_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


7⃣


Ganin halin da take ciki yasa likotoci suka amsheta tare da umarta da sukai report a wajen police, matashin nan ne ya tafi dan cika umarnin, baisha wahala ba ya samo takardar izini a dubata, yana kawowa likitoci suka duk'ufa kanta, tun matashin nan na kai da kawowa harya fara zaune yana jiran fitowar likotocin, mutanen da suka taho tare ma jira suke tare da jimami, ana haka wata docteur ta fito tana tambayar wanda suka kawota, a sukwane suka rufeta suna fad'in sune, a nitse tace "kune 'yan uwanta?"

Matashin ne yayi karaf yace "a'a, muma tsitarta mukayi, ina fatan dai lafiya ko?"

Wani kallo ta masa tace "kai baka ga yanda kuka kawota bane har kake maganar lafiya, muna buk'atar dan ginta dan akwai aiki da za'a mata ana buk'atar saka hannunsu."

A raunane yace "gaskiya bamu san kowa nata ba, amma in ba damuwa mu saimu saka hannun."

A wulak'ance ta kalleshi tace "ok ina zuwa."

Juyowa matashin yayi yace "dan Allah iyayena kuyi hak'uri, ina so ku bani had'in kai mu taimakawa baiwar Allah nan."

Wani dattijo ne yace "ba komai yaro, muma fa iyayene, fatanmu dai Allah ya bata lafiya."

Fitowar docteur d'in tasa suka maida hankalinsu a kanta, matashin ta kalla tace "ka biyoni tare da wani dattijo d'aya a cikinku sai kusa hannun."

Binta sukayi ta kuma nuna musu suka saka hannu, saida suka tashi zasu fita matashin yace "dan Allah wane irin aikine za'a mata?"

"Kai baka san aikin da za'a mata ba kasa hannu, saboda ba yar uwarka bace kenan?"

Kai ya girgiza yace "ba haka bane, kawai dai muna so ne mu taimaketa."

Tsaye ta mik'e ta wuce tana fad'in "d'inki za'a mata saboda tana zubar da jini dayawa."


A haka suka kasance har rana ta take sosai amma ba wani labari, ganin haka yasa dattijawa biyu suka bar wajen ya rage sai su uku a wurin.


*Tun daren jiya* Mamie ta kasa bacci saboda ganin k'arfe d'aya tayi, a al'adar Khairat kuma bata kai wannan lokacin, kai kawo ta dinga yi a tsakiyar falo ita kad'ai duk hankalinta a tashe, *03: 17* Papa ya bud'o k'ofar d'akin ya shigo a halin daya fi shigowa, tsaye tayi tana kallonshi harya k'araso ya zube saman kujera yana maganganun dashi kanshi baisan me yake fad'a ba, durk'ushe tayi gabanshi cikin kuka tace "Alhaji, Khairat fa bata dawo gidan nan ba har yanzu, dan Allah kayi wani abu kar komai ya samu 'yata, dan in haka ta faru wallahi ba zan yafe maka ba."

Wani fizgo hannu ya fara a cikin muryarshi ta maye yana fad'in "to saime idan bata dawo ba, ita d'in yarinya ce? ki barta tayi sha'aninta taji dad'in rayuwarta, ke kad'ai ce a duniyar nan baki waye ba ai."

Cike da damuwa ta sake cewa "dan Allah Alhaji ka taimaka ka dubo min ita ko kasa a dubota, wallahi nasan Khairat ba zata jima haka kawai ba a waje saida dalili, jikina yana bani kamar akwai wani abu dake shirin faruwa, wallahi hankalina ya kasa kwantawa gabana fad'uwa yake."


Abin takaici ashe duk maganar da take yayi bacci, dole ta gyara zamanta a k'asa tana ci gaba da kiran wayar Khairat gashi tana kururuwa amma ba'a d'auka ba, haka ta kasa rintsawa har gari ya waye lokacin kuma Papa ya farka a cikin hayyacinshi, a lokacin data fad'a masa halin da ake ciki hankalinshi ya tashi sosai kuma harya fara mata fad'a wai bata fad'a masa ba, nan ta fad'a masa halin daya shigo da abinda suka tattauna kafin bacci ya d'aukeshi.

Aifa hankaline ya tashi dama na Mamie tuni a tashe yake, a lokacin kuma su Musa sunzo wajen aikinsu cikin kaki, nanfa ya sasu nemo mashi Khairat duk in da take, saboda su sun san komai kawai sai suka fara tafiya gidan rawar suna binciken k'arya, anan kuma suka samu wayarta , haka a wajen da suka jefar da ita suka tsaya suna tambayan mutanen wajen ko basu ga wani bak'on al'amari ba, saboda ganinsu da kayan soja yasa aka fad'a musu abinda ya faru, nan fa suka dawo gida da qarfin gwiwa sun samu labarinta, Papa da Mamie basu zauna ba suka rankaya zuwa asibitin, kai tsaye asibitin *Clinic Poudrière* anan suka samu mutanen da suka kawo Khairat asibitin, matashin ne ya fad'a musu halin da suka kawota, cikin fitar hayyaci Papa ya shak'i wuyan matashin yana fad'in,

"Wallahi baku isa ba sai kun fad'a min abinda kukawa 'yata, ka fad'a min me kuka mata?"

Matashin kam zare ido ya fara yi baisan me zaice ba, suna haka likitoci biyu maza da d'aya mace suka fito daga d'akin da Khairat take, da sauri suka nufi wajensu banda Mamie data zube wajen kamar gawa sai hawaye kawai dake zuba a idonta, "likita meya faru da yarinyata?"

A tsanake likitocin suka kalleshi kafin babban docteur d'in yace "kaine mahaifinta?"

"Eh nine, dan Allah ka fad'a min meya faru da ita?"

"Ok to, yallab'ai ka biyoni ciki saina maka bayani."

Kamar zai tashi sama haka ya bishi har kamar zai shiga gabanshi, sun d'auki 'yan mintuna da shiga Mamie ta dawo hankalinta ta tashi tabi bayansu dan taji abinda za'a fad'a, da isarta yayi daidai da bayan kwantar da hankalin da likitan yayiwa Papa ya kalleshi yace "kayi hak'uri yallabai, fyad'e akawa 'yarka."

Mamie na jin haka ta k'arasa fad'uwa a gurin somammiya, Papa kuma wani kuka ya saki kamar yaro yana kiran "a'a, a'a, ba dai akan 'yata, me yasa ba za'a rama a kaina ba, na shiga uku na lalace."

Likitan ne yace "yallab'ai ka saurareni kaji."

Kallonshi yayi yana goge hawaye da babbar rigarshi yace "ina jinka."

A hankali kuma a nutse likitan ya fara magana "'yarka tana cikin wani hali da take buk'atar kulawa, bawai fyad'en ne ba abun tashin hankali, yawan mutanen da suka mata fyad'en sune abun dubawa, duk da mun rasa wasu hujjoji saboda ba'a kawata da wuri ba a asibiti, amma dai munyi k'ok'arin gano wasu abubuwan, mun bata duk wata kulawar da take buk'ata a yanzu tare da taimakon wanda suka kawota, mun mata gwaje gwaje na cutuka da akan iya d'auka ta hanyar saduwa, kuma alhamdulillah a yanzu dai babu wani abu mai yiyuwa ko nan gaba, sai kuma akwai raunika da dama da aka ji mata mai yiwuwa tayi fad'a da mutanen sosai, dan mun samu karaya a hannunta da tsakanin cinyarta da k'ugunta, sai kuma gocewa a yatsunta biyu da kuma wasu raunika da suke nuna dukanta akayi, akwai ciwo a kanta daya ja mata matsala sai dai munyi k'ok'arin shawo kanta, badan ciwon a cikin gashinta yake ba da iska ya shiga akwai yiyuwar ta kamu da ciwon mantau.

"Ciwon daya bamu wahala, shine ciwon da suka ji mata a gabanta, 'yarka tana d'aya daga cikin irin matan nan masu tsukakken gaba, wasu daga ciki zaka ga ko haihuwa basa iya yi da kansu sai an masu aiki, wasu kuma ba zasu haihu da farko ba amma sai kaga cikin ikon Allah sun haihu a gaba da kansu, gaskiya 'yarka bana jin tana daga cikin masu samun damar haihuwa da kansu ko a gaba in ba wani iko na ubangiji ba, ko mijinta ne na aure zai shigeta dole saiya had'a da dabaru, amma kasancewar sun mata ta k'arfi hakan yasa sun b'arkata sosai, idan kaga gabanta kafin a mata aiki zaka d'auka *anus* d'inta da *vessie* (gabanta da duburarta) a had'e suke, amma cikin ikon Allah mun di'nketa sosai d'inki kuma ba adadi, sai kuma jini da muka d'auka a lab muka saka mata dan tana buk'atarshi."

"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un." abinda Papa ya dinga maimaitawa kenan, hawaye taf da ido ya dag'o yace "kana ganin zata rayu ma? danni na cire rai da ita."

"Haba yallab'ai, ya zaka cire rai da rahamar ubangiji? ai insha Allah babu abinda zai sameta, zata tashi in Allah ya yarda ma."

Sake kallonshi yayi yace "to ya take yanzu?"

Cikin i'ina yace "eh...to, yanzu dai..tana kwance...insha Allahu,zata farka , amma dai har yanzu a some take bata san in da kanta yake ba, kawai muna gane tana raye da ta hanyar na'urar dake nuna mana numfashinta."

"Yanzu miye abunyi?"

"Eh yanzu kam babu wani abu, akwai magungunan da za'a d'orata ne kawai idan aka siyo, sai kuma kud'in duka aikin da aka mata, gashi nan a rubuce." ya fad'a tare da mik'a masa takardar.

A sanyaye ya amshi takardar ya mik'e ya fara takawa, yana bud'e k'ofar yaci karo da Mamie kwance a wajen, da sauri ya zube yana jijjigata yana kiran "Na'ima, Na'ima, dan Allah ki tashi, meya faru dake?"

Likitane ya k'araso ya kiran likita mace suka kamata aka shiga da ita emergency dan bata taimakon gaggawa, Papa ji yake shima kamar zai fad'i amma da taimakon su Musa ya samu ya zauna numfashinshi na fita d'aya d'aya, saida suka d'auki kusan awa d'aya sannan likitan ya tsaya gaban Papa, ganin halin da yake ciki yasa yace masa "ka kwantar da hankalinka yallab'ai, Hajia na samun sauki, zata farfad'o nan da zuwa yamma."

Cikin kuka yace "dan Allah zan iya ganinsu?"

"Eh to, sai dai Hajiar amma banda 'yarka."

Sake sunkuyar da kai yayi yana ci gaba da zubar hawaye, wucewa likitan yayi shi kuma ya bawa su Musa takardar maganin yace su duba mota akwai kud'i su siyo, saida suka tafi ya nufi wajen mutanen da suka kawo Khairat asibiti ya basu hannu yana musu godiya, wani dattijo ne yace,

"Ba komai yallab'ai, ai yiwa kaine, Allah dai ya bata lafiya."

Idon nan jawur ya kalleshi yace "ameen na gode, amma dan Allah kun shaidani?"

Murmushi sukayi d'aya yace "yallab'ai waye bai sanka ba, ai mun shaidaka tun shigowarka."

Duk da baiji dad'i ba amma haka yace "to dan Allah wata alfarma nake nema a wajenku? ina so dan Allah abin nan daya faru akan yata ya zama sirri tsakanina daku, idan maganar nan ta fita wallahi zamu shiga uku, ko yarfen siyasa saiya addabemu bare kuma jama'ar gari."

Had'e hannaye yayi alamar rok'o ya sake cewa "dan Allah, ku rufa mana asiri, kar maganar nan ta fita waje, wallahi za'a mana dariya ne ana fad'in munanan kalmomi a kanmu."

Matashin saurayin nan ne yace "yallab'ai karka damu, wallahi babu wanda zaiji maganar nan, insha Allah zamu rik'e wannan sirrin tunda ba wani abun fad'a bane, duba da zamanin da muke ciki, idan bai faru akan k'anwarka ko yayarka ba, to zai iya faruwa da wata shak'ik'iyarka."

"Na gode sosai, Allah ya saka muku da alkairinsa, Allah ya taimakeku kamar yanda kuka taimakeni."

Haka suka bar wajen suna mata fatan samun lafiya, shi kuma ya zauna zuciyarshi na tafasa, sai dai a yau yana ji har abada ya daina neman mata da kuma shan giya, kanshi qasa a hankali ya furta "in dai anyi duniya dan Manzon Allah S.A.W, to nabar giya da matan banza har abada, domin abinda nayi da yaran wasu yau gashi an ninka wannan abun akan yata, ban tab'a ma 'yar kowa fyad'e ba tunda nake, kowace mace na kusanta to da son ranta ne na kuma biyata, amma yau sai gashi namiji fiye da d'aya ya kusanci 'yata da k'arfi, wannan cin zarafi yayi yawa, Allah ina rok'onka gafara abisa zunubaina, wannan tuba tubane na gaskiya, wallahi ba zan sake ba har duniya ta nad'e."

Bayan su Musa sun kawo maganin da wasu allurai an kaiwa likitan, Papa kuma ya tara su Musa yayi tsaye gabansu yace "ku jini da kyau, ina so ku koma gidan rawar nan ku bincika min komai daya faru a wajen, ina so ku zage damtse ku samo min wad'annan 'yan iskan da suka lalata min rayuwar ya, dan wallahi ba zasu ci banza ba dole na d'auki mataki a kansu, dan haka kuyi da jiki ku gaggauta kawo min su cikin kwana uku, ina so kafin Khairat ta dawo hayyacinta su fuskanci hukunci."

D'orawa yayi da "kun fahimta?"

Da k'arfi suka amsa da "Eh yallab'ai."

"To ku motsa, ni ku barni da driver, yanzu wannan shine aikinku kuma yafi tsarona mahimanci."

Anan ya basu umarni shi kuma ya shiga d'akin da Mamie take, k'ura mata ido yayi yana tunano rayuwar da sukayi, hakika yana k'aunar Na'ima fiye da yanda yake k'aunar kanshi, abubuwan da yake kawai sabone yasa kasa dainawa duk da bata so, amma yau kam yayi tuba na gaskiya, likitace ta shigo tana fad'in "sannan yallab'ai, ya mai jiki?"

Kai ya girgiza yace "ku zaku fad'a min, dan har yanzu banga ta farka ba."

Murmushi tayi tace "zata farka yallab'ai, saboda hawan jininta yasa aka mata allurar bacci, kuma gashi jininta ya hau, amma yanzu zan sake dubawa na gani."

Sake awo ta mata sannan tace masa "mu gode Allah yallab'ai, jininta ya koma daidai, amma dole a guji abinda zai tayar mata da hankali idan ta farka."

Shiru yayi dan yasan ba lallai taso ganinshi ba idan ta farka, dan kullum maganarta kar abinda yake ya shafi yarsa, kuma yanzu yasan da bai tab'a kusantar 'yar kowa ba ba abisa sadaki ba, to da duk rashin kunyar Khairat babu wanda ya isa ya mata irin wannan cin zarafin , dan haka ya tashi ya fita daga d'akin, a lokacin 'yan uwa na kusa dana nesa har sun fara samun labarin Khairat ba lafiya da Hajia Na'ima, zuwa bayan magrib yan uwa sun fara zuwa ganinsu, Mamie kad'ai suke gani su koma hakan yasa Papa ya shawarci likitan suka k'ara tsaurara tsaro akan Khairat.


*Tun daga wannan rana*....
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


*Bismillahi walajna, wa bismillahi kharajna, wa 'allah lahi rabbina tawalkalna* _addu'ar shiga gida._


_Bismmilahir-rahman-rahim_


8⃣


*India* tun jiya Mammie ke kiran shalelenta Khairat amma bata dagawa, bayan gari ya waye ta sake doka mata kira amma shiru, abinne ya dameta dan haka ta fara kiran Mamie, amma itama ba'a dauka saboda wayar na gida, ganin itama an kasa dauka yasa ta fara kiran Papa cikin b'acin rai, shi kuma tun daren jiya yasa wayar vibration saboda kar a takura masa, nan ma ba amsa dan haka Mammie take jin in har aka sake riskar gobe a haka to tabbas zata shigo gida niger.


Wani jami'i ne aka tsayar dashi a kofar d'akin da Khairat take ba'a bari kowa ya ganta, kannan Papa da Mamie ne kad'ai suka ganta shima sau d'aya, tunda Mamie ta farka take kuka tana wa Papa Allah ya isa cikin fitar hayyaci, hakan yasa itama ta zama cikin tsaro tunda ya zama kamar suna fallasa sirrin gidansu ne, har yanzu Papa baije gida ba haka ma Mamie gaba d'aya basa cikin nutsuwarsu, hakan yasa kuma sai maganganu suka fara fita musamman daga wajen yan uwa wanda suka ga jikin Khairat d'in

Nan suka fara fad'in kila wa kala ama dai suna gani kamar fyade aka mata, dama duk abinda aka ce ya fara da jitajita to dole a samu banbancin kalamai, a cikin *kwana uku* sai gashi manganu suna yaduwa akan amma Khairat fyade, duk da tsaro da kuma boye abinda ake amma bai hana maganar fita ba.

Wasu kuma suna cewa ba wani fyade kawai dai dubunta ce ta cika watakila sun samu matsala da abokanan shekewarta ne kawai, to haka dai aka dinga yada wannan magana, kuma abu ga manyan mutane dan danan sai labari ya game gari, mutane nata tururuwar zuwa dan ganin kwam amma babu mai ganinta koda kuwa cousine d'inta ne, haka labari ya samu masana'antarta kuma suma sun zo ganinta sai Papa kawai suka ma jaje, amma manager Papa yace a barshi ya ganta saboda sun jima tare ya aminta dashi.

*Duk badakalar nan* da ake Khairat bata san me ake ba, tana kwance da na'urori a jikinta kamar wacce ta shiga halin doguwar suma, ruwa da sassaukan abinci duk ta tiyo ake bata su, duniya kenan.


*Umar Faruk* ma tun ranar bai sake zuwa masana'antar ba, sai dai ya shirya ya fita kamar ya tafi aikin saboda Babanshi amma kuma fafutukar samun wani aikin yake zuwa, dan ya riga daya cire rai da aiki a karkashin Khairat.


Yau ta kama *lahadi* Faruk na kwance d'akinshi akan kafarshi Baba ya shigo, yana ganinshi ya mike zaune yana fad'in "sannu da zuwa Baba."

Bai amsa mashi ba sai kallonshi da yake, tsarguwa yayi da kallon dan haka yace "Baba, da wata matsala ne?"

"Eh, da matsala."

Kallonshi yayi yace "subhanallah, meya faru Baba?"

Gyara tsayuwarsa yayi yace "Faruk, yanzu har kiyayyar da kake ma yarinyar nan ta kai haka, da har zata kwanta rashin lafiya amma ka kasa fad'a mana ko dai mu mata addu'ar samun sauki?"

Duk da bai fahimci Baban ba amma haka yace "kayi hak'uri Baba, wace yarinya kenan?"

Dakuwa Baba ya masa yace "ban sani ba, har ni zaka tambaya wace yarinya? aiku ku kafi kowa labarin abinda ke faruwa tunda ku ke aiki a ma'aikatarta."

Cikin mamaki yace "Baba wai, Khairat kake nufi? meya sameta to? ni bana da labari."

Shima da mamaki ya kalleshi yace "Umar Faruk kamar ya baka da labari, kai yanzu kace baka san meke faruwa ba? bayan kullum kana fita."

Ganin karya ballowa kansa wani liki kawai sai yace "a'a Baba, kasan da yake ina da aiki sosai shi yasa bana da lokacin wani shirme , amma wallahi bansan meya faru da ita ba."

Juyawa Baba yayi zai fita yace "amma Baba me yake damunta?"

"Humm, idan kaje bureau d'in gobe kaji meke faruwa."

Yana fad'a ya bar d'akin shi kuma ya fad'a duniyar tunanin abinda ya samu Khairat, gashi dama har yanzu yana ganinta a idonshi a cikin wannan shigar, tsaki yayi kawai ya kwanta amma
Showing 15001 words to 18000 words out of 186119 words