d'auki makullin mota ya nufi gidansu tare da Baba, Papa ne ya tarbesu a masaukin bak'inshi, bayan sun gaisa malam ya fad'a mishi abinda ya kawosu, cikin nuna dattako Papa yace "ba komai malam, dan kunyi saurin zuwa ma dani zan mayar da ita da kaina, amma ku jira ni zan taho muku da ita insha Allah."

Takalmi Papa yasa ya tunkari d'akin Khairat yana tunanin rage mata daular da take samu, dan yana ganin kamar harda sakewar da take samu yasa haka, yana shiga d'akin ya sameta kwance, a tak'aice yace "tashi ga mijinki nan yazo ki tashi ku tafi."

Tashi tayi zaune tace "a'a Papa babu inda zanje, kawai kace ya tafi ni bana son ganinshi."

Rai had'e Papa ya kalleta ya tara mata hannu yace "ban makullin motarki."

"Motata kuma?"

"Eh."

"Amma Pap...." tswar daya mata yasa tayi shiru, d'orawa yayi da "ki bani makullinki kuma ki tashi ki wuce."

Mamaki ne ya hanata magana, dan ko a mafarki haka bata tab'a faruwa ba, tashi tayi a hassale ta fita daga d'akin ta sauka qasa, fitowa Papa yayi ya musu magana sannan suka wuce tare suna godiya, Khairat kuma kamar zata qurma ihu komai ya mata zafi har suka kai gida.....
20/08/2019 Γ  14:26 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_



5⃣0⃣


Bayan tafiyarsu Mamie take fad'awa Papa batun b'atan sarqarta da kuma kama matar, cikin b'acin rai Papa yace "yanzu yarinyar nan har takai matsayin da zata iya sakawa a d'aure mutum kuma ma mace, to ba zan d'auki wannan iskancin ba, jiya ba yau bace dan haka gobe nan zansa a fitar da ita."


Yana komawa d'akinshi yasa aka kulle duk wani asusun baki da Khairat ke dashi, bawai dan wani abu ba sai dan ta d'and'ana rayuwar rashi hakan zaisa ta qara hankali, haka ma ya kira manager da accountant ya gargad'esu, duk da ayukan da suka masa yawa yayi qoqari ya d'orawa kansa wani nauyin, ta yanda babu sisin kwabon da zata fita daga ma'aikatar ba tare da saninshi ba, da haka kuma yake burin ganin gobe.


***************

Zuby na k'ofar d'akin Mama su Khairat suka shigo, baki bud'e take kallonsu harta shiga d'akinta, rufe baki tayi tace "jaraba ba zata rabu dashi ba cikin sauk'i."

Khairat na shiga d'aki ta d'auki maganinta tasha na ciwon kai sannan ta kwanta, ganin tak'i kulashi yasa ya fita daga gidan, bai dawo ba saida yayi sallah isha'i, a lokacin suka shigo tare da Ruk'ayya da Mama, sallama sukayi ta amsa tare da cewa "shigo." saboda taga babu wanda ya shigo.

Shiga sukayi da wata sabuwar sallama, zaune sukayi akan kujera Umar Faruk kuma akan gado, Mama ce tace "Khairat, nazo na sake baki hak'uri ne akan abinda ya faru, kiyi hak'uri kinji, insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba."

Zaune tayi bakin gadon ta kalli Mama tace "Mama ba komai, komai ya wuce ai tunda gani na dawo."

Wani kallo da tabi Ruk'ayya dashi yasa cikin Ruk'ayya murd'awa, a hankali ta sauka daga kan kujerar ta durk'usa ta rik'e rigar Khairat tace "dan Allah aunty Khairat kiyi hak'uri ki yafe min, wallahi ba nayi haka ba danna tozartaki ba, raina ne naji baimin dad'i ba da naga yah Umar na kuka, amma wallahi ina sonki aunty Khairat kuma ina son zamanki da yah Umar, dan Allah kiyi hak'uri." ta qarashe da fashewa da kuka.

Allah sarki Khairat da taushin zuciya, hannun Ruk'ayya ta kama ta zaunar da ita kusa da ita tace "shikenan Ruk'ayya, komai ya wuce, ban fahimceki bane da farko saboda bana da d'an uwa ko 'yar uwa, amma yanzu da kika fad'a min na fahimta, ba komai wallahi."

Ruk'ayya ce tasa hannu ta share mata hawayen da suka zubo mata tana fad'in "dan Allah aunty ki daina kuka, wallahi ni daga yau ma na koma qanwarki, bani ba yah Umar zan d'aukeshi a matsayin mijin yayata ne kawai, kin amince?"

Ta fad'a tana nunata da hannu, murmushi tayi da yasa hawaye suka qara zubowa tace "Ruk'ayya waye zaik'i d'an uwa, da ina ni kad'ai yanzu kuma na samu qanwa."

Tashi Mama tayi ta fita tana goge qwalla dan wani irin tausayin yarinyar taji sosai har zuciyarta, Umar Faruk kusan qwallan yayi yayin da qaunarta ke qara ratsashi, fita yayi ya barsu Ruk'ayya kuma ta gyara mata kayan da suka zube a lokacin da take shirin tafiya gida, sunayi kuma suna hira har Khairat ta fad'a mata zata fara zuwa wajen koyan girki, da farin ciki Ruk'ayya tace "gaskiya kam aunty Khairat ya kamata, kuma kinga nima munyi magana da Mama akan zan shiga, amma tace na bari har aurena ya taso saina fara zuwa."

"Ah haba, indai kina so kawai kishirya gobe muje muji yanda abubuwan suke."

Shiru tayi ba tayi magana ba, tana mamakin hali irin na Khairat, katseta tayi da cewa "ki shirya kinji, zan miki magana."

"To." ta fad'a cikin sanyin jiki, ta jima sosai suna hira har saida taji sallamar Umar Faruk sannan ta mata saida safe, yana shigowa kayanshi ya cire ya shiga wanka, koda ya fito yana shiryawa Khairat itama ta shiga wankan, cikin doguwar rigar bacci ta shirya mai kyau fara tas sannan ta kwanta, kallon qeyarta Umar Faruk yayi danta juya masa bayane , cikin taushin murya yace "Khairat, kiyi hak'uri abis....."

"Ya isa haka, nace komai ya wuce." ta katseshi, murmushi yayi ya d'ora kanshi a tsakiyar wuyanta yace "indai hakane me yasa zaki bawa mijinki baya, kin manta hakan babu kyau?"

Juyowa tayi ta sauke idonta a kanshi tace "to na juyo, hakan yayi?"

Murmushi ya sake yi yakai bakinshi a hankali zai sumbaceta, da sauri tasa hannunta tsakiyar bakinsu, b'ata rai yayi yana kallonta, ba alamar wasa tace "kayi hak'uri Faruk, bana so ka sake neman wani abu a gareni, dan ba zan iya baka ka, ina ji har yanzu kamar ban cika cikakakkiyar mace ba, domin kuwa ana kallona a matsayin wacce ka taimaka."

Janye hannunta yayi yana kallon qwayar idonta yakai bakinshi a hankali harya had'e bakinsu, saida ya gaji da tsutsa ya saki ya kalleta da idonshi harsun canza kala yace "ki bani dama ta qarshe na nuna miki kece wacce zuciyata take so, dama d'aya tak nake so ki sake bani Khairat, ni kuma zan nuna miki matsayinki a wajena ya wuce yanda kike tunani."

Kallonshi kawai take da ido ta kasa magana, ganin haka yasa ya sake lulawa da ita wata duniyar, saida ya jima yana lashe ko ina kafin ya fara shirin gangarawa , kallon fuskarta yayi cikin siririn haske daya bayyana a d'akin, yana ganin yanda ta rintse ido sosai hawaye na zubowa ta kama damtsenshi sosai ta rik'e, yana danna kai ciki ta saki wata tausassan qara, harshenshi yasa ya dinga lashe hawayen fuskarta yana ci gaba da daidaitawa kansa zama, numfashinshi na fizgarshi yana neman shid'ewa sai hawaye dake zubo mishi yana qara matseta a jikinshi sosai yana sauke numfashi da qyar, tausayinta ne ya sake kamashi ganin kullum sai taji wannan azabar, kuma har yanzu ya kasa gane dalilin haka, kuma har yau yana mamakin yanda bata bud'ewa.

Bakinshi yakai a kunnanta yana fad'in "Allah ya miki albarka alkairina, Allah ya biyaki da gidan aljanna, Allah ya tashemu a aljannatul firdaussi, ina sonki Khairat, ina qaunarki Khairat, wallahi ba zan iya rayuwa babu ke ba, Khairat ki tausaya min karki kasheni dan Allah, wallahi ina so na zauna dake har qarshen rayuwata, Khairat ki fad'a min abinda kike so a duniyar nan, ni kuma nayi alk'awarin yi mikishi ko menene a duniyar nan, Allah ya saka miki da alkairi baby."

😎😎😎 *Ba magana*


******************


Shiryawa Khairat tayi tace ma Umar Faruk "nida Ruk'ayya zamu je wani wuri, ina neman izininka."

"Wani wuri bashi da suna?" ya fad'a yana tsefe sumar kanshi.

Matsowa tayi kusa dashi tace "da zaka taimaka saika ajemu , tunda motata na gida."

Juyowa yayi yana kallonta yace "muje
to." juyawa tayi zata wuce ya janyo hannunta ta fad'a jikinshi, rumgumeta yayi tare da sumbatar kanta, wani numfashi yake saukewa ido lumshe yana tuno....jiya (kun gane ai), d'agota yayi daga jikinshi ya kalli fuskarta yana dafe kumatunta yace " ina qaunarki *bugun zuciyata*."

Kallonshi kawai tayi ta janye jikinta daga nashi ta fita, bayanta yabi ita kuma tama Ruk'ayya magana suka tafi tare, akan hanya ya nuna mata aikin daya fara na d'aya compagnie sai dai baiyi komai ba, kallonshi tayi tace "meya janyo haka to?"

Kallonta yayi ya d'an cije gefen lips d'inshi yace "kwana biyu kin daina bani kulawa, wannan ne yasa Umar Faruk rasa duk wani kuzarinshi." ya qarashe tare da kanne mata ido.

Harara ta cilla mishi tana kallon computer bata sake mishi magana ba, suna daf da isa wajen kiran Papa ya shigo wayarta, d'auka tayi Papa yace "ki sameni a gendarmerie yanzun nan."

D'if ya kashe wayar, kallon Umar Faruk tayi za tayi magana wayarshi tayi qara shima, daga yanda yace "ok Alhaji insha Allah." yasa ta gane Papa ne.

Ajiyar zuciya ta sauke ta aje computer ta rumgume hannayenta tana kallon titi, tana tunanin me zai faru, shima baice da ita komai ba suka d'auki hanya......

_Bara muji meya faru bayan fitarsu_

*************


Abdul waid ne yayi irin durk'ushin nan nakan tafikan qafafu da kulki a hannunshi yana zarewa Mama ido, a nutse yace "Mama, Mama, Mama, sau uku ko? ina ganin girmanki shi yasa ban dakeki ba tunda kika zo nan, amma yanzu kin kaini bango mafita d'aya itace nasa a lallasa minke, in kuma baki son a dargajeki to ki fad'a mana yanda akayi kika samu sarqar tunda kince bake kika d'auko ba."

Cikin rawar jiki da tsoro dan ganin ba sauk'i a al'amarin yasa tace "a'a yi hak'uri zan fad'a, wallahi zan fad'a maka gaskiya."

"Ina jinki Mama."

Cikin kuka tace " 'yata ce, sunanta Zubeida, wallahi ita ta d'auko bani ba."

Zunbur ya mik'e tsaye yace "bani adresse d'inta?"

Had'e hannaye tayi tace "dan Allah kamin rai yaro karka tona mata asiri, wallahi tana da aure kuma tana da kishiya, idan maganar nan ta fita wallahi aurenta zai iya mutuwa, nima kuma zan iya mutuwa."

A tsawace yace "tasan da auren nata kuma tayi sata, mu aurenta bai damemu ba, aikinmu kawai mukeyi, ki bani kwatancen gidanta." ya fad'a da sake d'aga murya.

Cikin kuka ta fad'a musu takwacen gidan malam, fitarsu Khairat ba wuya motar jami'ai tazo gidan, guba biyu daga ciki ne suka kutsa kai cikin gidan, a lokacin Zuby na zaune tana gurgurar tsamiya, saida gabanta ya fad'i data gansu, idon jami'in akan Mama Sa'a yace "sannu ko, dan Allah Zubeida muke tambaya a gidan nan?"

Ba Zuby ba har Mama Sa'a saida kayan cikinta suka murd'a, a duburbuce take kallonshi tana kallon Zuby da ido ya raina fata , cikin d'aga murya yace "Hajia dake muke magana kinyi shiru."

"Gata nan, wallahi gata nan, bani bace." cewar Mama Sa'a cikin harshen zarma, dan dama shi tafi iyawa.

Ganin sun tunkari inda Zuby take yasa Mama Sa'a tashi da dugu ta shige d'akinta, tun basu qarasa wajenta ba ta fashe da kuka tana kiran sunan Mama ta fito ta taimaketa, Saratu Mama da Mama Maimuna ne duk suka fito, Mama kad'ai tayi k'arfin halin tambayar "bayin Allah lafiya, me tayi?"

Shirun da sukawa Mama yasa dole taja baki tayi shiru, tsawa d'aya suka mata ta tashi ta d'auki hijabi tasa suka wuce, cikin qanqanin lokaci sai gata a prison (cell) tare da Mama, hannu ta d'ora a kai tana fad'in...

"Na shiga uku Mama kin cuceni, yanzu da wane ido kike so na kalli yah Umar, haka kawai kinja mana abin kunya, akan me zaki fad'i sunana kamar ba 'yar da kika haifa ba?"

Tsaye Mama ta mik'e tace "wallahi ubanki zaki ci idan baki min shiru ba, mahaukaciya kawai, dan ubanki ke ba banza ki kayi dani ba anan d'in kina can kina iskanci, shine ni kuma saina rufa miki asiri, to mu shirya d'aukar hukuncin da za'a mana, danna gama lura yarinyar nan 'yar akuya ce, ba zata tab'a sawa a fitar damu ba."

Kuka ta sake fashewa dashi tana fad'in "haka kawai na jawa kaina, yanzu ya zanyi da cikin dake jikina? kina nufin zanyi rainon cikine a magarqama kome? wallahi ni dai ban yafe ba."

Kwaf, Mama takai mata bugu a baki tana fad'in "ubanwa kike cewa baki yafe ba, ni Zubeida, ni?"

Murgud'a baki tayi ta kawar da kanta, suna haka Khairat suka qaraso, nan ta samu Papa ya hakimce yana jiran zuwanta, masu tsaron lafiyarsa ne suka sara mata alamar gaisuwa kafin ta zauna, bayan sun zauna Abdul waid yace "Khairat dama yanzu nake tunanin kiranki , saboda an samu wanda ta d'auki sarqar."

Kallon Umar Faruk tayi ta maida kallonta ga Abdul waid tace "an sameta, wacece, tana ina?"

Papa ne ya katsesu da "bana kiraki bane danna saurari haka, ina baki umarni da ki janye qarar nan sannan kisa a rufe qarar, wannan ba girmanki bane."

Kallon Papa tayi tace "amma P..."

"Amma me, kiyi yanda nace kawai."

Furzar da iskan bakinta tayi ta kalli Abdul waid da ido kawai ta masa alama, kai ya d'an jinjina yace "an gama."

Da mamaki Umar Faruk ya kalleta, shi girma da ikonta ne kawai ke qara bashi mamaki, wata takarda ya bata tasa hannu sannan ya kalli wani jami'i yace "ka fito dasu."


Da mamaki duka suke kallonsu kowa da abinda yake ayyanawa a ranshi, har suka tsaya gabansu cike da kunya dan sun kasa d'aga kai su kallesu, da qyar Umar Faruk yace "Zubeida, dama da ha...."

Papa ne yace "tunda kun sansu , kuyi hak'uri ku koma gida, bai kamata kuyi magana anan ba."

Kai kawai Khairat ke girgizawa yayin da Ruk'ayya ta rik'e baki, tsaye ta mik'e ta nunasu da hannu tace "na tabbata izuwa yanzu kun gama fahimtar abin kunyar da ku kayi, kunci albarkacin mahaifina wallahi, badan haka ba da sai kun gane shayi zalla ruwane, amma duk da haka nasan kun gane wacece ni, kuma in halinku ne nasan zaku koma, a wannan lokacin kuma zan muku d'aurin da goro ma saiya fiku kyan gani, daga qarshe kuma dole za'a shiga tsakanina daku, danna tabbatar ba alkairi kuke nema dani ba, kamar yanda jikina ke bani ba kun d'auki sarqar bane dan kawai ku siyar, ina fatan zaku gyara halinku in kuma hakan yaci tura to da fatan zaku kiyaye qara yiwa Khairat sata a karo na biyu."

Da harara ta bisu tare da tsaki ta fice daga wajen, Abdul waid ne ya bawa Umar Faruk sarqar yasa aljihu, bin bayanta sukayi shi da Ruk'ayya, Papa ma tashi yayi ya wuce da qyar suka rarrafa suka fita daga wajen, tun a bakin titi Zuby ta fad'awa Mama abinda ya faru bayan tafiyar Khairat gida, a wahalce Mama tace "muje gidana."


Taxi suka hau ta ajesu gidan Mama, suna shiga sukayi zaune kamar kayan wanki suna jajantawa kansu, Mama ce tace "ashe haka yarinyar nan take?"

"Humm, ai bata da mutunci ko kad'an."

Kafin Mama tayi magana Zuby tace "bama wannan ba, nifa akwai wasu maganganu da yarinyar ta fad'a min a ranar sun d'aure min kai sosai, amma nasan ke zaki sansu."

"Wace magana?" cewar Mama tana neman cire riga dan tayi wanka.

Maganganun da Khairat ta fad'a mata ta maimaita mata, cak Mama ta tsaya da cire rigar da take, da sauri ta juyo ta kalli Zuby ta kafeta da ido, ta kasa d'auke idonta kuma ta kasa magana, saida Zuby ta d'aga murya tace "Mama."

Zabura tayi ta sake kafeta da ido, "lafiya Mama?"

A hankali ta girgiza kai tace "ba komai, bara na fito daga wanka saiki tafi gidanki."

Harta d'ibi ruwa ta shiga bayi jikinta ba qwari, saida ta fara kwararawa kanta ruwa ta dawo hayyacinta, *wacece Khairat, ya akayi tasan sirrin dako 'yan uwanta basu sani ba, taya tasan wannan sirrin? shine dai kad'ai nasan abinda na aikata wanda nake tsoron duniya ta sani, inba shi ba me Khairat take nufi???* wannan sune tambayoyin da takewa kanta harta fito daga wanka, Zuby ma tattarawa tayi ta kama hanyar gida, da sand'a ta shiga gidan dan ba zata iya had'a ido da kowa ba, d'akin Mama ta nufa kai tsaye ta samu ta kwanta.


Khairat kuma daga nan gida suka dawo saboda takaici da zulumin abun, Ruk'ayya da Umar Faruk kuma babu wanda ya fad'i maganar a gida, d'aki take kwance tana karatu dan yanzu shi kad'ai ne ke cireta damuwa.


Ana sallah magrib kuma Mama tasa Zuby ta shirya tace ta koma d'akinta, ba gardama ta shiga ta hakimce tana sabgar gabanta, Umar Faruk na shigowa bayan sallah isha'i yaga d'akin bud'e da alama qarara tana ciki, wata shegiyar qwafa yayi ya cire belt d'inshi ya tunkari d'akin........


_Wallahi nima gidana zanje, wannan hushi haka Umar Faruk_πŸ˜‚

*Kuyi hak'uri da rashin cika alk'awari da nayi jiya, hakan ya faru ne saboda daukewar da wata tayi ina cikin typing.*
23/08/2019 Γ  12:51 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


*Allah Ka qara mana tsoronka*


_Bismmilahir-rahman-rahim_


5⃣1⃣


Daf da zai shiga d'akin Mama ta kira sunanshi, juyowa yayi yaga Mama tsaye a k'ofar d'aki, b'oye belt d'in yayi ya nufi wajen Mama, sunkuyawa yayi har qasa yana fad'in "gani Mama."

Saida ta shiga d'aki yabi bayanta daga tsaye tace masa "na mayar maka da matarka, dan Allah bana son jin wata hayaniya, kayi hak'uri da duk abinda ya faru, kaji?"

Jim ya d'anyi kafin yace "shikenan Mama."

Tsaye ya mik'e zai fita ta sake cewa "azumi ke tahowa,amma banga kana shirin tarbansa ba kamar yanda kake kowace shekara."

Ajiyar
Showing 138001 words to 141000 words out of 186119 words