ganinsu ka san ba kananan mutane ba ne. A lokacin da suka isa dakin da Hurriya take sai Captain ya kalli iyayensa ya ce.

“Wata kila ba zata so ta gan mu tare da ku ba, zan fi jindadi idan na shiga ni kadai, na san idan na ce ku zauna a mota na shigo ni kadai ba za su yarda ba shiyasa ban yi magana ba”

A nan kam Momy kasa hadeye maganar ta yi cikin bacin rai ta ce.

“Mu iyayenka mu zamu jiraka har sai ka shiga duba wata banzar yarinya tukuna mu tafi? Sai kace kai ka haife mu?”

“Idan hakan zai faranta ransa me ye a ciki? Shiga ka yi abun da zaka yi son zamu jiraka a mota”

Daddy ya fada sannan ya kalli bodyguard dinsa daya.

“Ka tsaya a nan idan ya fito ku same mu a mota”

“Okay Sir”

Daddy ya juya tare da Ammy domin komawa gurin motarsu, Momy ma dole ta bi bayansu iyayen yaro sun goyi bayansa ita a su ta ki bi, a nan ta samu damar karanta musu kabli da ba'adi na Hurriya, tana ta kusheta. Sai da suka wuce sannan Captain ya murda kofar dakin ya tura ya shiga, tana zaune saman gadon ta lankwashe kafafuwanta tana fuskarta hadu da kofar dakin.

“Kai kuma kai ne wa?”

Gwaggo ta tambaya tana kallonsa. Sai a lokacin ya tuna be yi sallama ba. Dan haka ya jadada sallamarsa sannan ya karasa cikin dakin yana gabatar da kansa.

“Sunana Jamal amman an fi sanina da Captain ni dan Momy dan yayanta...”

“Toh ko me ya sa ka zo?”

Ya kalli Hurriya da babu gilashi a idonta hawaye na zubo mata ya ce.

“Na zo na duba Hurriya ne? Namra ta fada mana tana nan”

“Namra ta tafi gida tun dazu, kuma dan Allah ba ma bukatar kowa, daga dangin Nafisa har na Kaltume, wannan kiyayyar ta yi yawa, ba bar uwa ba a bar ya ba, babu kalar azabar da ba a nunawa yarinyar nan ba yanzu abun ya wuce nan har sai a hada da kazafi? Kazafin ma na zina? Ita da gidan ubanta amman bata da walwala? Bata da jindadi? Akan me? Yanzu gashi nan kun yi sanadi idanuwan nata sun rufe gaba daya, bata iya gani ko da gilashin, buri ya cika tun safe da ta farka bata cewa komai ba, an kashe yarinya tana ji tana gani”

Gwaggo ta karashe fadan da kuka, Captain ya sauke idonsa kasa hawaye suka zubo masa.

“Ina kyautata zaton ni ne mutum na farko da ban yarda Hurriya ta aikata wannan abun ba, ban zo nan domin cin mutumcinta ba, ita ma ta sani kawai dai na kasa natsuwa ne har sai na zo na dubata, ban san matsayinki a gurinta ba, amman dan Allah ina rokon Alfarmar ki bar ni na ga Hurriya”

“Gata nan ka ganta, amman ba zan je ko'ina ba, kai ma ba zaka dauki hotonta ka yadawa duniya ka bata mata suna ba, kuma ko waye da hannu a lamarin kada Allah ya bar shi da salama, daga yaron har kowa”

“Ameen”

Ta saka yatsansa ya cire hawayen sannan ya karasa gaban gadon Hurriya saitin inda take zaune ya tsaya yana kallon fuskarta. Hawaye take malalarwar irin malalar da gulbi yake idan ya kawo, babu yankewa kuma babu fasa zuba, yanayin yadda take kallon saitin da yake tsaye ya isa ya kara tabbatar masa da bata iya tantance fari da ja a yanzu, sai bakin da ya rufe ganin idanuwanta.

“Hurriya...”

Bata amsa ba, motsa ba bata bar masa wata alama da zai gane tana jin muryarsa, ibadarta kawai take ta kuka. Cikin kuka Gwaggo ta ce

“Bata cewa komai, kuma bata gani”

Captain ya hadeye yawu mai matukar ďaci fa maƙaƙi a maƙoshi.

“Likita ne ya ce bata gani ko kuma ke kika ga alamar bata ganin?”

“Na ga alama, sa safe da ta tashi zata shiga bandaki ga gilashi a idonta amman lalabe take, na fada Likitan da ya shigo suka duba idon suka ce ua samu matsala, shiyasa suka canja mana daki ai, yanzu ba maganar sumanta ake ba, maganar idonta ake Likita biyu ya duba idon zamanmu a nan sun ce sai an yi aiki wai jijiyar dake hada idonta da kwakwalwarta ta samu matsala”

Captain ya daga kansa sama kamar zai fashe da kuka.

“Ya Rahma....”

Ya ambacin mafi rahamar masu tausayi, sannan ya sauke kai ya kalleta pointing finger dinsa ya kai saitin idonta kamar zai tsokale ido amman bata matsa ba, a nan ya tabbatar da bata gani da gaske.

“Jiya kin zo min a suma, kin fada min baki aikata ba, kuma na yarda da ke. Yau kuma ina tsaye a gabanki ne domin na fada miki wani abu, kowaye ya aikata miki wannan abun Hurriya, ba zai sake samun farinciki ba a rayuwarsa, sai ya kunyata fiye da yadda ya so ya kunyata ki, sai na sa duniya ta tsine masa irin tsinuwar da zai ce ina ma be aikata ba”

Ya kama hannunta ya rike a gaban Gwaggo.

“Na miki wannan alkawarin Hurriya, kamar yadda na yi miki alkawarin dawo miki da dan'uwanki, shi ma wannan ki rubuta ki aje nauyin yana kai na....”

Gwaggo ta share hawayenta ta taso daga inda take zaune da sauri tana fadin.

“Kai kai kai sake mata hannu, ban san sharin da ka zo da shi ba kai ma”

Captain ya sake mata hannun ya nufi kofa yana share hawaye, be ma kula maganar Gwaggo ta halin da ya ga Hurriya da damuwar da yayi arba da ita a fuskarta ta tafi da tunaninsa. Gwaggo ta kama hannun Hurriya ta shafe mata da hijabinta.

“Babu abokin yarda a cikinsu, ni da na san haka rayuwa zata miki Hurriya da ban bari kin zauna a gurin Ubanki ba, ko da kuwa shari'a ce zan yi da shi...”

Wani irin numfashi Hurriya ta fara fitarwa da karfi, kamin ta daga kanta sama ta kwala wani uban ihu....

“Gwaggo ban aikata ba....!”

Gwaggo ta rumgume ta da sauri tana kuka.

“Wallahi ban aikata ba....!”

“Na sani, babu wanda ya yarda kin aikata daga ni har Rukayya”

“Allah ka hana, wanda ya aikata min wannan abun farinciki, Allah ka hana shi jindadi da kwanciyar hankali, Allah ka nisanta shi da natsuwa ka kusantar da shi ga kunya da damuwa, fiye da yadda yayi min”

Cikin tsananin kuka Hurriya ta yi ma kanta addu'a tana fatar mahallincinta ya amsa mata.

“Ameen Hurriya Ameen”

Gwaggo na amsawa Hajiya Binta ta turo kofar dakinta ta shigo da sallama. Hurriya na jin muryarta ta juyo ta kai hannu tana lalaben inda take.

“Hajiya komai ya kare min, idanuwa sun tafi, mutuncina ya zube... Na barar da kimar Appa da Ammana a idon duniya, komai ya kare yanzu babu abun da ya rage min, kullum bakinciki ne yake kusanto ni yana nisanta ni da farinciki....”

“Share hawayenki yarinyar, farincikinki mai kyau shiyasa yake da tsada, duk mai hassadarki yana son ganin bayanki sai ya dawo karkashinki, wannan alkawalin Allah ne mai hakuri yana tare da riba Allah da kansa ya ce dukannin tsananin sauki yana nan damansa, idanuwanki za su bude Hurriya, damuwa zata yaye farinciki sai ki samma wani, karki damu da hotunanki sun shiga duniya, ko karuwanci zaki yi, ki je ki yi ki dawo Hurriya ni FATIMA BINTA zan karbe ki... ”

Hajiya Binta ta fada tana dukan kirjinta da karfi, kana ganinta kasan tana cikin bacin rai...
If you read my book ba tare da kin biya ba, indai hakkina ne Wallahi ban yafe ba, ku kuma masu sharing Allah ya muku yadda kuke min. I rest my case 🙌


CAPTAIN POV.

Ko da suka isa Family House dinsu, gidan yana cike da mutane, abun ka dake mai jama'a, daman sun tun a lokacin da yake asibitin suka tafi ganinsa aka hana su shiga. Kowa sai murna ganin Captain yake kamar wani Sarki, domin kowa a familynsu yana son Captain ko dan duniyar Ubansa da Hajiya Turai. Duba daya zaka yi ma Captain ka fahimci baya cikin farinciki ko kadan, ya zama so silent daga lokacin da ya baro asibitin da Hurriya take zuwa motar har kawowa gidansu. Wani abun da ya bawa Ammy da Engr AA Turaki mamaki shi ne takardar sammacin kotu da suka tarar an kawo a gidan. Engr ya karanta takardar ya sake karantawa ya dago ya kalli yan'uwansa dake cike da katon falo na Mahaifinsa.

“Waya kawo takardar?”

“Ma'aikacin kotu?”

Wata kanwarsu dake zawarci a gidan ta amsa masa. Momy ta tabe baki.

“Daman na raya a raina na ce sai abun nan yayi tsananina, karya yaron mutane fa Captain yayi kuma ya fasa masa hakora!”

Ammy ya kashe ido.

“Ashe kariya ce ma kawai shi nw za a kai ďana asibiti? Ko kashe shi Captain yayi ba zan bari ya tafi kotu ba balle kuma karaya kawai da zubar da hakora”

Engr ya sauke ajiyar zuciya cikin takaici ya ce

“Anya Bashir Sarauta ya san Jamal ďana ne kuwa? Har zai yanko sammacin kotu ya aiko a gidan nan? Kuma ďana yake kara? Ni Bashir Sarauta zai saka ďana kotu? Bashir Sarauta talaka a cikin masu kudi? Bashir Sarauta da yake karkashin inuwar dukiyata...! Ai wani sarkin kakan wani sarkin ne... Amman ya ba ni mamaki, ni ma kuma zan ba shi mamaki”

Momy ta ce.

“Ai duk Hurriya ce sanadi, gashi masu arziki za su yi fada akanta, yarinyar da bata kai ba”

Captain ya kalleta kamar daman jiran yake tace wani abu a kan Hurriya.

“That's it, Hurriya this Hurriya that... Komai Hurriya kike blaming, yarinyar da bata isa ta daga idonki ta kalleki a matsayin uwa ba, yarinyar da bata isa ta shiga dakinki ta rokeki wani gata ba, yarinyar da bata isa ta shiga Kitchen dinki ta zuba abinci ta ci ba, yarinya kamara kun matsa mata kun firgita mata kwakwalwa, yanzu ga wata bakin hayakin ya rufe ta amman still baki ji tausayinta ba?”

Ammy ta kalleshi tana kai hannu ta taba shi kuma ta kwantar masa da zuciyar dake fisgar ďanta.

“Captain you can't talk to Momy this way... Haba.. ”

Cikin lalama take fada tana dan kallo Momy. Captain ya kalli Ammy.

“Kiyayyarta da yarinyar nan wani abun ne da ya shafe ta na dabam, babu ruwana a ciki ni dai abun da na sani babu abin da zai hana ni auren Hurriya...”

“God forbid...”

Ammy ta dauke hannunta daga jikinsa da sauri kamar ta taba mugun abu.

“Yarinyar da duniya ta gama ganin tairaicinta? Yarinyar da bata da kamun kai? Karuwa? Kuma makauniya? Ba zan karbe ta a matsayin suruka ba har abada”

“Enough....!”

Daddy ya daka mata tsawa, sannan ya kalli Captain ya ce.

“Tashi ka shiga ciki ka huta”

Captain ya mike tsaye ya kalli mahaifiyarsa hawaye na zubo masa.

“A halin yanzu, Wallahi duk duniya Ammy ke kadai kika kai ki kira Hurriya da karuwa, na hade ban ce komai ba, kuma ban dauki mataki ba... Ki gafarce ni Ammy ni dai kam ban taba jin tsananin son wata mace a zuciyata ba kamar yadda nake jin Hurriya a yau, i love her more than life....”

Kowa kallon Captain yake domin yau yayi abun da be taba ba, fadar yana son wata a gaban kowa, kuma har ya zubar da hawaye.

“Ko Aljana ka ce zaka aura Jamal zan aura maka ita matukar hakan ne farincikinka, kuma zan raba ka da wanda baka so matukar hakan zai dada ranka... Ka bar wannan maganar a hannuna tafi ka huta....”

Cewar Daddy yana nuna masa hanyar bedrooms din dake stairs... Captain ya nufi bedrooms din yana jin kamar za'a raba kirjinsa gida biyu, Hurriya ce aka watsa hotunanta amman shi da ita ne suke raba nauyin bakincikin.




Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[12/13/2023, 6:18 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*

3️⃣9️⃣





Yana shiga dakin ya nufi wata kujera ya dafa kanta ya sauke kansa kasa ya rufe ido. Kamar an tsikare shi ya bude idonsa ya juyo da sauri ya fito daga dakin, tafiya yake mai kama da gudu ya sauko stairs din.

“Ina wayata?”

Ya tambayi Ammynsa sai Momy ta bude jakarta ta dauko ta mika masa tana hawaye. Ya saka hannu biyu ya karba ya juya ya koma ciki.

“Yaya da gaske barinsa zaka yi ya auri yarinyar nan? Wallahi bata kai ba Yaya bata yi matsayin da zata zama surukar mu ba”

“Idan aurenta ne abun da Captain yake so, zamu nemi aurenta kuma iyayenta za su ba mu ita dan dole ko da bata so, Allah ba hallatawa iyayen autawa Yayansu wanda basa so ba, ya dai mata ikon zaba musu na gari, kamar yadda ya hallata auren mazina idan sun tuba”

Ammy ta dubi Engr

“Ni fa ban gane ba, da gaske zaka aura masa yarinyar nan kenan? Ni ba da yawun bakina ba ba zan yarda Captain ya zauna da wannan yarinyar ba, ai abun kunya ne ace wannan yarinyar ta zama surukar mu duk matan duniya a rasa wanda zai aura sai karuwa?”

“Ina tunanin kin fi ni son farinciki Captain...”

Ta kawar da fuskarta ta fashe da kuka.

“Wannan goyon bayan da zaka ba shi be yi ba Yaya, be kamata ka biye masa ba shi fa soyayya ce take dibansa lokacin da zata zubar da shi zai fada a mugun guri ne”

Wata kanwarsa ta fada. Engr ya mike tsaye rike da takardar sammacin ya ce.

“Idan har kuna ganin akwai rashin dacewa a auren yarinya to ku roki Allah ya sauya masa da wanda ta dace, kuma ki kwantar masa da hankali ku nuna masa illar hakan, idan ya sauya ra'ayinsa Falillahil-hamdu ”

Ya nufi kofar fita ya fice daga falon yana kiran wani Assistant manager. Sai da ya fita sannan Momy ta dubi Hajiya Turai ta ce.

“Karki yarda Wallahi ta ya za'a kawo miki wannan yarinyar a matsayin suruka? Taya? Ai da kunya ma”

“Wani gine ne Captain yake son na dora wanda ba zai iya karasa ba, ni dai kam ba zan taba karbar yarinyar nan a matsayin suruka ba”

Ammy ta fada tana share hawayenta. Wata step Mother din Engr ta dubi Momy ta ce.

“Kuma da gaske yarinyar nan ta aikata abun nan?”

“Ba mu da tabbaci, ko da ace ba da gaske ba ne, ai be kamata ya aureta ba Hajiya, saboda duniya ta gama ganinta”

“Idan shari aka yi mata bana ganin illar aurenta a gurin Jamal, illar kawai ace ta aikata ne, shi ma kuma idan ta tuba Allah zai karbi tubanta kuma yayi mata sakamako mai kyau, domin Allah yana son bayinsa masu komawa a gurinsa suna kuka suna rokon ya yafe musu, shin idan hakan ya faru da yarki zaki so wani ya juya mata baya? Ku yi tunani mana”

“Ko ma dai minene Hajiya ba zamu yarda Captain ya auri yarinyar nan ba”

Momy ta amsa mata kai a ranta tana cewa saboda ba jikanta ba ne take fadar haka. Safa da marwa yake waya a kunnesa yana jiran wanda ya aikawa kiran ya amsa.

“Nafi'u ka duba hotunan kuwa?”

Ya gabatar masa da abun da yafi daukin ji fiye da gaisuwarsa da sallama.

“Sir barka da yamma, eh na duba”

“Ya ake ciki? Editing ne i know”

“I'm sorry Sir gaskiya ba editing ba ne, na duba na yi bincike ni da entire team dina ba mu ga wata alama dake muna editing ba ne”

Captain ya kai hannu ya shafa kansa ya runtse ido sosai.

“Maybe baka iya aikinka ba, maybe baka duba inda ya kamata ka duba ba”

“Na iya aikina ranka ya dade kai ma ka sani, wata kila da wannan gaskiyar mai nauyi ce shiyasa ka kasa karbarta, amman na gano wani abu”

Ya bude idon da sauri ya nufi bathroom ya bude ya shiga ba dan ya boyewa wani ba sai dan rudewa da yayi jin abun da yake nema zai samu.

“Alamu ya nuna yarinyar nan bata cikin hayyacinta aka yi hotunan, ko kuma tana cikin bachi mai nauyi domin jikinta ya saki sosai, yadda yake rikota da ace a hayyacinta take ba ta yi yaukin jiki haka ba, kuma babu inda take shauki ko murmushi shi ne kawai yake yi, shi ma kuma akwai alamar tsoro a tare da shi ko kuma rashin kwanciyar hankali, yadda hannayensa ma suke a jikinta ya nuna shi yake rike da ita”

Captain ya zauna a jikin bathtub yana murmushi.

“Thank You, Thank You...  Ka gano wanda ya dora hotunan?”

“Shi ne ban gano ba, na yi bincike na biyeye abubuwan da suka kamata ban gane komai ba, amman na bibiye wandanda na ga hotunan a account dinsu na Facebook wasu unverified pages ne masu neman labari wasu kuma daidaikun mutane ne, sai da na bibiye wanda aka fi sharing hotunan da ya rufe wasu bangarora na jikinta sai na samu wani dan jarida ne a Kano, and na dauki wayarsa na fada masa daga ina nake kiransa kuma na tambaye shi a ina ya samu hotunan sai ya ce min a wani
Showing 135001 words to 138000 words out of 215510 words