tayi ta fita Umar Faruk kuma yace "na gode."

Kwanukan ya d'auka a aza saman karamin tebur d'in dake tsakanin gado da doguwar kujerar nan sannan ya zauna yana kallonta, ita kam ta d'aure fuska dan haushin Ruk'ayya taji sosai, ganin shirun ba zai gyarashi ba yasa yace "ki taso ki zuba mana abinci muci."

Cikin jin zafi tace "nice zan zuba maka abincin? to kar Allah yasa kaci, ni kaga nayi kama da masu zuba abinci, ka tab'a jin koda labari cewa an ganni ina zuba abinci ko a gidanmu, ai kaima ka gani ranar, dan haka in zaka zuba ka zuba kaci."

Shiru ya d'anyi na dakiku kafin ya tashi inda yaga tarin kayan anfani ya d'auko plate da cokali guda biyu ya zo ya fara zubawa, saida ya gama ya kalleta yace "ki taso kici."

Sai lokacin ta juyo ta kalleshi, plate d'in ta kalla ganin malku ne (naman kan rago) yasa ta yamutsa fuska tace "wacece? ni zanci wannan abun? bana cin a wannan lokacin, kawai kaci abunka."

Banza yayi da ita kawai ya d'auki bred ya fara ci, yana cikin ci yaji tace "wannan itace matar taka?"

Cak ya tsaya daga kai lomar da zaiyi, cikin rashin fahimta ya kalleta amma sai tace "wallahi ban tab'a tunanin zan iya auren mutumin da bai min alk'awarin zama dani ba ni kad'ai, amma sai gashi wai na auri mai mata, mtssss, rayuwa kenan."

Shi kam tunani yake ko bata san jiya ne aka daura masa auren ba, to kenan iyayenta basu fad'a mata ba kome? ji yayi abincin ya fita a ransa kawai ya fita ya wanke hannu ya dawo d'akin, zaune ya sake yi a inda ya tashi yana kallonta yace "wannan ba *matata* bace, kanwata ce, jiya ne aka daura aurena kuma bata tare ba sai nan da wata biyu."

Kallonshi tayi amma saboda harbawar da zuciyarta keyi yasa ta kau da kai tana guna guni, ganin ba za tayi magana yasa ya mik'e ya d'auki turare ya fesa a hannayenshi sannan ya fice ya barta.

Wani bala'in haushinshi take ji dama matar duk da bata ganta ba, ta jima cikin d'akin har rana ta take sosai sannan ta mik'e ta nufi waje, tana fitowa daga 'karamin kewayen nata ta ja ta tsaya tana 'kerewa gidan kallo, yana da girma amma yawan mutanen gidan yasa duk an matseshi , duk yara na islamiyya sai Ruk'ayya kad'ai dake k'ok'arin hura wuta dan d'ora abincin rana, sai kuma Saratu dake kamata da alama a tare ake girkin , iyayen kuma su uku suna zaune duk da dai biyu sun had'e kai waje d'aya, ta jima tsaye babu wanda ya lura da ita har saida haushi ya kamata yanda Ruk'ayya keson wutar ta kama amma tak'i kunnuwa.

Cikin d'aga murya tace "waike dan Allah ba zaki bar hura wutar nan bane, duk kibi kin cika mutane da hayak'i, wai dama da ice kuke d'ori? tabb'."

Sai lokacin kowa dake wajen ya kalleta, Ruk'ayya ma juyowa tayi sai dai kafin tayi magana ke Mama Maimuna sai kika ce "kaji kuma wani iyayi , to in tabar hura wutar dame za ayi d'orin kenan, ko kin tanadar mata wani abun ne? kiji rashin kunya kai."

Mama Sa'a ce tace "ah to dai ganin min hanya, mu za'a yiwa fitsara anan."

Takowa Khairat ta fara yi saida tazo har gabansu ta tsaya tace "daku nake magana? kunji nace kune da kuka samin baki? to karku sake min irin haka in baso kuke na muku rashin mutunci ba, ku in banda ma qaddara kun isa ku ganni cikin gidan nan bare har kumin katsalandan a harkata."

K'wafa tayi ta juya zata wuce Sa'a tace "ke mu kike wa rashin kunya? kinsan komu su waye? muma fa iyayen Umar Faruk ne."

"Saime? idan ku iyayenshi ne nace saime? na shiga harkarku ne? ko kuma shi yace ku dinga shiga tawa sabgar? to bana so."

Tana fad'a ta juya su Mama da Saratu kam mamaki ma ya gama kashesu daga inda suke, sun d'auka ta tafi ne amma sai suka ga ta sake fitowa da wayarta a hannu da da d'aya daga cikin kujerun nan, ta zauna a bakin k'ofar shiga b'angaren nata, waya take sai dai basa jin me take fad'a, Ruk'ayya dai ta samu wutarta ta kama bayan wuya da tasha ta fara aikinta gadan gadan, su Mama Sa'a kuma sai satar kallonta suke daga nan amma baki ya mutu murus, a qalla awa d'aya aka d'auka tana zaune ta d'auki wayarta ta kara a kunne saboda kiran daya shigo, tana d'auka tace "ok ina zuwa." ta kashe wayar.

Mik'ewa tayi ta nufi hanyar da take tsinkayan mutane na wucewa ba kallabi a kanta sai wannan k'aramar rigar da zane ta fita, a k'ofar gidan ta tsaya wasu samari ne guda biyu, "yawwa ku shigo dashi." ta fad'a tana komawa cikin gidan, Umar Faruk dama ba wane wurin yaje ba suna k'ofar gida shida Ishaq da wasu abokansu su hud'u, ji yayi kamar zai fashe daya tsinkayeta amma ya zaiyi, sharewa kawai yayi ya basar, suna shiga gidan ta kalli Ruk'ayya tace "ki nuna musu inda zasu aje miki."

Kowa da mamaki yake kallonta da samarin nan saboda ganinsu sun shigo da cuisinière mai guda hud'u da kuma butalin gas 5kilo, duk da suna cikin zulumin abinda tayi saida kowa yayi farin ciki, sai dai mahaifiyar Umar Faruk najin d'ard'ar, da ba lallai malam ya amince ba, nan Ruk'ayya ta nuna musu cikin wata rufa suka had'a mata shi sannan suka juya inda Khairat ke tsaye, dama ta shiga d'aki ta fito kudi ta mika musu masu yawa sukayi godiya suka tafi, itama d'akin ta koma tayi kwance Ruk'ayya da Saratu kam ai sai suka mayar da tukanansu sama cikin jin dad'i, ai sai suka manta da rashin kunyar da tayi, yayin da Mama Sa'a da Mama Maimuna suka waro ido suke tunanin sunci arzik'i dan haka su kwantar da kai kawai.



Yara na dawowa kowa baki bud'e sai farin ciki, nan suka rankaya suka nufi d'akin dan ganin amarya, suna zuwa sun sameta ta kasa bacci tunda ta shiga zafi ya dameta duk da pankar data aje gabanta, binsu take da wani kallon tsana da qyama suma yaran kallonta suke saboda kallon da take musu, ganin sunyi zaune wasu qasa wasu akan kujera yasa tace "ku kuma fa daga ina?"

Mai wayon cikin ne yace "ina kwana aunty amarya, mu kannan yah Umar ne, jiya bamu ganki ba kuma kuma da safe muka tafi islamiyya, shine yanzu muka zo mu ganki."

"Tofa." ta fad'a a wahalce.

Sauka tayi daga kan gadon ta nufi wata coffre ta bud'a ta d'auko chocolat tazo ta bawa kowa d'aya d'aya, haba ai da gudu aka fita ana murna ana ji wannan amarya mai ja ce, πŸ˜‚haba kudai baku sani ba, dan ita ta basu ne dansu tafi su barta, suna fita cikin farin ciki suka had'u da Umar ya shigo gidan shima, cike da murna sukayi kanshi Zeinab na fad'in "yah Umar, kalla aunty amarya ta bamu."

Fuskarta ya shafa yace "ince dai kun mata godiya?"

Shiru sukayi suka kalli juna dan sun manta, ai da gudu suka sake komawa shi kuma ya nufi wajen Ruk'ayya da Saratu dake girki baki bud'e har sun kusa kammalawa, "wannan fa 'yan mata?"

Saratu ce ta harareshi tace "na fad'a maka ka daina kirana yan mata fa."

"To naji na daina, ina kuka samu wannan?"

"Aunty Khairat ce tasa aka kawo mana." cewar Ruk'ayya.

Baice komai ba sai juyawa da yayi ya nufi b'angaren nasu ya rasa wane hali zuciyarshi ke ciki, farin ciki ko k'unci, yaran na fitowa shi kuma ya shiga, tana ganinshi ta sauko daga kan gadon tana fad'in "yawwa, dama kai nake jira dan Allah ka nuna min inda zanyi wanka, tun jira rabona da wanka fa."

Kallon kwanukan daya ci abincin safe yayi yace "amma aina nuna miki ban d'akin, watak'ila dama wankan bai dameki ba shi yasa kike so ki d'ora laifin ga ban d'akin."

"Humm, nida nake shiga cikin baho cike da ruwa nayi link'ayata son raina, shine zaka nuna min wannan banzan douche d'in kace wai a ciki zanyi wankan, kaima kasan ba zai yiwu ba wallahi, koka nuna min inda zanyi, ko kuma na tub'e a tsakar gidan nan nayi wanka na dan nan ne kad'ai zai isheni , in yaso sai kace ma kowa ya rufe idonshi."

"Kije kiyi mana ga wajen nan, inkin fasa ba sunanki Khairat ba."

Yana fad'a ya juya ya bar d'akin saboda rashin sanin wacece Khairat, bayanshi ta biyo ya dauka shi take bi hakan yasa ya tsaya yana kallonta, wuceshi tayi ta fito tsakar gidan ta fara kalle kalle, Ruk'ayya ce ta hanga tana kashe wuta da alama ta gama, "ke." ta kira Ruk'ayya dashi.

Kallonta Ruk'ayya tayi tace "na'am."

"Zo nan." da sauri ta taho ta tsaya gabanta, babban bokiti nake so ki cika minshi da ruwa ki aje min nan, saiki fad'awa iyayenku su koma d'aki zanyi wanka."

Da mamaki fal a fuskarta ta kalli Umar Faruk dake bayansu, ce mata yayi "kije kici gaba da aikinki."

Wucewa tayi Khairat kuma ta kalleshi tace "aini ba musaka bace zan iya da kaina."

Kewayen nasu ta shiga ta samu bokiti ta fito da nufin d'ebo ruwa a bakin panpo kawai ya rik'e hannunta yace "ke mahaukaciyar inace ne? me yasa baki da h...."

Bai k'arasa ba tace "wallahi karka kuskura ka k'ara kirana bana da hankali ko mahaukaciya, wai ka mantani ne da kake fad'a min haka, ko dan kaga ana kiranka da mijina shi yasa, to bana so wallahi kaji na fad'a maka."

Fizge hannunta tayi zata wuce yayi saurin tare gabanta yace "kinga saurareni, kiyi hak'uri ki shiga nan kiyi wankan , daga baya zansa a gyara miki tunda ba kya so, kinji?"

Zuyawa tayi ta kalli douche d'in sannan ta kalleshi tace "idan ma baka gyara ba wallahi ni zansa a gyara, kawai douche sai kace gidan b'eraye."

Wucewa tayi ta fad'a douche d'in ta cire kaya ta cillo kamar yanda ta saba, rigar data jefo qarshe sai a fuskar Umar Faruk da zai shiga d'akin, a hankali ya janye rigar ya kalli sauran kayan pants bras da zanin, sunkuyawa yayi ya kwashesu ya shiga dasu d'akin ya aje mata, ruwa ta makama jikinta ta d'auki sabulu ashe bata d'auko ba ta d'auka douche d'inta ce wacce ke akwai komai da komai, cikin d'aga murya tace "ka d'auko min sabulu."

Shirun da taji yasa ta sake bud'a murya tace "ka d'auki min sabulu, kona fito na d'auka."

Tun maganar farko ya jita ya kuma tashi d'auka, jin abinda ta fad'a a qarshe yasa yana fitowa daga d'akin yana b'are sabulun a cikin kwalishin yace "kizo ki d'auka mana."

Yana daf da kaiwa bakin douche d'in ita kuma ta zuro da kai za tayi magana, da sauri ta dage qirjinta saboda bayyanar da yayi tare da komawa ciki tayi shiru, yana ganin haka ya juya bayanshi ya mik'a mata sabulun yana fad'in "gashi."

Amsa tayi sannan ta fara wankan shi kuma ya fita daga gidan, Ruk'ayya ya turo ta d'auki kwanunan ta wanke sannan ta zubo musu wani abincin ta kawo ta aje, duk lokacin Ruk'ayya na mamakin irin wankan da take data jima haka, amma a b'angaren Khairat fad'a da guna guni kawai take rusawa daga cikin douche d'in, sai gashi ta fito ba tare da tayi abinda ta saba yi ba, ta fito daga wanka cikin minti sha biyar zuwa ashirin, d'aki ta shiga ta fara shiri tana ci gaba da masifa akan douche d'in.

K'aramar riga ce mai siraran hannaye ta kamata sosai duk ta fito mata da mamanta , sai kuma jan siket data d'ora a saman rigar har kusa da qirkinta, a bud'e yake siket d'in sai dai iya gwiwa ya tsaya mata, raba gashinta tayi gida biyu tasa k'ananan chouchou (ribom) ta d'aureshi, bata wani kwalliya ba sai turare data shafa ta kuma fesa sannan ta d'auki wayarta tasa takalma ta fito farfajiyar gidan.

Wata kujerar ta d'auka ta aza 'kofar kewayen nasu ta zauna dan zafi ya isheta, daga yaran har iyaye satar kallonta kawai suke babu wanda yayi magana, mahaifiyar Umar Faruk kuma tana so tayi magana amma tana jin tsoron wulak'ancin da zata mata, waqa tasa a wayar ta fara biyarta tana rausaya daga zaune, mak'ota da yan uwa suka fara shigowa ganin amarya, amma duk wanda ya shigo saiya nufi wajen mahaifiyar Umar Faruk ya zauna yana tambayar ina amarya, da an nuna masa Khairat saiya tashi yana addu'a Allah ya kyauta, a qarshe da taga kowa ita yake kallo, aje wayar tayi ta zuba tagumin rainin hankali tana bin kowa da ido itama, hakan yasa gidan yayi shiru sai magana qasa qasa.


Baba da Abbakar ne suka taho zasu shigo gidan ganinsu yasa Umar Faruk ya biyosu suka shigo, da sallama suka shigo amma ta Umar Faruk saita tsaya saboda ganin Khairat da wannan kayan a jikinta, Abbakar ma dai duk'e kai yayi qasa ya nufi inda mahaifiyarsu take zaune ya tsugunna, Baba ma haka ya k'araso jiki ba k'wari saboda ya riga daya shigo, kamar wanda k'wai ya fashema a ciki Umar Faruk ya tako ya nufi wajenta, yana kaiwa cikin zafin nama ya finciko hannunta yayi cikin d'akin da ita.

Qarar da tayi lokacin daya fizgi hannunta yasa Baba ya kalli Mama yace "kinga, tashi dan Allah kira minshi, sai yayi b'anna yaron nan kin sanshi da bak'ar zuciya, karya lahanta 'yar mutane."

Da sauri ta tashi ta nufi d'akin nasu, suna shiga ya jefata saman gado cikin b'acin rai, zaiyi magana ta rigashi da cewa "meye haka wai, kana haukane? ni sa'arka ce da zaka min wannan pigar kazar mahaukaciyar."

"Mtssssss." tsaki tayi ta fito daga d'akin zata sake komawa inda take, shi kuma dama tsakin yafi bashi ma haushi, da azama ya biyota ya cakumo hannunta ya juyo da ita da k'arfi, wani irin zafine daya ratsata saboda rik'on daya mata yasa ta janye hannunta daga gareshi hawaye fal idonta, kasancewar shima yayi niyyar sakinta yasa ta fad'a saman kujerun dake wajen, kuma bata fad'a da kyau ba kawai sai kujerar ta wuntsila da ita ta fad'i qasa, qara ta saki mai k'arfin gaske hakan yasa Baba dake can tsaye hankalinshi ya sake tashi, Mama kuma ta karasa danno kai ciki, samu tayi Khairat na kokarin tashi tsaye hakan yasa ta kamata ta tashi tana kallon Umar Faruk, "meye haka Umar Faruk, kana lafiya kuwa?"

Kallon matar Khairat tayi tace "kece mahaifiyarshi?"

Kai kawai Mama ta d'aga mata, kallon bayan hannunta tayi da har gurin ya karce jini ya fara fitowa saboda hannun ya had'u da bango, maida hawayenta tayi ta fizge hannunta daga Mama kawai ta koma d'aki, Mama kuma harara ta bishi da ita tace "ai saika fito mahaifinka na nemanka."

Juyawa tayi zata fita ya kamo hannunta ya rik'e ya marairaice yace "wallahi Mama ban mata komai ba, dan Allah ki fad'awa malam."

Wucewa tayi ta barshi kawai dole ya biyo bayanta, da hannu Baba kawai ya masa alama ya boyoshi d'akinshi, cikin sanyin jiki ya bishi d'akin suka zauna, cikin hikima Baba ya dinga mashi nasiha da gargadi har a qarshe ya dora da "ba haka ake ba Umar Faruk, a matsayinka na namiji, dole akwai bukatar kafi matanka hak'uri, saboda su matane kuma masu rauni , mace zata iya yin abu, kai a ganinka waouta tayi amma ita sai tace kuskure ne, dan haka dole ka dinga hak'uri wannan zuciyar taka ka dinga tausarta, musamman kai daka fara da mata biyu, duk ranar da Allah ya had'aku zama gida d'aya, dole zaka gane ba kada wayo dan dole sai sun gwara maka kai, nasan ka sani dan kai shedane akan zaman da nake da iyayenku, dan haka dan Allah bana son wannan yawan hushi da zafin zuciya, ka rage kaji ko?"

"To Baba, insha Allah zan gyara."

"To Allah yasa, yanzu kaje ka bata hak'uri dan Allah, sannan ka mata godiya akan d'awainiyar da tayi, dan mahaifiyarka ta fad'a min, tashi kaje Allah ya maka albarka."

"Ameen Baba, na gode ."

A haka ya tashi ya tunkari b'angaren nasu yana tunanin ya bata hak'uri kamar yanda Baba yace, ko kuma dai ya shareta kawai.

_Ya kuka ce? kuna ganin zai bada hak'uri, ko kuma zaiyi taurin kai?_😎😏


*Ina barar addu'arku yan uwa, Allah yaba mahaifiyata lafiya, tana jin jiki, yer uwata ma na fama da tasku na rayuwar aure, gidan miji da tsangwamar kishiya , plss ku tayamu da addu'a.*

_I love you sis Alawiyya._😘❀
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

*ALLAH KA KYAUTATA MAKOMARMU*πŸ‘πŸ˜­


_Bismmilahir-rahman-rahim_


2⃣2⃣


Da sallama ya shiga ya sameta zaune a tsakiyar gado tana share hawaye, har ga Allah har zuciyarshi yaji ba dad'i kuma yaji bai kyauta ba, bata amsa sallamar ba harya zauna kan kujera yana kallonta, hannunta na dama da yake fitar da jini ya gani, shi kanshi baisan lokacin daya zaburo ba yayo kanta yana fad'in "subhanallah, kinga jini kike fitarwa."

Zai kama hannun tayi saurin janye hannunta ta d'aga masa hannu tana fad'in " karka kuskura ka tab'ani, mugu kawai azzalumi, wallahi Allah saika sakeni na koma gidanmu, ba zan iya zaman wannan takaicin ba."

Wani tafarfasa yaji zuciyarshi nayi tare da bugawa da k'arfi, wajen kayanshi ya nufa ya bud'e ya d'auko wani magani pommade ya bud'e ya lak'ata a hannunshi ya matso zai shafa mata, tsaye ta mik'e akan gadon tana fad'in "nace karka tab'ani ko, ko ana dole ne? ban son taimakon naka."

Danya nuna mata ba damuwa yayi da ita ba kawai ya cilla mata maganin a jiki yace "idan kinga dama ki shafa da kanki, yarinya sai taurin kan tsiya."

"Nice yarinyar? Umar Faruk ni kake fad'ama yarinya? lallai *zaka gane kurenka* wallahi."

Zaune tayi akan gado shi kuma ya matso kusanta yace "yaushe aka haifeki to?"

Sama da
Showing 54001 words to 57000 words out of 186119 words