tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻[12/15/2023, 4:14 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*
4️⃣1️⃣
“Ban zan iya fadar wata rana da ka samu matsala da abokinka ba sai yau, duk wannan akan yarinyar da bata kai ta kawo ba ne? Kana kokarin fita hayyacinka, duk wasu abubuw ada ba dabi'unka ba su kake aro ka yafe yanzu! Idan idonka ya rufe ni nawa be rufe ba, ba zan taba karbar yarinyar da duniya ta gama ganin tsiraicin a matsayin suruka ba...”
Be ji zai iya musu da mahaifiyarsa ba, saboda haka ya karasa gurin da take tsaye ya kama hannayenta ya sumbanta yana murmushi.
“Zaki so ta Ammy saboda kina son farincikina, kuma a yanzu farincikina yana tare da yarinyar nan, ba ni da wani buri a yanzu da ya wuce na ga na tsamota daga kogin da aka jefata”
“Wai me yarinyar take da shi ne da babu a sauran mata?”
“Na so wasu matan kamin ita Ammy kin tuna? Har an min baiko da wasu, duka baki ce komai ba ga wannan? Wanda ta fisu komai?”
“Babu wani abun da ta fi su sai tallata tsiraici”
“The more da kike zaginta the more da nake jin kaunarta na karuwa a zuciya, zagin da kike mata ya kara bude min hanyar son taimaka mata”
Kallon rashin fahimtar inda ďanta ya dosa Ammy take masa, cikin bacin rai da daga muryar ta ce.
“Zamu wuce Kaduna gobe”
“Ban samu amincewa daga gurin aikin mu ba”
“I don't care zamu tafi Kaduna gobe idan hutun da ka rubuta ya kare sai ka dawo”
Yayi murmushi sannan ya wuce ciki, da kallo Ammy ta bi danta, kiyayyar da take yi ma Hurriya a yanzu ba dan tana talaka ne kawai ba, har dan hotunanta sun fita a duniya ne, taya zaka kalli kazantacciya yarinya irin Hurriya a matsayin matar danta guda daya tilo? Duk shekarun nan da ta dade tana jiran zuwan wannan ranar? Ace daga karshe Hurriya ce? Duk matsayinta a idon duniya da yadda mutane suke kallon mahaifinsa? Wai ina kishin danta ne? Taya ya barar da komai idonsa ya rufe akan yarinyar nan? A yanzu ne take ganin ya dace ta yi wani abu saboda haka ta bi bayansa ta shiga dakin da yake, sai ta same shi yana canja riga.
“Captain... We need to talk”
Ya karasa jan rigar kasa ya nufi gefen gadonsa ya zauna yana kallonta. Ta daure ta zauna tana aje numfashi a gurin da ba muhallinsa ba, daga bisani ta saita fushin zuciyarta.
“Magana ce da nake son ka ba ni aron hankalinka kuma ka bude zuciyarka ka karbi abun da nake son fada maka”
Ya daga mata kai yana kara tattara hankalinsa gareta.
“Ba zan hana ka taimakawa yarinyar nan ba idan taimaka mata kake son yi, abu mai kyau amman kar hakan ya saka na manta waye kai, Captain ya kamata ka dawo cikin hayyacinka, ka tsaya ka yi tunani mai kyau yarinyar nan bata dace da kai ba, future dinta ya lalace sanadin haka zai iya taba naka rayuwar, taya zaka shiga taron mutane da fuskar yarinyar da duniya ta gama kallon tsiraicinta? Ni ma ta ya zan kalli kawaye na gabatar musu ita a matsayin suruka?”
Yayi murmushi yana saka hannunsa na dama cikin kishiyarsa wato na hagu.
“Ammy kina so?”
“Wane irin magana ne wannan? Taya zaka tambayi uwa tana son danta musamman uwa irin ni?”
“Dan Allah kin amsa min”
“Ina sonka irin son da babu uwar dake yi ma danta shi”
“Toh dan Allah ki so Hurriya, duk mai so na, kamata yayi ya so abun da nake so, duk wani illarta da zaki ina min a yanzu ba zan gani ba, wata kila sai nan gaba shi ma kuma bana fata”
“Ta ya soyayya zata rufe maka ido, ka kasa yin biyaya ga mahaifiyarka Jamal? Akan yarinyar daka hadu da ita da girmanka? Ka bijirewa mahaifiyar fa ta haife ka ta yi wahala da kai? Ko dan saboda kai kadai Allah ya ba ni shiyasa kake min haka?”
Ta karashe maganar idonta na cika da kwalla. Ya kalleta da fuskar da babu wasa a cikinta.
“Zan hakura da Hurriya Ammy, matukar hakan shi ne zai faranta ranki, na hakura da ita Ammy, soyayya ta yi kadan ta yi min irin wannan rufin, zan hakura da nawa farinciki”
Ta share hawayenta tana murmushi ta dafa shi.
“Allah ya maka albarka, ba zaka gane amfanin abun da na yi maka ba sai nan gaba, yarinyar ba ta dace da kai ba, be kamata ta zo a matsayin surukar mu ba”
Ya daga mata kai yana murmushi kadan, sannan ya sauka daga kan gadon ya zauna a kasa ya kama kafarta ya rike.
“Ina rokon alfarmar ki bar ni na karasa aikin da na dauko, na yi ma yarinyar nan alkwarin zan gyara mata komai, shi wannan karki hana ni Ammy”
Ta kama hannunaa da sauri cikin farinciki.
“Ba zan hana ka ba, na amince ka taimake ta, matukar ba zaka auro min ita a matsayin mata”
“Na gode”
Yayi mata godiya ransa babu dadi, domin a iya gaskiyarsa yayi mata alkawarin hakura da Hurriya saboda bata sonta, ba zai zabi farincikinsa sama da na mahaifiyarsa ba, sai dai yayi ma kansa wani alkawari daya zai taimaki Hurriya zai cireta a damuwa kamar yadda ya fada.
“Daddy yana nema na bari na shiga dakinsa”
“Yana can bangaren mahaifiyarsa, dazun sau biyu Bashir Sarauta na aiko masa da mutane yana neman ka ba shi dansa”
Be ce komai ba ya dauki wayarsa da keys din Nene dake kan gado ya fice daga dakin, gaba daya sai yanayinsa ya sauya, rashin kuzari da walwala sun tattara a fuskarsa da jikinsa. Kamar wanda aka yi ma mutuwa haka ya shiga bangaren kakarsa dake cike da mutane a falon da yaranta da jikokinta cikin ƴaƴanta har da Daddy dake zaune kusa da ita. Kowa zai iya shaidar Captain baya cikin farinciki domin abun a bayyane yake a fuskarsa balle kuma mahaifinsa da ya fi kowa sonsa.
“Ina makullin motata? Ashe fitina zaka je ka tayar shi ne ka karbi motata?”
Nene tana maganar tana kallonsa, sai ya karaso ya mika mata key motar ba tare da yace komai ba, sannan ya nemi gurin ya zauna yana mamakin kansa da ada ne idan aka bata masa rai kadan sai yayi kamar zai tashin kowa balle kuma babban abu kamar wannan, amman a yanzu ya kasa yin komai sai ma sauyin yanayi da ya zo masa.
“Jamal.... Lafiya?”
Nene ta tambaya mahaifinsa kuma sai kallonsa yake yana karantar damuwarsa. Captain ya kalli Nene ya kalli kowa dake falon sannan ya mike tsaye
“Ba komai, Daddy ka ce kana son ganina?”
Momy Ikilima ta ce.
“Captain akwai wata matsala ne?”
Ya girgiza mata kai alamar babu. Daddynsa ya sauke ajiyar zuciya cike da kulawa ya ce
“Shiga ka jirani a falon Hajiyar Maru”
Ya amsawa Daddy da kai sannan ya fice daga dakin.
“Baka tambaye shi ina ya kai yaron mutane ba? Kuma na ga yanayinsa kamar da matsala, Allah yasa ba kashe shi suka yi ba, kasan zuciyar Captain fa idan abun ya motsa baya iya rike kansa”
“Zan yi magana da shi Hajiya zan ji ko minene”
Daddy ya mike tsaye ya fice daga falon, kowa sai mamakin yadda yanayin Captain ya canja. A falon Hajiyar Maru wato step mother dinsa Daddy ya samu Captain zaune ya soke kai kasa yana jiransa.
“Karantawa min abun da ya saka ka cikin damuwa?”
Daddy ya tambaya tun kamin ya zauna. Captain ya dago ya kalli Daddy ya fara magana da muryar da ke kara bayyana damuwarsa.
“Ammy ce....”
Ya fada masa abun da ya faru tsakaninsu ya kuma jadda masa cewar ya hakura da Hurriya saboda mahaifiyarsa. Daddy yayi murmushi ya kawar da kai kamin ya juyo ya dauko masa zancen daukar Adam da aka yi, a nan ma Captain be boyewa mahaifinsa komai ba, har video da ya dauka na Adam sai da ya nuna masa.
“Samarin yanzu hauka tana damunsu, idan yarinya tace bata sonka sai ka koma bibiyar bayanta kuma? Da alama dai ba son gaskiya yake mata ba shiyasa ya koma bibiyar rayuwarta”
“Ni ma haka na ce”
Captain ya fada babu kuzari babu nishadi da jindadin da ya shigo da shi. Daddy ya ce.
“Amman Barrister tana da gaskiya, mahaifin yarinyar ba zai kawo matsala ba, ka san wasu iyayen basa son bibiyar irin wannan lamarin”
“An abun haushi ma mahaifinta be san ina son yarinyar ba, be san na dauki wannan matakin ba, na shigar da karar ne a matsayin wanda zai aureta ba tare da tunanin wata matsala zata biyo baya ba, amman yanzu ina tunanin zan yi magana da Barrister na fada mata a canja abun”
“Saboda me?”
“Ammy bata so kuma. Na fada mata na hakura Daddy”
“Hakan yana da kyau, amman ka bari mu yi magana da mahaifinta mu sanar masa halin da ake ciki idan ya aminta sai a sauya labarin daga kai zuwa mahaifinta kai tsaye, a matsayin mahaifinta ya shigar da karar ba kai ba, daman hakan zai fi mutuncin saboda kai ba aurenta ka yi ba, da ace kai mijinta ne kana da full hujja”
“Okay, Daddy amman idan ka tafi please ka lurar da shi wasu abubuwan na rayuwa, na tafi asibitin ban ga yarinyar ba kuma na tafi gurin Momy tace min yarinyar tana gurin mahaifiyarta, ina tunanin korarta yayi gashi bata gani kuma mahaifiyarta bata da lafiya bakinciki sai yayi mata yawa”
Daddy ya ji tausayin Hurriya ya kama shi.
“Amman me zai hana a nunawa mahaifinta video nan maybe zai sauko ya yafewa yarsa laifin da bata aikata ba”
“Aa bana son nuna masa shi a yanzu, already case din yana hannun DSS idan aka fitar da video lauyoyin Adam zai su iya cewa an masa cin zafi ne an masa da karfi ya fadi abun da ba ayi ba, kuma na yi ikirarin ban dauke shi ba fitar da video zai rushe wacan ikirarin nawa, and Salim zai iya samun kofar shigar da koke a kaina, bana son ya samu wannan damar, amman idan aka je kotun shi da kansa zai sallamo yarinyar ai kuma dole kowa ya san me suka shirya kuma na saka a bincika mutanen da suka yada hotunan kowa zai fadi inda ya samu ai daga nan gaskiya zata fito”
“So shari'a biyu za'ayi kenan?”
“Yeah... Yarinyar nan mai tsada ce Daddy, su sun shigar da ni saboda na karya ma dansu hannu, mu kuma mun shigar saboda dansu ya ci mutuncin Hurriya, and na yi alkawari kowa sai ya karbi kasonsa sai na kunyata su kamar yadda suka kunyata yarinyar nan”
Yana fada yana jaddawa jikinsa na rawa yana matse hannunsa.
“Allah kadai ya san halin da take ciki yanzu, sanadinsu ta rasa idonta gaba daya daman ba lafiya ta wadace ta ba”
Daddy dai sai kallonsa yake da yanayin.
“Zan tare da mutane a gobe zan jajanta masa abun da ya faru kuma na fada masa matakin da ka dauka, idan ya ba mu hadin kai shi ke nan idan kuma be aminta ba dole mu yi aje case din”
“Daddy please ba zamu aje case din ba, na mata alkawari ko da ba zan aureta ba be kamata na kasa cika alkwarin da na yi mata ba”
Daddy be sake cewa komai ba, ya ciro wayarsa dake aljihu yayi yana tabawa. Can ya dago ya kalli Captain yana murmushi.
“Lawyer na ne ya aiko min sako, wai Bashir Sarauta yace ba a janye case din a gobe, wata kila yana tunanin saboda an kai case din dukan da ka yi masa a kotu ne ya saka ka sake daukeshi”
“Ya zo nan ne?”
“Ya zo nan amman ban yi magana da shi ba na fada masa be kai wannan matsayin ba a yanzu, da kam ina ganin mutuncinsa amman ban da yanzu, kuma na fada masa idan ya sake zargin ďa na da daukar yaronsa sai na shigar da kara a kansa”
Captain yayi murmushi da be wadaci fuskarsa ba.
“Daddy wannan ai shi ake cewa fin karfi”
Daddy ma yayi murmushi mai sauti irin na masu dollars and pounds.
“I have to do the needful kamin na bar garin nan, gobe da yamma zan koma Kaduna ban sani ba ko Ammynka zata bi ni ko kuma zata tsaya jinyar ďanta ne”
Captain yayi murmushin da ya kusan za a iya cewa ya zame masa dole ne kawai, sannan ya mike tsaye yayi ma mahaifinsa sai da safe ya fice.
HAJIYA KALTUME POV.
“Tun jiya da muka yi waya da ke baki sake kirana ba, abun har ya soma ba ni tsoro, da na shirya zuwa gidanki a yau”
Hajiya Fatee ta yi murmushi.
“Ai ni dole na zo na same ki Hajiya Kaltume shiyasa da Fadeel na kira cikin na ce ya zo ya kawo ni gidan nan, amman Hajiya gajin hakuri kika yi ne har kika aikata mata haka?”
“Ina fa wai ni? Wannan ai can ya fito tsakaninta da dan'iskan saurayinta, wata kila matsala suka samu shiyasa ya watsa hotunan, ai ni ya biya ya hutar da ni wannan kadai ya isa ya hana Hurriya aure, domin babu wanda zai daukarwa yayansa uwa irin wannan? Sai dai a samu dan baro can ko masu gyaran talkama a hada su, idan ma ta samu domin babu mai auren makauniya”
“Kuma kika ce ta rantse da kur'ane?”
“Haka Khairy tace, wata kila kuma wani ne acan waje yake taya mu fadan, kuma shi ma yaron nan ta yi masa wulakanci ba, kuma abun da zai baki mamakin idan ba su saba haduwa ba a ina ya samu hotunanta”
Hajiya Fatee ta kyalkyale da dariya ta bawa Hajiya Kaltume hannu suka tabe.
“Ai wannan abun yayi dadi Wallahi ana ganin yarinya kamar ta kirki ashe ita ma yar banza ce”
“To kin gani dai gashi Allah ya tona asirinta, ko uwarta ai zaman banza ta so samu gurin Alhaji shi kuma da yake ba dan'iska ba ne sai ya bijiro mata da aure”
“Amman ni abun ya ba ni mamaki da kika ce Alhaji be koreta ba, ga irinsu nan da yawa ana kora da ya korata da mun huta ma”
“Ni ma abun da yasa na kira na tambaye ki kenan ko dai Malam be fara aikin nan ba har yanzu? Kin ga shiru fa ina zaune a gidan nan amman Alhaji be yi wani unkuri na maida aurensa da ni ba, jiya kuma Khairy ta fada min kuka yayi ta yi yana tsinewa wanda yayi abun nan”
“Zai yi wahala ace ba a fara ba, ya kamata dai mu kara hakuri kar mu yi gaggawa, domin tun ranar da aka tura kudin na kira shi na fada masa an tura kudin kuma yace min sun shiga ya gani, har na yace min anjima kadan zai shirya ya tafi gurin Malamin nasa ya kai masa kudin, tun daga ranar ban sake jin wayarsa ba, ko yanzu na kira bata shiga ba”
Ta sake gwada kiransa a gaban Hajiya Kaltume aka ce wayar a kashe take.
“Kin ji ko? Ina tunanin ko dai wayar tasa ta fadi ne, har wadda ta hada mu da shi na kirata tace ita ma bata samun wayarsa a yanzu”
Da mamaki Hajiya Kaltume ta ce.
“To kuma be siye wata ba? Ni fa jikina ya fara sanyi Hajiya Fatee”
“Karki ji komai, ni na yarda da Malamin nan dari bisa dari, mu kara hakuri idan aka kara kwana biyu ba mu ji komai ba ni zan shirya da kaina na tafi kauyen na bincika na ji”
“Allah yasa dai yayi mana aikin mai zafi, so nake Alhaji ya zo jiki na rawa ya roki yafiyata kuma ya maida aurensa, sannan a shafe masa Hurriya da uwarta a ransa kuma a hana shi auren nan da zai kara a mallaka min shi na juya shi yadda nake so”
“Wannan ai a rubuce yake, daman ya fada miki irin aikin zai yi kuma zaki gani, ke dai ki kwantar da hankalinki ba gashi kin fara gani ba, wata kila aikin ne ma ya saka hotunan nata suka yadu”
Hajiya Kaltume ta rike baki tana mamaki da dariya.
“Haka fa.. Kin ga gaba kenan sai kora, kuma da yardar Allah sai Hurriya da uwarta sun koma bara, tun da idon ya rufe ba zan bar Alhaji ya nema mata magani ba kuma ba zan bari ya maida uwarta ba, kin ga rayuwa ta kare musu kenan, daman na fada mata sai na dandana mata bakinciki kuma sai ta gani, ba za a ci amanata a zauna lafiya ba”
“Wani abun ma sai nan gaba”
Suka bushe da dariya, Hajiya Fatee ta mike tsaye ta dauki hijab dinta ta saka.
“Bari na tafi kar na batawa Fadeel lokaci aiki zai je na ce ya kawo ni na ganki ya maida ni direba na yayi tafiya”
Hajiya Kaltume ta mike tsaye ta yi mata rakiya suka sauko kasa suna hirar, bacin rai dake zuciyar Hajiya Kaltume tuni ya yaye saboda kawarta ta karafafa mata guiwa kuma ta kwantar mata da hankali. Ganin Khairy zaune a falon ya ba wa Hajiiya Fatee mamaki
“Ah... Na yi zaton kina waje? Tare da Fadeel muke fa”
“Na sani bana jindadi ne shiyasa”
Ta amsa a kasalance tana sauke ido kasa kamar munafuka. Hajiya Kaltume ta ce.
“Wai ke kam me yake damunki? Tun jiya kike wani laude laude kamar kazar da kwai ya fashewa a
Showing 144001 words to 147000 words out of 215510 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49 Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72