na shiga goma na lalace yau kashi na ya bushe, Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Wayyo Allah na ni....”

Kuka da ambaton Allah da take ne ya saka Hajiya Kaltume shigowa, sai kuma ta shigo a sa'a, domin ta shigo ne a daidai lokacin da matar take kara radawa Hajiya Fatee cewar.

“Matansa sunan na yamma da mu kadan, a sabon gidansa suke takaba, ai Malam ya kowa ya ji mutuwarsa duk wanda ya zo nan kuma yake mana”

“Mutuwa? Malam din ne ya Mutu?”

Hajiya Kaltume ta amsa a razane da karfi tana kallon matar dake rike da tabarya tana surfe.

“Yau kwana tara kuwa, gobara aka yi a gidan, komai ya kone, zane wannan na daura sai da aka taimakawa matansa da shi a lokacin da lamarin ya faru”

“Shi nan na shiga uku, ni kam ta kare min.... Al'amurra sai kara rinchabe min suke.... Yanzu Malam be tashi tafiya ba sai da wahala ta tunkaro ni gaba da yamma, na shiga uku na lalace”

“Ba ke kika shiga uku ba Kaltume ni na shiga uku, wayyo Allah wayyo ni kaina”

“Sai hakuri haka mutane suke ta kuka idan suka zo, ai mutuwar Malam ta taba kowa musamman customers dinsa”

Hajiya Kaltume ma ta kai kasa ta zauna kusa da kawarta suna kuka kowa da dalilin kukansa kuma da abun da yake yi ma fargaba. Tun matar na ba su magana har ta gaji ta zuba musu ido, domin ko da matansa ne iyakar kuka da bakinciki da za su yi kenan.

“Ku yi hakuri bayin Allah mutuwa ai ta gaji haka shiyasa kullum ake son a shirya mata, Salmanu tashi ka kai su gidan matan Malam”

Ta fadawa babban ďanta, domin kukan da suke ya fara yi mata yawa har makota na lekowa ta katanga wasu kuma na shigo suna kallonsu. Hajiya Fatee ta mike tsaye rike da jakarka ta tana kuka, taku daya ta yi kamin ta yi na biyu wani hudun zuciya da ido ya rufeta ta saki jakar ta fado kan Hajiya Kaltume da ko alamar tashi bata yi ba, domin jikinta ya mutu kamar an mata allurar kasala.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un idan kika mutar min a yanzu ai sai abun ya taru yayi min yawa ku taimaka min jama'a”

Matan dake kofar gidan suka karasa shigowa suka rika Hajiya Fatee suka daga ta daga jikin Kaltume, suka shimfidata a kasa wasu suka fara mata fifita matar idan kuma ta tashi da gudunta ta debo ruwa aka kwarawa Hajiya Fatee. Sai gata ta farko tana hakki.

“Malam ya mutu, Malam me yasa ka mutu a yanzu? Asirin an tonu na shiga uku wayyo Allah, Malam ya mutu ya bar ni da wahala wayyo Allah na....”

Wani irin shidewa ta yi luuuuuuu jikinta ya sake saki, har sai da matan suka jin tsoron wannan suman nata na biyu, Hajiya Kaltume kuma tana zaune a gurin ta kasa aikata komai sai kuka take kamar ita kadai ta rasa Malam. Ruwan aka sake zuba mata sannan ta farfado tana kallon matan karkarrar dake juya mata tana jin sannun da suke mata kamar a mafarki, fada mata da matar ta yi cewar Malam ya rasu ma sai ta ji abun shi ma kamar mafarki ne ba gaske ba.

“Abun da zai fi akaisu gidan Matan Malam ko kuma a kaita asiri”

Wata daga cikin matan dake rike da ita ta fada, Hajiya Kaltume ta kalleta da jajayen idanuwanta ta ce.

“Ina ne gidan”

“Daga nan ne yamma kusa da kuka uku, Sslmanu wuce gaba ka kaisu”

Yaron da aka kira da Salmanu ya dauki tayarsa da karen kada tayar ya wuce gaba yana zumuncin nuna musu hanya, ganin mutanen daga birni suka zo. Ba dan taimakon Allah da rahmarsa ga bayinsa ba da Hajiya Kaltume bata kai kanta gurin motar da suka shigo ba, domin gaba daya kafafuwan rike mata suka yi, Hajiya Fatee kam sai da aka riko aka saka ta motar idonta sai juyawa yake kamar bata san inda take ba. Yaron ne ya wuce gaba da tayarda yana turawa su kuma suna cikin motar zaune a baya, Hajiya Kaltume ce kadai ke iya kuka a yanzu Hajiya Fatee kam kai kawai take juyawa kamar mai kokarin fita daga hayyacinta, direbansu na biye da su har suka isa katon gidan ginar bolu kana ganin gidan da ba'ayi ma filista ba ka san ba duk kauye ba, ko a kauna sai wanda ya tsaya da kafafuwansa.

“Wai yanzu da gaske Malam ya mutu Hajiya Kaltume? Shikenan Malam yayi tafiyar da babu dawowa? Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, shi ke nan ta kare min dari ta hade min da dubu, Wallahi ganin nake kamar ba gaske ko dai mafarki nake Kaltume?”

Hajiya Kaltume kam kaddara ta riga fata, bata iya cewa Hajiya Fatee komai a yanzu domin ita ma bata da wannan kwarin guiwar. Hajiya Fatee ta unkura zata fita ta kasa saboda jiki yayi nauyi a zaunen da take ma jiri ke debanta yana zubarwa.

“Dukiyata.... Cikin nan..... Ga Afrah... Indai Malam ya mutu a yanzu Malam be kyau min ba”

Direban motar ya juyo ya kalli Hajiya Fatee dake sabbatu tana wani mashalo kamar mashayiya. Cikin gidan Hajiya Kaltume ta shiga babu ko sallama sai tafiya take a gajiye, daga a tsakar gidan ta fadi zaune tana kallon matansa dake zaune da kayaransa.

“Daga tsohon gidanku muke aka fada Malam ya rasu, dan Allah ku ce mana ba gaskiya ba ne”

Karamar ta sauke kai kasa idonta na cika da kwalla, mai karfin halin ce fa amsawa Hajiya Kaltume.

“Malam kam rai yayi halinsa ya riga mu gidan gaskiya, sai dai mu bishi da addu'a, ba Malam kadai ba har da yara biyu”

Hajiya Kaltume ta rushe da kuka tana dora hannu akai tana ihu kamar zata tara musu mutane.

“Kashi na ya bushe a yau, ashe shiyasa komai yaki daidai, na zuba kudi ina duban Malam yana nan yana aiki ashe Malam yana barzahu, na kira waya shiru ashe babu Malam”

Matan suka taso suka rika Hajiya Kaltume suna kuka domin ta tsikaro musu bakincikin rasa mijinsu da suka yi. Hakuri suka rika bata sannan suka rikata suka zaunar da ita a ciki barandar gidan (Balcony) dayar ta debo mata fridge ta aje mata sannan ta zauna tana bata labarin abun da ya faru tana kuka.

“Kin ga gidan nan be dade da gama shi ba, ya saka komai a ciki tv da fridge irin na yan birni ya saka mana, kayan daki ma masu kyau ya zuba mana, na dubu 70k, duk kauyen nan sai labarin gidan nan yake ashe Allah be kaddara a koma tare da shi ba sai bayan ransa”

Hajiya Kaltume ta sharce kwalla ta girgiza kai tana kuka, kai ka ce kukan rashin Malam kawai take da gaske ba kukan neman mafitarta ba.

“Yaushe ya rasu?”

“Yau kwana tara, kuma mutuwarsa ta bawa kowa mamaki, shiyasa har wasu suke zargin ko jifansa aka yi, domin Malamai suna haka, idan aka ga ka taso ana yi da kai a gari sai hassada ta shiga ciki”

Dayar ta karba mata.

“Ai ba kama ba ce wannan abun jifa ce kawai, domin yana cikin aikinsa karfe daya na dare sai wuta ta fara kamawa a dakin, ihunsa kawai muka ji muka fito aka yi ta dukan kofar ta ki budewa sai da ta cinye shi tass, kuma wutar bata tsaya nan na haka ta bi gidan nan ta cinye komai har da yarana biyu iro da dan inna, zane wannan na daurawa ba mu fita da shi ba, sai da makota suka kawo mana Hijabai, bayan wutar ta cinye komai ta kama ginin gidan ta kone kamar watsa fetur, wannan abun ya bawa kowa mamaki bayan an yi masarar kashe wuta aka bude dakin wuta ta ci Malam abun babu kyau gani, haka ma aka saka shi ba tare da an yi masa wanka ba sallah akwai aka yi masa aka saka shi a rame, saboda jikin ya kone wanka ba zai yi ba”

Ta karasa cikin kuka.

“Dole ayi masa jefa mana, a kauye ne wane Malami ne yake irin aikinsa? Babu shi kuma gashi Allah ya amince masa komai girman gona ko gida sai aji Malam be ya siye va dole hankalinsu ya tashi ba, mota ma wannan wanda Malam yake hawa abar kallo ce”

Hajiya Kaltume ta Kalli babbar matarsa tace.

“Amman duk wanda ya aikata nasa wannan abun mu ya aikatawa ba Malam ba, mu ya jefa a matsala”

“Haka kowa yake fada, ga Malam da mutane manyan mutane kala kala gari gari zuwa ake saboda iya aikinsa, kowa ya zo cewa yake ba mu aka yi ma mutuwa ba su aka yi ma”

“Wannan abu be yi dadi ba, Kawata na kiran wayarsa a kashe kullum ina sauraren ko zai kira amman shiru ashe wani labarin ake na dabam”

“Malam ai be fita da komai ba, wayarsa ko ganinta ba ayi ba”

Hajiya Kaltume ta sauke ajiyar zuciya, idanuwanta suntun suntu tsabar kukan da tasha.

“Kuma be bar muku sakon komai ba?”

“Ina zancen barin sako a mutuwar da ba a san da zuwanta ba balle a shirya mata, kuma ko da ya bar wani abu ai wuta ta kone komai ina za a gani ma”

“Ba shi nake nufi ba, sako haka ko na kalami cewar an turo masa kudi ko kuma kudin da filin da yake guri kaza ba nasw ba ne? Ko gona?”

“Aa babu kayan kowa a hannun Malam, domin idan ya siye gida ko gona ko fili ya kan kiramu ya fada mana cewar gidan da yake guri kaza ko fili ko gona sun zama mallakinsa ya siye, har takardun da ake yi na shaida yana nuna mana, kuma yawanci idan sai siya da aminsa yake zuwa Malam Musa, bayan rasuwarsa kuma Malam Musa ya hannata mana komai na Malam kuma ya bi mutane da dan abun da yake hannun malam na mutane aka biya, babu hakkin kowa a gurin Malam yanzu”

“Da dai zan samu ganin Malam Musa na yi magana da shi, saboda akwai mai yawa da na turo masa a account da sunan zai tafi gurin Malaminsa yayi min aiki, kuma kawata ma Hajiya Fatee ta bashi kudi mai yawa ya siya nata gona da fili a kauye, da zan ga Malam Musa sai na tambaye shi ko ya san wani abu a kai”

“Gaskiya babu, kuma wani be taba zuwa mana da irin wannan maganar ba sai ke, amman saboda kaucewa zargi, bari a kira Malam Musa sai ku yi magana da shi”

Amaryar ce ta aika yaro gurin da ta san aminin mijinta na zama aka kirashi, da ya iso ya shigo cikin gidan suka gaisa da Hajiya Kaltume ta yi masa gaisuwa sannan ta kora da bayani.

“Ni sunana Hajiya Kaltume akwai kawata Hajiya Fatee tana mota yanzu haka, mutuwar ta taba ta sosai ba zata iya takowa nan ba, ni na tura masa kudi kwana goma da suka wuce ko sha daya, kudi mai yawa akan cewar zai kawai Malaminsa ayi min aiki domin wannan aikin ya fi karfinsa, yace Malaminsa zai siye rakumi da kayan aiki, shi ne nake tambayar ko ka san wani abu akan haka”

Mutumen da ake kira da Malam Musa ya girgiza kai.

“Aa Wallahi be yi wata magana kamanciyar wannan ba, kuma Malam ai Malaminsa ya dade da rasuwa shekara kusan goma sha wani abu yanzu”

Hajiya Kaltume ta yi tagume.

“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un...”

Tana jin wani sabon kuka na taso mata.

“Ita kawata dake mota har filaye take bashi kudi ya siya mata da gona ita be yi maganarta ba ko? Ko kuma ya bar wata wasiya? Ko a cikin gidajen da yake siye yace wannan na Hajiya Fatee ne ko na wata”

“Aa babu wannan, Malam be taba fada min haka ba, Maimuna a cikinku akwai wanda ta taba jin magana makamanciyar wannan abakin Malam”

Uwar gidan ta girgiza kai.

“Aa ai na fada mata ba mu san wani abu da Malam ya siye ya ce na wani ne ba, sai dai idan sheri za'ayi masa anji ya bar dukiya a haka kai da mutanen birni azo ace za a kwace”

“Aiko ba zata sabu ba, komai ai sai da hujja ake yinsa, Malam yana kafa shaida idan zai siye abu, har takardu ana yi sai dai wutar da ta kone komai yasa ba a tsira da takardun ba, amman shaidu ai suna nan da ransu, babu wanda ya isa ya zo mana daga wani guri da sunan dan boko ya karbi duniyar Malam, idan ma manufar ku kenan to tun wuri ku tashi ku kama hanyar garinku ko na tara muku mutane yanzu nan”

Hajiya Kaltume ta daga kai ta kali mutumen da ya mike tsaye yana nuna mata kofar fita bakinsa da asuwaki hannunsa kuma rike da carbi.

“Indai kai aminin Malam ne tabbas ka san gaskiya sai idan cinye dukiyar zaku yi, zan tafi amman ba zamu kyale wannan maganar ba”

Ta dauki jakarta ta mike tsaye ta fice a gidan cikin bacin rai tsabanin shigowar da ta yi da zullumi. A mota ta tararda Hajiya Fatee ta fito da kafafuwanta waje tana zaune daga ciki ta jingina da motar.

“Malam ya mutu, kuma ta tafi da dukiyarmu amman na ke kin yi wauta Hajiya Fatee kuma kin yi sakarci irin haka ake gudu daman, Malam be bar wata wasiya akan kudinki ko gonakin da yake cewa ya siya miki ba, kuma babu wata shaida ke ma kuma baki nemi ya baki shaidar komai ba lokacin da yake raye, yanzu ga irin ta nan nan ke baki ga duniyarki ni kuma ba ni ga aiki ba kudin rakumi....!”

“Ni ai idai wannan abun ba zai tashi ba, kudin mai sauki ne indai wannan abin kunyar ba zai bayyanar min ba to zan iya hakura da komai”

Direban ya kai dubansa garesu.

“Subhanallahi wai Malamin da kuka zo gurinsa ne ya rasu?”

“Ba a sani ba, ina ruwanka? Ka kama bakinka ka yi abun da ya kawo ka, ba gulma da sa'ido ba”

“Ah Hajiya daga tambaya Allah ya baku hakuri, ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni”

Ya bude da yake jingine ya shiga ya rufe.

“Shiga mota mu tafi Hajiya Kaltume, zancen gida da gona zamu yi tunanin abun da ya kamata mu yi daga baya”

Hajiya Kaltume ta juya ta dayan bangaren ta shiga motar, tana kuka.

“Abubuwa duk sun lalace min, idan na taba nan wani gurin ne zai kwance, idan na dawo ta nan wani gurin kuma sai ya balle, ina saka ran za'ayi min aiki na samu sauki wannan rayuwa da nake ciki sai kuma mu zo mu tararda bakin labari wannan abu da me yayi kama... ”

“Ke naki ai duk mai sauki ne, ni cw a ruwa tsundun kuma babu tudun dafawa”

Haka suka yi ta juya zancen suna bakinciki da kukan da ya mantar da su akwau bandits a hanya, direban yana sauke su a gidan Hajiya Fatee yayi tafiyarsa. A bakin kofar dakin Hajiya Kaltume ta zube zaune ta cire mayafi ta je jaka a gefe tana kuka.





NAMRA POV.

Gaba daya ta jika screen din wayarta da hawayen dake zuba a idonta, hoton Captain take kallona gurin da yake sanye da kayan sojoji yana daga tsaye aka dauke shi hoto. Ta san ta yi rashi na har bada domin abu ne mai wahala a yanzu Captain yace zai dawo ya aureta ko da kuwa ya rabu da Hurriya, ta san ba haramun ba ne amman ai da kunya, ace miji ya saki kanwa ya auri yaya, kuma yadda ta san halin dan'uwanta ba zai aminta ya aikata haka ba.

“Tun farkon zuwanki bangaren nan, ban miki komai ba sai alheri, ke kika saka na canja ashe ma kara da na canja domin kin nuna min cewar ke ba halak ba ce mai tausayi, kin raba ni da Salim na hakura ina murna Allah zai musanya min da ďan'uwan sai kuma ki zo ki karbe min shi? Baki ji kunya ba? Kin raba yayarki da samari har biyu?”

Ta runtse ido tana kuka.

“Ina sonka Captain ina sonka me yasa baka gane ba, duk zuwan da kake gidan nan baka fahimci hakan ba? Ko kuma dai Hurriya ta dauke maka hankali ne saboda ta fi ni kyau? Me ya rude ka ka auri yarinyar da ba ajinka ba, yarinyar da bata dace da kai ba, irin wannan jihadin da ka yi a finafinai nake ganin yana faruwa, ko kuma a wasu kasashen turawa amman ba gidab Malam Bahaushe ba, waya ce maka hakan zai baka kwanciyar hankali? Me yasa zuciyarka bata shawarce karka aikata ba?”

A firgice ta bude ido ta kalli wayar da ke ringing, zuciyarta ta shiga shawarar ta daga kiran na Salim ko kuma ta kyale shi. Bata gama yanke hukunci ba ta samu kanta da amasa kiran.

“Hello”

“Namra... Ai da kin fada min dan'uwanki Captain zaku bawa auren Hurriya da ban wahalar da kaina ina neman ta so ni ba”

Namra ta yi shiru hawaye na sauko mata.

“Na ji an daura aure a yau, ina taya ku murna, amman ki sani amana ba zata bar dan'uwanki ba, ya ci amanata ya aikata abun kunya, ya aure budurwar abokinsa abokin ma na kusa da shi, yanzu na gane dalilin da ya sa baya son ma na yi masa zancen Hurriya ashe kansa yake yi ma campaign, kuma bukata ta biya tun da yayi nasara sai dai ina son ku sani KARMA is real kuma kowa ya aikata mai kyau zai sani”

“Salim bana da masaniya akan komai, laifin ba na Captain ba ne na Hurriya ne, daga mahaifiyarsa har mu ba musa san da zancen daura auren a yau ba, sai sanar mana aka yi, wata kila ta yi magana da shi ne ta roki yayi mata haka, amman Captain ba zai yarda a aikata hakan da son ransa ba, waye zai so ya auri Hurriya bayan duk abun da ya faru a yanzu, kuma idonta ya rufe bata ganin komai a yanzu...”

“To me yasa ya aureta?”

“Shi ne abun da nake kokarin ganewa, ni kaina a rikice nake Salim...”

Be sake ce mata komai ba ya katse kiran, sai ya jefar da wayar a kasa ta fada a gadonta tana kuka mai karfi, bata taba jin kaunar Captain ba irin yau bata taba sanin tana sonsa so mai tsanani ba sai
Showing 162001 words to 165000 words out of 215510 words