tafiyar da ta yi ta bar mahaifiyarta cikin fushin abun da ta aikata musu ashe ma ba mai dade bace a duniya, a yanzu kam sun zama ba su da kowa daman uban ya dade ta rasuwa yanzu kuma uwa ta bi bayansa. Har aka yi amsar gaisuwa aka kare Hajiya Kaltume bata zo gidan ba, sai da aka kara kwana sannan Yasir ya zo gaisuwa gurin Fadeel Maama kuma ta shiga ciki ta yi ma matan. Yasir ya fada masa halin da Hajiya Kaltume take ciki na rashin lafiya da ba zata ita zuwa gaisuwa ba, sai Fadeel ya tausayawa mata duk da kasancewar Yasir din be fito fili wikiwiki ya fada masa hauka take ba. Sai dai hakan be hana shi tausaya masa ba, domin daga ta shi Hajiyar har Hajiya Kaltume bin bokaye da rashin yarda da kaddara be haifar musu da ďan mai ido ba.
*** *** ***
Lokacin da Captain ya kira Appa ya fada masa sun kusa shigowa garin Gusau, sai Appa ya fadawa Amma ita kuma ta kira mutanen gidansu ta fada musu sai duk suka taru a gidan na Appa a bangaren Amma. Shi kan shi Appa sai ya dawo gida da wuri, kamin su iso, Amma ta kasa zama ta kasa tsayuwa sai safe da marwa take ta kagara ta ga ďanta shi din ne ko waninsa. Suna Haka Hajiya Binta ta iso daman tun da Appa ya fada mata take ta mamaki kuma take daukin ganin jikan nata.
Duk yadda Appa ya so ta natsu sai ta kasa saboda abun da yake gabanta ma son ganin Yarta da Ďanta. Daga Hurriya har Mama Rukayya babu wanda ya san da daurin auren Alhaji Haruna da Iyami da aka sake daurawa bayan dawowarta saudi balle tarewar Amma a gidan Appa sai da suka dira a gidan.
Motarsu na tsayawa Amma ta fito da sauri tana sanye da Hijab. Hindu, Gwaggo da Inna Uwani suna bayanta Appa tare da Alhaji Musa da Malam Zakiyyu kanensa da Hajiya Binta duk suna tare da shi, Yasir ma da a lokacin ya iso gidan ya fito motarsa da sauri yana kallon Hamad da Hurriya da suka fito motar. Amma ta durkushe a kasa tana rufe baki tana kuka, tabbas danta ne amman kamaninsa sun sauya yanzu girma ne yake kamashi ya zama ba kamar lokacin da aka dauke shi ba, banbancin wacan ranar da Ruma ta fito mota tana fada mata Hamad ya mutu da wannan shi ne wannan yana a raye ne, amman kukan kusan daya ne, Appa ma hawaye yake kusan kowa kuka yake har shi kan shi Hamad ne.
Amma ta dubi Hurriya dake kallonta garau tana gani babu gilashi ga kuma Hamad sai ta juya baya tana kuka tana godiya a gurin Allah. Hamad ya nufi inda take da gudunsa yana kuka kamar za a cire masa rai irin kukan da ya fi kama da rashi. Ya rumgume Amma yana kiran sunanta jikinsa na rawa muryarsa na rawa Amma ma ta rumgumeta danta tana kuka sosai. Hurriya ma kuka take Hajiya Binta, Rukayya Yasir kusan kowa sai da yayi hawaye a gurin saboda tausayi. Amma ta taba fuskarsa ta taba kunnesa ta lalaba jikinta ta shafa bayansa kamar wanda ta rude.
“Hamad... Hamad... Hamad.. Hamad... Allahu Akbar.. Hamad.. Da gaske ne ashe Hurriya gaskiya ta fada maka mutu ba...”
Hamad ya dago ya rumgume Appa yana kuka.
“Na yi marmarinku Appa na yi kewarku, rayuwar da babu iyaye babu dadi no matter what mutum zai samu a duniyar nan”
“Mun yi bakinciki rashinka Hamad ashe kana raye, Alhamdulillahi”
Appa ya share hawayensa sannan ya kalli yarsa yana murmushi.
“Hurriya an samu lafiya Alhamdulillahi”
Hurriya ta nufi mahaifinta ta rumgumeshi tana kuka.
“Kukan ya isa haka ku shiga ciki mana”
Hajiya Binta ta fada, sai da Hamad ya rumgume kowa a gurin sannan ya daga kansa yana kallon gidan ta ko'ina.
“Ashe zan dawo na yi rayuwa a nan”
Ya fada yana tuna ranar da Amma ta shirya kayanta zata bar gidan, tana boye musu sakin da Appa yayi mata, shi kuma a lokacin ya gama fahimtar komai saboda ya fi Hurriya wayo da fahimtar abubuwa. Yasir kallonsa yake yana jin tausayin mahaifiyarsa ita kawai yake tunawa halin da take ciki yanzu da kuma wanda zata shiga a nan gaba.
A falon Amma suka zauna gaba dayansu, Hurriya na ganin yadda aka kawata falon aka saka furniture da komai ta fahimci Mahaifiyarta ta dawo sai farinciki ya lullube ta daman abun da take da burin gani tuntuni kenan dawowar mahaifiyarta a gidan.
Sai da suka yi sallah suka dan huta sannan suka sake haduwa a bangaren Appa har Momy da yaranta Hamad ya ba su labarin yadda aka daukeshi zuwa lokacin da suka buga masa karfe a kai suka fita da shi daga dakin be sake sanin inda yake ba sai da ya farka ya ganshi a wata kasar tare da wasu mutanen da ba yarensa ba kabilarsa ba.
“A haka na yi ta rayuwa a cikinsu, sun suna min kauna sosai sun dauke ni kamar ďansu ba su tana muna min banbanci ba, saboda mahaifiyar Salim mace ce mai son mutane, musamman ni, tana yawan cewa tana ganina kamar ďanta Salim ne, tun daga lokacin da Captain ya fada min cewar ba ni da kowa a duniyar nan, sai na rike su a matsayin yan'uwa da iyaye amman babu daren da bana kewarku...”
Captain yaja numfashi ya sauke har lokacin yana jin fever dake tare da shi ya kwadayin son abu mai ruwa be fita jikinsa ba.
“Wannan dalilin ne kadai ya saka na dagawa Salim kafa, ta bangaren nan yayi min hallaci kuma mahaifiyarsa ta cancanci ko wane kalar tukuici daga gareni”
“Me yasa ka ce min kowa ya mutu?”
Hamad ya tambaya, sai dai Captain be kula tambayarsa ba ya dauko zaren labarin tun daga tushe.
“A ranar da na zo gidan nan, na shiga bangaren Momy na samu Hurriya tana kuka ta fada min cewar an dauke dan'uwanta, kamin ita Namra ta ba ni labarin abun da ya faru saboda tana saka ran ko akwai hannuna a ciki ne saboda fasa min tayun mota da Hamad yayi da kuma kyautar da na yi ma Hurriya a lokacin ta gilashi sai ta ki ta karba, na ce mata sai na dauki mataki, a yanayin yadda aka ba ni labarin ma sai na fahimci ba Hamad aka zo dauka ba Hurriya aka so sacewa da ba sameta ba ne aka dauke Hamad, a ranar Hurriya ta roke ni wata alfarma ta tambayi sunana na ce mata ni Soja ne sai tace Malam soja ka nemo min dan'uwana dan Allah, ni kuma na mata alkawarin zan nemo mata shi har na yi mata rubuta a takardar na ranar da na dauki alkawarin da sign na bata, tun daga lokacin sai na baza mutane na neman yaron sai dai ba a same shi ba sai after an yi sanarwar cewar ya mutu a nan, sojojin da suke aiki a hanyar sokoto suka samu gawarsa a cikin wata gona shi ma kuma saboda sun za su shiga cikin kauyen dake gurin ne gurin kai farmaki, a take suka sanar da da headquarters Mu cewar sun samu gawar yaron da na ba da cigiya na shigar da report akansa, su kuma suka sanar min, a take na shirya ni da kaina na tafi gurin tare da wasu soldiers daga headquarter saboda bincikar yadda komai ya faru, sai muka samu har lokacin yana zubar da jini fresh blood ba daskarare ba irin na wanda ya mutu, kuma da na taba shi sai na samu yana da rai amman baya numfashi, a take muka dauki gawarsa zuwa asibitin tureta dake sokoto muka saka likitan gurin ya duba shi sai ya fada mana cewar alama sun nuna yana raye, amman yayi nisan da abu ne mai wahala ya iya tashi saboda ran sa yayi nisa kadan ya rage masa, i never give up na dauke shi daga wannan asibitin zuwa asibitin dake cikin garin sokoto wato asibitin anan suka karbe shi suka yi iya abun da za su iya kuma aka yi nasara numfashinsa ya dawo, sai dai sun fada mana abun ya taba kwakwalwarsa, da ya fara jin sauki sai ya zama be bude ido be cewa komai baya motsi numfashin ne kawai a duk tsawon lokacin nan yana karkashin kulawata ne, ni da kaina na nemi Salim ya taimaka min na je da yaro a kasar da mahaifiyarsa take, saboda mahaifinsa dan garin gusau ne, dan Sarauta Family's, sai dai mahaifiyarsa yar kasar Ethiopia ce aiki ya kai mahaifinsa a can ya aure suka haifi Salim da Ziaw sai suka rabu ya dawo nan Nigeria tare da Salim ya bar nata Ziaw a can wannan dalilin ne ya saka ke kiran Salim da Ethiopian saboda yana zuwa gurin mahaifiyarsa sosai yana zama a gurinta, be musa min ba ya amince sai na nemi transfer daga asibitin zuwa asibitin Medical Center Hayat MCM, saboda ina tunanin duk wanda zai saka ayi ma karamin yaro kamar Hamad haka zai iya kashe shi idan ya san yana raye, kuma gashi mu ba mu da full evidence na wanda ya aikata hakan balle mu kama shi, tun da ba mutanen aka kama ba gawarsa kawai aka samu, ko ba komai a can kasar zai fi samun kulawa fiye da nan, da Salim muka shirya komai bayan na fada masa halin da ake ciki shi kuma ya sanar da mahaifiyarsa sai ta yi mana duk abun da ya kamata muna isa aka karbeshi a asibitin, kuma sai aka yi sa'a yana ta samun sauki, sai dai hankalinsa ya tabu ya kan yi wasu abubuwan masara dadi yana yawan firgita da kiran sunayen Iyayensa sai likitocin suka tabbatar min da cewar matukar ba a sama masa abun da yake so ba zai iya haukacewa kuma zai yi wahalar warkewa, wannan dalilin ya saka idan na kai masa ziyara ko Ziaw take ko Mahaifiyar Salim mu kan cusa mata cewar bashi da kowa, na kan ce baka da kowa Hamad kai kadai yake rayuwa ko bachi yake idan na fada masa haka sai ya zabura, na fada masa kowa naka ya mutu a yanzu mu wasu Iyalin ne da ka samu wadanda ba ka sani ba, a haka sai da Hamad ya kwashe shekara daya a asibitin sannan ya ji sauki har suka sallame mu, sai na kai shi a gidansu Salim a gidan ya fara rayuwa kuma ya rayu da karyar dana cusa masa cewar ba shi da kowa”
Captain yayi shiru yana jan numfashi kamin ya cigaba.
“Be cika damuwa ya bani labari ko yayi hirar rayuwarsa ta baya ba, wata kila saboda na riga na fada masa cewar ya rasa kowa ba, wata rana ya taba tambaya ya aka yi ya rasa kowa sai na fada masa, yadda na tsince shi, kuma a lokacin da yake nan asibiti ma nemi iyayensa sai na samu bakincikin rashinsa ya kashe su, sai ya tambaye ni ina da wata wata yar'uwa Hurriya ita baka ganta ba? Haka ne Hamad...?”
Captain ya tambaya sai Hamad ya daga masa kai yana tuna lokacin.
“Na ce mishi ita ma na yi mata irin yadda aka yi maka, shin kana sha'awar komawa garin da babu kowa sai yace min aa, da haka na samu ya fuskanci rayuwarsa na saka shi makaranta a can, saboda ya fada min lokacin da yayarsa yake raye yana da burin zama likitan ido saboda ita, na karfafa masa guiwar yin karatun saboda ya cika burinsa, har kai inda yake a yanzu, a lokacin da ya gama high school sai na nema masa makaranta a kasar kuma muka nemi bangaren da yake aka ba mu, saboda sun yaba da hazakarsa, a yau Hamad yana cikin best students na makaranta mai su kwazo da maida hankali, na taba daukar hotunan Hurriya na tafi da su na zimmar nuna masa sai kuma na kasa hakan, saboda ban san ta yadda zan amsa masa tambayar da zai min ba, kuma a lokacin ba ni da kakkafar alaka da ku kamar haka, kuma na san mahaifiyarsa ba zata iya daukar wani mataki ba, tun da ga Hurriya ma a lokacin ana musguna mata babu wanda yace komai na san wanda ta aikata wannan zata samu wanke kanta cikin ruwan sanyi ko ma ta sake kashe shi”
Captain yayi murmushi yana tuna bawa.
“Na bawa Hamad labarin sabuwar budurwar da na yi, har nace mishi ya dauketa a matsayin yayarsa sai ya ba ni abun hannu a matsayin kyauta kuma na kawo miki Hurriya gashi nan a hannunki”
Hurriya ta kalli abun hannun ta kalli Hamad Hamad ma ya kalli abun hannun da ya taba bawa Captain.
“Ta yadda zan juyar da karyar da na yi ta zama gaskiya ne abu mai wahala a gareni, shiyasa na bar abun a haka har zuwa lokacin da gaskiya zata yi halinta, kuma wannan ne dalilin da ya saka na zabi zuwa Ethiopia aikin idon Hurriya fiye da ko wace kasar, lokacin da na yi wacan lafiyar tare da Salim muka tafi a lokacin ya gane ina son Hurriya hakan yasa har yanzu nake kyautata zaton shi ya yada hotunan Hurriya a kafofin sada zumunta, kuma zatona ya tabbata domin hacking din da na saka ka yi min da kuma bincike sirrin wanda na saka aikin ya fada min haka, sai dai yadda ya samu hotunan ne abun da ya daure min kai, a lokacin da yayi min furucin cewar yana da sauran amfani a gurina sai na saka aka dauke ka daga gidansu aka kama mata masauki a makarantarku saboda gudun kar zuciya ta saka shi ya cutar da kai, na san akwai tsaro a makarantar ta yadda ko da ya aikata maka hakan za gane ko waye...”
Sai a lokacin Hamad ya gane dalilin Captain na maida shi hostel din makarantar da yayi.
“Wata kila ya samu hotunan ne ta hanyar Adam”
Hurriya ta fada, Captain ya daga mata kai.
“Ni ma haka nake zato, ko da sanin Adam ko kuma a sirrance domin dan'uwansa zai iya fada masa matsalarsa shi kuma kishi da haddasar ni na same ki ba shi ba ya saka shi aikata hakan....”
Amma ta share hawayenta tana taba Hamad dake zaune kusa da ita yan biyu suna zaune a cinyarsa.
“Na dauka da gaske Hamad ya mutu, na karbi wannan kaddarar amman Hurriya ta ki ta karbi wannan”
Hamad ya kalli Hurriya ta kalleshi. Captaim ya ce.
“Ya taba fada min cewar Yana fada yawan fada da yar'uwarsa yanzu kuma yana son neman lafiyarta kuma gashi bata nan...”
Suka yi Murmushi. Yasir ne mutum na farko da ya fara mikewa tsaye ya fice daga falon. Sai da ya dauki lokaci sannan Rukayya ta bayansa. Gingine ta same shi jikin motarsa ya rike kansa ya rasa me ke masa dadi a duniyar nan.
“Yasir...”
Ya dago ya kalleta sai ya kawar da idonsa.
“Minene Rukayya?”
“Ya kake?”
“Lafiya kalau”
“Dan Allah karka boye min ya kake?”
Da ya dube ta sai ya ga hawaye take zubarwa shi ma sai na shi hawayen dake makale suka zubo.
“Ban sani ba, ko za su zabi kai Hajiya gidan yare ko akasin haka, amman ba zan iya zama garin nan matukar mahaifiyata ta kasance a gidan yari, ba ni da sauran farinciki a yanzu. I respect your parents decision da suka hanani aurenki suna da gaskiya”
“Yasir shin har yanzu kana so na?”
Ya dubeta da kyau sai yayi murmushi ya dago wayarsa ya nuna mata hotonsa da yake a screen din wayar, sannan ya sauke ya tafi ya bar a gurin tsaye. Amma da yan'uwanta suka koma bangarensu suna tattauna abun da ya dace Appa ma yana tattauna da nasa yan'uwan. Captain kuma ya fito yana magana da Hurriya, so yake ya dauketa su je family house dinsu su ganta even though Magariba ta gabato, ita kuma tana son kasancewa da yan'uwanta a yanzu.
“Idan mun tafi can Nene zata iya cewa na kwana a can ai ko?”
“Ya za'ayi tace miki haka bayan kuma ta san kina da MiJinki?”
Ya duba yaga babu mai ganinsu sai ya kama fuskarta yana kallon kwayar idonta.
“Alhamdulillah you can see now my baby my heart my soul my duniyata”
Ta yunkura zata yi dariya sai amai ya cika mata baki, da sauri ta ja baya ta juya ta fara kwarara amai a gurin kamar zata amayar da yan hanjinsa. Captain ya shiga cikin ya dauko mata ruwa ya wanke mata bakinta sai da yayi da gaske sannan ya iya danne zuciyarsa domin shi ma aman ya ji yana taso masa. Ya taba jikinta.
“Sannu kina jin rashin lafiya ne?”
“Aa amman kai jikinka da zafi, ko zaka tafi asibiti ne?”
“Maybe gobe, amman ba yau ba dare yayi, ki shiga ciki ki huta gobe zan tafi na kai ki gurin su Nene”
“Toh.. Sai da safe..”
Har ta juya sai ta ji an riko hannunta an dawo da ita.
“Hurry na.. Me kika ci ya saka ki aman nan? Me yasa kika yi amai?”
“Ban sani ba”
Ta dan yamutsa fuska.
“Turarenka nan ne bana so yanzu”
Yayi murmushi ya rika hannunta ya nufi gurin motarsa.
Ya bude motar ya saka ya zagaya ta dayan bangaren ya shiga yayi ma motar key. Sannan ya kama hannunta daya ya rike yana tuka motar.
“Ban a kwashe aman ba, idan wani ya gani zai ji kazanta”
“Idan mun dawo sai ki fada a kwashe”
Be tsaya ko'ina ba sai asbitinsu na Barrack yana zuwa aka hau yi mata gwaje gwaje mamaki ya hana ta magana bayan kuma yace shi zata raka, ba ayi taru ba sai a gurin da za a debi jininta a auna, nan kam sai da ya zauna a kujera ya rumgume da karfe ya rike hannun sannan aka dibi jinin. A nan ya barta ya tafi yayi sallah ya dawo sannan ya karbi results. Be bude ba sai da suka isa gurin mota yana karantawa yana murmushi.
“Me suka ce? Ka shafa min rashin lafiya ko? Kai ne fa mai ciwo”
“Baby na kin dai shafa min laulayi”
Ya kashe
Showing 204001 words to 207000 words out of 215510 words

“Me ye ina zamu je?”
“Asibiti”
“Babu asibiti da yamma fa..”
“Ta barrack zamu tafi likotocinsu kullum available”
“To ai ni lafiyata kalau”
“Ni zaki raka”
Ya bude motar ya saka ya zagaya ta dayan bangaren ya shiga yayi ma motar key. Sannan ya kama hannunta daya ya rike yana tuka motar.
“Ban a kwashe aman ba, idan wani ya gani zai ji kazanta”
“Idan mun dawo sai ki fada a kwashe”
Be tsaya ko'ina ba sai asbitinsu na Barrack yana zuwa aka hau yi mata gwaje gwaje mamaki ya hana ta magana bayan kuma yace shi zata raka, ba ayi taru ba sai a gurin da za a debi jininta a auna, nan kam sai da ya zauna a kujera ya rumgume da karfe ya rike hannun sannan aka dibi jinin. A nan ya barta ya tafi yayi sallah ya dawo sannan ya karbi results. Be bude ba sai da suka isa gurin mota yana karantawa yana murmushi.
“Me suka ce? Ka shafa min rashin lafiya ko? Kai ne fa mai ciwo”
“Baby na kin dai shafa min laulayi”
Ya kashe
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69 Chapter 70Chapter 71Chapter 72