hannunta ce ta fara faduwa kasa sannan jikinta ya bi baya, daga Momy har Namra da Captain suna kallonta har ta jikinta ya kai kasa kanta ya bugu numfashi yayo halinsa, aka rasa mai riketa. Momy ta karasa ta dauki wayar ta duba

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”

Shi ne abun da ya fito daga bakinta tana rufe ido, Namra ta karaso gurin da sauri ta karbi wayar ta duba, bata gama ta tantancewa ba Captain ya karbe wayar a hannun Namra, ya duka ya kai yatsansa biyu ya taba wuyan Huriyy, sannan ya dago

“I will be very happy idan na samu babu hannun kowa a cikin nan”

Momy ta dauke shi da wani kallo.

“Baka ma yarda ta aikata ba kenan? Kuma idan sheri aka yi mata mu kake zargin mun aikata mata right?”

“Wutar data halba a zuciyata ba zata bar ni na yarda ta aikata hakan ba, kuma kowa abun zargi ne a gurina because kowa yana da target dinsa akan Hurriya, and the innocent soul a saw in her ba zata aikata ba, akwai wanda ya shirya wannan abun..”

“Kuma wani nan kanwar ubanka ce uwa daya uba daya ko?”

Ya dafe kansa.

“Momy please...”

Kamar wanda magana ta karewa a baki haka ya yanke kalamansa ya kasa kara wani furucin ya fice daga falon.

Momy ta juyo ta kalli Namra cikin tsananin takaici da bacin.

“Wai ni Captain zai zarga?”

Namra ta duka ta taba Hurriya dake kwance a suma kamar gawa tana fadin.

“Kamin mu yi tunanin abun da Captain yayi mu kai yarinyar nan asibiti bata motsi fa”

“Ke da kika ji zaki iya sai ki yi, ni ko mutuwa ta yi a yanzu Alhamdulillah, zamanta a nan be kara mjn komai ba sai bakinciki da damuwa, dramer queen”

Momy ta saka kafa ta take ta wuce Hurriya ta haye sama, Namra ta bita da kallo kamin ta kalli Hurriya hankalinta a tashe. Da gudu ta nufi kitchen ta kunna tap ta dauki roba ta zubo ruwa ta zo ta zubawa Hurriya ta girgiza ta amman shiru.

“Hurriya Hurriya...”

Ta kara mata ruwan ta sake girgiza ta nan ma shiru, tsoron kar ta mutu a gurin ya saka ta tashi da gudu ta fice daga bangaren Momy zuwa bangaren Hajiya Kaltume, and abun mamaki ta isa gurin a daidai lokacin da Khairy take nunawa Ruma hoton Hurriya.

“Ba sai kin fada mana ba, mu ma mun gani video ta is all over the internet...”

“Ba wannan ya kawo ni ba”

Namra ta kawar ma Khairy kai ta nufi stairs tana kiran sunan Yasir domin ta san shi kadai zai iya taimaka mata a yanzu.

“Ya Yasir ya fita Yaya Namra”

Ta juyo ta sauko da sauri.

“Dan Allah zo ki kama min Hurriya mu kaita asibiti kar ta mutu, faduwa ta yi kuma bata motsi”

Ruma ta mikawa Khairy wayar da sauri ta bi bayan Namra suka fice a falon cikin tsananin tashin hankali. Khairy ta bi su da kallo then ta maida idonta kasa tana kallon wayarta dake hannunta. Contact dinta ta shiga ta yi dialing number Adam sai kuma ta yi saurin yanke kiran ta fadi zaune kan kujera kamar mai mamaki.





CAPTAIN JAMAL POV.

“Wasu hotuna zan turo maka yanzu, ina son ka yi aiki mai kyau akansu ka gano min idan editing aka yi, kuma ina son ka bincika a ina aka dauki hoto nan kuma ka gano ne waya watsa hotunan a media”

“Okay Sir”

Ya sauke wayar daga kunnensa ya shiga Whatsapp ya aika masa da hoton sannan ya goge su a wayarsa, ya saka wayar aljihu ya nufi gaban teburinsa ya dafa teburin ya rumtse ido....

Zuuuuuu zuuuuu wayarsa dake aljihunsa ta yi vibration alamar kira, ba tare da ya bude idon ba ya saka hannunsa aljihun ya ciro wayar, bude idonsa ya kalli wayar shi ne abu na biyu da yayi sannan ya kara wayar a kunnesa kansa ya mugun tsarawa har yana jin jiri.

“Salam”

“Captain me ya hada ka da Momy?”

Ita ce tambayar da mahaifiyarsa Hajiya Turai ta fara yi masa a madadin amsa sallamar da be karasa yi ba. Yana jin haka ya san Momy ta yi magana da mahaifiyarsa kenan.

“Ammy ba zan iya miki bayani yanzu?”

“Why? And she told me to wannan yarinyar kake so is that right?”

“YES”

Ya amsa da manyan baki, sannan ya mike tsaye gaba daya ya nufi windows din office din.

“I Love her unconditionally Ammy, ni ma ban sani ba sai yanzu ita ce haske rayuwata! Amman wani yana kokarin shata layi mai hudu a tsakaninmu, and the most painful thing is yarinyar tana shan wahala rayuwa, i just..... ”

Yayi shiru, sai Ammy ta karasa masa.

“You just want to marry her and make her a princess? Haka zaka fada min?”

Ya kalli green grass din dake harabar windows din ya girgiza kai.

“Not a princess but a QUEEN....”

“That's back then ban da yanzu, ko a da can idan ita ce ba zan yi farinciki ba, sai dole, ka tafi ka bawa Momy hakuri kuma ka watsar da lamarin yarinyar nan? Is not your type”

Ya kai hannunsa ya taba saitin zuciyarsa.

“Har yanzu tana nan cikin zuciyata Ammy, wutar son yarinyar nan sai ruruwa take a zuciyata little bit confused little bit angry”

Daga can cikin wayar Ammy Ammy ta yi dariyar da ta fi kama da almara.

“Captain ka fara fita hayyacinka ne? Are you crazy?”

Yayi shiru for some seconds.

“Ammy zai fi idan ba mu maganar nan a yanzu ba”

“Why?”

“I'm felling dizzy...”

Ya rike haif curtains din dake jikin windows yana jingina kansa jikin glass window...

“Where are you?”

Amsar da be samu bata ba kenan ya wayar hannunsa ta fadi kasa, ya rike curtains din da karfi sosai yana runtse ido ya bude be daina gani dizzy ba, Curtains din cirewa suka yi suka fado sai dai Captain ya rigasu isa Kasa...!


Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[12/12/2023, 7:10 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*

3️⃣8️⃣





Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/COM8NE7rDs8HAG0Oqfr9wm


Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲


Da sauri ya rikota tsoro ya cika zuciyarsa na abun da take kokarin aikatawa.

“Hurriya kashe kan ki zaki yi?”

Ta daga masa kai tana kuka.

“Mutuwa ta fi rayuwata a yanzu”

“Rayuwarki tana da amfani mana Hurriya karki kashe kanki”

Yayi saurin kankameta ya saka a kirjinsa.

“Ban Aikata ba Jamal ban aikata Wallahi ban aikata ba, ban aikata ba, ban aikata ba”

Shi ne abun da take ta maimaita sai ya daga kansa sama yana kallon ruwan da aka sako ba tare da hadari ba...

“Captain... Captain”

Ya bude idon a hankali har a lokacin dizzy yake gani kamin fuskar Momy ta fito masa clear, duka hannayensa biyu suna rumgume a kirjinsa dayan mai drip dayan babu.

“Sannu...”

Ya kalli wata yar'uwar mahaifinsa dake tsaye a kansa, a lokacin ne ya gane mafarki yake na rumgume Hurriya da kokarin hanata aikata kisan kan da take son yi. Maida idon yayi ya rufe zuciyarsa na wani irin fisga. Momy ta kai hannu ta taba kansa

“Jikin nasa babu zafi kuma”

“To Doctor ya kamata a kira, sun ce idan ya farka a kira su”

Cewar kanwar Momy Hajiya Ikilima, Momy ta mike tsaye tana rike da wayarta dake ringing.

“Namra ce”

Ta fada sannan ta amsa wayar

“Eh ya farka..”

“Ita ma sai yanzu ta farka”

“To yayi kyau sannu da kokari uwarta, ta farka ba dole sai kin sanar da ni ba”

Captain ya bude idon tun gabanin Momy ta yanke wayar.

“Bari na kira likita”

Momy ta fice da sauri domin kiran Likita, Hajiya Ikilima kuma ta zauna a gurin da Momy ta tashi tana kallon Captain da ya tsayar da gudun ruwan ya cire drip din hannunsa ya sauko da kafafuwansa.

“Ina zuwa? Kai da ka tashi yanzu? Hankalin kowa a tashe yake tun jiya baka farka ba sai yanzu, saboda yana asibitin sojoji ne suka hana kowa shigowa sai ni da Alhaji Usman suka bari sai kuma Hajiya Nafisa”

Be ce mata komai ba ya sauko daga kan gado sai ta mike tsaye ta rikoshi.

“Ina zaka je wai?”

Be samu amsa mata ba, Hajiya Turai ta turo kofar dakin ta shigo tare da Mijinta Engr Aliyu Turaki, Ammy ta jefar da jakarta ta rumgume Captain da sauri tana kuka sosai. Sai a lokacin ya samu kuzarin yin murmushi cikin nauyin baki ya ce

“Ammy I'm fine”

“You're not... Baka taba suma ba tun da na haife ka, kuma ka dauki lokaci baka farka ba, na tsorata da na rasa ka ban san ya zan yi ba”

Cikin kuka take maganar tun a jiya da ya kasa amsa tambayarta take cikin tashin hankali har zuwa yau da ta yi zuwan da bata shirya ba, ta dago tana shafa kansa ta taba jikinsa.

“Me yake damunka? Me kake ji?”

Yayi baya baya ya zauna yana kallon mahaifinsa da ya kasa cewa komai sai damuwa da tsantsar kulawa ke dawainiya da shi.

“Ya jikinka Jamal?”

“Na ji sauki Daddy, da ba ku zo ba ai Momy ta isa ga Momy Ikilima ma sun wadatar”

“Da ba mu zo ba, hankalinmu ba zai kwanta ba”

Daddy ya fada yana kai hannu ya taba kan Captain cikin tsananin so da kauna. Ammy ta shafa kansa da fuska tana taba ko'ina na jikinsa hawaye na sauko mata.

“Na yi waya da Dr George na saka Mustapha yayi booking appointment tun a yau, ko da ka farka ko baka farka ba zan mu fitar da kai England a duba lafiyarka”

“Ammy wannan duka na minenen? I'm”

Ta girgiza kai tana kuka sosai tana shafashi ji take kamar ta bude cikinta ta saka shi ciki ta rufe, tsoro take kar ta rasa ďa ďaya tilo da Allah ya mallaka mata iyakar zamanta a duniya.

“You're not sauran kadan ni ma na mutu a jiya, da na kira Momy ka ta zo kuma na kira abokan aikinka suka shigo suka fada min ka suma, na fi son na tabbatar da lafiyarka... ”

Yayi murmushi a kokarinsa na karfafawa iyayen nasa guiwa.

“Ba zai wuce stressed ba, kin san yanayin aikin Ammy babu hutu kullum”

“To zaka aje aikin da daga yau...”

Daddy ya fada kai tsaye da fuskar dake nuna ba da wasa yake ba, Captain yayi masa kallon mamaki.

“Is this a joke?”

“No... I have alot of money, ina da arziki ina da dukiya ina da hannayen jari dabam dabam, ina da Campany's ba daya ba, ina kasuwancin jiragen ruwa Alhamdullah... Ina da komai Jamal kai ka zabawa kanka wannan aikin ba dan ka rasa komai ba, kuma ba dan bana bukatarka a cikin kasuwanci na ba, ina da arzikin da har ka mutu ba zaka iya cinyewa ba, har jikokinka sai sun gada, fada min akan wane dalili zaka wahalar da kanka? Idan har wannan tarin duniyar bata hana ka gajiya ba da samun hutu miye amfaninta?”

Wannan karon dariya yayi mai sauti ya kama hannayen mahaifiyarsa da suke fuskarsa ya rike yana kallonta.

“Na musu alkawari ina lafiya, kuma zan kara samun wata lafiyar dan Allah ku kwantar da hankalinku”

Ya rumgume mahaifiyarsa tana kuka har lokacin. Momy Ikilima dake kallonsu gwanin sha'awa ta ce.

“Dole hankalinsu ya tashi, mu ma hankalin mu ya tashi balle kuma su? Kar ka ga laifinsu”

Ya kalleta yana murmushi kamin ya kalli Momy wanda ta dawo dakin tare da Likita.

“Hajiya Turai ashe kun iso?”

Ammy ta dago ta kalleta fa jajayen idanuwanta tana share hawaye.

“Eh mun iso Sannu da Kokari Hajiya Nafisa”

“Haba dai? Sai ka ce wata bare?”

Cewar Momy sannan ta nufi gefen gadon tana yi ma Captain ya jiki. Likitan ya duba shi da kyau sannan yayi masa sannu.

“Rashin hutu ne kawai yake damunsa, akwai bukatar ya samu ya huta kuma ya bi dokokin maganin da zamu dora shi akai da kuma shawarwari”

“In Shaa Allahu zai bi mun gode Likita”

“Allah ya bada lafiya”

Cewar Likitan sannan ya nufi kofa, Captain ya kira sunansa.

“Dr Rafiq ko zaka taimaka ka ba ni sallama yau? Idan ba haka ba iyayen nawa ba za su yarda stressed ne ba kawai, kuma ba za su bar ni na huta ba”

Likitan da aka kira da Dr Rafiq ya dawo ya dauki takardun Captain yayi rubutu akai yana murmushi.

“Zai iya bari asibitin a duk lokacin da ya so”

Sai ya fice daga dakin sannan Ammy ta girgiza kai.

“Ni ban yarda da wannan asibitin ba, ba ayi wani gwaji ba'a duba komai ba kawai ya ce ya sallameka kuma wai stressed ne, zaka je England a can za a duba lafiyarka da kyau za su gano ko minene”

“Saboda stressed din ne Ammy ko a can ne haka za su fada, ni kaina na san bana samun hutu, kuma wannan asibitin da kike gani asibiti ce mai kyau da akw kula da marar lafiya kamar a waje, asibitin Barrack ce fa, Barrack din ma babba”

“Idan haka ne me yasa ya sallame ka a yanzu? Ko da stressed din ne ai ya kamata ya rike a nan ka huta ko na kwana uku, ko dai suna son su kashe ka ne?”

“Da na musu me?”

Ya tambaya yana murmushi Momy Ikilima da Momy kuma suka yi dariya, daman sun san Ammy duk wani abun da ya shafi danta bata daukarsa da sauki bata saka wasa a ciki.

“A gida zan fi samun hutu, yanzu zan tafi na rubuta musu takardar na hada da shaidar takardun da za su tabbatar da ba ni da lafiya, na saka hannu na aje musu, Idan suka yi bincike suka tabbatar da gaskiya za su daga min kafa na kwana uku ko sati ko kuma wata, wata kila ma har shekara ya danganta da abun da likitan ya fada musu da kuma yanayin ciwon nawa da yadda suka gamsu”

“Dole sai na yi haka? Kuma dole kai zaka yi?”

“Aikin Soja ba kamar sauran aiki bane Ammy, dole na bi dokoki da ka'idodin manya kamar yadda na kasa da ni ma za su bi ni, zan iya tafi na yi yanzu?”

Permission kawai ya roka daga gurin Ammy sai ta kara masa da tukuici.

“I will escort you”

Duk yadda ya so ta zauna yaje yayi abun da ya kamata da akansa be samu haka ba, sai da Ammy ta raka danta da kanta har gurin da ya kamata shi kadai ya shiga sai da ya karya dokar ya shiga tare da ita. After ya dawo abokan aikinsa suka yi ta shigowa suna masa ya jiki, ciki har da manyansu and da yawansu sun san Engr AA Turaki wato mahaifinsa ba dan yana aikin sojan ba sai dan connection da kuma kudi mai sa asan mutum dan dole. Wasu kuma suka shigowa ne saboda Captain jindadin aikin da suke da shi da kuma kokarinsa. Momy bata bari sun fita a office din ba sai da Captain ya wanke bakinsa ya yi breakfast sannan suka fito wasu sojojin na take masa baya har gurin da aka faka manyan motocin gidansu, Daya ta Momy, daya wanda Ammy da Engr suka shigo sai kuma dayar da bodyguards din mahaifinsa suke ciki, dayar kuma ta Momy Ikilima ce. Captain ya kalli Mahaifiyarsa ba tare da fargabar komai ya ce.

“Kamin mu wuce Ammy ina son muje mu duba Hurriya asibiti....”

Ammy zata yi magana Engr yayi saurin girgiza mata kai alamar kar ta hana, sai kuma ya tari numfashin mahaifiyarsa ya amsa masa.

“Okay zamu fara zuwa mu dubata tukuna sai mu tafi gida ko Family House?”

“Family House”

“Okay My Son”

Direban ya bude masa mota ya shiga baya, tare da iyayensa Ammy da Engr, wani Knight ya shiga Front seat, Hajiya Nafisa wato Momy da Momy Ikilima ma a dole suka bi Captain da iyayensa dake kokarin cika masa kudirinsa. A harabar Federal Medical Center wato FMC suka faka, security dake gaban motar Engr ya bude motar da sauri Captain ya fito tare da iyayensa, Bodyguards na take musu baya. Ko kadan Momy bata so zuwa duba Hurriya a asibiti ba, ba dan Captain ya so haka ba kuma iyayensa suka biye masa ba zata taba zuwa dubata ba, domin ta fi jin tsanar Hurriya a yanzu fiye da koyaushe, sanadinta suka fara samun da Captain gashi kuma yanzu ta ja musu abun kunya, sai dai babu yadda ta iya saboda ďan ďan'uwanta ya so haka. A dokar asibitin lokacin da suka zo ba lokacin ganin marar lafiya ba ne, amman ba a hana su shiga ba domin ko na goye ya san kura.

“Ina ne?”

Captain ya tambayi Momy ba dan ita ma ta sani ba, sai da ta sauke ajiyar zuciya ta kalli yayanta sannan ta daga wayarta ta kira Namra.

“Gamu mun shigo asibitin, wane daki ne?”

Ta fada musu har da number dakin, a nan suka juya zuwa wani ward din da ba wannan ba, ko'ina suka wulga sai ya kallesu kana
Showing 132001 words to 135000 words out of 215510 words