iya zama ba gaskiya, indai har canzi gaba da zama dashi, to zan dinga jin kaina a matsayin wacce ta kasa samun mijin aure, saida Umar Faruk ya taimaka yayi *jihadi* ya aureta, kusan kowa da abinda yake kira da jihadinsa, amma aurena shine *Jihadi* _Umar Faruk_."

Fizge jakarta tayi ta wuce abinta, motarta ta shiga ta wuce gida tana kuka, daga nan Umar Faruk yace Zuby ma ta had'a ta bar mishi gida ba zai iya zama da ita ba tana mishi haka, Baba ma baiji dad'i ba shi yasa babu ma wanda bashi hak'uri, itama tana kuka ta had'a yan kayanta, zata fita Mama ta tausaya mata tace ta koma d'akinta da zama, saboda Mamanta ba tanan kuma gata da cikinshi, taji dad'in haka sosai da haka take jin basu rabu ba tunda dama ba sakinta yayi ba.

**************

A gigice su Mamie ke tambayarta amma ta kasa magana sai kuka, kiran Papa Mamie tayi yazo shima saida yayi lallab'a da dubara ta fad'a masa abinda ya faru, a take Mamie da Mammie suka fahimci kawai sharrin kishiya ne, nan suka dinga bata magana tare da sake koya mata wasu sabbin salon na shanye makircin kishiya kowace iri ce ,sannan suka ce ta koma gidanta, nanfa tace ba zata koma ba ita ba zata sake zaman gidanshi ba, zuwa yamma kanta ya fara mata azababben ciwo, gashi kuma maganinta na can gidan.

**************

Umar Faruk nayin sallah la'asar ya
Showing 135001 words to 138000 words out of 186119 words