Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻𝐁𝐨𝐨𝐤 𝐓𝐰𝐨

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲

Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660


𝐏𝐚𝐠𝐞 4️⃣

“Gaba daya an juye kan Alhaji Haruna, kuma ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, ba zai wuce Kaltume ba, domin bata hada hanya da imani ba, kai ko gurin da ya bi ya wuce bata bi ba”

Amma ta share hawayenta bayan ta gama sauraren Gwaggo dake fada mata abun da ya faru.

“Ni yanzu ba ta Kaltume nake ba ko Alhaji, ta dana nake burina ma ga ya fito, kuma tun da har ya kai ga furta cewar ba zai bada kudin ba, ni zan bada albashi shi sai ya bada na Ruma”

“Ko daukar yaron nan da aka yi bana raba dayan biyu, Kaltume ce ta saka aka sace shi, yadda na ga ta sha ado ta sauko hankali kwance har tana neman fada min magana ya isa ya tabbatar da cewar da sa hannunta aka sace yaron nan, tasan yarta tana cikin kwanciyar hankali shiyasa hakan be daga mata hankali ba, kuma yanzu na kara tabbatar da ita ce ta aiko Maama gidan nan saboda ta rabaki da dan abun da kike da shi, ni dai da zaki yarda da shawarata da kin saurara karki kira su ki kyale su da yaron ki gani shi za a karbo Ruma ba a karbo Hamad ba?”

Amma ta daga kai ta kalli Hurriya dake zaune a waje tana cin indomie da Gwaggo ta dafa mata kamin ta fita.

“Gwaggo shin idan wani yayi garkuwa da ni yace sai an bashi kudi alhalin kina da hanyar za ki bi ku bada kudin nan zaki bada ko kuma zaki tsaya jiran sai ranar da wani ya bada ne?”

“Zan fada”

“Toh ki saka kani a matsayinki, ni ma fa uwa ce tun daga lokacin da na baro gidan uban yaran nan kullum da kalar tunanin da nake kwana a raina balle kuma yanzu da yarona yake hannun wasu mutane da ba mutanen kirki ba, marasa tsoron Allah, duk abun da nake da shi a duniyar nan be kai ran Hamad ba, Gwaggo ko rayuwata suke ce sai na basu sannan za su sako Hamad Wallahi zan ba su”

Tana maganar hawaye masu zafi na sauko mata, ita kadai take iya jin abun da ko wace uwa take iya ji idan danta ya shiga mugun hannu.

“Kana ina dana? Ka ci abinci baka ci ba? Wane kalar abinci suke baka, ina kake kwanciya? Suna azabtar da kai ko basa yi? Ka yi marmarin gida?”

Amma ta gargiza kai tana kara jin ba zata iya jure har lokacin da Appa zai ga dama ya biya kudin ba. Haka kuwa aka yi, Bappa ma ya bata goyon baya domim ransa ya bace sosai akan abun da Alhaji Haruna yayi masa, Amma da kanta ta kira number da aka bata sai suka tararda line a kashe, sai dai mai neman baya fitar da rai, jajircewa suka yi ta yi suna kiran line kullum ba dare ba rana ba safiya, har suka yi sa'a a rana ta uku kiran ya shiga da misalin karfe goma sha daya na dare. Abun da baka saba ba zuciyar Amma ta hau zillo tsoro ya kamata kamar suna gabanta, duk kokarin da Bappa yayi na ba su Hamad su yi magana da shi sai mutanen suka ki, Bappa ya tambaye ina za a kai musu kudin suka fadi gurin da za akai musu kudin a aje, wani kasurgumim daji ne dake tsakanin mafara da Gusau.

Bayan sun gama wayar Bappa ya ce.

“Allah yasa dai yaron nan yana raye, na ga duk kokarin da muka yi sun ki yarda su ba mu shi mu yi magana”

Amma ta girgiza kai.

“Yana nan raye Bappa, yana raye In Shaa Allah”

“Yanzu waye zai shiga wannan guri ya kai kudi mai yawa haka? Ai shi ma sai su rike shi kamar yadda suka yi ma kanen Hajiya Kaltume, ni dai da zaki hakura mu ga abun da hukuma za su yi, ko kuma idan za a je kai musu kudin aje tare da police”

Bappa ya kalli Gwaggo dake maganar ya ce.

“Baki ji sun sake jaddada mana kar mu kuskura saka police a ciki ba, kai kuma kuma zan iya zuwa na kai, indai za su sako yaron nan hankalin kowa ya kwanta zan aikata haka, kawai ku yi ta mana addu'a”

Cikin yanayin damuwa Gwaggo ta sauke ajiyar zuciya.

“Kowa ke da hannu a cikin lamarin Allah ka wulakanta shi ka tona asirinsa”

“Ameen”

Bappa ya amsa. Gidan da Appa ya bata a lokacin da zai sake ta aka fara sakawa a kasuwa, domin filayen da ta mallaka guda biyu a gidan Appa ta san idan ta saka su a kasuwa ba lallai ne ayi saurin siya kamar gidan da yake gyararre ba, duk da haka kuma sai da aka siyar da shi a nakashe, gidan da zai yi miliyan 45-50 aka siyar da shi a miliyan 35 ta hada da kudin da Appa ya bata da dan abun da take da shi ciki har da sarkar gold din da Appa ya siyawa Hurriya duk ta siyar ta hada kudin ta bawa Bappa, ranar da za aje kai kudin babu yadda Gwaggo bata so a saka police a cikin lamarin ma amman Amma ta ki yarda ganin take idan aka yi haka an bata lokaci kuma za su iya kashe mata da kamar yadda suka yi ikirari, Gwaggo kuma na ta ganin rautar Bappa da Amma taya za a dauki kudi mai yawa haka a shiga daji a kaiwa barayi ba tare da sanin sami'an tsaro ba, abu dai kamar a shirin film.

Cikin karfin hali da yarda da kaddara Bappa ya shiga dajin tare da wani dan'uwansa, bayan yayi addu'o'in da be san adadinsu ba, Gwaggo da Amma, Rukayya da duk wani dan'uwa ma suka raka shi da addu'a. Dan'uwa ya tsaya daga waje shi kuma ya shiga ciki ya kai kudin ya aje a gurin da suka bukata. Har ya kai ya fito babu abun da ya same shi, a lokacin da ya fito ya kira gida ya fada musu ya fito sai kowa yayi ta hamdala ana jin sanyi. Kamin hankali ya karkata gurin ganin kiransu ko sakon inda za su ce a je a dauki Hamad amman shiru. Daga bisani suka bi sawun kiran da number da suka kira da ita last time, domin kullum canja number suke idan za su kira. Haka aka kwashe two days babu kira daga garesu kuma babu wani sako kuma idan aka kira wayar bata shiga, hankali Amma sai ya kara tashi, ta kai bata iya cin komai rashin lafiya ta taso mata har sai da aka kwantar da ita asibiti kowa yayi zaton haihuwa ce duba da tsohon cikin da take da shi, sai dai likitocin sun tabbatar musu ba haihuwa ba ce hawan jini ne, har suka so riketa saboda jinin nata ya hau sosai kuma bata iya cin komai sai dai ruwan da suke saka mata suna taimaka mata ta bangaren kuzari. Sai dai yadda ta nuna bata son zaman asibitin da kuma rokon da aka yi ta musu sannan suka yarda suka sallame ta bayan sun fada musu cewar a rika kokarin kwantar nata da hankali if not idan ta zo haihu zata iya samun matsala ta kasa haihuwar da kanta ko ma arasa danta ko ita ko a rasa duka. All zaman da ta yi asibitin Appa be zo ya dubata ba, even for once be daga waya ya kira ya ji jikinta ba, Hajiya Binta kan kwana ne kawai bata taba yi aabitin ba amman kullum can take wuni, babu yadda bata yi ba Appa ya zo ya duba tsohuwar matarsa, na dan Hurriya da Hamad kadai ba har dan cikinsa da take dauke da shi, amman ya kasa zuwa bayan be saba mata musu ko jayyaya mai tsauri haka ba. Yaran Kaltume ma babu mai mata fatan tashin sai na mutuwa, Yasir ne kadai yayi ta zirga zirga a asibitin gurin dubata ta kuma biyan duk wani bills na magani ko na gado, Namra ma taje duba sau daya tare da wata Neighbor dinsu kawar Hurriya da suke good time da ita, shi ma a sace domin idan Momy ta sani sai ta karya kafafuwanta. Hankalin Hurriya ya tashi sosai ta fara nata zazzabin a tsaye, tunanin sai ya hade mata biyu tana ganin kamar zata rasa mahaifiyarta ta kuma rasa dan'uwanta ne a lokaci daya.
Washe garin ranar da aka sallamo Amma asibiti bayan ta shafe kwana biyar a asibitin, Yasir ya zo gidan sake dubata yake musu albishir da cewar Appa zai bada kudin a yau, sun ce a yau din nan za su fadi gurin da za aje a dauko Hamad da Ruma.

“Kai.. Allah ka sasauta mana mutanen nan ba su da imani ko kadan, yanzu bayan kudin da suka karba gurinmu kuma za su za su karba?”

Cewar Gwaggo tana ta juya zancen.

"Wallahi kuwa, ni da kun yi shawara da ni ba za ku bada wannan kudin ba, komai dai ta kama daman na san dole Appa zai biya kudin”

Rukayya ta kalli Yasir tana masa alamar yayi shiru ta ido.

“Kasan jiya muka dawo daga asibitin nan kuma ta nanata zancen nan sai ku saka ranta ya bace”

Amma ta kalleta tana murmushi.

“Rukayya kenan, rai ba zai bace ba dan na bada kudin, ni dai burina su dawo min da ďana”

“In Shaa Allah, zai dawo inda ba sun yaudare mu ba to zai dawo yau din nan tare da Ruma”

Hindu ta kalli Yasir dake maganar ta yi masa tambaya.

“Waye zai je ya kai kudin?”

“Rilwanu me zai kai, yace zai iya zuwa domin gurin da suka fada hanyar garinsu ce yana yawan bi ta gurin?”

“Waye haka dan'uwanku ne?”

“Eh da yake ga Hajiya ta bangaren kanenta”

“Allah sarki Allah yasa su cika alkawari”

“Ameen”

Daga haka babu wanda ya sake wata magana a falon, har Yasir ya mike tsaye ya yi musu sallama ya fice. Hindu ta kalli Rukayya ta ce.

“Je ki raka shi mana”

“Anty Hindu ban saba yi masa rakiya ba”

“Toh ki fara daga yau, je ki raka shi mana, daga can ba sai ki jiyo mana wani labarin ba”

Tashi ta yi ta bi bayansa ba dan ranta ya so ba sai dan ba zata iya musawa kawar Yayarta ba. Ko da ta fita yana tsaye bakin kofar tsakar gidan tsaye yama jiranta kamar ya san zata fito. Suna hada ido sai yayi murmushi ya juya ya cigaba ta tafiyarsa ita kuma ta bi bayansa har gurin mota, ta tsaya yana juyawa kunya duk ta rufeta.

“Ke lafiya kike?”

“Lafiya kalau sai anjima”

Ta juya da sauri ta bar shi tsaye ya bita da kallon mamaki, before murmushi ya baibaye fuskarsa. Misalin karfe hudu na yamma Yasir ya kira wayar Amma yayi mata bushara da cewar an kai kudin kuma sun fadi gurin da za a je a dauko su Hamad da Ruma yanzu haka suka hanyar daukosu tare da Kanen Appan Alhaji Sa'idu sai kuma Kawu Garba wani dan'uwan Hajiya Kaltume da kuma Yasir din duk a mota daya.

“Alhamdulillah”

Amma ta bada tana sauke wayar, jikinta ya hau tsuma ma dadi farin ciki ya ziyarci zuciyarta ya mamaye ilahirim jikinta, dan zazzabin da take ji sama sama da rashin kuzari duk sai ta neme shi ta rasa. Hurriya ta mike tsaye da sauri tana murna.

“Amma zan hau Napep na tafi gidan yanzu ina son Hamad ya dawo ina nan”

“Ai ni ma ba zan iya jira a nan ba, kira Gwaggo na fada mata”

Hurriya ta fita dakin da sauri ta kira Gwaggo, a nan murna ta kaure Gwaggo sai Hamdala take, ta waya Gwaggo ta fadawa Bappa halin da ake ciki, sannan ta dauki permission din fita tare da Iyami, sanin yadda ďa da uwa suke ya saka Bappa ya amince su tafi ba dan wannan babban dalili ba ba zai taba yarda dayansu ya sake takawa gidan ba, domin be manta cin mutunci da kuma wulakancin da Appa yayi masa ba. Gwaggo da kanta ta fita makota ta samo direban da zai tukasu a motar Amma domin bata iya tuka mota yanzu ita kuma ba iyawa ta yi ba, haka ma Rukayya balle kuma Hurriya da bata gama girma ba ma. Gwaggo da Amma suka shiga baya, Hurriya ta shiga gaba aka bar Rukayya tsaron gida, ba su isa gidan ba sai da suka biya suka dauko Hindu domin dazun kamin ta bar gidan ta fadawa Amma idan aka dauko Hamad a fada mata.

“Alhamdulillah Allah ya kawo mana su lafiya”

Shi ne abun da Gwaggo da Hindu ke Fada, direban da ya dauko su kuma yana kara basu labarin yadda aka sace wani shi ma suka karbi kudi mai yawa.

“Kasar ce ta lalace Allah ka kawo mana sauki”

Amma ta amsa addu'ar da Hindu ta yi da Ameen daman bata cewa komai sai murmushi take tana ta daukin arba da ďanta. Sai da ta isa gidan sai kuma ta soma tambayar kanta me yasa ta zo? Wani bakinciki ya rufeta ta kasa shiga bangarenta da babu komai ta tsaya, kuma ta ki yarda ta shiga bangaren Hajiya Kaltume daga ita har Gwaggo a babbar harabar gidan da direba ya faka motarsa a nan suka tsaya suna jiran isowar su Hamad.



**** **** ****

“Iyami kuma?”

Namra ta daga kai.

“Me ta zo yi?”

“Tarbon su Hamad mana Momy, kin manta yau za su dawo? Ya Yasir ma sun tafi gurin dauko su”

“Au haka ne fa, kin san badan da babu ruwanka dadin kallo gareshi, ni na manta ma”

“Toh ina take”

“Tana can babbar haraba tsaye ita da wadanda suka zo har da Gwaggo da Hurriya”

Momy ta dan yi jimm kamin ta girgiza kai.

“Wallahi har ta bani tausayi, ta yi going though alot shekarar nan, ga ciki ga saki ga sace ďa, da dai Appanku zai tausaya mata ya dawo da ita, ta rike yayanta ni na huta ma, daman bana son rikon yayan wasu, dan na san yanzu Alhaji zai ce su dawo gidan nan da zarar sun dawo kuwa ba su da gurin zama sai bangarenna.”

“Ni tausayi suke ba ni”

“To sarkin tausayi je ki ce su shigo cikin falon nan mana su zauna”

Namra ta wara ido with surprise.

“Su shigo Momy? Ko bakar mana kike min?”

“Toh ya za'ayi, ai da anyi haihu kuma zance ya kare, ba dan tana da yaya a gidan ba ai ba zata zo ba, da zarar an haihu ai kuma shi ke nan sai hakuri, kuma dai an girma kishi na miye ina zan tsaya kishi da karamar yarinya kamar Iyami? Level dina kuma ba zai taba haduwa da nata ba, har abada dukansu na fi karfinsu sai dai ta kara da Kaltume bakar akuya”

Namra ta tashi da kuzarinta ta fice daga dakin ta sauri ta sauko downstairs ta bude kofar falon ta fita. Sai da ta fara gaishe su bayan ta isa gurin da suke a lokacin Amma har ta kai zaune a cikin mota domin bata yarda ta zauna ko da a kujerun baki da ake ajewa a gidan ba.

“Amma Momy ta ci ku shigo ciki ku zauna kamin su iso”

Amma ta kalli Namra tana murmushi.

“Ki ce mun gode zamu tsaya a nan”

“Ai tun da ita tace mu shiga, mu shiga kawai zai fi mana tsayuwa a nan”

Hindu na rufe baki, masu gadi suka bude gate motar da aka je dauko su Hamad da ita ta kunno kai cikin gidan, gaba daya sai hankali ya koma can Hajiya Kaltume, Salma, Maama Khairi suka fito daga bangaren Hajiya Kaltume da gudunsu har Hajiyar da jiki ya hana ta walawa yadda take so, Namra ta shiga bangarensu da gudu kiran Momy. Appa ma ya fito da waya a kunne sai dai fuskarsa babu annuri ko kadan, ba irin da wanda ransa ya bace ba, rashin annuri ne irin na wanda ya rasa wani abu fuskarsa ma gaba daya launinta ya canja. Amma ta fito daga cikin motar ta nufi motar da Yasir ya sauko yana hawaye Ruma kuma na rutsar kuka.

“Ina Hamad? Ina Hamad?”

Amma ta tambaya domin yaronta ne kadai bata ga ya fito daga cikin motar ba. Aka rasa mai ce mata komai har ta isa gurin ta tsaya tana kallonsu murmushin dake fuskarta na kokarin gushewa.

“Yasir ina Hamad? Dan Allah ku amsa min...!”

“Amma sun kashe shi, sun kashe Hamad...!!!!!!”

Ruma ta fada da karfi tana kuka. Momy ta dora hannu saman kai tana fadin Innalillahi. Amma kuma ta yi baya baya kamar mai tafiyar baya sai Hindu ta rike ta, runtse ido ta yi ta kai hannunta ta dafa cikinta dake
Showing 9001 words to 12000 words out of 215510 words