da zuwa Yallabai”

Ya amsa mata da kai.

“Momy fa?”

Ya tambaya yana cire talkaminsa

“Sun fita da yamman nan ita da Namra”

“Okay”

Ta mika hannu zata karbi kayan da suke hannunsa sai ya hanata.

“No bari na shiga dasu ciki”

Ya karasa shiga cikin falon sannan ya nufi stairs, dakin Miwan ya bude ya shiga, yadda dakin yake a gyare yana kamshi sa ka rantse da Allah ana zama a ciki ne ko'ina clean an gyara komai tsaba. Saman gado ya fara zuba kayan da ya shigo da su, sannan ta shiga bandaki ya kama ruwa ya fito ta nufi kusa da windows yana cire safarsa, sai da ya jefa safar a cikin kwandon dake gurin sannan daga curtains din Windows yana kallon yadda ruwa ke sauka a itacen gidan, ba ruwan ko itacen yake son gani ba dan haka yayi kasa da idonsa zuwa inda zuciyarsa take muradin gani.
Hurriya ce kwance daidai tsakiyar filin, ta ware hannayenta fuskarta da cikinta suna fuskantar sama ruwan yana sauka a kanta, be san dalilinta na yin haka ba amman sai iya fadar akwai natsuwa da nishadi a cikin wasa da ruwan sama a lokacin da suke yara, kamin girma yayi talking over. Tana ganin anyi walkiya ta tashi zaune da sauri ta rufe kunnenta, tsawa na biyo baya jikinta ya fara rawa sai ta tashi gaba da sauri ta koma gefe ta tsaya. Sai da aka gama ta sake dawowa cikin ruwa tana ganin wata walkiya ta sake komawa da gudu kamar wata yar yarinya, da ta ji ba ayi tsawa ba ta sake shiga cikin ruwa, this time around jumping take tana ajijiya cikin ruwa. Murmushi ya samu kansa da yi, he miss alot daga kurciyarsa zuwa yau, and wanka a ruwan sama are one of his childhood memories.

Fararen curtains din ya saki ya saka hannunsa aljihu ya pistol ya bude jakar dake ka yi gado ya sakata a ciki, sannan ya dauki jakar System din da takardun ya saka talkamin Musib da suke dakin ya nufi kofar fita ya bude ya fito yaja kofar a hankali. One after the other ya rika bin dakunan da suke gefen dakin da Namra take yana budewa har ya ci karo da wanda yake kyautata zaton an Hurriya ne, tsaye yayi yana kallon dakin kamar mai nadar bayanai sannan ya ja kofar ya rufe ba tare da bari ta yi kara ba. Downstairs ya sauko ya zauna a sofa ya ja wani karamin tebur gabansa ya bude system dinsa ya aje a kai, takardunsa da wayarsa kuma ya da wallet dinsa da pistol ya dora sama gefen kujerar da yake zaune.

“Ranka ya dade kana bukatar wani abu?”

Inna Shatu ta tambaya tana mikewa tsaye.

“Aa na gode”

Ya amsa ba tare da ya kalleta ba.

“Toh”

Ta nufi kitchen domin ba zata iya fita cikin ruwa ba balle ta tafi gurin da suke zama, kuma ta san Momy tana hana su zama a falonta idan tana ciki ko bakinta suna nan. System din ya bude ya fara tabawa, yana tsaka da typing kofar falon da yi kara alamar da mutum a waje. Inna Shatu ta fito daga kitchen da saurin da nufin zata tafi ta bude.

“Lemme Handel it bari na bude”

“Tou”

Ta juya ta koma. Dauke hannunsa yayi daga typing din ya mike tsaye ya nufi kofar ya bude. He thought Hurriya zai gani domin ita ya san da shigowarta gidan, sai kuma yayi arba da Momy da Namra rike da umbrella suna mamakin ganinsa.

“Captain kai ne kuma?”

“Eh na zo baku nan ai”

Ya matsa jikin kofar suka shigo.

“Ka dade a nan?”

“Aa ban jima ba, Momy sannu da zuwa”

“Yauwa, ya aikin?”

“Alhamdulillah shi na zo na yi a nan ai”

“Captain sannu”

“Sannu Namra”

“Bari naje na canja”

“Okay”

Ya amsa mata ta siga biyu amfani da kai, da kuma furtawa. Momy ma ta bi bayanta tana fadin.

“Ai da na san zaka zo ba zan fita ba ma, gashi nan ruwa duk ya jika mu”

“Be kamata ai ka ki fita saboda ni ba”

“Babu wani abun da ya fi uwa ta saka danta a gaban ta yi ta kallo, da ka san irin dadin da nake ji idan ka zo gidan nan wata kila da kullum sai ka zo”

Murmushi kawai yayi ya bi su da kallo har suka haye stairs din. A madadin ya rufe kofar falon ya samu kansa ta takawa ya fita tare da janyo kofar ya rufe daga waje, balcony ya tsaya yana kallon yadda ni'imar Allah ke sauka ko'ina a gidan tana jika gidan. Dan matsawa yayi kadan yana takawa a hankali har ya isa gurin da ruwan yake zuba ya tara jikinsa ya saka hannunsa aljihu ya lumshe ido yana maida numfashi a hankali, sanyin ruwan saman dake sauka a kansa suna ratsa zuciyarsa da ilahirin jikinsa, da abun ya masa dadi sai ya daga kansa sama daga tsayen da yake ruwan na sauka a fuskarsa and the thing is so funny kana jin ruwa na sauka a fuskarka kamar an watsa maka wani abu. Haka ya jike kansa shakaf da ruwan saman hannayensa biyu duka cikin zube cikin aljihu daga ipod din dake kunnesa da wristwatch da wallet dinsa babu abun da be jike ba, shi ma ba wai ya shirya hakan ba ne, zuciyarsa ce ta ingiza shi har ya samun kansa da bukatar aikata abun da ya ga wata ta yi. Is he a teenager like her ya tambayi kansa kamin ya juyo ya kalli Namra dake masa magana...




Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar  MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne  cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai  shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[11/28, 5:21 AM] AMINA KABIR CAPS: *KHADIJA CANDY*

*PAGE 2️⃣6️⃣*



HURRIYA POV.

“Assalamu Alaikum Warahamatullah
Assalamu Alaikum Warahamatullah”

Ta sallame sallah magariba ta karo da azkar din sallah, sannan ta daga hannunta ta yi addu'a kusan rabin kowace addu'arta Amma ce, burinta Allah ya bata lafiya ta tare kamar da, sauran addu'o'in bukatu na rayuwa suna biyo baya ne bayan ta yi ma mahaifinta. Daf da zata shafa addu'ar Namra ta shigo dakin, saman gadonta ta jefa mata ledar dake hannunta kana ganinta kasan Hurriya ta shigar mata hanci da yawa.

“Na gaji da ajiyar wayar nan, idan ma baki bukata ki jefar ko ki kyautar, bana bukatar wani abu naki ko na Salim”

Ta juya tana jan kofar dakin da karfe Kamar zata ballata. Hurriya ta juya ta kalli ledar sannan ta mike tsaye ta nade carpet din ta zauna a bakin gadonta ta dauki ledar tana dubawa. Babbar waya ce har da sabon line da chocolate sai turare mai kamshi. Komai sai da ta bude ta gani musamman ma wayar da take jin kamar ta yi amfani da ita, sai dai tana tsoron kar Yayanta yayi magana domin bata taba rike waya ba, kuma kowa zai tambaye ta ina ta samu, idan ta amsa da cewar Salim ya bata za a tambaye ta miye alakarta da shi, to me zata ce? Wannan tunanin ne ya saka ta maida wayar a ledar ta cire chocolate din da turare ta janyo kwalin da Adam ya bata ta saka wayar a ciki, turaren kuma ta dora a mirror tare da sauran turarukanta da suke gurin. Sannan ta hau gado ta dauki chocolate ta fasa ta fara ci tana lumshe ido, daman ta san dadinsa domin Appa na siya mata lokacin da Amma take gidan, Amma ma da kanta takan siya mata ko ta bata kudi ta siya wani lokacin amman ban da wannan lokacin da komai ya canja. Knocked din kofar dakin aka yi, ta tashi da sauri tana cin chocolate din, kamar zata tambaya ta ce waye sai kuma wata zuciyar tace tashi ki duba mana, ta sauka saman gadon ta nufi kofar ta bude, Khairy ce tsaye tana lasa wayarta suna hada ido ta sakar mata murmushi ta kunno kai cikin dakin.

“Hurriya ruwa be saka ki zazzabi ba?”

“Aa”

Ta juyo tana amsa mata. Khairy ta kalli bakinta da hannunta.

“Me kike ci?”

“Chocolate”

“Eyyyy yar gayu, wannan mutumen da na gani a falo ya kawo miki?”

Tambayarta take irin tambayar nan mai halshen damo, tana wani murmushi ta kalailaye ido ita ga mai wayo. Ita kam Hurriya sai ta ji cewar ta samu mafita ai daman bata san ya amsawa mata ga wanda ya bata ba dan haka ta amsa mata da.

“Eh shi ya ba ni”

Khairy ta kama hannunta suka zauna bakin gado.

“Ba ni labari shi ma sonki yake?”

“Aa ni aa”

“To ai kin san ke din mai kyau ce ga farinjini, tsaraba ce?”

“Haka nan dai ya ba mu”

Hurriya ta amsa tana jin kanta guilty saboda ta yi karya, abun da ba halinta ba.

“Dan'uwan Momy ne ko, ina yawan ganinshi ai ance dan yayanta ne”

“Eh”

Ta amsa tana daukar dayan chocolate din ta mika mata, a nan Khairy ta juya ta kalli bayanta, Chocolate ta gani ba daya ba ba biyu ba uku ba zai kai 12 kala dabam dabam kuma duk masu tsada.

“Kin ce ba sonki yake ba, amman ya kawo miki chocolate haka, maybe dai baki son na sani ne ko? Haba Hurriya ki dauke ni kamar kawarki mana, ko da yake dai be kamata na takuraki ba”

Ta mike tsaye.

“Daman Hajiya ce ta ce na kiraki”

“Ni kuma? Me na yi to?”

“Sai kin yi laifi za a kiraki? Haba Hurriya karki ma Hajiya wannan kallon mana”

Hurriya ta hade yawu tare da sauran chocolate din dake makoshinta, gabanta ya shiga faduwa ita dai ta san alheri baya sakawa Hajiya Kaltume ta kirata, sai da ta wuce gaba sannan Hurriya ta bi bayanta gaba daya ta saka mata tunani cewar Hajiya Kaltume tana nemanta sai ta fara tunanin ko fitar da suka yi ne a dazun, ko dai wani abun aka shirya mata? Ko Hajiya Binta ta sake yi ma Hajiya Kaltume wata maganar ne? Da tambayoyi kala kala ta sauko stairs din, a daidai lokacin da Captain yake hada takardunsa Namra na saka masa laptop din a jakarta. Sai da ta fara kallon Khairy kamin ya kalli Hurriya dake biye da ita a baya, a shi da alaka ta Hurriya dan haka ba shi da hurumin tambayar ta ina zata je ko kuma da waye take tare. Sai da suka fice sannan ya kalli Namra ya ce.

“Amman wannan yarinyar tana shaye shaye ko?”

“Me ka gani?”

“Fada min kika yi?”

Ya jefa mata bakar magana kamar yadda ya saba.

“Allah ya baka hakuri, tambaya ce kawai”

“Ni m amsa na bayar, ke ma idan kika fara yi zan gane”

Namra ta yi murmushi tana mamakin yadda yayi saurin ganewa bayan kuma bata fada masa ba.

“Amman ba a tabbatar ba, haka dai ake zargi saboda friends dinta wasu daga ciki suna yi”

Be ce mata komai ba ya daga kansa ya kalli Momy ya kalli agogonta.

“Tun dazun ake ta kirana Momy sai gobe idan na dawo”

“Zaka dawo”

Ta tambaya daga inda ta tsaya ganin kamar yana sauri, ya daga mata kai.

“Kullum zaku rika ganina har na gama watannin da zan yi In Shaa Allah”

“Haka nake so, Allah ya taimaka ya maka albarka Jameel”

“Ameen”

Ya amsa suna hada baki da Namra, sannan ya karbi Laptop dinsa.

“Dauko min wasu kayan da suke dakin Musib”

“Okay”

Ya fita Momy na binsa da kallo, Namra kuma ta nufi stairs domin dauko masa sauran kayansa. Dan lokaci da ta bata kamin ta kawo masa jakarsa da ipod da agogon daya cire a dazun, har ya fusace ransa gaba daya bace, tana bude kofar falon ya ja motarsa ya barta nan tsaye rike da kayan tana kallonsa.

“Kuma har ka yi fushi?”

Ta juya ta koma cikin falon.

“Be karba ba?”

Momy ta tambaya tana operating remote ganinta da rike da jakar ga kuma fuska na bayyana labarin zuciya.

“Wata kila cewa zai yi na bata lokaci, wai har yayi fushi”

“Ya kamata ki saba, ki lura da duk wasu abubuwan da baya so ki rika kiyayewa, kin ga yanzu hankalinsa ya dawo gidan nan wata kila ma saboda ke ne, kuma kin san halin Captain ba sai an fada miki ba shi da fushi da zuciya da saurin kai hannu ba su da maraba”

“Amman Momy wani lokacin abun sa ya kan yi yawa, dauko kaya kawai sai ya zama laifi?”

“Toh haka Allah yayi dan'uwanki ya zaki yi? Je ki aje kayan amman make sure kin kira shi a waya kin bashi hakuri”

Ta lumshe ido ta bude alamar damuwa.

“Shiyasa ya kasa zama da budurwa, komai aka yi masa bacin rai ne”

Momy bata bi ta kanta ba ta cigaba da kallon tv ba. Namra ta yi wuce da kayan ta fara taka stairs.




HURRIYA POV.

Da tsoro ta shiga bangaren na Hajiya Kaltume, da farko ta ji tsoro ganin Yayanta da Salma a falon sai ta yi zaton za ace ta yi wani abun ne, cikin karfin hali ta gaishe shi ta gaishe da Salma, yanayin yadda ya amsa mata ya fahimtar da ita bata da laifi a gurinsa. Khairy ta zauna kusa da shi.

“Wai yau na gaji da yawa, ina yin Sallah Ishan'i zan sha magani na kwanata”

Yasir ya dubeta

“Maganin me? Aikin me kika yi kika gaji?”

“Pain killer nake son cewa, zan shafa a kafa driving na yi yau mun yi yawa sosai”

“Good shiyasa na yi ta shigowa ina ganin kowa ban da ke, ke kawai kin fi son rayuwar waje, ki je yi ta abubuwan da kike so babu mai ce miki uffan, kawaye ma idan an rabaki da wannan gobe da wata za'a ganki? Khairy abun da kike yi fa ba shi da kyau, kuma ina miki fada ne ki gyara ba dan ni kadai ba sai dan ke kanki da future dinki, idan kika dauko wani abun magana ko, mutane za su zageki kuma kimar gidan nan zata zube, amman ke da Hajiya kun kasa gane haka”

Salma ta ce.

“An kusa aurar da ita Yaya ka kusa hutawa”

“Mtscheeeeee”

Tsaki Khairy ta yi ta mike tsaye, ita dai har yanzu ba wani son auren take ba, ganin take gana cikin cin lokacin ta ne za a yanke mata, ko da wani ne balle Fadeel da ke da mata kuma da dukan alamu ba zai dauki irin rayuwar nan ta barin mace ta yi wasu abubuwan da suka tsabawa dokar Musulimci da al'adar Malam Bahaushe ba.

“Hurriya shiga ciki Hajiya na kiranki”

“Toh”

Hurriya ta nufi stairs din tana jin cewar idan dai ba mahaifinta zata tarar a dakin ba irin wacan karon da aka koreta, to komai mai sauki ne domin zagi da wulakanci na Hajiya Kaltume ta saba da shi dan haka be daga mata hankali. Sai da Hurriya ta haye sama sannan Khairy ta kalli Yayanta cikin sifar magiya da lalama ta ce.

“Yaya dan Allah ka daina irin fadan nan a gaban Hurriya”

“Hurriyar bakuwarki ce? Ko kuma ita wata bare ce da ba zan miki fada a gabanta ba? Kuma da kin zama yadda nake so zan miki magana ne? And Salma was right idan an miki aure dole ai ki tsanu, and wannan ya zama na karshe da zaki fita ba tare da kowa ya san gun da zaki tafi ba! Dazun na tambayi Hajiya tace min baki fada mata gurin waye zaki je ba, ki daina wannan dabi'ar tun a yanzu”

“Zan daina Yaya ba zan sake fita ba tare da na fada”

“Ya fi miki, ai saboda kun samu Appa yana musu sauki ne yanzu, ace kamar baya ne da yake daukar zafi baku isa duk ku yi wannan ba, kuma ko. Yanzu idan kika sake irin haka sai na fasa miki jiki”

Ya mike tsaye.

“Yaya, ka yi hakuri dan Allah ba zan sake ba, ko dazun ma fa ba ni kadai na fita ba, tare muka fita da Hurriya ita tace gidan so boring shiyasa muka dan fita ta samu ta sake ita ma”

“Ki dai koya mata fitar kike so, shekara nawa tana zaune a gida bata gidan so boring sai a yanzu, ita ma ta fara raina wayon mutane, wata fadawa da zata fita?”

“Ita ai bangaren Momy take laifin ba na Hajiya ba ne”

“Shiyasa kullum Rukayya ke fadar na kula mata da Hurriya, wani lokacin sai a rasa ta ina ma za'a fara controlling dinku Mtscheeeeee”

Ya karasa yana jan saki, Khairy da Salma suka kalli juna a gurin da Yasir yake ambatar sunan Rukayya. Sai dai babu wanda ta isa tace wani abu domin sun san halin yayan na su. Sai da ya fice sannan ya Khairy ta koma kusa da yar'uwarta suka tasa gulmarsa da na Rukkayya.


HURRIYA POV.

Ta shiga dakin na Hajiya da Sallama ta zauna a kasa tana gaisheta, Hajiya Kaltume ta amsa irin amsawar nan kamar ta dole fuska babu yabo ba fallasa, idan ta kalli Hurriya wani kololin bakinciki ke taso mata saboda tuna Iyami da take yi.

“Lafiya Kalau, ya jikin Iyami? ”

“Ta ji sauki”

“Eh”

Ta daure ta kirkiro murmushin yaƙe.

“Maa Shaa Allah, haka ake so ai, Allah ya kara rikawa yanzu tana tafiya ko?”

“Aa bata tafiya”

“Ah ah kuma kika ce
Showing 84001 words to 87000 words out of 215510 words