“Ina da aiki sosai ma Hajiya, gyaran gidan da Appa yace za'ayi ne mutanen nake jira su iso”
Wani kallo Hajiya Kaltume ta yi masa na rashin zato balle tsammani.
“Gyaran gida za'ayi? Ba mu da labari”
“Ni ma ban sani ba, kawai ya kira ni yace min na jira kar na fita da wuri so that idan sun zo na nuna musu lungu da sako na gidan”
“Ikon Allah to gyaran gida na minene? Na ga dai ko auren Hurriya ba'ayi gyaran gidan nan ba, baka fada min shi yasa aka gyara gidansu Iyami ba? Amman ba a gyara nan ba, to yanzu kuma gyara me za'ayi”
“Wallahi ban sani ba Hajiya, kin san ba komai ne Appa yake shawara da ni ko ya sanar min ba, amman dai ko minene ai zamu ji”
Hajiya Kaltume ta sauke wani dogon numfashi tana jin wani sabo na tukare mata a kahon zuciya.
“Ya kafar taki?”
“Da sauki”
Ta amsa irin amsawar dake nuna hankalinta baya gurinsa.
“Da dai kin daure kin fita a duba kafar nan kar abu ya zame miki babba fa, Appa ma na ji yana zancen yana son fita a duba lafiyarsa shi da yake lafiya ma kenan balle ke da ciwon kafa ya matsawa ya kamata a bincika ko minene”
“Zan yi Yasir akwai abun da yake gabana yanzu, ina son na gama da shi ne tukuna”
“Minene Hajiya?”
“Be shafe ka ba”
Ta mike tsaye cikin jan kafa da dingishi ta sake haurawa sama ta shiga dakinta zuciyarta har rawa take kamar zata fado. Ta zauna bakin gadonta ta rasa me zata yi kuka ba mafita ba ne, to miye mafita, yanzu tana ji tana gani Amma zata dawo gidan nan? Ko kuma dai sabon aure Appa zai daura.
“Na shiga uku na lalace..”
Ta fashe da kuka. Ta lalabo wayarta ta kira Number sabuwar kawarta Hajiya Larai dake ke karata gurin masu magani a yanzu.
“Subhanallahi Hajiya kamar fa kuka kike yi..”
“Ba dole na yi kuka ba, ciwo ya dame ni ga kuma auren nan Alhaji jin sa zai yi ko kuma ya maida iyami abun duniya ya isheni Hajiya Larai, kullum sai ramewa nake ga ciwo ga bakinciki”
“Komai zai warware Hajiya Kaltume karki damu kanki, kin ga duka malaman nan da na kaiki gurinsu sun iya aiki babu wasa babu kama hannun yaro kuma tun da aka yi musu biya mai kyau ki saka ido zaki ga yadda komai zai tafi daidai”
“To ai abun ne kullum shiru Hajiya Larai abu sai kara gaba yake, yanzu fa har Alhaji ya saka ayi masa gyaran gida, ni dai ina tunanin ko zan bo ta bangaren Hajiya Binta ne idan na je yi mata barka da dawo na bata hakuri ko abubuwa za su daidaita, wani abun fa dole sai ana saka baki”
“Karki kuskura zubar da kimarki Hajiya Kaltume da yardar Allah sai Alhaji ya zo yana kuka yana neman yafiyarki”
“Toh Allah yasa, da wacan Malamin ne da ya rasu da yanzu aiki ya fara amman su babu wani motsi har yanzu”
“Gaggawa aikin shaidan ne ki saka hakuri sa sannu zaki ga aiki yayi, kuma yanzu ma idan mun gama wayar nan zan sake shiryawa na tafi gurin Malam na gangare na sake masa bayani”
“To sai na ji ki Allah ya taimake mu”
“Amin”
Ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya.
*** **** *****
Ya shafa fuskarta sannan ya tsika ci abarba ya kai mata a baki, daker ta dago daga kirjinsa ta bude baki ya saka mata.
“Tauna mana haba Baby, an fada min gida ma fa haka kike yi ba ki wani cin abinci, shiyasa ko kibar amarci da kowa yake yi ke baki yi ba, sai dai ni na yi”
“Daman ni bana wani cin abinci”
“Ai mantawa na yi na ce Amma ta roka mana ki rika cin abinci tun da Hajiya ta dawo balle na ce da ita”
Hurriya ta yi dariyarta mai kayatarwa.
“Har da cin abinci sai an roka”
Ya sumbance ta.
“Eh mana, yanzu ma ba mu yi latti ba, cikin week din nan za su dawo kamin su dawo zan fada musu su roka miki cin abinci”
“Daman na sha addu'a a gurin Kakata Hajiya Binta tun tana Saudi gurin Ummara har ta dawo addu'a take min, su Amma ma da suke can addu'ar suke ta mana Allah ya tsaremu ya bani lafiyar ido ya sa a yi aikin cikin nasara da sa'a.”
“Amin ka ji yar gata, ta ko'ina roka miki ake”
Ta dago kamar tana ganinsa.
“Allah yasa kamin mu tafi aikin nan su dawo”
Ya kai mata kiss a goshi.
“Da wahala gaskiya, mu da zamu tafi jibi su kuma sao karshen satin nan za su dawo ai”
Ta bata fuska.
“Ko ka daga har wani satin please”
Ya kwaikwayeta yana jan hancinta har ta turo baki gaba yadda ta yi.
“Ko ka daga har wani satin please”
Ta daga hannu zata dokeshi sai ya rike hannu ya matse har sai da ta yi kara sannan ya sake ta yana dariya.
“Ke ba ganin kike ba sai fitina, ka ji min mata haka kika fitini zuciyata kina dukan kirjina har sai da kika shige ciki...”
“Ba wani nan kai ne daga ganin yar yarinya kyakkyawa ka cusa kai har da wani ba ni chocolate da gilashi kana saka ni cin abinci dole a office dinka”
Ya zaro ido yana dariya.
“Ta nan kika bullo kuma”
Ta nauyi cikinsa.
“Yanzu duk sai na rama abun da ka yi min har da marina da kai yi”
Ta lalaba fuskarsa ta kai ma kumatunsa cizo har sai da yayi ihu ya rumgumeta yana dariya yana mata chakulkuli.
“Na daina... Na daina...”
Ta yi dariya sosai har da su dari.
“Ki biyani chocolate din da kika ci nawa, daman na rubuta duk abun da kashe miki ai ba dan Allah na yi ba”
“Ka fadi ko nawa ne, idan Saurayi Captain ya zo zai biyaka, amman fa soja ne kana yin wasa zai harbeka yana da fushi sosai”
Yayi dariya ya cigaba da tsakalar cikinta tana ihu da dariya a lokaci daya.
Two days later... Jirginsu ya tashi daga Abuja tafiyar awa hudu da mintuna 40 suka yi sannan suka sauka Addis Ababa babban birnin Ethiopia. A Oasis hotel apartment /Haya Hulet suka sauka Hotel ce mai kyau da aka wadata a abubuwan more rayuwa. Mama Rukayya da ta kasance yar rakiya daga bangaren Hurriya sa kuma Momy Ikilima daga bangaren Captain suka sauka a daki daya, Captain da matarsa kuma suka sauka a daki daya, sai wanda suka zo da shi domin hidima shi ma aka ba shi nasa dakin dabam. Kwana biyu a hotel din Hurriya na tafiya kwararrin likitocin da suke Bethel Hospital, addis Ababa, Landmark General Hospital, Medical center hayat hospital MCM suna duba idon, daga karshe dai aka yanke shawara yi mata aiki a Medical Center Hayat Hospital MCM, saboda kwarewar aikinsu da kuma kyakkyawar alakar dake tsakaminsu da wani na kusa da Hurriya.
Ana gobe za ayi mata aikin ta tsora sosai duk kuwa da irin karfafa guiwa da tabbacin da likitocin suka bata cewar za'ayi nasara. Har yanzu zuciyarta bata yarsa 100% idonta zai bude ta samu lafiya kamar kowa ba, ganin tun haihuwa take da ciwo har zuwa yanzu d ta girma.
“Baki yarda da ni ba? Baki yarda za'ayi nasara ba? Baki yarda Allah zai iya warkar dake ba? Baki yarda Allah ya karbi addu'ar da ake ta yi miki ba?”
Ta kwantar da kanta a kirjinsa.
“Na yarda, kawai ina tunanin idan ba ba ayi nasara ba, zan tabbata a haka ne har abada”
“Za'ayi nasara da yardar Allah”
Ya kwantar da ita kan gadon ya fara kissing din wuyanta, tana ta kokarin hana shi amman be saurara mata ba sai da ya raya daren kamar darensu na farko har tana masa kuka a yanzu din ma. Da asuba shi ya taimaka mata ta yi wanka suka yi sallah, ta hau gado da niyar bachi kamin lokacin zuwa asibitinsu yayi, a nan ma be bar Hurriya ta huta ba, sai da ya sake gajiyar da ita har tana masa miya. Misalin karfe daya na rana suka isa asibitin aka wuce da ita dakin da aka ware mata na musamman sannan aka fara yi mata wasu treatment din. Ba a shiga aikin da ita ba sai karfe bakwai na yamma. And the most expensive news is anyi aikin cikin nasara sai dai babu tabbacin ko zata gani daidai ko kuma irin na da ne ko ma idon be bude gaba daya ba sai idan ta bude idon, hakan kuma ba zai samu ba sai nan da sati idan idonta ya warke. Daga ranar da aka yi aikin suka saka mata dokokin na abun da zata ci ko ta sha da irin motsi ko aikin da zata yi. Sun bada damar mayar da ita gida ayi jinyarta kamin ranar da za a bude idon, sai dai Captain ya zabi ta zauna asibitin saboda ta fi samun kula kuma ya san a gida ko a Hotel din da suka sauka zata iya karya dokarsu.
A asibitin Hurriya ta yi jinyar idonta for one week, ranar da za a bude idon ba ita kadai ba har Captain da Rukayya da Iyayensu dake gida da fargaba suka wuni na tsoron rashin nasarar aikin. A hankali aka fara warware daurin dake idonta har aka cire, ita kanta ta ji alamar nasara a tare da aikin domin tana iya jin haske a idonta dake rufe tun kamin ta bude.
“Hurriya can you open your eyes please....”
Ta fara motsa ido da take jin kamar ya like mata. Wani likitan an ganin haka ya dauko wani magani ya diga mata a idon dake rufe.
“Open it slowly...”
Ta bude idon a hankali, sai dai bata iya daga shi sosai yayi mata kamar na masu shan kwaya (Irin na Ummu Falsak) sai dai tana iya ganin abun da yake gabanta da dishe dishe hakan kuma ya faranta ranta.
“Don't let tears drop”
Ta yi kokarin hade kukanta bayan dayan likitan ya bukaci haka. Sai ta sake maida idon ta rufe sannan ta bude a hankali. Fuskar Captain ta fara cin karo da ita kamin ta bi sauran Likitocin hudu da suke dakin da kallo dukansu farar fata ne kamar kasa mijinta babu daya da ta sani.
“Alhamdulillah”
Captain ya fada yana durkusawa kasa yana kallonta tsabar farinciki.
“Congratulations”
Cewar Likitocin suna tabawa kansu kowa ne na gaisawa da dan'uwansa. Captain ya dago ya rumgume ta yana farinciki.
“Ina gani yanzu ina gani ina gani Alhamdulillah”
“Daman na fada miki za'ayi nasara gashi kuma anyi”
Hawaye ya sauko mata tason ta share tana tsoron saka hannu a gurin, blink din sa take da idonta ma ganin take kamar idan idon ya rufe ba zai bude ba. Captain ya sumbance ta a gaban Likitocin sannan ya sake ta ya juyo.
“Dukansu sun yi kokari gurin aikin nan Baby Aisha Alhamdulillah, wannan shi ne Dr Camil, sai a Dr Nille....”
Haka ya bi yana gabatar mata da Likitocin da suka yi nasarar yi mata aikin Maza uku mace daya tana musu godiya.
“Bayan su akwai wani matashin yaro mai karatun Optometrist.. Wato likitan ido who will perform medical and surgical treatment for eye condition, shi ma ya kamata a gode masa, domin tare da shi aka yi aikin a kokarinsa da yake na koyon aikin kuma duk saboda ke ne, ina da yakini Allah ba zai kunyata shi ba shiyasa na yarda 100% idonki zai bude Babyna kuma saboda shi Muka zabi yin aikin a wannan asibitin da yake karatu gashi kuma an yi nasara Alhamdulillah”
Hurriya ta kalli Captain tana murmushi kamin ta maida dubanta gurin kofar da Dr Nyala ta bude. Wani matashin yaro ne ya shigo sanye da lab coat fuskarsa da idonsa sun yi ja sosai kana ganinsa ka san ba karamin kuka ya sha ba, domin har a yanzu ma hawaye zuba suke a idonsa. A take murmushin dake fuskar Hurriya ya gushe ta kalli Captain da sauri ta sake duba yaron dake tsaye gabanta sai jikinta ya fara rawa kamar zata kamkame guri daya ta rufe ido da sauri tana shisshika da karfi....
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻[1/5, 9:04 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*
5️⃣6️⃣
Captain yayi saurin rike matarsa da sauri yana leka fuskarta.
“Hurriya...”
Ta kama rigarshi da karfi ta rike har lokacin idonta a rufe yake jikinta kuma rawa yake. Ta kasa yarda ba mafarki take ba, kamar yadda take jin kamar tsananin son rayuwa da ďan uwanta yana neman haukata a yanzu da yake mata gizo, to amman kuma kalaman da Captain ya furta fa? Wani hannun ta ji a jikinki wanda ya banbanta da na mijinta, dumin hannun ya fahimtarta da alakar jininta da jinin mai taba ta, shi ma dai sunanta yake kira kamar yadda Mijinta ma yake kiranta, wata kila ta yi dagon zango ne ko kuma kokarin farkawa take da daddadan mafarki. Hakan ya kara mata kuzarin bude idonsa sai ta sake arba da wani mai irin fuskar dan'uwanta mai irin hanci da idonta mai hasken fata kamar nata, sai dai ya girmi Hamad fuskarsa ya sauya sosai. Hannayenta sake rawa ta dago zata murza idonta Captain yayi karaf ya rike
“Karki murza ido”
“Gizo suke min”
Ta amsa a cikin wani sauti mai kokarin gauraya da kukanta.
“Ba gizo ba ne, da gaske ne wannan ma...”
Ta sake bude idon a karo na uku ta kalli matashin yaron dake a yanzu yake dukushe gaban gadon da take zaune yana kuka har lokacin hannunsa ya kan hannunta ya rike ta gam. Ta kalli Captain hawaye na sauko mata.
“To waye wannan?”
Captain be ce komai ba sai da yayi magana da Doctors din suka fada masa dokokin abubuwan da zata kiyaye da kuma abun da da zata ci sannan yayi musu godiya suka fita.
“Hurriya...”
“Na'am”
Ta amsa da sauri domin amsarsa kawai take jira.
“Ba kin ke kika fada mim dan'uwanki yana raye ba? Shim ba ke kika kasa yarda cewar Hamad ya tafi ya barku ba? Kowa ya karbi mutuwar Hamad amman ban da ke haka ne?”
Ta daga kai tana kuka ta kalli Hamad din da shi ma kuka yake sosai.
“Saboda jikinki yana baki dan'uwanki wadda ya fi kowa kusanci da ke yana raye, jikinki be fada miki karya ba tabbas Hamad yana raye, kuma shi ne a gabanki yanzu”
“Taya wannan karyar zata zama gaskiya? Ji yanayin yau nake kamar ba ni ba, tsoro nake kar na farka daga wannan bachi na ga komai ba gaske ba”
Hamad ya kalli Captain cikin wani yanayi marar misaltuwa da wata murya ta samari masu tashen balaga ya ce.
“Me yasa ka yi min karya? Why? Ka ce min kowa ya mutu bana da kowa a yanzu why? Ko kuma kowa ya mutu Hurriya ce kadai a raye?”
Cikin tashin hankali da ba a sakawa rana Hurriya ta dubi dan'uwanta muryarsa ta sauya kamar yadda siffarsa ma ta sauya, ko a can baya daman wasu shi suke dauka yayanta ita kanwa saboda girman jikinsa.
“Dan Allah ya zan yarda Hamad ne...? Ya zan yarda? Ki kira Amma.. Kira min Mama Rukayya... Dan Allah”
Ta rike Captain da karfi kamar zai tsere mata, taya idanuwanta za su bude a yau kuma ta yi arba da wani mai kama da Hamad yace mata Hamad din ne.
“Amma tana raye? Daman Amma tana raye?”
Hurriya ta kalleshi kamar yadda yake kallonta da tsananin mamaki da al'ajabi.
“Magana kake kamar ka san kowa...”
“Na san kowa mana Hurriya, Hamad ne Hamad dinki mai yawan dukanki mai yawam fada dake mai saka ki kuka, Hamad yaron Amma da Appa ni ne Hurriya”
Hurriya ta rike baki tana kallonsa hawaye na sauko mata sharrr. Captain ya zauna kusa da ita ya rumgumeta.
“Abu ne mai wahala dukanku ku yarda da wannan”
Ya dago hannun Hurriya ya nunawa Hamad.
“Awarwaron da ka taba bani as a gift ka ce na bawa budurwata, shi ne nan, Hurriya kin tuna lokacin da na baki kyautar wannan na ce miki wani ne wanda ya dauke ki d
Ƴar'uwanki ya baki?”
Ta daga kai fuskarta na kirjin Captain tana kuka kamar ba gobe.
“Shi ne ya ba ni”
“Me yasa ka bar ni na yi rayuwa a cikin duhu? Why? Me yasa ka ce min kowa ya mutu?”
Hamad ya tambaya da karfi yana wani nishi sai kallon Captain yake cike da bakinciki yana jin kamar ya shake shi.
“Na rayu da wasu mutanen da ba jinina ba, a kasar da ba tawa ba, na rayu akan cewar kowa nawa baya raye, recently nan Salim take yake fada min cewar akwai gaskiyar da kake boye min ashe da gaske kake”
“Shiyasa na saka aka canja maka gida ai, wata kila da ban maka wannan karyar ba da baka samu lafiya ba, da ban maka wannan karyar ba da baka rayu ka kawo yau ba, da ban maka wannan karyar ba da baka natsu ka
Showing 198001 words to 201000 words out of 215510 words
“Me kake ayi nan? Yau baka da aiki ne?”

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67 Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72