da zarar an aje abu za su zo da gudu su dauke.

Captain da kansa yaja mata kujera ta zauna, sannan ya zauna yana magana da mahaifiyarsa da ta zabi serving din matarsa da kanta ba kamar Momy Ikilima da Mama Rukayya da masu aiki suke zuba musu abinci ba, sai da ta fara ajewa Hurriya plate din abinci sannan ta zubawa Captain ta aje masa warin kwai dake kan salad ya saka shi jin tashi zuciya da sauri ya kawar da fuska yana yunkurin amai.

“Me ya faru wani abu ka gani a abinci?”

“No kwan ne na ji shi wani iri, bana son warinsa”

Ammy ta dauke plate din ta zuba masa wani abinci babu kwai har ya fara ci sai kuma ya ji baya son abinci kawai wani abun kwadayi yake so.

“To ko dan kun yi tafiya a jirgi ne?”

“Ammy karki sa na ji kunya mana, yau na saba hawan jirgi?”

Hamad ya kalleshi.

“Ko dai baka da lafiya ne?”

“I think so, jikina ma yayi zafi, tun da muka je ba wani lafiya nake ji ba, kawai dai ina daurewa ne saboda akwai abubuwa da yawa a gabana”

Ammy ta kalli Hamad.

“Wannan ne yaron? Shi da wanda kake yawan zuwa Ethiopia gurinsa daman? Da zarar ka samu sarari sai ka tsallake ka tafi Ethiopia ashe duk saboda shi ne?”

“Wallahi kuwa Ammy”

“Bari na kira Family Doctor ya dubaka kamin ku tafi”

“Okay”

Ammy ta tashi ta bar dinning din, Captain ya kalli daya daga cikin masu aikin gidan ya ce.

“Samo min wani abu mai ruwa ruwa na sha”

“To ranka ya dade”

Sai da Ammy ta kira likitansu na gida ya zo ya auna Captain ya duba shi ya fada musu fever ne kawai yayi masa allura ya kuma dorashi akan magunguna sannan suka bar garin Kaduna a business flight din Daddy da baya kasar domin ta waya ya gaisa da Hurriya yayi mata maraba da zuwa gidansa kuma ya saka Ammy ta hada mata goma ta arziki a madadinsa.
[1/8, 9:53 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*

5️⃣9️⃣




Ya bude Mota ya saka matarsa sai da ya sumbanci hannunta sannan ya rufe motar ya zagaya dayan side din ya shiga ya sake sumbantar ya kama hannunta ya rike yana tuka motar.
Wani irin farinciki yake ji marar misaltuwa a zuciyarsa, be taba tunanin haka ake ji ba idan mace tana dauke da cikin ďan mijinta sai yau, baya iya bayyana yadda yake ji a zuciyarsa son matarsa ya ninku a ruhinsa.

“Ki kula da kanki please”

Ya fada a lokacin da ya bude mota ta fito. Ya waiga ya ga idan babu mai kallonsu sannan ya juyo ya rumgumeta ya sumbanci goshinta. Ya kama fuskarta ya aika mata da wani killer look.

“I Love You so much sanyin idanuwana, thank you for this”

Ya taba cikinta. Hawaye ya zubo idonta ita kanta she can't believe ciki ne a jikinta so she's going to be a Mother now..

“Ni ya kamata na gode maka, you came in to my life by accident sai kuma ka zama cikar farincikina, abokin rayuwata, silar share hawayena, ka min alkawarin kyakkyawar duniya mai ciki da farinciki kuma ka fara va ni tun a yanzu... Buri yana ta cika saboda kana kusa da ni, ina matukar kaunarka Jamal duk mace da ta samu namiji irinka a matsayin miji hakika ta dace da Abokin Rayuwa na gari mai son farincikinta, kai din wata babbar kyauta ce da Allah yayi min ta inda ban yi zato ba kuma a lokacin da ban yi zato ba...”

He weep her tears yana murmushi ya sumbanci bakinta ya latsa kasan lips din.

“My cute Baby my happiness, anything for this Girl”

Ta yi murmushi ta sauke hannunsa kasa.

“Kar wani ya gan mu fa...”

“Zaki kwana gidan nan ne just for today, i can't wait na bude ido gobe na gan ni a kusa da ke, i love you”

Zata amsa masa da i love you too Hindu da Inna Uwani suka fito, sai ta yi saurin juyawa daga fuskantarsa da take ta kallesu.

“Hurriya ke kika yi amai dazun? Twin yace mana ga aman nan a waje Rukayya ta kwashe kuma sai ba mu ganku ba..”

“Eh Captain ne yayi ba shi da lafiya tun a gida shi ne yau sai yayi amai, yanzu ma na raka shi asibiti ne aka ce malaria ce take damunsa”

Captain ya kalleta da sauri, jin yadda ta daure shi a take tace shi yayi mai kuma shi ta raka asibiti.

“Subhanallahi... Jamal babu lafiya?”

Hindu ta tambaya, sai dan yi shiru kamar wanda ya rasa me zai ce.

“Eh...... Amman da sauki asibiti muka fito yanzu suka ce Hurriya...”

Ta kalleshi da sauri tana zare masa ido. Sai ya sauya maganar daman yayi haka ne kawai saboda ya tsorata shi ba zai iya fadar tana da ciki ba a gurin yan'uwanta.

“Sai suka ce ma Hurriya ina dauke da malaria”

Ta daga mishi kai alamar haka ne daidai.

“Sannu har da gajiya ai, kana kokari sosai Wallahi....”

“Na gode zan tafi sai da safe...”

Ya musu sallama ya bude Motarsa ya shiga yana jin zazzabin da Hurriya ta kira masa yana kara rufe shi. Hindu da Inna Uwani suka nufi gate Hurriya kuma ta shiga bangaren mahaifiyarta tana jin komai kamar ba gaske ba. Ta daga kai tana kallon bangaren bayyana yadda farinciki yake a gurinta yanzu abu mai wahala, mahaifiyarta ta dawo a karkashin inuwar mahaifinta a yayinda ita kuma take karkashin kulawar nata mijin, ga dan'uwanta a kusa da ita. To yanzu me ya rage mata? Mai hakuri mawadaci wahala ko bakinciki basa taba daurewa a rayuwa, haka ma dade da farinciki basa dauwama har abada, sai an bude ko wane shafi na rayuwa... Ta shafa cikinta tana murmushi ta samu amincewar ubangiji zata iya ganin abun da ta haifa nan gaba. Jin kukan Rukkaya ne ya kawar mata da duk wani tunani da take a lokacin sai ta yi hanzarin shiga cikin falon dake dauke da mahaifiyarta, Gwaggo da kuma Rukayya.

“Ashe baki da hankali har yanzu? Ke yanzu duk wannan abun da ya faru har sha'awar auren Yasir kike...”

“Allah yana fitar da mai kyau daga mummuna gwaggo kuma yana fitar da mummuna daga mai kyau, ni ban ce sai na auri Yasir ba, ban zan iya auren mutumen da zuciyarku bata gamsu da shi ba, amman dai na sani farinciki ko wane ďa yana tare da uwarsa, idan aka kai Hajiya Gidan yari, Yasir ba zai sake farinciki ba, ni kuma nawa farinciki yana tare da Yasir, dan Allah Yaya Iyami karki saka a rufe ta Allah ya riga ya gama miki komai...”

Tassss Gwaggo ta wanke fuskar Rukayya da mari.

“Ke yanzu soyayya har ta isa ta rufe idonki ki ce kar a hukunta Kaltume akan abun da ta yi?”

Amma ta bata rai sosai tana kallon Gwaggo da alamar dake nuna bata jidadin marin da Gwaggo ta yi ma kanwarta ba.

“Da baki mareta ba Gwaggo, soyayya babu abun da bata sakawa, idan har so zai rufe idon mutum kamar Jamal ya yarda da Hurriya ya aureta a lokacin da take cikin tsananin rayuwa da damuwa, me zai hana so ya rufe idon Rukayya? Kuma gaskiya ta fada, ni Allah ya gama min komai daman idan mutum ya cutar da kai karka ce sai ka rama kawai ka bar shi da Allah sakamakon da yake zuwa daga gurin Ubangiji ga azzaluman mutane mai tsanani ne, irin wanda ruhi baya iya jurewa. Kuma Yasir ya cancanci ko wace kalar alfarma a gurina ko a gurin yayana, yana da kirki be taba nuna min banbanci da mahaifiyarsa ba ko sau daya...”

“Ko ma dai minene ba za a kyale ta ba, tun da na gane hankalinki da nata ya zama iri daya”

“Daman maganar ba a gurinmu take ba, tana gurin jami'an tsaro ne sai yadda suka yanke..”

Gwaggo ta ja tsaki tana jin haushin yadda Amma take da sanyi a wannan bangaren. Hurriya ta karasa ta zauna a kusa da Rukayya tana bata hakuri.

“Barta ta yi ta kukan, ta dade bata mutu ba yara ba su da kunya soyayya na rufe musu ido su kasa ganin daidai”

Cewar Gwaggo cikin tsawa. Hurriya dai bata ce komai ba ya ta tashi ta fice daga falon zuwa bangaren Hajiya Kaltume a nan ta samu kofar falon a bude bata yi tunanin babu kowa a ciki ba sai da ta shiga, tun ranar da yan'uwan Hajiya Kaltume suka tafi da ita suka tafi tare da Khairy da Ruma. Yayanta ta gani zaune ya hade kai da guiwa yayi shiru gwanin tausayi. Ta matsa kusa da shi ta zauna a kasa sai ya dago ya kalleta da karfin hali irin na maza sai ta yayi mata murmushi.

“Hurriya...”

“Yayana ka yi hakuri dan Allah na san baka cancanci haka ba..”

“Kaddara bata duba cancanta, hakuri kuma ya zame mana dole. Sai a yanzu nake kara jinjina kokarinki a lokacin da Amma ta tafi ta barki, yau ji nake kamar ba ni da kowa a duniyar nan, i Felt Empty, da zarar na tuna cewar Hajiya bata da lafiya sai ta ji komai ya tsaya min cak, and ba ma wannan ba taya zamu kalli duniya da abun da Hajiya ta aikata..?”

“Kowa yana kuskurea Yayana, na tabbatar da ace kana sane ba zaka bar Hajiya ta aikata haka ba, komai ai kaddara ne ka fada, ya kamata idan ta same mu mu rumgume ta da hannu biyu...”

“Haka ne Hurriya Allah ya ba mu ikon cinyeta...”

“Ameen”

Ta amsa tana kallonsa cike da tausayawa.

CAPTAIN POV.

Da zazzabi ya isa gidansa, har ya faka mota yana kokarin fita sai kuma ya tuna da wani abun da ya kamata yayi, hakan ya saka shi komawa motar ya sake yi mata key mai gadi ya sake bude masa gate. Unguwarsu Salim ya nufa ya shiga har cikin gidansu ya aika a kira shi, mai aikan yaje ya dawo ya sanar masa da Salim baya gidan. Captain ya sake juya kan motar yana tunanin a ina zai ga Salim a yanzu, ya kira shi a waya ko kuma dai ya gwada ziyarar gurin da yake dan taba zuwa da dare. Da shawara ta biyu zuciyarsa ta aminta dan haka ya nufi wani gurin da Salim yake yawan zuwa idan yana free da dare.

Captain ya faka motarsa waje ya fito ya shiga gurin yana duddubawa sai kuwa ya ci karo da Salim zaune shi kadai yana lasa wayarsa. Captain ya karasa gurin yaja kujera ya zauna, Salim ya dago ya kalleshi gabanshi na dan faduwa.

“Na dauka ka ce babu ni babu kai, me ya kawo ka nan? Zuwa ka yi ka ci min mutunci a gaban mutane?”

“Ba wannan ya kawo ni, zuwa na yi na buga maka warning na karshe, kuma na fada maka abin da baka san na sani ba...”

Captain ya bude wayarsa ya nunawa Salim duk wani evidence da ke nuna shi ya aikata abun da yake zarginsa.

“Ka cutar da Hurriya Salim, saboda bakar zuciyarka ka runtse ido ka yada ďan'uwanka da yarinyar da baka isa ka hana ni sonta ba, hakan duk be maka ba sai da ka sake aikata a karo na biyu bayan mun yi aure, wannan abun zai iya saka ka rasa aikinka ba wannan aikin Soja ba har wani aiki a nan gaba ma, kuma zai iya daureka a gidan kaso ka sani ko? Kuma zai iya lalata character dinta a idon duniya... Ina ka samu hotunan?”

Yayi shiru zuciyarsa kamar zata cire sabisa yadda take bugawa da karfi.

“Wata rana ne na dauki wayar Adam zan tura abu, sai na ci karo da hotunan, abun ya daga min hankali sosai kuma na yi mamaki amman a lokacin na yi tunanin da gaske Hurriya ta aikata hakan da Adam ne, ban ce masa komai ba na tura hutunan da abun da zan tura na goge na bashi wayarsa, har sai zuwa lokacin da muka tafi Ethiopia tare na ganka kana kallon hotunanta da ban san a ina ka samu ba, sai ya fahimtar da ni son Hurriya kake yi, kuma ka san ka yi betrayed dina tun da ka san ina son yarinyar nan be kamata ka so ta ba...!”

“Saboda ubana ne kai? Kamin na nuna ina son Hurriya kai baka nuna ta nuna bata bukatarka ba? And let me tell you something Wallahi ban fara tausayi Hurriya da taimakonta saboda na fada soyayya da ita ba, ban kawa wannan a kusa ba, sai tsintar kaina na yi abun kuma haka Allah ya tsara, me yasa baka karvi Kaddara ba ka hakura sai ka zabi cin zafinta...”

“Na yi tunanin ta aikata da gaske ne, shiyasa tun muna Ethiopia na saka aka yada hotunan, kuma na yi tunanin hakan zai canja alakarku”

“Ka bari zuciya ta yaudareka ka aikata amininka mummunan aiki na cin mutuncin Iyakinsa, a yau da na gane gaskiya idan ina so zan iya hukunta ka Salim ta ko wace siga, amman ba zan yi ba, kasan saboda me?”

Salim yayi shiru ya kasa cewa komai.

“Ba zan manta alherinka a gareni ba, kuma saboda mahaifiya zan daga maka kafa, amman dai alaka da ni da kai na yankata har abada, and duk lokacin da ka sake batawa Hurriya rai zaka rasa damar abubuwa da yawa”

Captain ya mike tsaye ya bar shi a gurin yana gumin tsoro da kunya a lokaci daya. Misalin Tara da rabi na dare Hurriya na zaune tare da Hamad da Amma suna hira kiran Captain ya shigo wayar Amma har ta yi kamar ta bawa Hurriya kai tsaye kuma ta amsa suka gaisa sannan ya tambaye matarsa.

“Amma Hurriya na kusa zan yi magana da ita ne...”

“Eh”

“Hurriya ga mijinki zai yi magana da ke”

Hurriya ta tashi ta karbi wayar ta koma ta zauna.

“Ke shiga ciki mana idan magana ta sirrin yake son yi dake fa?”

Ta tashi ta nufi stairs domin cika umarnin Amma. Sai da ta shiga dakin sannan ta rufe kofa sannan ta ce.

“My Noor ya jikin?”

“Ba dadi har yanzu zazzabi nake ji, i just call to say Hi and kin ci abinci?”

“Na ci, kai fa ka ci...”

“Na sha tea shi kadai na ji ina so, ya kike..?”

“Lafiya kalau”

“Ya Baby na?”

Ta bata rai kamar yana gabanta.

“Ba kyau ka daina”

“Me ye ba kyau? Tambayar babyn nawa?”

Ta masa banza sai yayi dariya.

“I miss you so much, ina jin kamar mun yi shekara ba mu hadu ba haka nake gani”

“Dazun fa kawai muka rabu”

“Yeah kin san na yi alkawari i will spend every hour keeping you safe kuma yau bana tare da ke maybe that's why na kasa natsuwa”

“I'm safe My Noor baka bukatar ka damu”

“I love you”

“I love you more more more”

Yayi murmushi sannan ya ce.

“Wane hukunci Appa ya yanke? Akan Hamad? Na manta ban tambaya na yana lafiya?”

“Yeah... Amman har yanzu ba su yanke hukunci ba”

“Okay... Je ki kwanta kin ji mai tsada, sleep tight”

“I will i love you”

“Ki yi mafarki kin ji babyna”

Ta yi dariya ta kashe wayar, ta bude dakin ta fito a lokacin da ta sauko sai ta samu Hamad da Amma suna hawaye little Hamad yana kan cinyar Hamad yana rike da hannunsa.

“Me aka yi ma kuka kuma?”

“Farinciki, ban yi tsammanin rayuwa zata sake ara min lokaci na ga wannan ranar ba, ban yi tsammanin dawowar Hamad ba, yanzu iyalina sun cika maza uku mace ta daya”

Hamad ya share hawayensa ya kalli Hurriya.

“Da ace da gaske kowa ya mutu, da ba zan sake farinciki ba, kullum ina tunanin rayuwar baya, idan na tuna ni kadai ne a raye sai na ji na tsani kaina ina yawan tuna gargadin da kike mana na zaman lafiya da juna ni da Hurriya, a lokacin da na yi zaton bata raye my heart keep bleeding, kullum ina tunanin da ma ace ban yi ba”

Amma ta kalli Hurriya still tana hawaye.

“Jamal yaron kirki ne sosai, mai tunani da hangen nesa mai rikon amana mai tausayi ba tare da duban mai zai samu a gaba ba, karki yarda ko da wasa ki batawa mijinki rai Hurriya, ba ko wane namiji ba ne ďan kunama, Jamal namijin da ko wace mace zata dauka uba ne har ta goya da zane, kar wata rana yayi miki wani abu ki manta duk wannan, Allah baya son mai butulci”

“In Shaa Allahu Amma”

Ta maida kanta kasa tana kara godiya ga Allah, a yanzu kam abubuwa da yawa sun daidaita a rayuwarta...



*** *** *** **** ****

BAYAN WAƊANSU SHEKARU....

Ruwa aka sheka yau a Calabar kama da bakin kwarya, sanyi ya sauko ta ko'ina ni'imar Allah ce da rahma. Ko ina yayi tsit abubuwa da yawa sun tsaya saboda ruwan da aka yi wasu na tuni suka shige gidajensu. Ta bangaren bangaren Hurriya ma haka labarin yake daman ba sanin kowa ta yi a garin da aiki ya kawo mijinta ba, idan ma ta sani ba barinta fita yake ba, ya saba mata da zaman katon gidan da sojoji suke gadinsa by fire by force, tun tana complain har ta gaji ta karbi dokar ta zuba masa ido.
Jamal ya fito bathroom yana daure da bathrobe ya nufi dansa dake kuka yana ta masifa.

“Tun da na shiga wanka yaron nan yake kuka amman kin gagara rarrashinsa, saboda kawai baki san zafin haihuwa ba”

“Shi din ne ya cika zuciya fa, wai idan ya fara kuka ba a kama shi ba shi ba zai hakura ba, to ni za a nunawa zuciya ni da nake da Hamad da...”

Ya dora dansa a kafada sannan ya juyo ya kalleta.

“Da wa?”

“Da oga Jamal...”

“Wato idonki yayi kwari har wani kiran sunana kike kai tsaye ko?”

Ta kashe masa ido daya.

“Wayar kai tana ta ringing dazun”

“Waya kira?”

Ya nufi wayar ya dauka yana jijjiga dansa.

“Har five missing calls miyasa baki dauka ba?”

“Yaya Namra ce fa, ko na dauka idan ta ji ni ce ba zata yi magana ba, ka san ai ta saba kira idan ta ji muryarna ba zata ce komai ba sai ta kashe waya”

“Amman ai wani baya zama daya da wani, idan ita tana yanke alaka dake ke sai ki sada ai ke din jininta ce babu yadda zata yi”

“Amman dai
Showing 210001 words to 213000 words out of 215510 words