safe Mama."

Hannunta taji ta rik'e hakan yasa ta koma ta durk'usa tana kallonta, cike da jin dad'i da tsantsar qauna Mama tace "na gode yata, ubangiji ya saka miki da mafificin alkairinsa, Allah ya kareki daga sharrin masharranta, Allah ya baki abinda kike so, Allah ya saka miki da gidan aljanna, Allah ya albarkaci rayuwarki da zuri'arki baki d'aya, Allah ya sakawa iyayenki da alkairi, Allah ya kareki daga bakin duniya, Allah....."

Rufe bakinta Khairat tayi ta fashe da kuka ta fad'a jikin Mama ta rumgume, saida tayi mai isarta ba wanda ya bata hak'uri kafin ta d'ago ta share hawayenta ta rik'e hannun Mama sosai tace "Mama, kin kusa kasheni da farin ciki saboda wannan addu'ar taki, tunda nake a rayuwata ban tab'a jin addu'a irin wannan ba, ko mahaifiyar data haifeni bata tab'a kwatanta yimin irin wannan addu'ar ba, Mama nice da godiya bake ba, ina da yak'inin wannan addu'ar taki ba zata fad'i k'asa banza ba, a yanzun nan sai nake ji kamar ni 'yar aljanna ce kuma zan gama da duniya lafiya, Mama Allah ya bar mana ke, kuma nayi alk'awarin zama a gidan nan har qarshen rayuwata in dai har zan dinga samun irin wannan addu'a a wajenki."

Tana fad'a ta bar d'akin tana kuka, Umar Faruk ma bayanta yabi bayan sunyi sallama da Mama, yana shiga ya sameta kamar ba ita bace mai kukan nan harta murje idonta tayi kwance, sai dai abinda Umar Faruk bai sani ba ta rufe ido ne amma addu'a Mama ce ke yawo a qwaqwalwarta, kashe wutar d'akin yayi bayan yayi shirin kwanciya sannan ya kwanta a saman kujera, zunbur ta tashi zaune tana lalubar wayarta ta kunna haske, a daqile tace "malam nifa bana bacci a cikin duhu, ka kunna fitilar mana in dai ba wani abu bane a ranka."

Wayarshi ce a hannunshi yana duba kiran da Zuby tayi bai d'aga ba, ba tare daya kalleta ba yace "ni kuma gashi bana bacci a cikin haske, ya kenan za ayi?"

_To fan's ne zasu bamu shawara, ya kuka ce akashe ko a barta kunne?_

_Idan an kashe akwai d'an dannau mai taushe mutun cikin dareπŸ˜ŽπŸ˜‚, idan an bari kuma shed'anun aljanu na anfani da hasken su cutar da bil'adama._
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

*_MasoyanaπŸ’–, kune abin alfahari na, ina matuk'ar ji daku fiye da tunaninku, fatana Rabbi ya bar qauna tare da soyayya, nasan ba zamu iya had'uwa daku ba dukanku, amma ina fatan Allah ya sadamu da alkairinsa sannan ya taramu a aljannatul-firdausi._*πŸ‘πŸ‘

_Bismmilahir-rahman-rahim_


2⃣6⃣


Wajen makunnin ta nufa tana shirin kunnawa yayi saurin tare gabanta, d'auke idonshi yayi daga nata saboda masha Allah akwai girma kamar idon Barbie ga kuma kyau da yalwataccen gashi, "dan Allah ka matsa min na kunna, bana iya bacci a cikin duhu, tsoro nake ji."

Da kanshi ya nuna mata gado yace "kije kiyi addu'a saiki kwanta, babu abinda zai sameki da yardar Allah."

"Ba zaka gane ba, dan Allah..." bata qarasa ba saboda hannunta data kai ta kunna wutar shi kuma ya rik'e.

Janye hannunta tayi tana sauke ajiyar zuciya tace "shikenan, kar Allah yasa ka kunna, amma wallahi naji hannun mutum a jikina ana lalubata, to zaka sha mamaki dan saina fasa maka kai wallahi."

Dariya ce ta subece masa komawa yayi kawai ya kwanta, harta kwanta itama amma data rufe ido saita ga su Musa a idonta, sosai ta rintse ido amma duk da haka bata daina gani ba, bud'e idon tayi taga duhu sosai, zaune tayi ta kalli wajen da Umar Faruk yake tace "malam nasan ba kayi bacci ba, dan Allah ka taimaka ka kunna ko hasken fitalar wayarka ne."

"Wayarki fa?" ya fad'a cikin taushin murya.

"Haka kawai zan kunna harsken wayata har safe, ai tunda ka hana a kunna wallahi na wayarka zaka kunna."

"To zan gani, wayata ce kota wani."

"Kaji kamar mai wata wayar million d'aya, wallahi saika kunnata ko kuma."

Ta fad'a tana saukowa daga kan gadon, jin tahowarta yasa ya tashi zaune yana fad'in "ko kuma me?"

"Gani nan ai a aikace zan nuna maka."

Da hasken wayarta taga wayar tashi akan qaramin teburin dake tsakanin gadon da kujerar da yake, tunkararta tayi gadan gadan tare da kai hannu zata d'auka, da sauri ya d'auki wayar tare da ajeta bayanshi ya rumgume hannaye yace "ki d'auka idan ke jan wuyace."

"Dan Allah ka bani, wallahi bana iya bacci a duhu, kuma gashi dare keyi har yanzu banyi bacci ba, zanfa maka kuka wallahi ko kuma na fad'awa Mama."

"Wace Mamar?" ya tambaya.

"Mamank...." kuma kawai sai tace "Mamana."

Kallonta yayi dan ya mata tambayar ne dan yaji me zata ce, a hankali ya zura hannu ya d'auko wayar ya mik'o mata kamar sakarai, hararanshi tayi tace "ka kunna mana, meye saika wani bani a hannuna."

Baiyi magana ba kuma bai bar mik'a mata ba, cike da haushi tasa hannu ta karb'a ta kunna fitilar, murmushi tayi ta kalleshi tace "kaga tasirina ya fara aiki a kanka, tun ma ba'a je ko ina ba kenan."

Zaune yayi yana fad'in "ke bani wayata, tasirin me? kin d'auka dabararki ce tasa na baki?"

Juyowa tayi tana kallon qwayar idonshi ta soka wayar a cikin rigarta tsakiyar mamanta sannan ta rik'e k'ugu tace "kazo ka d'auka idan ka isa."

Murgud'a baki tayi ta koma gado ta haye tare da fitowa da wayar ta aje gefenta, baki sake ta barshi yana kallonta har bacci ya d'auketa, saida ya tabbatar tayi nisa sannan ya taso zauna bakin gadon yana kallon fuskarta, baisan menene asalin abinda yake ji ba, sai dai yana ji kamar a yanzu haka baya so ta masa nisa, to amma me yasa? *my aunt Aishan Umma* ce zata baka amsa a gaba, wata irin nutsuwa ce yake ji tana sauko masa, ga kuma taimakon da tawa mahaifiyarshi wanda yafi komai faranta masa rai, ya jima a wajen sosai yana tunani akanta kafin ya tashi ya koma wajenshi, ko bacci bai d'aukeshi ba yaji Khairat ta farka a tsorace.

Da sauri ya dawo kanta yana kallonta, numfashi kawai take saukewa kamar wacce tayi tseren gudu, a hankali ya furta "Khairat, lafiya? meya faru dake?"

Kallonshi tayi a firgice sai kuma ta rufe bakinta da hannu tana fashewa da kuka, wata nauyayyen ajiyar zuciya ya sauke ya kau da kansa danya lura tana da saurin kuka akan komai, sake cewa yayi "Khairat, meya faru?"

Share hawayenta tayi tana kallonshi tace "ba komai, kaje ka kwanta kawai."

"Ya zaki ce ba komai? bayan ga komai nan ya faru."

"To me kake so nace? na fad'a maka bana son duhu, sune ke sake zuwa min duk da qoqarina nasan ganin na manta komai, fyad'e ba abu bane mai sauk'i, amma duk da haka ina so na manta dan nayi rayuwata ba tare da damuwa ba, naso na zama marar tsoro da fargaba, amma su sun saka na zama mai tsoro, sunsa min fargaban da bana iya sakewa a kowane lokaci, kullum ji nake kamar zasu qara dawowa gareni ne."

Hawaye ta goge tace "ka kwanta kawai." tana fad'a ta koma ta kwanta ta bashi baya.

"Tashi zaune." yanda ya fad'a yasa ta tashi ba tare da gardama ba.

"Kiyi addu'a kafin ki kwanta."

Kallonshi tayi kuma lokaci d'aya ta dauke idonta, a hankali yace "baki iya bane?"

Nanma shiru tayi kawai sai yace "to ki d'aga hannayenki, saiki dinga fad'ar duk abinda na fad'a, kinji?"

Yanda yace tayi, *ayatul kursiyu* ya fara karantawa sannan *ammana rasul*, kafin suka karanta *falaq* da *nas* sannan ya karanta mata *Allahuma aslaftu nafsi ilaikh, wa fawadhatu amri ilaikh, wa wajahtu wajhi ilaikh, wa aljahtu zahri ilaikh, ragabatan wa rahabatan ilaikh, lamalja'a wala manja minka illa ilaikh, amantu bi kitabikal-lazi anzalta wabi nabiyikal-lazi arsalta.*

"Ki shafe jikinki." ya fad'a.

Shafawa tayi sannan ta koma ta kwanta, a hankali ya tashi yana sake nanata kalmar fyad'e a bakinshi, karo na farko daya ji haushin masu laifi kuma yaji inama shiya d'auki mataki akansu , wutar d'akin ya kunna tare da komawa shima ya kwanta, ganin haske yasa ta kashe na wayarsa sannan ta sake rufe ido sai bacci.


******************

Koda tanti ta koma gida tasa Zuby ta kira mata sauran 'yan uwanta a waya kasancewar duka matane 'ya'yanta guda hud'u, nan fa ta fad'a musu matar Umar Faruk taci mutuncinta tare da fad'a musu qudirin Khairat, nan fa suka fara zaginta suna aibatata tare da cin alwashin fitar da ita daga gidan, sannan suka qara kitsama Zuby wani sabon shiri a kanta tare da alk'awarta mata sabon had'in magani na musamman domin yaqar Khairat.

Sai dai tanti ita burinta ya wuce nasu dan haka safiya ma take jira kawai tayi, danta lura yarinyar dole sai an had'a da malamai.

******************

Tunda Khairat take a gaba d'aya tsawon rayuwarta, bata tab'a bacci mai dad'in na yau ba, bata tab'a jin natsuwa da farin ciki ba a cikin bacci kamar yau, gashi kuma ubangijinta ya nuna mata wani abu da ko kad'an bai firgitata ba saboda nutsuwar data farka da ita, a baccinta Allah ya haska mata tanti Ma'u tana matuk'ar biyarta da sharri , sai dai ta rasa waye kuma me yasa ya fad'a mata cewar ta rik'e addu'a tafi komai mahimmanci, koda Umar Faruk ya tasheta tayi sallah zaune tayi ta murje idonta kafin yace mata "ki fad'i abinda zan fad'a."

Kai ta jinjina alamar tana sauraro, *Alhamdulillahi lazi ahyana, ba'ada ma'ama tana wa'ilaihir-nushur.*

Nanma fad'a tayi kafin ta shafa ta sauka daga kan gadon shi kuma ya nufi masallaci, har tayi alwala tazo ta kabbara sallah tana tunanin akan me matar nan zata nemeta da sharri, shin akan yarta ne ko kuma akan abinda ya faru tsakaninsu? da qyar ta saita nutsuwarta ta samu tayi sallah tana gamawa kuma ko hijab bata cire ba ta zauna bakin gado, a hankali take tunano addu'a da Umar Faruk ya fad'a mata jiya, tana haka kuma ya shigo d'akin.

Kayanshi ya bud'a ya d'auko duk litattafan daya fad'a jiya sannan ya zauna akan kujera, kallonta yayi yace "dawo nan ki zauna."

Ba musu tayi yanda yace, littafi mai tsarki ya bata sannan yace ta bud'e, a farko ta bud'e sannan ya fara biya mata daga qananan surori har guda goma, kallonshi tayi jin daga nan yake tsayawa yasa tace "to wai meka d'aukeni, iya haka zaka tsaya min? kaga ni qara min kawai ai zan iya."

"Da farko dai ina so ki d'aukeni a matsayin malaminki, dan ta hakane za kiga haske da albarka a karatun, sannan ki girmamani domin samun sauk'i, sai kuma jin maganata a duk lokacin dana miki, kin fahimta?"

"In dai sai nayi haka zan samu albarka a karatuna, to na shirya zama dalib'a 'yar shekara biyar a gaban malaminta."

"Da kyau." ya fad'a kafin yace "idan kina so na qara miki, ki fad'a min wanda na fad'a miki sannan."

Gyara zama tayi kamar zata kwanta jikinshi sannan ta d'ora yatsarta a littafin ta fara biya masa, duk da a cikin salon koyo take karatun, amma abin abin birgewa da sha'awa, bakinta yake kallo wanda take motsashi a hankali tana biya karatun domin gudun kar tayi sauri tayi b'ata kuma, sosai Umar Faruk ya girgiza domin kaf a cikin waje d'aya kawai ya mata gyara, shima kuma ta fad'a ne ba daidai ba, murmushi yayi har hak'oransa suka fito fili yace "kinyi qoqari sosai, kuma ina fatan zaki kasance haka, har ranar da zaki hardace al'Qur-ani a kanki."

Wata irin lallausan dariya tayi data tafi da imanin Umar Faruk dan bai tab'a ganin irinta ba a fuskarta, cike da jin dad'i tace "nima zan hardace a kaina, na zama kamar k'anwar nan taka?"

"Zama ki fita in har kika saka kanki."

"To shikenan qara d'ora min wani." ta fad'a cike da zumud'i.

Nan ya sake dora mata har suka kai suratul *Qari'a* sannan yace ta rufe littafin tare da cewa "ki tabbatar kin kawosu gobe, idan ba haka ba kuma."

"Idan ba haka ba me?" ta tambaya tana kallonshi.

"Zaki sha bulala ne, saboda ke dalib'a ce."

Wata dariya ta kece da ita mai qarfi kafin tace "ai bama zaka fara ba kaima, dan kasan zamu iya dakuwa da kai."

Kunnanta ya kama ba zato ba tammani ya murd'e fuska a had'e yace "ni kike fad'awa haka? anya kina neman albarka kuwa?"

Hannayenshi ta kama duka biyu tana rokon ya saketa tana fad'in "dan Allah kayi hak'uri wallahi ba zan sake ba malam, dan Allah kasa min albarka ko nayi saurin fahimta."

Sakinta yayi yana tunanin ya samu hanyar da zaibi da ita cikin sauk'i dan haka yace "idan akayiwa malam laifi har qasa ake duk'awa a bashi hak'uri, dan haka ki fara in dai har da gaske dalib'a ce mai neman albarka."

Ita kuma yanzun nan taji a ranta bata da wani buri daya wuce na karatu, musamman da taji wai yau itace take karatun littafi mai tsarki haka, shaukin abin ya shigeta sosai dan haka bako tunani ta zube qasa ta kamo hannunshi ta rik'e tana murzawa ba tare dama tasan me take yi ba tace "naji to kayi hak'uri dan Allah, ba zan sake ba, nidai ina sonna samu albarkar karatuna."

Shima biye mata yayi ya dinga murza tattausan hannunta yace "ba albarkata kad'ai kike buqata ba, akwai ta iyayenki, dama mutanen da kike zaune dasu."

Cikin mamaki tace "wai har suma?"

"Eh, basu cancanci saka miki albarka bane?"

Cikin turo baki tace "toya zanyi?"

Mik'ewa tayi yace "yanzu zaki fara ai."

Ta qasan ido ta harareshi kafin tace "toya zanyi yanzun?"

Wani shu'umin murmushi yayi ya tashi tsaye yace "biyoni muje."

Saida suka fita sun nufi d'akin Mama Maimuna yace "za muje ne mu gaida iyayenmu, sai kice kina neman albarkarsu."

Kallonshi tayi kamar zata fashe da kuka tace "zafa ka rusa min jiji da kaina, gaskiya ba zan iya ba."

"Shikenan, koma ki zauna, amma ki sani za kiyita karatu bakya fahimta, saboda ba albarkar manya a ciki."

Bubbuga k'afafu tayi cikin shagwab'a ta kutsa kai d'akin Mama Maimuna, ganinta kawai tayi ta fad'o mata dan haka ta tsorata, da sallama ya shiga sosai ya gaisheta duk idonshi na kan Khairat da har yanzu ta b'ata rai, da ido ya mata alama kafin ta fahimta ta kalli Mama Maimuna tace "ina...kwana, an tashi lafiya, ina neman albarka dan Allah ki saka min."

Mama Maimuna mamaki ne ya hanata magana, saida Khairat ta sake cewa "ba zaki samin bane kome?"

Kai ta girgiza da sauri tace "a'a 'yata, kin tashi lafiya? Allah ya miki albarka."

"To na gode, sai an jima." tana fad'a ta tashi ta fita shi kuma ya mata sallama ya fita.

Kewayensu ta nufa shi kuma ya janyo hijab d'inta ya nuna mata kewayen Mama Sa'a, ciki suka shiga amma Mama Sa'a harda rumgume Khairat tanata wasar baki tana gaisheta, haushi ne yasa Khairat yin shiru ta kasa gaisheta, danta lura irin mutanen nan ne masu shishigi, Umar Faruk kad'ai ya gaisheta kuma yanawa Khairat alama da ido akan tarbiyar gaisheta amma tak'i, fitowa sukayi suka shiga d'akin Mamanshi, suna shiga da sauri ta qarasa ta durk'usa gaban Mama tana rik'o hannunta da fad'in "Mama ya jikinki?"

Cikin sakin fuska tace "da sauk'i 'yata, kin tashi lafiya."

"Ina kwana aunty Khairat." murayr duka yaran dake d'akin ta daki kunnuwanta.

D'an murmushin gefen labb'a kawai ta musu kafin suka juya kan Umar Faruk suka ce "ina kwana yah Umar."

"Lafiya lau, kun tashi lafiya?"

"Lafiya lau." suka amsa.

"Mama kinsha maganinki?" cewar Khairat.

"A'a 'yata, yanzu dai zanci abinci sai nasha."

Juyawa tayi ta kalli Ruk'ayya dake shirin fita tace "har yanzu baku gama bane?"

"Eh aunty Khairat, yanzu ma zan d'ora."

"Me? yanzu fa? kuma Mama ta zauna tana jiranki? me yasa ne wai kuke haka? kamar dai baku damu da ita ba."

Mtsssss, taja tsaki tare da tashi rai bace ta fita daga d'akin har tana karo da Abbakar da Saratu da zasu shigo suma, wayarta ta d'auko ta dawo d'akin tana ci gaba da kira amma ba'a d'auka, saida ta aika kira na hud'u sannan mutumin ya d'auka jiki na rawa, tana jin ya d'auka tace "ka kyauta, amma yanzu bata kai nake ba, ka gaggauta had'a min duk wani abinda kake dashi yanzu, amma karka saka arom (d'and'ano) a ciki na mai tension ne, da zaran ga kama ka kirani."

"To Hajia." ya fad'a ta kashe wayar.

Umar Faruk ta kalla wanda suma dukansu kallonta suke tace "dan Allah ka d'auki makullin motata kaje *riva side* ka karb'owa Mama abinci."

Fita tayi shi kuma yabi bayanta, makullin ta d'auka ta bashi ta bud'a post d'inta ta d'auki kud'i ta bashi, kai ya girgiza mata yace "ki barshi zan biya."

"Kai kayi magana a maka oder koni? kaine ka sani koni nayi niyya? dan haka karb'i kawai."

Karb'a yayi ya cire doguwar rigarshi ya sake kayan sannan ya fita, yana fita ita kuma ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin riga da siket na shadda, kwalliya tayi sosai kafin ta d'ora gyale a kafad'a ta d'auki jaka da takalmi, wayarta ta d'auka da nufin kiranshi sai gashi ya shigo, hannu kawai ta tara masa ya bata makullin sannan ta fita.

Bayanta yabi amma sai yaga ta shiga d'akin Mama, Mama ce kad'ai a d'akin dan haka ta sake zubewa qasa tace "ga abinci nan kici Mama, sannan ki saka min albarka zan fita wajen aiki."

"Allah yayi albarka yata ,daga yanzu har zuwa fitar numfashina na qarshe sanya albarkata ba zai tab'a nesanta dake ba."

"Na gode Mama." ta fad'a tana yunk'urin tashi.

Hannunta Mama ta rik'e tace " 'yata."

Komawa tayi yanda take tace "na'am Mama, akwai abinda kike sone?"

"A'a 'yata, ina so na fad'a miki wani abu."

"Ina jinki Mama."

" 'Yata, wannan kayan na jikinki, bai kamata ki fita dasu ba a matsayinki na matar aure, ki sani Allah ya umarcemu damu dinga rufe jikinmu a duk lokacin da zamu fita daga cikin gidajenmu, kuma hakan nada alfanu sosai, hakan da zaki fita baiyi ba sannan shi kanshi mijinki zaiji ba dad'i, yata, ina so ki zama salihar mace kuma
Showing 69001 words to 72000 words out of 186119 words