bazu wanda tun tana kwance aka since matashi.

Jin qarar ruwa yasa Rashida ta tabbatar wanka ta fara hakan kuma yasa ta gyara zama, dan tasan awa d'aya ce zata fito da ita daga bayin, bugu da qari itama ba zata iya barin gidan ba har saita samu abinda take so, dan in bata jira ba zata ma kanta asarar kud'i kuma tana da tabbacin zata samu.
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


1⃣4⃣


Fitowa tayi da d'aurin qirji iya cinyoyinta taja kujera ta zauna a kai tana kallon kanta a madubi, mai take so ta shafa amma tana jin k'iwa, Rashida ce ta taso ta tsaya bayanta tasa hannu tana shafar kanta tana murmushi, ta madubi ta kalleta tayi qaramin tsaki, sun jima a haka babu wanda yayi magana, saida ta gaji da miskilancinta sannan tace "me kike so?"

Kallonta tayi ta madubi amma ba tayi magana ba, sake cewa tayi "kiyi magana macho, nasan wani abu kike so shi yasa kika zo."

Kai ta sosa ta fara magana "eh to, wallahi macho, gidane babu kudi gashi babu kayan abinci, mun shiga wani hali saboda ba kya nan, yanzu ma banso na zo wallahi dole ce tasa na zo."

Juyowa tayi ta kalleta tace "d'auko min kayana nasa."

Juyawa tayi ta nufi wajen kayan nata tana hararanta ta qasan ido, da hannu ta nuna mata wanda zata d'auko mata, tana kawo mata tace "ki kira min Biba."

Nan ma a qufule ta juya ta fita, Khairat ma nayin hakanne da gangan dan abotarta da Rashida bata da wata mamora, shi yasa wani lokacin take sata aikin ma da bai kamata tasa ta ba idan ta lura akwai abinda take so a wajenta.

Ta riga Biba shigowa kafin itama ta shigo tace "gani Hajia."

Ciki ciki tace "ki wanke hannuwanki a ban d'aki kizo ki shafa min mai."

Saida ta kalleta sannan ta shiga dan wanke hannuwan, haka ta fito ta fara shafa mata man a jiki har suka ida Rashida na zaune, da taimakon Biba tasa kaya sannan ta zauna gaban madubi ta murza powder kad'ai sannan tasa Rashida ta d'aura mata d'an kwali, masha Allah tsaf ta fito cikin riga da siket d'in atamfa wacce tasha d'inki tsadadden.

Saida ta gama kallon kanta a madubi sannan ta juya ta bud'a wani coffre ta d'auko poshet (post) ta tsaya gaban Rashida, budawa tayi ta d'auko kudi yan jikka goma goma sababbi guda biyar ta mika mata, tana sa hannu ta karba Khairat ta juya zata fita Rashida tayi saurin rumgumota ta baya tana fad'in,

"Oh, mon chouchou, na gode sosai Allah bar min ke ta wajena."

Murmushi kawai tayi ta janye kanta daga jikinta ta fice, binta tayi a baya haka ta sauka daga kan matakala kamar wata sarauniya, kai tsaye wajen cin abinci ta nufa ta zauna saman kujera, Rabi ce tayi saurin zuwa ta fara zuba mata farfesun kayan cikin rago da kuma soyayyar kaza ga kuma doya da aka mirginata cikin k'wai, fresh milk ta d'auko mata ta zuba mata sannan ta fara ci, Rashida kam an samu kud'i ko ta abincin bata bita, sallama tama Mamie sannan ta kalli Khairat tace "macho na tafi, sai mun had'u."


Ba wani sosai taci ba, dan Khairat a rayuwa bata san k'iba, dan d'an kumarin dake gareta ma yanzu jinshi take a wani babbar matsala, dan haka take kula da jikinta sosai amma bata son motsa jiki saboda ragwantaka, tana kammalawa ta komo falo ta zauna kusan Mamie, hankalinta na a wayarta Mamie kuma na kallo tana d'an satar kallonta wani lokacin tana murmushi.

*****************


*Umar Faruk* kuma tun jiya daya ga Khairat ya kwana cikin tunanin halin daya ganta, sam baiyi tunanin haka daga gareta ba, ya d'auka zata canza ko dan abinda ya faru da ita amma sai yaga akasin haka, ta wani b'angaren kuma haushin abinda wannan mutumin ya fad'a yake ji, da haka har safiya tayi ba tare da yayi wani baccin kirki ba, duk lokacin daya farka Khairat ce zata ziyarci tunaninshi da ganinshi.

Haka kawai yaji yana burin ya sameta a wajen aiki, shiri yayi sosai cikin qananan kayanshi bak'ar riga mai dogayen hannu da wando kalar qasa, yana shiga ma'aikatar ya fara duba wajen ajiye motoci ko zaiga motarta amma babu, duk da haka bai sare ba bayan ya shiga ciki ya aje jakarshi cikin dubara da sand'a ya nufi bureaunta, lekawa yayi ta madubi amma babu kowa kamar dai yanda yake, wata ajiyar zuciya ya sauke cikin sanyin jiki ya dawo mazauninshi, yana zaunawa ya fara tambayar kanshi wai me yasa ya damu da son ganinta ne, tsaki yayi kawai ya fara aikin gabanshi.


****************

Khairat ce ta 'kwalla kiran Biba, tana zuwa tace ta d'auko mata jaka a d'aki da gyale, cikin 'yan mintuna ta dawo da jaka da takalma da gyale duk kalar atamfar dake jikinta, tana sakawa tayi hanyar fita Mamie tayi saurin cewa "sai ina kuma Khairat?"

"Mamie zan lek'a bureau ne naga meke faruwa acan, saina dawo."

Harta wuce Mamie tace "zo mana gimbiyar Papanta."

Dawowa tayi ta tsaya gabanta, tashi tayi tsaye ta shafi fuskarta tace "Allah ya miki albarka Khairat, Allah ya baki yaya na gari, Allah ya kiyaye hanya kinji ko."

Cikin jin dad'i ta rumgume Mamie tace "yau dai da wayona naji addu'ar sa albarka ta fito daga bakinki, na gode Mamiena, saina dawo ba zan jima ba."

Sumbatar goshin Mamie tayi ta fita cike da farin ciki yau Mamie ta mata addu'a, ita kanta Mamie sai taji ba dad'i dan in zata iya tunawa gaskiya ta jima rabon data mata addu'a irin haka.

*Kuskure da iyaye mukeyi sakacin yiwa yara addu'a, wasu na ganin laifin Khairat data zama fitsararriya, amma bansa Khairat ta zama haka ba har saida na samu dalili, Mamie ta kasance mai zuciya da yanke hukunci cikin hushi, hakan ya janyo tun Khairat na qarama ta daina daina janta a jiki bare tasata a hanyar data dace, hakan kuma bai dace ba ko kad'an, yaro ko yana qarami kake masa addu'a zan sai kana masa, uwa uba kuma addu'ar na bibiyarsa ta alkairi ko akasin haka, mu kula iyaye Allah ya bamu ikon tarbiyantar da yaranmu.*


Da takonta na qasaita ta shigo wajen, kallon Abba yayi kowa da komai take da kyau, Umar Faruk daya duqufa da aiki, gabanshi ne yaji ya tsinke ya fad'i hakan ya tilasta masa juyowa da k'arfi, kasa dauke idonshi yayi daga kanta, duk da ba murmushi a tare dashi amma kuma fuskarshi a sake take, ganin yanda kowa ke kallonta kamar da wani abu a jikinta yasa ta tsaya waje d'aya, sake kallon kowa tayi dake wajen ta girgiza kai tayi murmushin takaici.

A hankali tace "kowa ni yake kallo saboda yanzu kuna ganin kamar na zama daban a cikin mutane, kowa so yake yaga ina cikin damuwa, ni kuma abinda nayi alk'awarin ba zan shiga ba kenan har abada."

Tana fad'a ta juya a fusace ta nufi in da ta aje motarta, Umar kuma buga tebur d'in dake gabanshi yayi tare da fad'in "kai."

Da gudu ya tashi yabi bayanta mutanen kuma suka bishi da kallo, Ishaq abokinshi ne yayi murmushi ya kalli na kusa dashi yace "dama ace duk soyayyar da aka fara da qiyayya to tafi zafi."

"Soyayya suke dama?" cewar mutumin.

"Kai ai basai an fad'a ba kasan akwai soyayya wannan wajen, watakila basu fahimci hakan ba."

"Lallai ko abokinka ya d'auko dala ba gammo, to ina had'in kifi da kaska? ai wannan qarmanje ne."

"Ban gane ba, ita kasan meye ra'ayinta to da za kace haka?"

Cewar mutumin "ai ko ban sani ba aikinta ya nuna abokinka baya da wani girma da qima a idonta, tunda nidai banga ko kallonshi tayi ba, zaifi ka bashi shawara ma tun wuri ya fitar da abinda ke ranshi, dan wahalar banza zaisha."

"Ai kuwa in dai har gaskene, to wallahi zaka sha mamaki, dan kana nan zaune za'a gayyaceka daurin aure."

"Tare dani dashi da kai za'a gayyata." cewar mutumin yana kama aikin gabanshi.


Tana daf da shiga mota Umar Faruk ya fito da gudu, juyawa tayi ta kalleshi ta tsaya saida ya karaso, tsaye yayi ya kuma rasa me zaiyi sai yanzu yake jin haushin abinda yayi, juyawa yayi zai koma ciki tace "kazo ka tambayeni me nake ji ne?"

Juyowa yayi yace "a'a, akan me?"

Dogon tsaki taja ta bud'e motarta ta shiga taja tayi gaba, shima ciki ya koma yana tsananin jin takaicin abinda ya aikata, shin me yasa yayi haka???

*****************

Tun yamma da Mujaheed ya dawo gida mahaifiyarshi ta fad'a mashi halin da ake ciki tare da zigashi akan karya yarda, bud'ar bakinshi cewa yayi "Mama bama sai kince ba, wato ni zasu rainawa wayo ko? kafin ta zama ragowa ina biyarta amma tana wulak'anta ni, su kuma sun biye mata aka su ba zasu bata wanda bata so ba, yanzu kenan sun saduda ne shine za'a kawo min ita ni d'an iska ko, to wallahi basu isa ba."


Tunda mahaifinshi ya dawo da dare suka sameshi da mahaifiyar tashi akan basu son wannan maganar auren, Baban baiji dad'i ba haka sauran matanshi guda biyu sun bada tasu shawara akan Mujaheed yayi hak'uri tunda yer uwa ce, amma mahaifiyarshi tace su rufe musu baki dan ba yayansu bane, an jima ana tattaunawa har saida Mujaheed yace in dai har aka takurashi wallahi zai shiga duniya, sanin halinshi da Baban yayi wanda dama ya ake dashi yanzu ma bare ya sake shiga wata duniyar, hakan yasa yace an fasa sai dai yana jin nauyin yanda zai fukanci d'an uwanshi.

Ganin baida wata mafita yasa ya kira Papa a waya ya fad'a masa yanda sukayi cikin raunin murya, a zahiri Papa ya nuna babu komai amma da suka gama waya bak'in cikinshi ya bayyana, bayan ya shigo gida shima bai iya fad'awa Mamie ba saboda gudun matsala, amma kuma ya kwanta da wani sabon shirin a ranshi, safiya kawai yake jira ta waye ya gudanar dashi.


_To Papa muji alkairi._


Kamar yanda Khairat tayi niyyar ba zata bari damuwa ta samu muhalli a zuciyarta ba, tunda ta dawo take d'akinta bayan tasha bacci ta tashi da yamma, da dare kuma tana d'aki tana tik'ar rawa abinta duk dan karta damu.


Ko kari Papa baiyi ba ya fita Mamie bata sani ba Khairat kuma na bacci, hanya Papa ya d'auka shi da drivenshi cikin awa d'aya suka isa fadar shugaban....fan's ku k'arasa min _(bana son tabo mukamin kowa, amma ku kuyanke hukunci ku d'auka babban Muzaffar shine qarshe a mulki baban Khairat kuma na binshi baya)._

Tarba ya samu sosai a babban falon bak'i na palace d'in shugaban , hamshakin shugaban mai dattako cikin fara'a ya kalli Papa yace "sai kuma gaka da safiyar nan, kamar da wata matsala ko?"

"Ba wata matsala shugaba, kawai dai nazo mu gaisane."

"To da kyau, ya al'amura kuma da fama da jama'a?"

"Alhamdulillah, ya naku k'ok'arin?"

"Alhamdulillah."

Shiru ne ya d'an biyo baya kafin shugaban yace "ya yarinyata da jiki, taji sauk'i ko? dan har yanzu bamu sake komawa ba."

Dariya yayi yace "shugaba ai dan mun kwana biyu bamu had'u ba, amma Khairat taji sauk'i sosai."

"Ah to alhamdulillah."

Papa ne yace "ina Muzaffar? na kwana biyu ban ganshi ba."

"Muzaffar ai yau kwananshi uku baya nan, na turashi saudi arabia dan halartar wani taro na qarawa juna sani akan yanda za'a inganta rayuwar matasa."

"Da kyau shugaba, in da kake birgeni kenan, kowane abu kana azashi a muhallinshi, Allah ya taimaka ya dawo dashi lafiya."

"Ameen ameen, fatanmu dai Allah ya mana mai kyau."

Wani shirun ne ya sake biyo baya kafin shugaba yace "'yata dai tak'i yarona, da yanzu mun gama da maganarsu."

Cikin dariya Papa yace "ah haba shugaba, taya zata k'i d'anmu, yanzu haka ma maganar aurensu ya kawoni, dan nayi tunani zamanta a gida haka yayi yawa sosai, kuma tunda suna fahimtar junansu naga zaifi kawai mu had'asu."

Gyara zama yayi a cikin lunstumemiyar kujerar yana fara'a yace "haba dai, kai amma naji dad'i sosai da maganar nan."

D'orawa yayi da "Muzaffar zaiyi farin ciki da wannan magana, gaskiya naji dad'i sosai, danni kaina burina bai wuce naga yayi aure ba."

"Hakane shugaba, dan haka yanzu wuk'a da nama na hannunku, kasa lokacin da kaga ya maka."

"Kuma dai? dad'in ai saiya mana yawa."

"A'a wallahi baya komai, idan kunsa ranar ku fad'a mana, iyakarmu addu'a kawai."

"Umm, to yanda mai zai hana asa nan da wata d'aya, tunda kaga akwai wani babban taro da za ayi 15 ga watan da za'a shiga, kuma dole mu dasu yaran duka zamu halarceshi, kaga zaifi dad'i suje a matsayin ma'aurata, koya ka gani?"

"Hakan ma yayi daidai yallab'ai, Allah ya nuna mana lokacin da alkairi."


A haka dai Papa ya baro gidan cikin farin ciki, take kuma shugaba ya dannawa Muzaffar kira, yana d'auka daga d'aya b'angaren yace "Papana ya kake?"

"Daidai yarona, albishirinka?"

"Nasan baka min albishir marar dad'i, goro fari tas Papana."

"Yanzun nan Mani ya fita daga nan, kuma bai bar nan ba saida muka tsayar da aurenku kai da Khairat."

"Wow, da gaske Papa? kai amma naji dad'i sosai, Papa yaushe kuka saka?"

"Nan da wata d'aya, aiya maka ko?"

"Sosai ma Papa, gashi dai Allah yayi zaifita zama mijin Khairat, to dan Allah Papa kuyi duk abinda ya dace kafin na dawo."

"Karka damu yarona, yanzu zan shiga ciki muyi magana da mamarka akan yanda za'a tafiyar da komai."

"yawwa Papana, a fara shirya komai kafin nazo, idan na zo zamu ci gaba da shiri, dan dole bikina da Khairat ya amsa duk gari a samu labarinshi, saboda kaga fa babbar yarinya ce nima kuma haka."

"To shikenan karka damu."

A haka suma sukayi sallama, haka ma a ciki ya fad'a ma mahaifiyar Muzaffar, sosai itama tayi farin ciki da alamarin dan a rayuwarta tana son bariki da tsare kai, hakan yasa Khairat ke birgeta sosai, dan lokuta da dama suna had'uwa a wasu tarurruka ta wakilci mahaifinta ita kuma ta wakilci shugaba, hakan yasa take sha'awar aurenta da d'anta.


Lokacin da Papa ya dawo Mamie ta gama karinta tana tunanin in da ya tafi bata sani ba, ganinshi yasa ta mike tana tambayar lafiya, saida ya zauna yace ta zauna, zaune tayi tana kallonshi kafin yace "daga gidan shugaba nake."

"Shugaba kuma? lafiya, wani abunne ya faru?"

"Lafiya lau, akan auren Khairat ne."

"Auren Khairat kuma? amma ba'a fasa ba?"

"Eh, an fasa Mujaheed sai Muzaffar."

"Muzaffar kuma, da gaske Alhaji."

"Sosai ma, kawai ke dai kici gaba da shirye shirye, Khairat kuma zan fad'a mata nan da kwana biyu idan muka ga komai na tafiya daidai."

"To Allah ubangiji ya sanya alkairi, Allah ya nuna mana ranar."

Suna gama maganar Khairat ta fito da riga da wando farare tas ta zauna, "ina kwananku?"

Kallon juna sukayi dan haka bata tab'a faruwa ba, amsawa sukayi Papa ya dora da "shalele kin tashi lafiya?"

"Lafiya lau, Biba." ta d'ora da kiran Biba a qarshe.

Da sauri Biba ta fito ta zube gabanta, cikin yauki tace "ki kawo min abinci na."

"To Hajia." ta fad'a tare da tashi.

Anan ta kawo mata ta fara cin abincin Papa kuma fita yayi gabatar da harkokinshi, Mamie ce tace "ki kammala cin abincin ki shirya zamu tafi dake gidan *Safiya*."

Kallonta tayi tace "Mamie nifa kinsan bana son zuwa gidan nan, wannan d'an iskan yaron da yake min maganar banza wai yana sona, bana son ganinshi ma."

Dariya Mamie tayi tace "ki shirya muje kedai, kinsan na jima banje ba, kuma yanzu nasan ba zai miki maganar soyayya ba."

Kallon Mamie tayi danta fahimci me take nufi da abinda ta fad'a, maida kallonta tayi ga abincinta tana tunanin yanda za tayi rayuwa a cikin mutanen da take kewaye dasu ba tare data iya tuna abinda ya faru da ita ba.


Da qyar Mamie ta lallabata ta shiga danta shirya, saida ta d'auki awa d'aya kafin ta shirya ta fito Mamie harta gaji da jira, a motar Mamie suka tafi tare da driventa suka nufi unguwar *yantala* (gidan Safiya diyace ga magajiyar mamar Na'ima, ma'ana cousine d'inta.), da sallama Mamie ta shiga gidan sab'anin Khairat dake binta kawai, da farin ciki matar ta taresu sai dai Khairat fuskarta a had'e take saboda hayaniyar gidan tayi yawa, saboda matan gidan hud'une yara kuma manya da qanana barkatai, haka suka shiga ciki suka zauna, matar ce ta fara gaishe da Khairat kafin tace "ina wuni."

Wata matashiyar budurwa ce ta shigo ta kawo musu ruwa, Mamie ce tasha ita kuma ko kallo, dama Mamie ta mik'a mata girgiza kai tayi tana b'ata fuska, ganin Mamie na janyo hirar da zata sa su jima yasa ta mik'e tsaye tace "Mamie ki sameni a mota, ba zan iya zama cikin zafin nan ba."

Safiya ce tace "gaskiyarki kam akwai fa zafi."

Kallonta kawai tayi ta fice a soron gidan suka had'u da *Aqilu*, wucewa taje yi ya tare gabanta yana fad'in "ya dai, yau kece a gidan?"

"Dallah matsa min a hanya."

"Ina zuwa mana, magana nake so muyi."

"Kar kace zaka min maganar banzan daka saba, dan bana da lokaci."

Wata irin dariya yayi yace "wai maganar so kike nufi, ai wannan tsohon yayi ne, abinda nake son fad'a miki yanzu kuma shine, dan in gaya miki cewa na janye son da nake miki ne, dan ba zan...."

Bai k'arasa ba tace "shashasha."

Wucewa tayi ta barshi nan tsaye kafin ya ida shiga ciki....
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana)_πŸ€œπŸ€›

*RABBANA ATINA FI-DUNIYA HASANA, WAFIL AKHIRATI HASANA, WAK'INA AZABAN-NAR.*


1⃣5⃣

Ba jimawa Mamie ta fito ta sameta a mota,
Showing 30001 words to 33000 words out of 186119 words