bari saboda Captain yayi aure ya zauna a gida daban, shi kadai Allah ya ba ni ba zan bari wata ta kwace min shi ba”

Daddy yayi murmushi ya dauke kai ya fice daga dakin, shi dai duk a tunaninsa Hajiya Turai take tana yi ne saboda ranta a bace, idan aka bata kwana biyu zata sauko ta.

“Wallahi ba zan taba bari ayi zaman auren nan ba, ba zan bar garin nan ba sai da yarinyar nan”

Bayan Daddy ya fice Ammy take fadar haka, Momy ta mata kallon rashin fahimta.

“To ai idan kika yi haka kin nuna kina sonta kenan, ai kamata yayi ki banza ajiyarta ki share yar banza ta fahimci familyn nan ba gidan aurenta ba ne”

“Shiyasa zan yi haka ai, idan na barta a nan cikin satin nan zata iya tarewa, idan kuma ta haihu da ďana ai zance ya kare, ina nan garin idan kuma ta tare sai dai ta tare a gidana”

“Wannan ba mafita ba ne lokacin da zai saci kafa ya tafi mai nawa ko gani be yi ba, ki dai canja shawara”

Ammy ta juyo ta kalli Momy kamar zata fasa kuka. Momy ta yi shiru domin ita ma bata san abin yi ba a yanzu kanta a rufe yake.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un wannan abu da me yayi kama? Wane irin rayuwa ne wannan? Ni na rasa ma me ye abun yi, babu abun da yafi min bakinciki kamar neman auren yarinyar nan da aka yo a cikin falona kuma aka yo sadakinta da sinari”

“Zinarin ma mai tsada, yarinyar ko gani bata yi. Amman ni na san abun yi ni na sani, ta yaro ai kyau take bata karko”

Ammy na maganar zuciyarta na kuna, kamin ta mike tsaye ta nufi bangaren da mijinta yake sauka idan ya zo gidan.
Daddy yana fitowa daga dakin ya hau sama ya shiga dakin Captain kicibus suka yi da Daddy shi zai fito Daddy kuma zai shiga dakin.

“Daddy”

Captain ya fada yana sauke idonsa saka haka nan dai yake jin kunyar Daddy a yau.

“Kai ba mace ba miye na rufe kai a daki? Ko Ammy kake yi ma boyo?”

Captain yayi murmushi yana sosa bayan kansa. Daddy ya ce.

“Mahaifin yaron nan ne Adam ya zo tare da Iyalinsa, ya fara koro min bayana na takatarda shi saboda ina ganin kai da mahaifin yarinyar ne kuka dace da yin shawara ko yanke hukunci”

A take bacin rai ya mamaye zuciyar Captain da tsananin fushi ya ce.

“Me suka zo yi Daddy?”

“Kamata yayi ka sauko mu ji, bana son bata lokaci 5pm zan wuce Kaduna”

Daddy ya karasa yana duba agogo hannunsa, a tare da Captain suka sauko, a tunaninsa iyayen Adam din za su sake bukatar ya basu dansu ne ko kuma wani abun da ya shafi karar da ya shiga a DSS. Captain be ji zai iya gaisawa da ko daya a cikin family ba domin dan su ya janyo musu kallon marasa mutunci yake musu. Salim be kalli gurin da Captain yake zaune ba domin kowa baya marmarin ganin abokinsa a yanzu.
Sai da Daddy ya kalli Captain da fuskarsa take a gintse sannan ya ce.

“Ina tunanin kun san Captain, ko da iyalanka ba su sani ba kai dai ka san da cewar Jamal ďana ne, Salim zai iya fadar hakan, dalilin da ya saka na dakatar da kai daga bayani saboda na kira shi ne, domin shi da mahaifinta suke masu hakkin akanta yanzu, kasancewarsa mijinta an daura Aurenta da Jamal a yau...!”

Da matukar firgici Salim ya kalli Captain da goshinsa ke kyalli kana arba da shi zaka san ango ne latest. Kallo kallo suke da Salim kowa ya kasa dauke idonsa.

“Maa Shaa Allah, abu yayi kyau Allah ya saka maka da alheri a wannan jihadin da ka yi, kuma ya baka wuyan dauka”

Cewar Bashir Sarauta yana jinjina kokarin Captain na toshe kunnuwansa a wannan mawuyancin yanayin da ba kowa zai iya ba. Salim ya dauke idonsa da mugun karfi ya mike tsaye fuuu ya fice daga falon

“Zaka iya cigaba ko kuma ka fara daga farko saboda ya fahimci me ke tafe da ku”

Alhaji Bashir ya kalli Captain cikin yanayin damuwa ya ce

“Daman mun zo nan ne akan maganar abun da ya faru da ne yi ma kowa dadi ba, DSS sun sanar mana su suka dauki Adam sakamakon karar da Captain ya shigar, sun ce sun dauke shi ne saboda bincike yanzu haka dai sun dawo da shi yana asibiti domin sun masa duka sosai daurin da aka yi masa ma likita yace sai an sake daura shi... Dalilin da ya saka muka zo nan shi ne mun bincike Adam akan abun da ya faru daman kuma tun farko an yi masa fada kuma mun tambaye shi taya hotunan suka fita, sai yace mana be sani ba, kuma ya fada mana cewar tabbas yana tare da yarinyar ne...”

A wannan gabar ne Captain ya kasa jurewa ya kalli Daddynsa cikin yanayin bacin rai domin baya bukatar a nanata masa abun da ya riga da haddasace.

“Daddy na dauka magana ce mai muhimmanci za su yi, amman wannan yana maida hannun agogo ne baya”

Daddy ya kalli Captain with serious face domin ko da Alhaji Bashir Sarauta ba abokin kasuwancin Daddy ba ne ta wata fuskar ya kai ya haifi Captain and duk wani abu na nuna rashin mutunci ko rashin girmama na gaba Daddy baya lamuntar dansa Jamal ya aikatawa kowa.

“Respect yourself ka saurare shi ka ji abun da yake tafe da shi”

Captain ya maida hankalinsa gurin Alhaji Bashir Sarauta ba dan ransa yana so ba, dai dan bin umarnin Daddynsa.

“A yanzu maganar da nake da ku, yanzu haka Adam ya fada mana gaskiyar cewar kazafi aka yi ma yarinyar nan!.. ”

Yadda ya fadawa Captain gaskiyar abun da ya faru haka iyayensa suka fada. Daddy ya girgiza kai cike da takaici ya ce.

“Duniya ta lalace, mun zo wani zamani da bayan tarbiyar dole dai muna hadawa da addu'a ga yaranmu, ban da abun zuciya da aikin shaidan miye abun chusa kai da nemana halaka akan me zaka dage sai yarinya ta so ka, bayan hakan be samu ba kuma sai ka ce sai ka nemi lalata rayuwarta? Yanzu ya bata sunansa ya bata nata da bata gidansu ina amfanin haka?”

Alhaji Bashir Sarauta ya ce.

“Babu ai na fada masa da abu ne mai kyau da yanzu celebration muke muna murna amman ga abun da ya janyo mana, ita kanta abokiyar shaidancin tasa gashi ita ma ta janyowa kanta ta samu nata kaso”

Daddy ya girgiza kai.

“Dole ai zata samu haka ko ma fi, ko bare ka aikatawa haka ai ba zaka ga daidai ba balle kuma yar'uwarka ta jini, sun jefa yarinya a damuwa ba tare da hakki ba”

“Shiyasa na zo na baka hakuri kuma na roki yafiyar abubuwan da suka faru, daman aiko sammaci bana nan Iyalina suka yanki ticket suka aiko da sunana, gashi kuma shari'ar ta zame mana biyu, sannan yaron nan gashi babu lafiya, dan Allah ayi hakuri a janye karar nan da Captain ya saka gudun kar mu kara yin abin kunya, domin idan aka ce za'ayi shari'a har wadanda ba su da waya da redio zansu iya jin wannan abun kunyar, wani ma zai iya cewa da kai nake shari'a ranka ya dade ba domin canja labari be da wahala a gurin mutanen mu yanzu...”

Daddy yayi jimmmm na dan lokaci, ya sauke dogon numfashi yana nazari, be kai ga yanke hukunci ba ya kalli Captain dake karanta sakon taya murna da Salim ya aiko masa ya ce.

“Captain yanzu meye abun yi me ye shawara, ko da yake ya kamata ace an ji ta bakin mahaifinta ma?”

Ya dago kai ya kalli mahaifinsa.

“Daddy zan janye shari'a daman kuma yin haka ba abu ne mai wahala ba, zan yi hakan on one condition Adam zai yi video ya fadawa duniya gaskiya kuma ya roki yafiyar Hurriya if not na zan janye shari'ar nan ba kuma Monday nan zamu shiga Kotu, hakan ne kadai zai wanke Hurriya a idon duniya kuma daman na mata wannan alkawarin”

Mahaifiyar Adam din ta dubi Captain ta ce.

“Haba ďana wannan matakin be yi tsauri ba? Zai iya bata hakuri a sirrance kuma ya fada mata gaskiya, amman fitowa yayi video yaje viral sai kara lalata lamarinsa ne”

“Ita da take mace ya lalata mata rayuwa balle kuma namiji? Da be aikata ba wata kila da duk hakan be faru ba”

Yan'uwan Alhaji Bashir ne suka shiga rarrashin Captain ko zai sauko daga wannan hukuncin amman fir yace idan ba haka ba shi ba zai hakura ba. Alhaji Bashir ya dubi Daddy ya ce.

“Ranka ya dade a taimaka a saka baki lamarin nan”

Daddy ya nuna Captain.

“Shi ne mijinta, kuma wannan case din a hannunsa yake, ina tunanin a yanzu ko ubanta be kai shi iko da ita ba, kuma ya saukaka muku a haka din ma, ni ban yi zaton zai yi saurin amincewa ba, yin haka zai wanke matarsa daga zargi da zagin da danku ya ja mata, kuma idan ma ba ku aminta yaron ya bada hakuri ta wannan sigar ba ko kotu aka je Kotu zata saka shi ya bada hakuri kuma ya fadawa duniya abun da ya faru, daga karshe kuma ya fuskanci hukunci”

Mahaifiyar Adam ya fashe da kuka domin a gurinsu yin abun da Captain ya bukata ma cin mutunci ne da kara zubewar kimarsu. Daddy ya mike tsaye ya kalli Captain

“Ina ganin shi kenan nan ai, idan sun zabi haka sai ku aiko mana da video idan kuma kotun kuka zaba duk daya ne, akwai uzurin da zan yi kamin na bar garin yau zan wuce Kaduna”

Captain ya mike tsaye sai suka fice tare da Daddy aka bar Alhaji Bashir Sarauta da matarsa da yan'uwansa da suka rako shi a falon.

“Adam ne ya ja mana wannan wulakanci, ni ban ga dalilin ma da zai sa a nemi janye shari'ar ba a bar shari'ar ba, da abar shi kotu ta koya masa hankali”

Cewar daya daga cikin kanen ubansa. Alhaji Bashir ya ce.

“Ba za'ayi haka ba, shi ma ai sai ya wahala kuma ko kotun muka je ba nasara zamu yi, tun da kudi za su zuba kuma su suke da gaskiya”

Mahaifiyarsa ta kalleshi.

“Yanzu kenan Alhaji dole Adam sai yayi haka? Babu wani abun da zaka iya yi? Shi Captain ba zai duba abotar dake tsakaninsa da Salim ba?”

“Kina kallo Salim din ya tashi ya fice be ma tsaya aka yi magana da sho ba, wata kila sun samu matsala da Captain din akan haka, kuma shi Adam ai ya fada mana cewar Captain ya masa video idan ma ba mu saka ya bada hakurin ba zai iya sakin video kuma ga shari'a a kotu, yara ne idan za su yi abu basa tunani, yadda Alhaji Turaki ya fice ya bar a falon nan ai kin san akwai abun da yake zuciyarsu da jira kawai suke”

Cikin kuka Hajiyar ta mike tsaye ta fice daga falon sannan sauran ma suka mike tsaye.

“Alhaji ka tashi mu tafi, babu amfanin zama ai domin ba saurarenmu za su yi ba”

Alhaji Bashir ya mike tsaye.

“Zan samu mahaifinta na yi magana da shi, zamu samu mafita a can”

Cikin rashin jindadi suka fice daga falon. Dayan falon Daddy ya shigo tare da dansa sai suka samu Ammy zaune tana jiransu, fuskarta a hade kamar ba ita ba.

“Ina tunanin ya kamata kaje ka samu mahaifinta ku yi magana, domin za su iya bi ta can su siye shi da kalamai ya yafe musu, bayan kuma ba su cancanci hakan ba matukar ba su aikata abun da ka umarce su ba”

Kamin su zauna Daddy yake fadar haka, Captain ya rausayar da kai

“Okay Daddy”

“Daga yin aure matsalar har ta tattara ta dawo mana a gida? Mu miye na mu da za su zo mana a nan?”

“Saboda danki ne ya shigar da karar kuma mijinta ne a yanzu, sannan lalama suke bi suna neman yadda za a kashe wutar ne cikin ruwan sanyi”

“Idan wani abu ne da ya shafi Hurriya ko mahaifinta kai ya kamata ka yi magana da shi kai tsaye, ba Captain ba yaron da lafiya ma bata wadace shi ba, tare da shi zamu tafi kaduna a yau....”

Captain ya kalli Ammy da sauri, Daddy kuma yayi murmushi ya ciro wayarsa yana lasawa.

“Kin kawo shawara mai kyau, haka ya kamata yi tafiyarka Jamal zan yi magana da mahaifinta da kaina”

Ya amsa masa da kai sannan ya juya ya fice daga falon.

“Ba zan tafi Kaduna na bar ďana ba, ko dai na fasa tafiyar ko kuma ka fada masa ya shirya mu tafi, kuma a fadawa iyayen Hurriya tun da an daura aure a ba mu amaryarmu zata tare”

“Wannan hurumin iyayenta ne ba na mu ba, ki je ki same su ku daidaita idan sun saka ranar da ta yi miki shi ke nan, amman dai ki sani duk wani abun na zubar da mutunci ba zan bari ya faru ba”

Yana kaiwa nan ya mike tsaye ya shige bedroom ya barta a falon zaune kunshe da bakincikinta.





Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[12/20/2023, 12:49 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*

4️⃣6️⃣





HAJIYA KALTUME POV.

“Wai ni kam ya ma sunan addu'ar nan da ake idan za a bar gida, wanda aka ce idan ka karanta babu abun da zai same ka har ka je ka dawo?”

Hajiya Fatee ta yi shiru alamar nazari tana kokarin tunanin addu'ar amman ta kasa.

“Akwai dai Bismillah a ciki, Bismilah da wani abu a ciki ni ma fa na manta addu'a”

“Kin ga da kin rike ai da mun karanta yanzu, mu tafi cikin kwanciyar hankali”

“Duk abun da za'ayi fa ba zan samu kwanciyar hankali ba, domin ba mu da shi a yanzu, tafiyar nan dai ta zame mana dole ne kawai, domin ni ma ina son na san lafiyar Malam”

“To kin gani, dole a haka zamu daure mu tafi, Allah dai ya kaimu lafiya, amman tashin hankali da nake ciki a yanzu ai ya fi na yan kidnapping”

“Babu wanda ya di wani, fatan dai Allah ya kaimu lafiya”

Cikin tsoro suka shiga motar ta suka dauki shatarta tun daga tasha direban ya zo gidan Hajiya Fatee ya dauke su. Hajiya Fatee ce mai rike carbi tana ja tana leka lake waje, Hajiya Kaltume kuma shiru take sai da suka iss cikin garin sannan hankalinsu ya kwananta Hajiya Fatee ce ta yi ta nuna ma direban hanyar gidan Malam be sauke su ko'ina ba sai a kofar gidan da yayi baki kirin har wani bangare na ginin ya zube. Hajiya Kaltume ta kalli kawarta.

“Anya akwai lafiya a gidan nan kuwa?”

“Ina lafiya kina kallon gida kamar an yi gobara”

“Ni ma abun da ya daure min kai kenan, amman dai bari mu shiga cikin gidan mu ji”

Hajiya Kaltume ta zagoyo ta gefen da Hajiya Fatee take suka jera suka nufi gidan da kusan ma za'a iya cewa ya zama kango.

“Ke yaushe rabonki da nan?”

“Wai ni? Ai tun zuwan da muka yi tare da ke van sake zuwa ba, to me zai kawo ni irin wannan gurin ma sai dole”

“Yanzu wai da gaske kike filaye da gonakin da kika ce mutumen nan ya siya miki duk baki ga ko daya ba?”

“Ai yarda ce ta kawo haka, ni na yarda da ko ban zo na duba ba na san ba zai cuceni ba”

A bakin kofar gidan da aka zagaye da ƙaya suka tsaya suna kallon yadda gaba daya gidan yake kone kuma babu alamar ana rayuwa a cikinsa.

“Hajiya wannan gidan da kike gani gobara aka yi, kuma kina kallon gidan ya zan kango babu kowa a ciki”

“Amman Hajiya Fatee ni da ke a nan muka san matan malam suna rayuwa?”

“Bari mu tambaya, ba mamaki ma ace ya tashi tun da yanzu linkafa ta yi gaba”

Juyowa suka yi suka fito daga zauren gidan suka yar tafiya sannan suka isa gida daman makotansa suka yi sallama. Hajiya Fatee ta shiga ciki Kaltume kuma ta tsaya daga waje tana waige waige kamar wanda bata yarda da garin ba.

“Sannu ina kwananku?”

“Sannu dai muna lafiya”

“Alhamdulillah dan Allah Malam muke tambaya ko ya tashi a nan ne shi da Iyalansa? Mun shiga gidan babu kowa a ciki na ga kamar ma ginin ya fadi”

“Ayyah wai Malam? Malam ai yau kwanansa tara da kwanta dama, Malam ai lokaci yayi”

Hajiya Fatee ta dora hannunta akan tulun kirjinta ido a waje kamar za su yi magana.

“Malam kike nufin ya rasu?”

“Malam ya rasu lokaci yayi, gobara yayi cikin dare wutar ta ci shi ta cinye yaransa biyu kuma bata bar komai da yake gidan ba, amman sauran yaransa da matansa sun fita da rai suna nan lafiya kalau”

Hajiya Fatee ta kai zaune tana dafe da kirji.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un,
Showing 159001 words to 162000 words out of 215510 words