ba, cikin taushin murya tace,

"Amincin Allah ya tabbata a gareka angona yayah Umar."

Nauyayyan ajiyan zuciya ya sauke yace "amincin Allah ya tabbata a gereki."

Cikin shagwab'a tace "kenan ba zan samu ko wane irin suna daga gareka ba?"

Murmushi tayi yace "ina tsoron nace amaryata kuma kiyi hushi ne."

Cike da wayencewa tace "ba komai yayah Umar, ka kirani amarya zan amsa, tunda aunty Khairat ta rigani zama taka."

"A'a, har yanzu fa babu wacce ta shigo hannuna, dukanku dai ina jira ku gama wainani sannan ku shigo gidan."

Haushi ne ya kamata danta lura soma yake Khairat ta shigo gidan bayan yace taimako yayi, shi kuma baya so ne ya bada wata k'ofa da zata sa Zuby ta raina Khairat musamman ace ta dalilinshi, koba komai itama matarshi ce kuma uwar gida, a dak'ile tace "dama na kirane na baka hak'uri abisa abinda ya faru, dan Allah ka yafe min ba zan sake ba."

"Ba komai k'anwata, ya wuce ai."

"Na gode, saida safe, dan naji kana cikin jama'a."

"Saida safe." ya fad'a suka tsinke kiran.


Haka taro ya tashi lafiya bayan addu'o'in da aka zuba musu, dare yayi kowa ya kwanta amma banda Umar Faruk, a qarshema d'akin Khairat ya bud'e ya shiga, fitilar d'akin ya kunna a hankali ya dinga sauke numfashi saboda wani baqaraken k'amshi dake shigar hancinshi, had'e yake da kamshin turaren wuta da kuma turaukan dake zube a saman coiffeuse da mayuka har babu wurin aza wani abun, bin d'akin yake da kallo ko ina yana kallon irin kayan da aka cika d'akin dashi, wai nan danma yana ba'a samu irin wurin da ake so bane, kusan komai na d'akin pink couleur ne hakan yasa yace "da alama shine couleur prΓ©fΓ©rΓ© (best coulor) d'inta."

A sannu yake tunanin ranar daya fara shiga d'akinta yana fad'in "girman d'akinta shine kaso d'aya na bisa ukun gidan nan, girman gadonta kuma d'akin nan ba zai daukeshi ba, duk da banga ban d'akinta ba, amma na tabbata ta kusa girman d'akin nan."

Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin murmushi yace "taya zata iya rayuwa a d'akin nan? bayan gashi tagar dake akwai ma kaya sun rufeta, taya zata iya rayuwa da wannan pankar? bayan acan ac take kunnawa , taya zata iya rayuwa a gidan nan da mutane haka? bayan ita acan ita kad'aice ba k'ane ba k'anwa ba yaya ba aunty."

_Wannan itace rayuwar daya kamata ta fara kota koyi hankali_


********************

*A b'angaren* tunda aka tashi da safe ta tashi jiki ba k'wari, gashi Mamie ta kira mai kitso amma sam tace bata so, ayi juyin duniya tace ba taso dole aka barta, da qyar ta bari aka mata jan lalle tunda waccen ya goge dan jikinta baya da kama lalle, duk da mutanen da suka zo dan rakiyar amarya Papa yace sam bashi ba wannan bidi'a, dan haka da kanshi zai kai yarshi gidanta tare da rakiyar kakanninta.

Abin yama Khairat yawa dan haka tun yamma ta fara kuka, amma sai tace musu kukan rabuwa ne dasu, haka akayi magrib akayi isha'i, ba wani shiri tayi ba atamfa ce ta zabga riga da zane d'inki simple, kasancewar bata tab'a saka zane simple ba saiya mata kyau d'as, Mammie da Hajia *Maryama* ne suka kamata Papa da kanshi ya tuk'a mota suka nufi gidan amarya bayan d'an jan kunne da Mamie ta sake mata, sai bayan fitarsu Mamie kuma ta fashe da kuka saboda tunanin rayuwar da yarta za tayi a gidan yawa.


Kasancewar a gidan Baba Papa ya koyi *sunna* hakan yasa basu tarar da wasu 'yan tarban amarya ba bare abincinsu, mutanen gidan ne kawai kuma yara na islamiyyar dare dan haka sai uwayen, tarba aka musu sosai tare da Baba aka musu iso zuwa d'akinta, Papa ne ya kama hannun Khairat ya zaunar da ita bakin gado sannan ya zauna zauna kujerar dake kallonta, su Mammie ma zaune sukayi kusa da ita kafin Papa ya kalli Baba yace "surukin namu yana nan? ina so zan d'anyi magana dashi."

"Ba damuwa, ina jin ai baiyi nisa ba, bara na dubo muku shi." Baba ya fad'a tare da fita waje.

A gidansu Ishaq aka kira Umar Faruk tun saman hanya gabanshi ke faduwa, haka ya shigo cikin gidan har kuma d'akin, Papa ne ya masa nuni daya zauna kusa da Khairat, kallon Papan yayi ya kalli wajen da zai zauna sannan ya matsa a hankali ya tsoma k'ugunshi, duk da fuskarta a rufe take da mayafi amma sai yake ji a jikinshi hararanshi take, kuma kuwa hakaneπŸ˜‚dan bayan harara harda murgud'a baki da gunaguni.


Papa ne ya fara da "Umar Faruk, ga Khairat nan, mun kawo maka ita, kuma amana muka baka, muna fatan zaka rik'e mana ita abisa gaskiya da amana, Umar Faruk na yarda da kai, bana jin akwai ranar da zata zo ka bud'i baki ka gorantawa Khairat akan taimakon daka mana, ka sani Umar Faruk akwai ranar da Allah zai tashemu kuma ya tambayemu yanda muka zauna da iyalenmu , kayi adalci a tsakanin matanka domin hakan ne kad'ai zaisa ka samu rabo a ranar gobe k'iyama, kasan wani abu Umar Faruk, ba wai gaggawar aurar da Khairat bane muke da har yasa muka baka ita a waccen ranar, kawai dai na yarda da tsatson daka fito, kuma ina da yak'ini akan tarbiyar daka samu, ina son Khairat sosai fiye da komai a duniya, domin ita kad'ai na mallaka, bawai ina son zamanta anan bane dan nasan dole kafin ta saba zata sha wuya, amma darasin da zata koya a zamanta anan d'in shine yafi min komai dad'i, dan nasan *tarayyarku* zata zamar mana alkairi."

"Daga qarshe kuma, ina sake jaddada muku da kuyi hak'uri da junanku, Umar Faruk, akwai abinda ya kamata ka sani a game da Khairat, tana fama da wata muguwar rashin lafiya wacce idan ta taso mata takan shiga tsakanin halin rayuwa da mutuwa, duk da ince kusan nine silar wannan rashin lafiyar, amma dai a yanzu ina fatan kai ka zama maganin wannan cutar, wacce damuwa da kad'aici ne suka janyo mata ita, da fatan zaku zauna lafiya, Allah ya muku albarka, Allah ya baka abinda zaka ciyar da matanka, Allah kuma ya baka ikon yin adalci a tsakaninsu."

"Ameen." mutanen d'akin suka amsa dashi.

"Insha Allahu Baba zanyi k'ok'arina wajen kawar da kowace damuwa a tare da ita." cewar Umar Faruk yana satar kallonta.

Murmushi Papa yayi yace "Allah ya baka iko , ke kuma baki ce komai ba?" inji Papa yana kallon Khairat.

A hankali ta d'ago da kanta tana d'aga mayafinta tare da kafe Umar Faruk da ido, shima ita ya kalla amma ganin kallon da take masa bana arzik'i ne yasa ya kawar da kanshi, maida kallonta tayi ga Papa tace "nayi muku alk'awarin zama dashi...." sai kuma tayi shiru ta sake kallonshi, sai dai shima a lokacin ya kafeta da ido yana jiran yaji me za tace, ba tare data d'auke kai daga gareshi ba tace "har abada."

Wani irin farin cikine Umar Faruk yaji ya mamayeshi ba tare da yasan dalili ba, su kaka kuma hak'uri dai suka sake jaddaja musu suyi da junansu, nan suka tashi zasu tafi Umar ma ya mik'e dan rakasu, da gudu Khairat ta k'arasa ta rumgume Papa ta fashe da kuka, nan ya shiga rarrashi da ban magana tare da k'ok'arin yakiceta a jikinshi amma ta cije , a lokacin kuma Mammie ta janyo hannun Umar Faruk ba tare da kowa ya gani ba ta bashi magungunan Khairat tace masa,

"Wannan sune maganinta idan ciwonta ya tashi, ina fata zaka zamar mata waraka , a k'arshe ma ku jefar da maganin saboda rashin anfaninshi gareku."

Kai ya girgiza yana mamakin wane irin ciwo ne, ko dai aljanu gareta? ya tambayi kanshi, murmushi yayi ya rik'e hannun Mammie yace "na miki alk'awarin haka, insha Allah."

Lokacin kuma muryar Baba ta dawo dasu yana fad'in "kai Umar Faruk, kamata dan Allah su samu su tafi."

Kallon Baban nashi yayi yana tunanin ta yanda zai fara rik'eta, wasu yawu ya had'iya tare da yin k'unar bak'in wake yayi kansu zai b'anb'areta, ita kuma tunda taji ance ya rik'eta ta sake sark'afe Papa tare da lab'ewa bayanshi tana fad'in "ni wallahi ba zan zauna, kawai ku tafi dani, wannan fa mugune ba imanine dashi ba."

Papa ne ya kalli Umar Faruk da yayi tsaye yana sauraronta yace "dan Allah ka rik'e matarka kaji."

A hankali ya matso ya fara k'ok'arin b'anb'areta daga jikin Papan, da taimakon Papan ya samu suka rabata dashi, da sauri Papa ya bar d'akin tare dasu Mammie, tana ganin haka ta sake fashewa da kuka tana fizge kanta tana so ta fita, shi kuma rik'eta yayi sosai hakan yasa take k'ok'arin zubawa a guje, da k'arfi ya sake jawota ta fad'o kanshi ya matseta sosai a jikinshi, sake volume tayi tana kukan shi kuma sai wutarshi ta d'auke d'uf , a hankali taji yana shafa bayanta yana fad'a mata wani "shiiiiiiii, ya isa haka to." kamar yarinya k'arama, da sauri ta janye jikinta ta fad'a saman gado ta kwanta tana ci gaba da kukanta , shi kuma tab'e baki yayi ya fita daga d'akin sai gidansu Ishaq.


Umar Faruk bai dawo gidan ba saida *23:30* tayi sannan, yana shigowa ya shiga d'akinshi ya cire kayan sannan ya shiga wanka a ban d'akinsu ta tsakar gidan, yana fitowa kuma ya sake shiga d'akin a shirya cikin doguwar riga fara qal duk kai da kawon nan yayi shine cikin sand'a kar Baba yaji, sannan ya fito ya nufi d'akin amarya.

_Kuzo mu raka ango siyan baki_πŸ˜‚πŸ˜

Yana shigowa ya sameta yanda ya barta sai ajiyar zuciya take saukewa a hankali alamar bacci ya d'auketa, kashe mata wutar d'akin yayi ya fita ya rufe k'ofar tare da rufe gaba d'aya kewaye sannan ya koma d'akin tuzurai 😁Umariri kenan.

Ya jima baiyi bacci ba suna waya da amarya Zuby wacce take farin ciki take ganin kamar ta hanashi gabatar da daren farkonshi , nikam nace 😏 _kin rako mata duniya dai, lokacin da zai yishi ma sai kin shigo gidan_, suna gama waya kuma saiya d'auro alwala ya fara jera nafilfili har asuba, kiran farko ya bud'e k'ofa a hankali danya koma d'akin amarya ya tasheta, amma ina duk hanzarinshi Baba ya rigashi , domin kuwa yana bud'e k'ofar sai kuwa Baba a bakin panpo yana d'ibar ruwa a buta , cike da kunya da sanyin jiki ya nufi d'akin ya bud'e ya shiga ciki, tana nan har yanzu kwanciyarta kawai ta gyara, saida ya gama kallon qafafunta da suka sha lalle suka yi tsaf dasu sannan ya tab'a qafar, a hankali ta fara motsawa harta tashi zaune ta wartsake sosai, kau da kai yayi yana shan k'amshi yace "ki tashi kiyi sallah, lokaci yayi."

Wata muguwar harara ta dalla masa tare da juya baki, qasa da sama ya kalleta sannan ya wuce abinshi, har tayi kwance kuma taji gumi ma ya isheta, tashi tayi ta cire mayafin jikinta da d'an kwali sannan ta mik'e ta cire rigar atamfar sannan ta d'auki t-shirt matsatsa mai k'ananan hannuwa tasa, bata cire zanin ba dashi ta fito d'an k'aramin kewayen nata, duk da duhun asuba saida ta gama kallon ko ina, tabb', wai itace zata rayuwa a wannan gidan, hayaniyar da take ji yasa ta lek'a ta gajeruwar katangar saboda ta fita tsayi, kai komo kawai mutanen gidan keyi yara da manya sunata alwala, da mamaki take kallon mutanen da ko ganinta ba suyi ba, a ranta tace "duk mutanen gidan ne wannan kamar ana biki, lallai ma.", a qalla sunkai ashirin kosu haura ashirin, kujerun da aka jera a wajen ta zauna duk da fitsarin da take ji amma tana so ya zo ya nuna mata ban d'akin.


Ana gama sallah suka kamo hanyar zuwa gidan, a hanya kuma Baba saida yama Umar Faruk fad'a akan abinda yayi, anan take ya bada hak'uri tare da alk'awarin kiyaye gaba, suna shigowa Baba ya tsaya d'akinshi na soro, Abbakar yayi kewayenshi dake had'e da nasu Umar, su Usman ma suka shiga d'akinsu dake kusa da kewayen iyayensu mata, saida ya shiga tsohon d'aki ya had'a kaf abin buk'atarshi dan tarewa d'akin amarya sannan ya fito da kaya nik'i nik'i, yana shigowa ya tsaya kallonta ganinta zaune da alama ba tayi sallah ba.

"Kinyi sallah?" tambayar daya wurga mata kenan.

Tashi tayi daga kishingid'ar da yayi ta fara rabka hannuwa tana jujjuyasu tana fad'in "toh malam, ina zanyi sallah? ka nuna min inda zan kama koda ruwa ma bare nayi alwala, naga gidan naku har yanzu bak'in da suka zo biki basu tafi ba, to ina zan fita bansan kowa ba."

Ya gane akwai cin zarafi a maganarta, amma saiya dake ya nuna mata da hannu yace "ga ban d'akin nan."

Yana fad'a ya wuce da kayanshi ya shige d'akin ya ajesu a inda yaga wuri kafin yayi zaune yana tilarwar karatu, tunda ta lek'a taga matsatsan bayin ta fito ta sameshi d'akin tace "wai malam me kake nufi? waccen abar itace wurin wanka, da komai da komai?"

"Itace, idan zaki shiga ki shiga, idan ba zaki shiga ba ki zauna a haka matsalarki ce." ya fad'a ba tare daya kalleta ba.

Cikin d'aga murya tace "inaaa, wallahi ba zan iya ba, to wannan idan na shiga zan iya tsayuwa ma kuwa? tunda ni dai ba gajera bace, uwa uba kuma kai, ya za kayi kenan?"

"Babu ruwanki dani." ya fad'a a daqile.

"To dama me yayi ruwan nawa da kai, ni dai ka samo min gurin da zanyi wanka a wale , amma ba wannan kurkukun ba."

Tana fad'a ta koma gado ta zauna, ganin da gaske take kuma gari na haske yasa yace "ki tashi kiyi sallah, in yaso kyazo kici gaba da zaman har sarkin zama ya sameki."

"Ba zanyi ba har sai nayi wanka."

"Ki tashi nace." duk da jin amon muryarshi ba wasa amma bata tashi ba.

A zafafe ya taso yayo kanta yana fad'in "dake fa nake magana kina jina kinyi shiru, zaki tashi ko saina b'allaki?"

Gabanta ya tsaya yana kallonta itama kuma shi take kallo, tsaye ta mik'e fuska a had'e tace "wai me? dukana za kayi? hahaha, kai dai kasan da ganina wallahi ba zan daku gareka ba, dan ba zan tsaya sanya ba wajen zage k'arfina mu daku da kai ba, idan kuma hakan ya gagara tofa akwai k'ungiyoyi da dama masu kare hakk'in mata, wallahi tsaf zansa a d'aure min kai."

Saida ya shafi kansa yace "idan harna tashi dukanki, to ki sani dukan da zan miki bama zaki iya tuna meya faru dake ba bare har kiyi k'arata ba, shi yasa nake so ki bini a hankali mu zauna lafiya."

"Yanzu wuce kiyi sallah, dan akan wasa da sallah wallahi sai ajimu dake a kaf garin nan."

Ba yanda ta iya dole ta wuce ta shiga ban d'akin ta kama ruwa sannan ta fito tayi alwala ta koma d'akin, saida ta jima kafin ta samu hijab d'in da Mamie ta d'inka mata sabbi sannan ta d'auki sallaya zata shinfid'a ta kallesa da harara tace "ina ne gabas?"

A tunaninshi iskanci ne kawai amma ta sani dan haka yace "ki kalleni kiyi sallahn."

Ai kuwa shinfid'awa tayi tana kallonshi ta kabbara sallah, ganin da gaske take sallaceshi za tayi yasa yayi saurin cewa "wai ke bahaguwar inace, yanzu nan shine gabas? dallah malama can zaki kalla."

Wata hararar ta sake banka masa sannan ta juya ta daidaita ta ci gaba da sallahta, tun daga sallah ya fahimci akwai matsala kuma yayi niyyar gyara mata, tana idawa shi kuma ya shiga wanka kasancewar akwai k'aramin panpo ciki, yana fitowa ya samu ta koma kan gado tayi kwance, gashi yana so ya canza amma ya kasa, lura da tayi da hakan yasa ta tab'e baki ta juya masa baya tana fad'in "me zan kalla a jikin? sai kace wata mayya."

Bai kulata ba harya gama shirinsa cikin jan raiga mai dogayen hannu da bak'in wando da takalma qafa ciki bak'ak'e, yayi kyau sosai sai turarenshi daya fesa sannan ya juya zai fita daga d'akin dan yau babu aiki , saurin juyowa tana fad'in,

"Kaga malam, wannan shirgin kayan naka ka tattaresu daga nan, ka bud'a armoire (drower) nan na qarshe akwai wuri ka zubasu."

Ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfi kafin ya fara d'iban kayan yana jerawa, duk kayan saida ya samar musu matsuguni sannan ya rufe, ya sake juyawa zai fita kenan Ruk'ayya ta rabka sallama daga k'ofar d'akin....

*Me kuka ce fan's a game da zaman nan*😁

_Ina sonku masoyana , addu'o'inku ma kad'ai sun ishemu farin ciki._ Allah barmu daku.πŸ’
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

_My πŸ…±K, ina tayaki murnar kammala wannan novel mai suna, πŸ’˜ *NA BAKI RAYUWATA* πŸ’˜, wallahi Allah har cikin raina nake ji kamar na gani da idona a lokacin mutuwar Affan, sosai wannan labarin ya shigeni dan saida na zubar da hawaye na gaske😭, Allah yasa wannan fad'akarwa da ki kayi taje inda muke so kuma ayi anfani da darasin ciki, Allah ya baki ladar tare da sakamakon gidan aljanna, Allah kuma ya qara miki lafiya sai mun jiki a next novel._ *ina yinki tawan.*


_My Seeya, barka da fara sabon novel mai suna *QADDARATA*, daga jin sunan kasan zai bada kala dan kowa da tashi qaddarar, Allah ya baki ikon kammalashi lafiya kamar yanda kika fara lafiya, fatan nasara my see see._😘

_Bismmilahir-rahman-rahim_


2⃣1⃣



"Wa'alaiki salam, Ruk'ayya shigo." cewar Umar Faruk.

Wata sallamar ta sake yi tare da bud'a labulan d'akin ta shigo, saida ta sunkuya ta aje kwanukan dake hannunta sannan ta d'ago tace " ina kwana yah Umar, ina kwana aunty Khairat." ta fad'a tana kallonta.

Umar Faruk dai ya amsa amma banda Khairat da take tunanin itace matar tashi, jin bata amsa ba yasa ta kalli Umar Faruk tace "dama Mama ce tace na kawo muku abin karinku."

Juyawa
Showing 51001 words to 54000 words out of 186119 words