sank'ama mata tambayoyi ita kuma tana kakkaucewa wajen bata amsar, a qarshe kuma cewa tayi "itama tana girki ne?"

"A'a, tunda tazo bata tab'a girki ba." cewar Ruk'ayya.

"To kenan me take? sai dai a dafa a bata taci."

"To ai kusan yanzu itace ma ke ciyar damu, tunda da kayan abincin data siyone muke anfani dasu."

"Me? wai kina nufin abincin da naci ma d'azu a cikin wanda ta siyo ne?"

"Qwarai kuwa." cewar Ruk'ayya cike da mata kallon baki da tunani.

"Tabb', bari yah Umar d'in ya dawo, wallahi ba zan sake cin abincin wajenku ba, kayan abinci kawai zai siyo min na dinga dafa nawa nima."

Cike da iya shege Ruk'ayya tace "amma da ice zaki dinga dafawa ko?"

"Kawai ma bayan naga harda gas gareku." ta fad'a tana hararanta.

"Toshi gas d'in dashi kika taho jiya? ai shima ita ta siyoshi, dan haka ki sake tunani ma dan wannan ba mafita bace."

"Keni dallah tashi ki bani wuri." korarta tayi daga d'akin ita kuma ta kira Mama ta fad'a mata halin da ake ciki.

Nan Mama tace "to bari kiji in fad'a miki, wallahi saikin tashi tsaye sosai, inba haka ba kin shiga uku a wannan gidan, kuma abinda za kiyi yanzu shine, da zaran ya dawo ki fad'a mishi ya siyo miki kayan abincinki da qaramin rechau wanda zaki dinga aiki dashi, tunda kinga nan da kwana biyar zaki fara zuwa ecole (school), kuma wallahi karki yarda ya fad'a miki wasu maganganu, ki dage saiya siya miki, kuma ki tabbatar kinyi aiki da abinda na baki jiya."

"To Mama, amma ai ita bansan yanda zanyi na bata tasha ba."

"Saboda ke ba mace bace? kisan duk irin dubarar da za kiyi tasha, inba haka ba wallahi data fara haihuwa kafin ke, kin shiga uku."

Da haka sukayi sallama tana tunanin hanyar da za tabi wajen saka ma Khairat wannan maganin.

**************


*12:15*, Khairat ta shigo gidan ba tare da sallama ba kamar yanda ta saba, ganinta da babbar leda a hannu yasa Ruk'ayya taje da sauri ta karb'i ledan tana fad'in "sannu da zuwa aunty Khairat."


Saratu da Zuby na zaune waje d'aya ko kallonsu ba tayi ba,
yaran ma duk suna zaune da sannu suka bita , jakarta ta bud'a ta fito da d'an qaramin kwalin chocolat taje inda yaran suke zaune duk rabawa kowa harta qare, godiya suka mata Zuby kuma ta bita da kallon banza, ita kuma ta wuce d'akinta saboda iyayen duk suna d'aki, Ruk'ayya ce ta bud'e k'ofar ta shigar mata da ledar har ciki, aje jakarta tayi tare da hijab tana kallon d'akin an kitsashi ba kamar yanda suka barshi ba, kallon Ruk'ayya tayi tace "Ruk'ayya waike ba kya gajiya da aikine, naga ko ecole ba kya zuwa sai d'ora girki da shara, a haka zaki qarene?"

Cikin dariya tace "aunty kenan, ai wannan aikin shine aka saba mana dashi, duk 'yan uwana mata wanda sukayi aure saida sukayi wannan aikin, kuma karatu na gama ne shi yasa bana zuwa, na addini kad'ai Baba yake qaramin wani lokaci yah Usman ko yah Umar, amma yanzu dai mun daina da yah Umar."

"Me yasa?" ta tambaya lokacin da take b'alle bras d'inta.

"Tunda yayi aure ne."

Towel ta d'aura a qirji ta nufi k'ofar fita tana fad'in "ki bud'a ledar nan dogayen rigunane ki d'auki wacce ta miki."

"Wayyo aunty Khairat na gode sosai, Allah ya saka da alkairi."

Bud'awa tayi sai dai bata tsaya zab'eba kawai ta d'auka ta fita cikin farin ciki, Zuby na ganinta taja dogon tsaki tace "aikin banza, ashe dai gulma ce tasa daga ganinta kika tashi harda wani karb'an abun hannunta kamar uwar data haifeki."

B'ata rai Ruk'ayya tayi tace "Zuby, ki fito idona na rufe, ba ruwana dake baruwanki dani, kar kisa muyi abinda za'a mana dariya, tom."

"Nak'i d'in marar kunya, kenan nice za kima rashin kunya dan kinga daidai muke dake? to ko kina so ko ba kya so nima matar yayanki ce, kuma na tabbata ni ya fara sani dan haka na fita kusanci dashi."

Wani dogon tsaki Ruk'ayya taja kafin tace "kishin ne haryake neman haukataki , ya muna magana zaki canza mana maudu'in da muke kai."


Tana fad'a bata tsaya sauraranta ba tayi d'aki ta nunawa Mama rigarta, godiya tama Khairat tare da saka albarka, dan tasan kyauta ce ta bata ba rok'a tayi ba.

****************


Koda ta fito daga wanka kwalliya sosai tayi sannan ta shirya cikin d'aya d'aga cikin rigunan data siyo, nanfa ta d'auki k'yali da shek'i ga gyaran data sha, gama shirinta ba wuya kuma taji dumin Umar Faruk a tsakar gidan, d'an kwalin rigar ta yane kanta dashi ta feshe ko ina da turare sannan ta tsaya tana jiran shigowarshi.

Shi kuma yana shigowa yaji wani sanyi ya ratsashi saboda ganin d'akin bud'e ya tabbatar da sanyin idaniyarshi ta dawo, Zuby ce tace "sannu da zuwa yah Umar."

"Yawwa,sannu da gida." ya fad'a tare da yin sama da Fateema.

"Ango kasha k'amshi." cewar Saratu.

Yana kallonta yace "ke ko ba kya gajiya da tsokana, to wane k'amshi kuma?"

"Au, nice zan fad'a maka wane iri? ai kai kafi kowa sani."

"Kinga da surutun nan, ki tashi ki kaimin ruwan wanka zafi miki ki samu lada."

Hararanshi tayi tace "bana so, sai yaune ka tuna dani kenan?"

Waro ido yayi yace "lah, ladar ce ba kya so? lallai ma matar nan, gaba d'aya ba kya kula dani yanzu."

"Haba Ummaru, 'yan aljanna biyu ne fa a tsakiyarka, ai kuwa kaga ba buk'atar na zama ta uku a bayansu."

Wani shu'umin kallo yama Zuby wacce itama shi take kallo yace "ga d'aya nan a kusanki ma, amma ya banga d'ayar ba?"

Da hannu Saratu ta nuna mishi d'aki tace "to ai kasan basan fitowa take ba, ina jin tana ciki tana shirin tarbanka, dan naji qarar ruwa alamar tana wanka kenan."

Cike da zolaya yace "toke me kike anan? baki je kiyi shirin tarban naki mai gidan ba."

"Ni! rufa min asiri, mu ai tsohine mun barma 'ya'ya da k'annanmu."


*Irin wannan tunanin shi ke kashe mata dayawa ta hanyar nakasasu, kice ke kin tsohuwa saboda kawai kinyi haihuwa uku hud'u, mijinki kuma yana buk'atar ganinki cikin kyakyawan yanayi da shiga, koda ke kika haife duniya, wallahi saimun gyara sosai idan har muna son ganin daidai, a duniya karki yarda namiji ya rainani saboda rashin tsaffa da kama jiki, daya rainaki ta wannan hanyar kin gama shiga tara.*

Wucewa kawai yayi bayan ya aje Fateema, tashi Zuby tayi tabi bayanshi hakan yasa ya juyo ya kalleta, cikin jin kunya tace "magana nake so muyi."

Baice mata komai ba sai sauya akalarshi da yayi ya nufi d'akinta, yana shiga ya zauna a bakin gado ita kuma ta tsaya, kallonta yayi ganin bata zauna ba kuma ba tace komai ba, kammo hannunta yayi ya zaunar da ita akan cinyarshi d'aya tare da zura hannunshi ta bayanta ya rumgumota, d'aya hannunshi yasa ya rik'o hannunta yana wasa da yatsunta ya qurawa fuskarta ido yana kallo, ita kam kunya ce ta rufeta hakan yasa tayi qasa da kanta ta kasa had'a ido dashi, cikin taushin murya yace "ina jinki, kince za muyi magana kuma kinyi shiru."

Wala-wala ta fara da ido tana tunanin yanda zai fahimceta idan ta fad'a masa, tasan halin Umar Faruk sarai, zai iya baud'ewa ya kuma bita da masifa, sumbar daya watsa mata a wuya yasa ta dawo daga tunani, hannunshi yasa cikin rigarta ya fara wasa da cinbiyarta, sake maimaita mata yayi "ki fad'a mana ina jinki."

Hannu tasa tana shafa wuyanta tana fad'in "yah Umar dama, nan da kwana biyar ne zan fara zuwa ecole, to kuma ni ba wani cin abinci ba nake sosai, shine nace da zaka siyo min nawa kayan abincin saina aje."

Shiru tayi tana d'an satar kallonshi dan ganin yanayinshi, shi kuma shiru yayi yana tunanin abinda ta fad'a, tabbas yasan wannan ba tunaninta bane, amma kuma ba matsala bane tunda ko Saratu itama wani lokacin ita kad'ai take abincinta, dan haka zaiyi yanda take so kodan gudun magana.

Fuskarta ya shafa yace "hakan ya miki?"

Kai ta d'aga alamar eh tare da fad'in "eh yah Umar."

"To karki damu, an jima zan siyo miki kayan abincin, abinda ban siyo ba kuma saiki fad'a min saina baki kud'in ki qarasa siyowa."

Ko kad'an ba tayi tunanin haka ba hakan yasa tayi murmushi tace da cewa "na gode yah Umar."

D'agata yayi daga jikinshi ya mik'e tsaye yace "ba komai."

Matso da ita yayi kusanshi yace "ba kiyi kewata ba ko?"

"Kai yah Umar." ta fad'a tana rufe fuska wai ita kunya.

Janye hannayen nata yayi yana kallon fuskarta yace "to naji, in dai ba kiyi kewata ba karki sumbaceni, amma idan kinyi ki sumbaci bakina."

Zuro mata fuska yayi yana jiran yaji saukar sumba, a tunaninta ta ballagazar da kanta sau d'aya dan haka ba zata qara ba, dan haka kawai ta fito daga d'akin ta baroshi tana dariya, dan gani take ya fad'a tarkonta, yana ganin haka ya fito shima kai tsaye d'akin habibiya ya wuce.



Da sallama ya shiga kamar yanda ya saba, amma saiya kasa shiga ciki yana kallon Khairat dake tsaye tana sakar masa tsadadden murmushi, ganin ya tsaya yasa ta karasa ta janyo hannunshi ya k'arasa shigowa ciki, saida ta sakar masa kyakyawar sumba a baki tare da wata a goshi kafin tace,

"Ya kake kallona haka?"

Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi kafin ya lumshe idonshi ya kuma bud'e a kanta yace "dole na kalleki, a gaskiya baby dana rasaki da nayi asara babba, sai yanzu nake qara fahimtar sa'ata a rayuwa."

Wani murmushi zaka gane kurenka ta masa kafin tace "ai dukanmu ne masu sa'a a rayuwa."

"Amma ba kamar ni ba." ya fad'a yana rumgumata jikinshi.

"Haka dai kace." ta fad'a itama tana qara shigewa jikinshi.

"Kema masallaci zaki je?" ya tambaya yana kallonta.

"Meka gani to?"

"Naga kema kinyi kwalliya sosai ga kuma doguwar riga, dan sau d'aya na tab'a ganinki da doguwar riga irin haka, shima a lokacin bikinki."

Duka ta kai masa a qirji tana fad'in "kaji mutum wai bikina, kace bikinmu, shagali da wani ango, kuma d'aurin aure da wani ango."

Dariya yayi yace "dama fa ara mishi ke nayi na wannan lokacin kawai, amma ba kiji yanda zuciyata ke tafasa ba."

Da kallo ta bishi tana fad'in "ashe dama ka jima kana sona, amma shine a lokacin dana mareka ka kasa hakura saida ka rama, ba kaji yanda naji zafi ba a ranar, har saida hannunka ya kwanta a kumatuna."


Dariya yayi ya fara cire kayansa yana fad'in "to ai ko yanzu idan kika min laifi ba zan tsaya wasa ba wajen zabgeki da mari, kawai dai nasan yanzu idan na mareki a kumatu , to ni kuma zanji zafin a zuciyata ne."

Mak'ale masa tayi a baya tana kukan shagwab'a tace "hamago kawai, wallahi saina rama marin soyayyata daka min."

Juyowa yayi da ita gabanshi yana kallonta yace "in dai zaisa kiji dad'i to na amince ki rama."

Yana fad'a ya bata kumatun da nufin ta rama, Khairat kam saida ta share 'yar qwallan data taho mata dan sosai taji zafin marin daya mata a ranar, hannu ta d'aga iya k'arfinta dan dama ce ta samu da ba zata bari ta wuceta ba.


Kamar saukar aradu Umar Faruk yaji saukar wani gundumemen bahagon makahon.....πŸ˜‚

_Wallahi kinmin daidai tawajena, hi yasa nake sonki._

*Wasu na mamakin Umar Faruk ya kwana a d'akin Khairat, to ai ban gama sati d'aya na d'akin Khairat ba, dan haka ku tayani lissafi, yau juma'a a labarin Khairat da Umar Faruk, kenan gobe asabar ne zata cika sati, lahadi kuma sai kuzo mu rakashi d'akin amarya Zubysss.πŸ˜‚*

_Koda yake naga mutuniyar ma bata da masoya._
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bansan me zan iya cewa masoyana ba, hak'ik'a kuna sakani farin ciki, comment d'inku na nishad'antar dani, tsakanina daku sai dai ince Rabbi ya bar qauna._ πŸ’žπŸ’•πŸ’—


_Bismmilahir-rahman-rahim_


3⃣4⃣


Kamar saukar aradu Umar Faruk yaji saukar wani gundumemen bahagon makahon kiss a kumatunshi, ji kake

"Muahhhhhhhhh."

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Sakin fuskarshi tayi data rik'e tace "idan kaga hannun Khairat ya tab'a fuskarka yanzu, toka sani shafata ne za tayi."

D'aukarta yayi ya dinga juyi da ita a tsakaiyar d'akin yana dariya yana fad'in "har kinsa zuciyar maza ta tsinke, na d'auka fa marina za kiyi, ashe dai sanin da nayiwa Khairat."

Itama dariyar take kafin tace "kaga saukeni kaje ka shirya lokaci na tafiya."

Sauketa yayi ya qarasa cire kayan jikinshi kafin ya shiga wanka, koda ya fito ta fito mishi da kayan da zai saka, da taimakonta ya shirya tsaf cikin farar shadda da hula da takalmi, kallon kanshi yayi a madubi yana qara daidaita hularshi, saurin d'auke hular tayi a kanshi ta d'ora a kanta tace "kenan ban iya sakawa ba? shine har kake gyarawa."

K'ugunta ya janyo ya had'a da nashi yasa hannayenshi ya fara daidaita mata zaman hular a kanta, murmushi ya sakar mata yace "dubi madubi kiga yanda kika gama had'uwa, shi yasa nace miki ni mai sa'a ne."

A tare suka kalli madubin yana bayanta ita tana gaba, wani irin bala'in kyau ne sukayi ga matuk'ar dacewa da junansu, wayarshi ya ciro a aljihu ya d'auketa photo ita kad'ai sannan ya musu tare, cire hular yayi ya mayar a kanshi yana fad'in "kinsan me zai faru?"

"Saika fad'a." ta fad'a tana d'anewa a bayanshi.

Goyeta yayi yana fad'in "kawai kizo muje tare, saina biya na ajeki gida wajen Mamie, idan na dawo saina biyo na d'aukoki."

Da k'arfi ta wuntsilo ta sauko daga bayanshi tana fad'in "da gaske baby, Allah kuwa ina son zuwa, ina kewar Mammie."

Kumatunta ya kama yace "sosai ma, tukwicin wannan kwalliyar ne na bayar."

Wajen aje jakunkunanta ta nufa ta d'auko qarama ta hannu baka mai walk'iya ta saka wayarta, Umar Faruk na kallo ta bud'a wata jakar ta kwaso kud'i ko k'idayawa ba tayi ba ta zuba a jakar, kallonshi tayi tace "na shirya, zamu iya tafiya?"


Da ido kawai ya mata alama sannan yace "d'auko min sallaya."

D'aukowa tayi ta rik'e a hannunta, shi kuma ya kama hannunta suka fita, saida ya saki hannunta ya rufe k'ofarsu hakan kuma yayi daidai da fitowar Abbakar shima ya shirya zai tafi, Zuby da Saratu kam kallon ikon Allah suke, wato masallacin ma tare zasu tafi kome? anya Umar Faruk bai haukace baπŸ˜‰ ku shinshina kuji, cikin taushin murya Khairat tace,

"Baby, tunda ga yah Abbakar ai saiku tafi tare ko."

Kallonta yayi ya juya ya kalli Abbakar dan baiga fitowarshi ba, cike da k'aunar juna Umar Faruk yace "abokina ka jirani saimu tafi ko?"

Abbakar dake nad'e sallayar hannunshi ne yace "amma ai naga kamar tare zaku fita? taya zan shiga wannan harka ta amare."

Wani wawan tsaki da Zuby taja tare da tashi tabi ta gaban Khairat ta wuce d'akinta, Umar Faruk kam ko kulata baiyi ba yace "kaga muje, dama akwai maganar da nake so muyi da kai."

Saratu dake zaune acan tace "Allah yasa dai ba cewa za kayi ya qara aure ba."

Kafin suyi magana Mama Sa'a tace "ke kuma shine matsalarki, kenan mu nan mutuwa mukayi da muke zaune da kishiyoyin?"

Umar Faruk ne yace "rabu da ita Mama, aure ai ya zama dole yah Abbakar ya qara, tunda ita yanzu ta tsufa."

"Kai tsufan lafiya, waya fad'a maka?" cewar Saratu.

Saida ya kama hannun Abbakar suka nufi hanyar fita yace "da bakinki kika fad'a, ko awa d'aya ba ayi ba."

Khairat ma bayansu tabi ko murmushi ba tayi ba bare dariya, Mama Sa'a kuma harda daga murya tana fad'in "saikin dawo 'yar albarka."

"Mtsssss, tusa kai ba kwarjini." cewar Mama Maimuna dake zaune akan tabarma.

A hassale Mama Sa'a tace "dawa kike Maimuna? ni kike fad'awa haka? ni tsararki ce da zaki shiga harkata?"

"Eh, dake nake kiyi abinda za kiyi, aikin banza kawai, duk kibi kina wani nanik'ewa yarinya ita kuma tana wulak'antaki, kawai saboda tsinannan kwad'ayi."

Aifa tsaye aka mik'e suka fara surfa bala'i Mama Umar Faruk dasu Saratu Ruk'ayya hak'uri kawai suke basu, dan duka mazan sun tafi masallaci Zuby kuma naji tayi banza dasu, saida suka kusan dakuwa sannan suka hak'ura kowace ta shiga d'akinta, amma duk da haka kowace na jefo magana daga d'akin nata.


**************


A mota kam Abbakar da Umar Faruk hira suke sosai data shafesu, Khairat na baya tana jinsu amma tana latsa wayarta har suka isa, tare suka fita da Umar Faruk suka tsaya a k'ofar gidan, saida ya d'an saci kallon Abbakar dake mota kafin ya shafi fukarta yace "ki gaishe dasu Mamie, idan muka taso zan biyo."

Cikin shagwab'a tace "amma fa nidai daka barni har zuwa dare, kaga idan ka dawo daga wajen aiki sai kazo muje."

"Nak'i d'in, ina buk'atar ganinki a kusa dani."

"An gama ranka shi dad'e , yanda kake so haka za ayi."

Tana fad'a ta matsa kusa dashi ta sumbaci bakinshi tana kallonshi ta kece da dariya, "meye?" cewar Umar Faruk.

"Ba komai, saika dawo." duk tayi maganar ne a cikin dariya tare da tura k'ofar gidan ta shiga.

Mai gadi dake alwala cikin shirinshi na masallaci ya taso da nufin gaisheta ta daga masa hannu tare da tsayawa tace "kaci gaba da alwalanka, ba'a so ana tsayawa idan ana alwala, komai mahimmanci abu kar yasa ka dakatar da alwalarka, musamman ma idan abun ya shafi harkar duniya ne."

Tana fad'a ta shige ciki shi kuma ya biya da kallo tare da tunanin yaushe Hajia Khairat ta zama Ustaza haka, yauma farin ciki sosai Mamie da Mammie sukayi, musamman data fad'a musu shiya kawota kuma yace zai biyo idan ya taso, hak'ik'a sunga shiriya sosai a tare da yarsu, kuma sunyi farin ciki marar misaltuwa."

*************


Yana shiga mota ya tayar suka wuce, Abbakar kam kallonshi yake yana dariya, ganin dariyar tayi yawa yasa kalleshi yace "wai miye haka dan Allah? ya zaka sani a gaba kana dariya."

Yanda yayi maganar yasa ya fahimci rai zai iya b'acewa dan haka yace "kalli madubi ka gani."

Gyara madubin yayi ya kalli kanshi a ciki, ganin bakinshi yayi ja kamar yasa jan baki yasa ya fahimci me yake wa dariya, a lokacin kuma ya fahimci
Showing 90001 words to 93000 words out of 186119 words