suna fara tafiya ta kalli Mamie tace "kin fad'i gaskiya, Aqilu yace baya sona yanzu."

Kallonta tayi tace "Khairat karfa ki fahimcini ba daidai ba."

Murmushi tayi kawai ta fito da abin sauraronta ta manne kunnuwanta suka ci gaba da tafiya, suna isa gida ta nufi d'akinta bata kuma sake fitowa ba sai da aka fara kiran sallah magrib, har tayi zaune Mamie tace "ki tashi kiyi alwala kizo muyi sallah."

Cike da nuna rashin jin dad'i tayi shiru, a tsawace Mamie tace "dake nake magana kina jina kinyi shiru."

Ganin ta tashi ta wuce cikin kasala Mamie ta dora da fad'in "kuma wallahi ya zama na qarshe da zan miki magana akan sallah, inba rainin wayo ba kamarki shekara ashirin da biyar amma ba zaki iya gaishe da unangijiki ba sai kinga dama."


*Wallahi a zamanin nan da muke ciki, matasanmu musamman yan mata bamu cika tsayar da sallah ba, musamman idan sunyi kwalliya a fuskarsu ba'a son asa ruwa a wanke, ya kamata muji tsoron Allah mu gane saida sallah ne muke iya banbanta kanmu da kafirai, Allah ka bamu ikon kyautata ibadunka, Allah kasa mu zama masu tsayar da sallah domin samun sassauk'an hisabi, Allah kasa mu tsayar da sallah domin ta zama abokiyar zamanmu a qabari dan haskaka makwancinmu.*

*Da sallah ne muke cika cikakki musulmi, idan sallanmu tayi kyaune ake kyautata mana zaton sauk'in hisabi, sallah itace take tayamu zama a qabarinmu kafin lokacin da za'a tashi qiyama, sannan mai tsayar da sallah ko a cikin al'uma zaka ga fuskarshi na annuri, sannan hadisi ne ingantance cewar wuta bata tab'a duk wata gab'a da take samun ruwan alwala, wannan 'yar qaramar tunatarwa ce badan na fiku sani ba.*πŸ‘

Babu wata matsala a game da alwalarta sai dai a game da sallah kam akwai yar mishkila, saboda cikin minti biyu ta gama sallah ta fito falo, hakan yayi daidai da fitowar Papa zashi makaranta, ganin littafi a hannunshi yasa tace "Papa sai ina kuma?"

Kallonta yayi yace "majlisin malam zani d'aukar karatu."

"Toh , Papa karatu aka koma?"

"Eh 'yata, kuma kema kin kusa komawa insha Allah."

Wata dariya tayi ta nufi fridge tana fad'in "wasa kake Papa, haka dani na shiga makaranta."

Papa ma wucewa yayi dan lokaci nayi yana fad'in "ba'a girma da neman ilimi, tunda ki kaga na fara zuwa to kema ki shirya dan kin kusa."


Yau ma dai kamar kusan kullum ita kad'ai taci abinci bayan iyayenta sunci, tana kammalawa ta koma d'aki tana chat tana sauraron waqoqi har dare yayi sosai tana bacci cikin kwanciyar hankali.

Mamie ce ta shigo d'akin ta zauna kusa da ita, ta jima tana kallonta tana murmushi kafin ta tofa mata addu'a ta sumbaci goshinta, zani taja mata ta rufeta ta tashi saida ta kashe mata wutar d'akin kafin ta fita, tun fil'azal Khairat bata bacci da duhu a d'aki hakan yasa ma bata kashewa.

Kusan abune daya zamar mata jiki mafarkin abinda ya faru da ita, kamar a zahiri haka ta dinga tuna lokacin da take kokawa da Musa har lokacin da yayi nasarar kutsa kanshi a tsakiyar matancinta, razananniyar qarar da tayi a mafarkinta itace ta bayyana har a zahirin baccinta.

"Ahhhhhhhhh, Mamiena, Papa wayyo Allah, Papa, Papa zasu kasheni, Papa gasunan fa, zasu sake min fyad'e, dan Allah kuzo ku taimakeni, Mamie, wai baki jina ne? wallahi gasu nan."

Wannan duhun d'akin shi ya qara firgitata haka ta dinga kiran su Mamie da Papa, kasancewar d'akinsu a qasa yake hakan yasa basu ji da wuri ba, Mamie ce ta fara ji ta tayar da Papa, a sukwane suka shigo d'akin nata Mamie ce ta kunna wuta Papa kuma ya tunkareta, tana ganin haske ya mamaye d'akin tayi saurin rarrafowa ta nufo Papa, fad'uwa tayi wajen tahowa Papa ne yayi saurin tashinta ya rumgumata a jikinshi yana shafa kanta yana fad'in "shiiiiii, shalele, gani nan Papanki ne kinji, ya isa haka."

A haka suka taka ya qarasa da ita bakin gado suka zauna yana ci gaba da fad'in "ya isa kinji gimbiya, ba kowa anan, d'ago idonki ki gani, nine Papanki da kuma Mamienki, ki nutsu kinji."

A hankali kuwa ta daga ta kalli Papa sannan ta kalli Mamie dake gefenshi, da sauri ta kamo hannun Mamie ta sake fashewa da kuka tace "dan Allah Mamie ki kwanta anan, wallahi zasu iya dawowa su sake min fy......" Mamie tayi saurin rufe mata baki.

A haka suka ci gaba da rarrashinta har Mamie ta d'ora kanta a qafafunta bacci ya d'auketa, a zaune Mamie ta kwana tana shafar kanta tare da mata addu'a.


Suna a haka Papa ya shigo ya tashesu suyi sallah asuba, tare da Mamie sukayi sallah sannan Mamie ta sauka ta shiga madafa, Papa na zauna yana hutawa a lambu tare da linttafinshi yana bitar karatu wayarshi tayi qara, ganin mai kira yasa ya rufe littafin ya d'auka, bayan sun gama a sukwane ya shigo cikin falo yana kiran sunan Mamie.

Da sauri ta fito tana fad'in "gani Alhaji, lafiya dai irin wannan kira haka?"

Cikin karsashi yace "lafiya lau, albishirinki?"

"Goro." ta fad'a tana masa kallon tuhuma.

"Yanzu mukayi waya da shugaba, kuma tabbatar min suna so ayi komai a gama, dan haka goben nan zasu kawo lefen Khairat."

Cike da tsantsar farin ciki tace "kai, Alhamdulillah, amma naji dad'in wannan albishir, Allah ya nuna mana goben yasa alkairi."

"Ameen, yanzu kije ki lissafa mana duk abinda za'a buqata dan tarbar bak'i, tunda kinsan fa harkar babba ce."

"Ah sosai kam, kar kaji komai, ba buk'atar kashe kud'inka, ni zan d'auki wannan nauyin insha Allah."

"Kenan dai bikin Khairat na nad'e hannayena nasha kallo?"

Cikin dariya tace "a'a ba duka ba, dole ai kasan zamu shiga cikin aljihunka idan biki ya matso."

"To shikenan, Allah ya kaimu."

πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ


Misalin 11:35 Khairat ta tashi ta fito falo, Mamie na madafa tare da masu kama mata aiki, cikin takon mai nuna magagin bacci ta shiga madafa, ma'aikatan ne suka gaisheta amma babu wanda tako kalla bare ta amsa, wajen kayan lambu ta nufa ta d'auki kokomba ta wanke ta fara kaiwa bakinta, sai lokacin ta kalli Mamie tace "ina kwana Mamie."

"Lafiya k'alau, kin tashi lafiya."

"Um." ta fad'a tare da fito ta koma d'akinta tayi wanka ta shirya cikin riga da siket na kanti kanta ba d'an kwali ta fito falo ta zauna, 12:30 su Mamie suka kammala abincin rana, jerawa sukayi a dinning sannan Mamie ta shiga wanka, 13:00 Papa ya shigo gidan tare da sabin masu tsaron lafiyarsa su biyu, suma da qyar ya yarda aka had'ashi dasu.

"Sannu." cewar Khairat.

Kallon teburin yayi sannan yace "sannu shalele, an gama abinci."

Tana kallon wayarta tace "umm , sun gama."

Hannunta ya kamo yana fad'in "muje ki zuba min naci gimbiya, yunwa nake ji sosai."

Itama cewa tayi "amma ai ban iya zubawa ba, bari na kira Biba ko Saude su zuba maka."

"A'a nike nake so ki zuba min." ya fad'a yana zaunawa.

Kallonshi tayi ta kalli kwanukan abincin ajiye wayarta tayi a gefe zata d'auki plate wayar Papa tayi qara, d'auka yayi yana fad'in "hello, manager har kun karaso ne?"

Jim yayi na d'an lokaci kafin yace "to ku shigo kawai ina ciki nima yanzu na shigo."

Aje wayar yayi ya kalli Khairat yace "wallahi wani hazik'in matashi ne aka samu a masana'antarki, baifi wata biyar zuwa shida da fara aiki ba, amma harya fito da sanfirin takalmin da suka karb'u a duniya, shine nace manager ya kawoshi nan mu gaisa na kuma masa godiya, sannan zan shirya masa qarin girma a ma'aikatar."

Ko qala ba tace ba, kwanon farar maca ta bud'a wacce tasha kwalliya da waken gwangwani, cokali ta d'auka ta fara k'walbatowa rabi na zubewa qasa rabi na shiga plate d'in, da qyar ta zuba a plate d'in har Mamie ta fito ta samesu, kwanan miya ta bud'e wacce tasha kaji daga-daga, (😁mutuniya ba) tana saka cokalin miyar ta fallatso mata sai a ido, qara ta saki tare da sakin cokalin a miyar, sake fallatsowa yayi sai kuwa a fuskarta da jikinta, zafin da taji yasa ta dinga tsala ihu tana fad'in "na k'one , na k'one, zafi Mamie ki goge min."

Mamie da hankalinta ya koma kan manager da matashin saurayin nan, Umar Faruk daya tsaya ya kasa gudawa yana kallon Khairat na tsalle tsalle duk jikinta na kadawa, da qyar ya had'e yawu suka fara takawa suka zauna inda Papa ya nuna musu, sai lokacin Khairat tayi shiru ta sauke idonta akan Umar Faruk.

Kallonshi take sosai shi kuma ya d'auke idonshi daga kanta, Mamie ce ta katseta da fad'in "ki zuba musu abinci mana shalele."

Da sauri ta kalli Mamie, da ido ta mata alama ta zuba musu, turo baki tayi gaba tace "nifa Mamie ban iya ba, kina gani abinda ya faru yanzu na k'ona kaina."

Wayarta ta d'auka ta juya zata bar wajen Papa yace "gimbiya baki zuba min ba."

Lokacin data juyo idonsu suka had'u dana Umar yana mamakin abinda ta fad'a wai bata iya zuba abinci ba, to kenan ya zata dafashi??? ya tambayi kanshi.

Zagayawa tayi wajen da yake zaune ta mik'a masa hannunta tace "zo."

Da mamaki yake kallonta yana mamakin fitsararta, kallon Mamie da Papa tayi wanda suma ita suke kallo tayi murmushi tace "kunyarku yake ji fa."

Kallonshi tayi tace "kaga ka taso magana za muyi da kai."

Tana fad'a ta ja hannunshi suka nufi d'akinta, tana shirin bud'a k'ofar d'akin ta tsaya cak saboda ji da tayi ya qara matse hannunta, kasa juyowa tayi saboda yanda taji tattausan hannunshi ga kuma gabanta daya fad'i, a hankali ta fara zame hannunta daga nashi shi kuma baisan ya akayi ya kasa rik'e kanshi ba harya qara matse hannunta, saida ta raba hannunta da nashi sannan ta ta bud'e d'akin ta shiga, kallonshi tayi ganin yaki shigowa, alama ta masa da ido akan ya shigo, a hankali yake takawa yana jin bugun zuciyarshi na k'ara tsananta, da sauri ya juya ya kalleta saboda ganin ta rufe k'ofa.

Gabanshi ta tsaya tace "ranar na tambayeka amma baka bani amsa ba, amma daga baya sai nayi tunani naga cewa, ai ko ban tambayeka nasan kai kana daga cikin mak'iyana, kuma kayi farin ciki da abinda ya sameni, kuma nasan ko kai ka samu dama zaka iya yin abinda wad'ancen sukayi."

"To ba komai, kuma ku sani ni Khairat ba zan nuna gazawa ba, ba kuma zan nuna bana da daraja ba, kamar yanda ba zan saka damuwa a raina ba, dan haka duk mai bak'in ciki sai dai ya mutu."

Wucewa tayi ban d'aki tana fad'in "zaka iya tafiya."

Shi kuma ya kasa komai gaba d'aya ji yake yayi sanyi ya rasa duk kuzarinshi, binta yayi da kallo ya kasa fita, Khairat ce daga ciki ta jefo da gaba d'aya kayanta data cire harda qananan ciki saboda bata tunanin yana nan har yanzu, yana ganin haka yayi saurin juyawa zuciyarshi kamar zata fito daga qirjinshi, saurin fita yayi daga d'akin hannunshi a kan saitin zuciyarshi a hankali yake takawa yana tambayar kanshi.

_Me yasa nake jin haka idan na ganta?_

_Me yasa na rasa duk wani k'arfi na dana tsaya gabanta?_

_Me yasa gabana ke fad'uwa idan na tuna koda sunanta?_

_Me yasa nake jin daban a tare da ita?_

πŸ˜›πŸ˜›πŸ˜›πŸ˜›πŸ˜›πŸ˜› _no amsa._

Khairat na sakar ma kanta ruwa ta lumshe ido, da sauri ta bud'e idonta saboda ji da tayi kamar hannun Umar Faruk a nata hannun, ajiyar zuciya ta sauke ta sake rufe ido saboda yanda ruwa ke sauka a kanta, Umar Faruk dai ta sake gani yana mata wannan kallon da fassararshi sai _my aunty Aishan Umma_, haka ta fito daga wanka wannan tunanin ya kasa barin qwaqwalwarta harta d'auki riga da wando ta saka qanana sannan ta sake fitowa.


Tare suka ci abinci dasu banda Umar Faruk da ruwa kad'ai yake d'an kurb'awa suma sai Papa ya mishi magana, anan Papa ya masa godiya tare dasa albarka sannan yace "kaci gada da k'wazonka, insha Allah za kayi nasara a duk inda ka samu kanka, Umar Faruk..ko?"

Cikin murmushi yace "eh, *Umar Faruk Ahmad Adam*."

Da mamaki Papa ya kalleshi yace "Ahmad Adam, kai d'an malam Ahmad ne?"

Shima da mamakin ya kalleshi yace "eh ni d'ansa ne."

Mamie Papa ya kalla yace "Allah sarki, kinga fa yaron nan d'an malamin da nake d'aukar karatu wajenshi ne, haba shi yasa ka zama mai hazak'a da basira."

Dariya Mamie tayi tace "yaron kirki ne kam, Allah ya maka albarka."

Kiran daya shigo wayar Khairat ne yasa ta tashi daga wajen, Mamie ce tace "baki ci komai ba fa tun safe."

Juyowa tayi tace "Muzaffar ne yake kira, ina zuwa."

Mamie da Papa ne quka kalli juna suna murmushi, sabanin Umar Faruk da gabanshi ya buga ranshi kuma ya b'ace, cup d'in ruwa ya d'auka ya kifa saida ya shanye sannan ya mik'e yace "ni zan wuce, na gode."

Ficewa yana jin tsanar Muzaffar a zuciyarshi ba tare da sanin shi Muzaffar d'in ba, kasa jiran manager yayi dan haka ya tari taxi ya mayar dashi ma'aikata, haka ya isa ya zauna yana kallon tafin hannunshi da Khairat ta rik'e, wani hamshak'in murmushi ya saki saboda tuna da yayi lokacin da take tsalle tana ihu, sake fashewa yayi da dariya haka kawai ya rasa dalili amma farin ciki yake ji har k'ark'ashin zuciyarshi, Ishaq daya lura da hakane ya tab'oshi ta gefe yana fad'in,

"Da alama fitar nan tayi kyau ko?"

B'ata fuska yayi yace "ban gane ba, kai baka san ina muka je bane?"

"Na sani mana, amma naga ka cika dariya kai kad'ai."

"Son gulma ko? to ba zaka ji ba."

Dariya Ishaq yayi ya maida hankalinshi ga aikinshi yana fad'in "da alama ka fad'a soyayya abokina."

Da k'arfi ya kalleshi yace "me? soyayya fa kace? to aini dama ba sabon shiga bane, ko ka manta ina da Zuby?"

Saida Ishaq ya kalli k'wayar idonshi yace "watak'ila yanzu ne ka fad'a soyayyar gaskiya kuma wacce ta dace, idan kuma ba haka to zai iya yiwuwa yanzu ne zuciyarka ta kamu da so."

"Son wa?"

"Son Khairat mana." Ishaq ya fad'a.

Sake kallonshi yayi dan baiyi tsammanin yaji abinda yace ba a fili, zunbur ya tashi daga wajen ya fita filin ma'aikatar, maganar Ishaq ce kawai ke dawo masa a qwaqwalwa ta cewa "son Khairat mana."

A zafafe ya furta "ina, hakan ba zai yiwuba, bata dace dani ba, zuciyata ba zata tab'a min wannan rashin adalcin ba."

_Aikin gama ya gama_πŸ˜›.

*Team Khairat, ku fito muyi rawa*πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ


Daga yanda Muzaffar yake wa Khairat magana yasa ta fahimci akwai wani dake faruwa, musamman da yace ya matsu gobe tayi a kawo kaya a tabbatar mishi ita tashi ce, kashe wayar tayi ta dawo falon lokacin manager ma harya tafi, tsaye tayi gabansu tana kallonsu tace "me yake faruwa? me Muzaffar yake fad'a?"

Papa ne yace "kinga shalele ki zauna kici abincinki , an jima za muyi magana."

Cikin d'aga murya tace "wane naci abinci bayan abinda wannan mahaukacin yake fad'a, kawai ku fad'a min koma miye naji."

Mamie ce ta d'aga murya itama ta tashi tsaye tace "Khairat!!! mu kuke d'agawa murya? kece kika haifemu ko mune muka haufeki? idan bamu fad'a miki ba me za kiyi?"

Kallon Mamie tayi fuska ba annuri tace "maganar aure yake, kuma nasan kinsan babu wanda zai min aure ba tare da ina so ba, idan alk'awarina kuka mishi to ku janye danni ba 'yar roba bace da za'a min haka."

Zata wuce Mamie ta fizgota da k'arfi za tayi magana Khairat ta fizge hannunta da k'arfi tana fad'in "ki sake ni, karki sake tab'ani, ki fita a harkarta."

Duk da qoqarin b'oye hawayenta kasawa tayi saida kukan ya k'wace mata ta fara magana cikin kuka "na sani kuma dake iyayena kuna ganin yanzu bana da wata kima da daraja ta 'ya mace, inba haka ba babu ta yadda zaku fara min maganar aure ba tare da sanina ba.:

Wucewa tayi ta barsu nan Papa kuma ya kalli Mamie cikin b'acin rai yace "....😁
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

_Wallahi har qasan raina ina jin dad'in addu'arki sister Alawiyyah, gaskiya ke ta dabance, samun fan's irinki abin alfahari ne kuma burin kowace marubuciya, duk da soyayyar da kike nuna min bata isa ba saida kika nunawa my Heenat d'ina itama tata soyayyar, lallai muna yinki over, luv u dear.😘_


_My aunty *Aishan Umma* ina mik'a godiyata sosai a gareki, kinsa naji cewar ni mai sa'a ce a rayuwa😊 muna alfahari dake a matsayin shugabar k'ungiyarmu._


*Welcome Back my πŸ…±K.*πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


1⃣6⃣


"Wai me yasa kike wa yarinyar nan haka, akan me zaki dinga d'aga mata murya, me yasa kika cika b'acin rai ne Na'ima?"

"Au, nice ma na daga mata murya kenan? kai yanzu baka ga abinda tayi ba? wai me yasa kake hakane? Khairat fa 'yarmu ce mu muka haifeta ba ita ta haifemu ba, to akan me zata dinga tsaya gabanmu haka tana fad'a mana abinda ranta yake so?"

Tsaye ya mike yace "koma dai miye kinsan muna da laifi, kamar Khairat ace mun tsayar da maganar aurenta ba tare da saninta ba a wannan qarnin da muke ciki, kinga dole ranta ya b'ace."

D'akin Khairat d'in ya nufa yana ci gaba da mita, tundada ta shiga d'aki ta kwanta kan gado tana kuka, jin kanta na sarawa yasa tasan yanzu zai fara mata azababben ciwon daya saba, tashi tayi da nufin d'auko magani tasha amma bata kai ga wajen ba jiri ya d'ebeta ya yadda, rintsegudu ido tayi ta dafe kanta sosai tana fad'in "wayyo Allah kaina, kaina zai fashe, kaina Papa ciwo yake, dan Allah kazo kai kad'ai ke sona, Papa kaina zai fashe, wayyo, ahhhh, wash."

Papa na shigowa ya ganta kwance a qasa, da gudu ya k'arasa wajenta yana tambayar "shalele lafiya, meya faru, kanne ke ciwo halan?"

Kamata yayi ta tashi ya taimakata ta zauna akan gado yana fad'in "wallahi shi yasa bana qaunar abinda zai b'ata miki rai saboda irin haka."

Da sauri ya nufi wajen maganinta ya d'auko ya kawo mata tare da ruwa ya taimaka
Showing 33001 words to 36000 words out of 186119 words